Showing 42001 words to 45000 words out of 155717 words

Chapter 15 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

637

idon tare da fashewa da kuka me cin rai
Humairah tace'' Nasrim meye haka?
Nasrim cikin kuka tace'' Humairah ku d'agani na gaji da kwanciyar bayana ciwo duk jikina ciwo yake min".
ahankali suka d'agata tareda jinginar da ita cikin murya ta dayake fitowa d'aker tace" dan Allah kudu ba min meye a k'asana Zahra tayi saurin yaye blanket din da take rufe dashi da sauri ta sake tana fashewa da kuka Izza ma da Humairah da sauri ka bude ganin jini meyawa
" inna'lilashi wah inna'ilai'hi rajuun" suka fada a tare Humairah ta fashe da kuka Izza " tace " me ya Agrif yayi haka Nasrim kinga yanda jini ya bata ki da bed shit din kuwa".
Nasrim cikin dauriya da dashewar murya tace" Izza ku temakamin banyi sallah ba kuma fitsari nake ji".
ahankali izza da Zahra suka sa hannun su cikin kafadun ta biyu suna d'a gata tasa wani irin ihu ta zube suma kukan suka saka sake yun k'ura tayi cikin dauriya amma sai ta kasa takoma da gudu humairah ta fita
a inda tabar iyayen anan ta samesu cikin kuka tace'' Mama Nasrim ce Nasrim ce sai nuna kofar waje take atare suka mek'e dukkan su suna tambayar meyafaru ina take'?
" Mama bata da lafiya ko iya tashi batayi".
agigice Kamal yace " tana ina".?
"Part din su".
da sauri sukayi hanyar fita Mama Abu Hajja Aiban da Abbaty Kamal ne akan gaba
Mommy da daddy kawai aka bari suma de sun zauna ne saboda kara
girgiza kai Kamal yayi yafita a bedroom din yana cewa "Humairah ku kintsa ta ku daukota mota muje asbitin".
Hajja fada sosai takeyi dan da ita aka gasa Nasrim sai de Abu ya hana akaita hospital sai da mommy tazo tagani tace "ai justice dole sai ankai ta asbitin dan za amata dinki".
Kamal ne ya dauke ta suka tafi asbitin mommy da kanta tashiga theaterroom ta mata dinki mekyu ta tausayawa y'arta ta dan ba k'aramin ai ka ai ka aka mata ba afili ta shafi fuskan Nasrim da take bacci tace'' lalle namiji wazaiga Agrif yace shi zayyi wannan aika-akan'.
Wanda badan ta samu kulawa ba zai iya janyo mata matsalan yoyon fitsari
***************
kwana biyu aka sallameta suka dawo gida
Abu yace "Hajja dade kin bari ko a part din Aishan ta zauna kafin mijin nata yazo bai kamata a kaita batare da mijin yazo ba".
Hajja ta b'ata rai tace''
"Abdulrahaman kafa ficemin a ido kaine me ja da umarni na yanzu bawani bangaren Aishan da Nasrim zata zauna a tar katata can inda ta kai kanta aka mata yugu_yugu ko tajira an kai tane ba da kafan taje ba hakan ko akayi adole aka kai Nasrim part din ta aranan sai mommy tana warning din ta da takula da shan magun gunanta akan lokaci
Agrif kuma har yanzu wayan sa baya shiga ba a kuma samu labarin inda yake ba har yanzu
Humairah da Izza ne suka rakota
suna shiga Izza tace " ummmm dan Allah Hummee wannan parlourn k'amshin wa yakeyi".?
Humairah tace'' ai ni tun ranan da mukazo muka sami nasy akwance naji turaren Nasara amma ganin yanda nasy take yasa banyi magana ba ya Agrif ya canza turare baki ji ita kanta har yanzu tana k'amshin sa ba nina rasa wane irin turare yake amfani dashi".
ta k'arashe maganan tana d'aga hanci alaman tana son shak'an k'amshin
Nasrim tabe baki tayi tana zubewa a kujera

*bayan sati biyu*
amare suna murmurewa suyi kyau amma banda Nasrim ta rasa awane matsayi zata ajiye kanta tun tana fushi da Agrif bata neman sa kamar yanda bai ne meta ba amma yanzu ta dawo neman sa babban abin da yake bata mamaki bata samun sa awaya ashe bai jeda wayoyin sa ba jiya taji mommy tana fada wai laptop din sa da wayoyin sa suna bedroom dinsa na part dinta
suna tattaunawa akan Agrif ba aiki yaje ba
tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafadun ta juyowa tayi taga Humairah ce murmushi tayi mata tareda kama hannu ta
mek'ewa tayi
Saida suka fita a parlourn Hajja din Humairah tace'' haba nasy duk kinsa my heart ya tada hankalin sa ko bacci bayayi yanzu ma cewa yayi na kiraki".
Ita de batayi magana ba binta kawai take a baya har zuwa part dinsu
a main parlour suka samu Kamal a zaune akan kujera one'siter kafan sa daya kan daya yana girgiza na saman dama zaman sa kenan Kamal kaman wani sarki haka yake ko yaushe
cikin sanyin murya tace " Yaya Kamal barka da hutawa".
tace tare da zama a kujeran two seater wanda yake facing din sa
kallon ta yayi na tsayon second 8
ya sauk'e numfashi tareda ajiye wayan hannun sa a hannu kujera yajuya ya kalli Humairah yace"
My one ki dan bamu waje ko zamuyi tsirri".
Humairah tace'' to abin hakane y'ar wariya ce".?

dariya yayi cikin son matar sa k'anwar sa yace "haba my wife dear ai kinsan ba abin da nake boye miki kawai dai naga ku ya kamata ku shawo kanta amma kun kasa shi yasa ni zan gwada amma ai kece k'arshe sirri my sweet love".
ya k'arashe maganan yana kashe mata ido daya cikin so mezafi Nasrim sun kuyar da kanta tayi hawaye yana shirin zubo mata gashi de Kamal da Humairah ba suyi wani dogon soyayya ba asali ma hadasu akayi amma gashi suna zaune cikin zazzafan soyayyar juna ita kuma Agrif yanuna mata so me zafi tun kafin suyi aure amma yanzu yasamu abin da yake so ya gudu ya barta tana cikin wannan tunanin taji tafin hannun sa cikin nata d'ago da kanta tayi tana kallon sa a tsugunne yake a kusa da ita yazuba mata manyan idon sa yana girgiza mata kai alaman kar ta bari hawayen ta yazubo amma ina yayi yawan da bazata iya maidashi ba sirtowa sukayi hannu biyu yasa ya shafe su cikin sannin murya yace" Kai cona mi Kamal y'ar uwata kwaya daya tak a duniya amma na barta take hawaye kuma a gabana kuma bani da matakin d'auka ban taba zatawa Agrif haka ba da bazan bari ya auri only one sisters dina ba amma nasan halin Agrif bazai tabayin hakan batare da wani hujjja ko dalili ba shiyasa nake neman alfarman ki gaya min akwai wani abu da ya faru tsakanin ku ne".?

girgiza kai tayi ta kasa magana
Humairah tace'' haba my dear wane lefi cikekkiyar amarya Wanda ta kawo cikekken budurci zatayiwa ango ai irin su nasy ko me sukayiwa ango dai_dai ne irin su ake Kira da amarya ba kya lefi".
d'agowa yayi yana kallon ta cikin murmushi yace " bana ce kibar nan ba".
natsaya ne because batun ya shafeni kasan nida my best sister bama moyewa juna komai".?

cikin kuka Nasrim tace "Yaya nima bani da wani wanda yafika Kai ne Dan uwa na wanda muke ciki daya dan Allah kasamo min inda mijina yake ina tsananin son ganin sa naji dalilin tafiyar sa nasan ya Agrif bazai tafi yabarni haka nen ba......
da k'er Kamal da Humairah suka samu nasaran lalashin ta har tayi shiru

****************
bayan wata 1
Nasrim kance take a bedroom din Agrif wanda ta maida shi nata yanzu juyi tayi ta tunanin tun fa last week ya kamata taga period dinta amma taji shiru gashi d'an d'anon bakin ta taji ya sauya ba abinda take so kamar kunun gyada alalan wanke
Knocking taji anayi
"Waye ."? tace
"Nice ranki shi dade."

taji muryar Barira me aikin Hajja
"shigo".
dan rissinawa tayi tace'' ranki shi dade ke ake Kira Breakfast."
shafa goshin ta tayi tare da mai da gashin ta da yarufe mata rabin fuskan ta tadan yamutsa fuska tace'' kai Aunty Barira bar breakfast din nan dan Allah idan ba damuwa ina son idan kika gama sallaman kowa ki dan had'amin min kunun madara".
"ba damuwa ranki shi dade yanzu zan hada miki na gama komai sai de hajiya babba tace lalle lalle kizo wajen break din sai na kai miki can ko"?.
tsaki tayi tace'' Hajja matsala".

Hajja tana kallon Nasrim tace'' wai ke meke damun ki kike wani tottoshe mana hanci".?
daya hannun tasake sawa akan haccin nata cikin in ina tace''
" Hajja warin tafarnuwa sai turaren daddy d.....
ai kafin ta k'arasa sai ga aman yayi yink'urin kwace mata da sauri ta mek'e ta k'arasa kan fanfon wanke hannun da yake gefen dirning din tana kwara aman cikin dan tangaran din cikin fanfon
Hajja sai gyada kai take tana kallon ta har tagama suma su ummu sun kuyar da kai kawai su kayi kowa da abin da yake sak'awa a zuciyar sa
Kamal ne ya tashi ya rike kafadun ta yana cewa sorry my best sister ko muje hospital ne".?
"a a Yaya Kamal hutawa kawai nake son yi".
tayi maganan tana Shirin sauk'a a dining room din
Mama tace'' amma baki ci komai ba daughter jiya ma baki zo wajen cin abincin dare ba".
"Mama zan sha kunnun Madara nasa Barira zata min".
Daddy yace "daughter how are you feelings now?
"Al'hamdulillah daddy tace tareda sauk'a dining room din zuwa cikin parlourn cikin kujera 2 sitar tazube tana cigaba da sauke numfashi
Humairah ce taje ta anso mata kunnu a cup tazuba ta bata tana dan kurba kamar dole cikin sanyin murya Humairah tace'' na rasa me ma zance miki Nasrim ina jin kunyar abin da dan uwa na yamiki ni naki dan uwan yana bani dukkan kulawa amma ni nawa ya kasa".
ajiye cup din hannu ta tayi akan Center table cikin murmushin k'arfin hali tace'' dan uwan ki fa kikace ni kin cireni cikin family kenan ko sannan ni ya Agrif bai min komai ba ni yanzu na ganshi da Ido ma nake so ina mugun zargin kaina da wasu abubuwan ni yaka mata naji kunya saboda kar yazamana tsilan auren mune yasa hakan ta faru dashi ban san dalilin tafiyar saba".
kafin Hummee tayi magana har iyayen sun taso suma
Hajja ta k'asara kan tum_tum dinta tadan k'ishin gida sanna tayi kyaran murya hakan yasa mommy daddy Abu da Kamal da kowane yake shirin fita acikin su komawa ya zauna akan kujera dan sun san magana zatayi
sai kowa yanutsu tace''
"Fanna Ina son ki kiramin miskilin d'an naki wanda in ba kiranki ba bazai dauka ba sai yaga dama dan na san a wajen sa kadai zamu samu labarin Agrif yasan inda yake tabbas duk inda Agrif yake da sanin Nasuru".
hannu mommy ta saka acikin jakan
ta zaro wayan ta tare da danna kiran ta mek'awa Hajja
Hajja tace'' a a ba sai kin bani ba saka a handfee".
Nasir da yake a kwance duk abin duniya ya ishe shi tun randa ya *sadu* da Nasrim bai samu sauk'i ba kamar yasa a sato masa ita yayi ta kasan cewa da ita yake ji danta canza masa duniyar sa sosai sai juyi yake akan makeken gadon sa dan a da shi ba mazinaci bane Nasrim ma yayi ne dan yasa Agrif ya tsaneta amma badan wai yana ra ayi ba sai kuma yajefa kansa wata duniyar da bai taba tunanin zai shiga cikin taba mamakin kansa yake da k'ara tsanan Nasrim dalilin ta ya fara aikata zina gashi ya zame masa masifa wai shi Nasir ne har ya wayi gari ya
afkawa yan matan da suke masa aikin tausa da sauran shidimomi wanda ada yake kallon su kamar maza jinsu yake tamkar jinsin sa bai taba ganin su amatsayin mata ba
amma sai gashi dumu dumu yatsici kansa da farko Raddeka y'ar India ya fara afkawa bai ji komai ba sai b'acin rai sai yasake afkawa dayan silinyan y'ar k'asan turkey ce nan made baiji wani sauki ba daga
k'ashe ma koran su yayi gaba daya agidan
gashi shi yana mugun tsananin matan turawa baya harka dasu kawai zuciyar sa tana bashi shawaran ya sato Nasrim ya kulle ta a d'aki me duhu yayi ta amfani da ita idan ya gaji sai yasan yanda zanyi da ita tsaki yayi ganin Wannan shawaran bayyi ba bai isa daukan fansan ran mahaifiyar sa da mahaifin sa da suka rasu adalili ta ba abin da ya shirya tun yana yaro shine dai-dai da fansan sa amma yanzu yazo ya ajiyeta yana amfani da ita ai zai iya fad'awa soyayyar ta abin da baya fata kenan afili yace Nasrim lefin ki yayi mugun k'aruwa aguna bayan na iyayena yanzu kin sani na aikata babban tsab'o wato ZINA Nasrim kifara hukun ta kanki kafin ki fad'a tarko na kifara yankan Naman jikin ki kina cinyewa kafin na juyo kanki
yana cikin wannan sun batun yaji wayan sa yana Ringing kuma ring din mommy ne
cikin dan masifa masifa ya d'aga Yana cewa
" haba mommy kinsan fa mu anan dare ne meyasa idan zaki kira b'akya duba lokaci da muke ciki anan ne".
"Please wait my Son kar ka kashe min waya tambayar ka zamuyi ina Agrif"?.
"Mommy kin san me kike cewa kuwa Agrif kike tambaya nafa waya ban ajiyar sa ummmm".

Hajja tayi saurin cewa"rasa kunya beran tan-tan mommy ta kama baka kyale ba to Agrif muke nema nasan kasan sarai inda yake ai dakai dashi nasan shegu biyu ne wake da shinkafa ya dirkawa yarinya ciki a daren farko mun sha wahalan jinyar b'arnan da yayi mata yugu-gudu har da d'inki ya farka ta ya gudu to ka binciko mana inda yake yanzu ga ciki ya bullo dan h..........
Nasir da har zai kashe wayan amma jin wannan kalaman na Hajja yasa hannu sa yafara mugun rawa cikin in in na yace " ciki ciki ciki Hajja Nasrim tayi daren farko mu amma Hajja dan Allah yatake yanzu tana lafiya ko Hajja dan Allah ki kula min da ita kafin gobe nazo dan Allah duk abin da take so abata amm kawai bawa Mama nasan tafi kula da ita ciki nan Hajja naw".
ji yayi anzare wayan ta bayan sa
Agrif cikin murna yace "Hajja Nasrim tana da ciki ki kace".?
Al'hamdulillah Allah na gode maka da ka nuna min Wannan ranan Hajja taya zan gudu in bar amarya ta da gan-gan akwai dalilin Wanda ita ma tasani amma insha Allah gobe zanzo kuma kuzuba ido cikin second ni k'adan zan goge dukkan lefina awajen Nasrim akula min da ita kafin goben amata albishir da tukuicin na musamman".
ya nagama fadan wannan ya kashe wayan tare da jefashi saman bed yajuyo zai fita
Nasir yace my friend ya kaga DAMA TA na biyu ya cika saura na ukku in sha Allah shima zanyi Nasara kamar yanda nayi nasara samun budurcin ta da samun cikin ta
yanzu saura ta haufanin da me kama dani sak kaga Koda ban fada ba za adasa ayar tambaya ayan Kai da ita kuke bak'ak'e ".

Agrif ya taka har inda Nasir yake ya d'aga kafan sa daya ya d'aura abakin gadon cikin murmushin k'arfin hali yace " hakan zai iya kazan cewa ta haifi d'a namiji kamar yanda ka buk'ata saboda Allah yana bawa masu tsabon sa dama amma kasani sab'on Allah guba ne da zayyi ta yawo ajinin ka musamman na ZINA har jiko kin ka Nasir ina matsayin ka kana yawo da lefi kwarara Zina cin amana to kasani bayan shika bawani lefin da take da girma awajen Allah kamar Zina duk lafin da mutum yakeyi tamkar guguwa take yana yawo amma idan yasamu Zina to rumfa yake kamawa yadin ga jifguwa ta yanda ba k'aramin tuba bane zai rushe she".?

Wani irin Dariya Nasir yayi sai kuma ya daure fukka yacin Izza yace " Eh nasani na sab'awa ubangijina amma kasani zai yafemin dan Wannan shine lefina na farko a duniya kuma ba shirka nayi ba wannan shine zai bani damar nayi yanda nake so da Nasrim da duk Wanda ya rabeta".
Agrif yace baka isaba inde ina raye ganin Nasrim sai yafi karfin ka balle ka cutar da ita in Sha Allah kayi na farko kayi na k'arshe ".?

murmushi Nasir yayi yace "ni Nasara har akwai wani abu da zan soyi ya gagareni dan uwa har yanzu da birbishin son ka a zuciya ta shine yasa nake raga maka amma har yanzu baka makara gaba daya ma ka tsaki Nasrim zamu koma kamar da".

Agrif yace " kai wawane a yanzu ko nace na bar maka Nasrim baka isa ka siyi soyayyar taba s.....
katse sa yayi cikin sauri yace kai kanka kasan bawani soyayya da bazan iya tsiyan sa ba ciki har dana auren mata dubu da zayyiwu ka taba jin wanda yace baya sona a duniya ai tare muka tashi daga kan iyayen mu yan uwa mu abokan mu ma ai'ka tan mu duk wa sukafi so kaga banyi niyar nl bawa mata dama su soni bane".

Agrif yace " haka ne nasheda anfi son ka amma kasani ba so bane tsoro ne duk Wanda kaga yace yana sonka to wllh ba sonka yake ba tsoron ka kawai ake ai kai baka isa ka siyi zuciyar mutane da soyayya ba sai de ka tsiyi tsoro da Izzar ka amma kasani
matan da zasu soka ba irin Nasrim bane mata irin su Nasrim kudin ka mulki ka sarautan ka duk baya d'ad'asu da k'asa kuma na baka dama ka zaga duk duniya ba zaka taba samun irin Nasrim dina ba Nasrim tawace dan ni Allah ya halicce ta".


Nasir yace ''Agrif kudi ba abin da baya tsayawa mutum kai yanzu ba matar ka na nema a daren farkon ka ba meyasa baka dauki mataki ba saboda kasan na maka nisa ne sabo da ni goshin jirgi ne me wuyar karau".
Agrif yacije lefin sa abin yana k'ona basa rai amma ya danne cikin murmushin yace
"ban kyale ka dan Ina jin tsoron kaba Nasir na kyale kane saboda Abu biyu ko ukku
Na farko narufa maka asiri ne saboda idan bawa ya rufa asirin wani bawa Allah zai rufa masa nasa na biyu inason Allah yabani garabasan da yake bawa masu hakuri musamman Wanda aka zalinta wanda yana da k'arfin ramawa amma yazuba ido to zai ga sakayya Kai kanka kasan ka zalinceni amma na cinye ba dan bani da k'arfin ramawa bane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login