Showing 102001 words to 105000 words out of 155717 words

Chapter 35 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

635

nursing din sun kuyar da kai sukayi suka gaidashi cikin ladabi nursing din suka fice suka bar dr da Ahaji a wajen adaidai lokacin wata ƙyakyawar buduwa da bazata wuce shekaru 20 bata shigo cikin taku irin na isassun yan mata wanda gata da kuɗi ya gama ratsasu cikin siririn murya ta tace "dad nafa gaji ko nayi gaba wllh ƙafafuwa na kaman zasu cire nakeji".
Alhajin yajuyo yace "haba Mamana kema wannan dogon takalmin haka ai dole ki gaji bana hanaki saka irin wannan takalmin ba".
"to dad aini a US bana iya tafiya da wani filet sai nadin ga jina ina sauri na saba da wannan".
taƙarashe maganan kamar zata saki kuka
murmushi dad din nata yayi yace ai nan ba US bane".

cikin shakwaɓa tace "dad wayyo ƙafata".
taƙaraahe maganan tana ɗaga doguwar rigan ta har zuwa cinyar ta akan ya tona asirin santala santalan cinyoyin ta farare fat
ta dago ta sake cewa" dad ka gani wllh kunbura yay......

maganan ne ya maƙale mata ganin Nasir kwance akan gado idon sa a lumsha cikin sauri tace dad
"who ts he ?. ta ƙarashe maganan tana matsawa
kusada Nasir din
Dad din nata yace patient ne ma na Mamana".
"Dad balarabe ne?".
doctor Ibrahim ne yace" ranki yadade Hanifa bahaushene sai uban taurin ka wllh ga fadin rai kamar dan wani ni duk ɓaci da shagwaban sa ya ishani gashi wanda suka kawoshi suna gane gaskiya ba shine me lefin ba suka gudu yan sandan ma sun gudu daganan ya kwashe ya fada musu labarin abin da yafaru Nasir
ya daura da cewa

"satin sa biyu anan aka kama wanda yacire idon yasake komawa anguwar da niyar yacirewa wata aka kamashi dayasha budu yace shi yayi wancen ma shine aka dauko
wanda akace yacirewa ido tazo ta sake ganin sa tace ba shi bane aka nuna mata wanda aka kama tace Eh ahine itama yarinyar da akace yayi rapping aka sake kawota tace ba shibane yaran ne kawai suke a gigice alokacin da sukace shine yataka sawon ɓarawo ne kawai".

kuka Hanifa ta fahe dashi sosai tana shafa fuskan Nasir tace "Dad kaga kaga abinda sukayi masa wllh Dad bazan yarda ba sai sai nasaka an kama duk wanda suka masa wannan Dad dan Allah kaga ƙafarsa yana fitar da ruwa Dad kasa akula dashi sosai mutafi dashi us kawai dad ".
ajiyar zuciya Alhaji Mudansir ya sauƙe yace " dr Ibraahim ya akayi akabar ƙafan ta lalace haka".
"sorry sir aikin nashi ne yana bukatar kuɗi sosai kuma yaƙi fada mana family sa".

cikin ɓacin rai alhaji Mudansir yace "Ibrashim danme na bude wannan asbitin badan temakon al'uma bane dole sai ya fadi familyn sa zaka temake shi so nawa zan cemaka ni nine familyn marar gata duk tsadan temako kataɓa jin nace yayimin yawa."
"sorry sir".
Dr yace yana sunkuyar da kai
Hanifa tace "Dad yanzu ba lokacin wannan bane atemaƙe shi".
Dr yace "sir inaga akai shi india zaifi warewa dawuri bawani bata lokaci aka dauki Nasir aka fita dashi yaja fece mask sosai ya rufe fece din yanda baza agane shiba

*******************

*bayan wata shidda*

Alhamdulillah anyi aiki kuma ansamu nasara sosai yana takawa da kafarsa sai ɗan abin da ba arasa ba dan yana ɗan ɗingisawa kaɗan har yanzu

Hanifa haukane kawai batayi akan Nasir wani irin mahaukacin so take masa shiko ko kalman baki bai taba hadasu ba idan tazo ma tana magana jan idon sa yake yarufe ya hade fuska yazama NASARAN sa sak sosai Hanifa take tsoron sa kuma duk wani wukakancin da yake mata baya hana ta kulashi

"Momy ya zan masa nayi duk yanda kikace ko kallona baya yi Momy ko da wasa ban taba kamashi yana kallona ba momy kamar ma yatsane ni wllh Momy bazan iya cigaba da daukan hakan ba Momy ki dafa ƙirjina kiji wllh duk saurin bugawan da yake da sonsa yake bugawa idan yabar Momy nashi ukku".

"please my daughter insha Allah zai soki kamar yanda keki son sa amma kici gaba da respect din sa sosai dan kinga da ganin sa ba baɗan ƙananun mutane bane dagani yana da hadi da jinin sarauta ko wani babban gida kin gane irinsu tsadane dasu sai kin dage sosai
bakiji Daddyn ku yace zoben hannun sa kaɗai zai iya sayan gidan nan da muke cikin ba balle agogon hannun sa wllh ni bazan ma iya lissafin miliyoyin kuɗin agogon nasa ba duk inda yafito dan wani ne a duniya
ni ban yarda ma ba afurike bane ".

cikin shagwaba Hanifa tace "ni Mommy bana mason yazama dan wani nafison ɗan talaka dan ai wannan ƙyan nashi kaɗai ya isa jari momy ƙyansa ya fanshi komai".

girgiza kai Momy tayi tana murmushi tace "kai my daughter Allah yabaki wannan Ahamed din".

"AMEEN Momy na bari na duba ko an gama breakfast na kai masa da kaina".
ta ƙarashe maganan tana yin hanyan kitchen
masu ai'ki har ukku ne suke biye da ita anshirya abinci kala kala kamar ba mutum dayane zai ciba cikin kadabi suka shige da abincin saida HAnifa ta tsaya ta ɗan gyara pert work din jikin ta sannan ta sake kalon fece dinta a jikin glass ɗin ƙofa murmushi yayi tana ɗagawa kanta gira alamam tayi ba ƙarya
tashige ciki tana canza tafiya


masu ai'ki suna fita ita tana shiga ahankali ta zube a gaban sa a ƙasa cikin sanyin murya tace " My bro ina maka fatan farka da zuwa Allah ya yarda zaka taka da ƙafafuwar ka am happy".

bai ko ɗago ya kalle taba sai ma daukan remote da yayi ya ƙara volume tayiwa kan da alƙawarin ayau sai yayi mata magana kamar yanda dad dinta yace yana magana ita de bai taba mata ba ahankali ta meƙe ta zauna a kan kujerar da yake three'sitter matsawa tayi sosai jikin sa duk da gabanta yana faduwa " my diar how are you feelings".
still bai ko kalle taba idon sa akan Tv
ajiyan zuciya ta sauke tace " dan Allah ko magana marar daɗine ka gayamin wllh zanji daɗi nasan kasan dani hakan zai iya sani farin ciki ban taba kula wani ba dan Allah ina son jin maganan ka koya yake dan ALLAH idan kana son MANZON ALLAH da ADDININ MU ina haɗaka da kirman Allah kayi magana ni ko zagina ma kayi ".

ta karashe maganan tana daura hannun ta akan cinyar sa
tacigaba "wllh kome kake so arayuwa zan baka ciki harda kaina ta ƙarashe maganan tana ƙara shige masa sosai har jikin su yana gogan na juna
cikin ɓacin rai da tsare gida yace" AL'HAMDULILLAH kince duk abinda da nake so zaki min ko".

Hanifa ware idon ta tayi tana control din numfashin ta dan jitake kamar numfashin ta bazai dawo ba cikin wani irin murna da sauri tace " yes yes my love wllh zanyi".

"ok bana buƙatar ki sake koda kallon inda nake ki gargadi idon ki sosai idan kika ƙaramin kallon da ya zarce 3 to ki kuka da kanki last woorning ".
ya ƙarashe maganan yana meƙewa ya shige bedroom murmushi Hanifa tayi
ta tashi dagudu tana ƙwallawa Momyn ta ƙira har ta haye tstep banko ƙofar tayi ba sallama balle knoking momy da dad din nata zaune abakin bed momy tana gyarawa dad sakin hulan sa ta faɗa tsakiyar su tana rungumesu ɗaya bayan ɗaya
"wayo dad yamin magana wllh yamin magana dad kaji voice dinsa wllh kamar anyi editing wllh dad guy din yayi very very".
dariya dad din nata yayi
yace " yawwa my daughter ai sannu sannu fata hana zu ai kina da kyau da duk abin da za asoki".
"Dad zan tsaya masa mota waya zan masa hoping masu tsada dad zan nunawa su ZEE ni nawa daban ne yafita daban dad ko a novels ban taba hasaso irin saba wllh dad marubuciya bata isa kwatantashi ba dolen ta tabar wani abun idan ko tace zata kwatan shi gabadaya saide taci pages 100 akan sa dad yahadu ya hadu dad dimple
fa akumatun sa duka biyun suke lumewa daga ya motsa bakin sa kamar irin na *RAJBIR* na wani shiri *jamai rajah* ".
DADDY yace " kinga dama three brother sun fara aiki akwai sabbin motoci ba kalan da babu sai ki zaɓa masa wanda kikaga zai masa".

wani irin tsalle tayi ta rungume dad din nata tana cigaba da murna
"amma Dad kai zaka kirashi kagaya masa zamuje shorping
"ok
" ok daughter bari ayi breakfast sai mu zauna".
"Ok daddy bari naje na sake showers na sake masa sabon makeup ".
taƙarashe maganan ta ficewa da sauri

kamar yanda ta fada kam tasha makeup ba ƙarya HANI ƙyakƙyawa ce ajin farko kuma yar gata
tasamu iyayen nata zaune a parlour har sun gama breakfast Nasir zaune a kujera ya gama damƙe fuska

Dad yayi gyaran murya yace " to ranka yadade Ahamed kaga ƴar shagwaban taka tafito kuwuce ko".

Nasir wani irin ɗagowa yayi ya wurga musu kallon ku shiga tai tayin ku daga uban har ƴar
sannan ya tsayar da idon sa ƙem akan UBAN yace "ni nace maka ina buƙatar fita".

yana yin yanda yayi magan kadai idan kaji kasan ishe she ne
Dad din Hanifa
yace " A malam Ahame ai fitan nakane kai zata sayawa mota da kayan gayu ai wanda kakeso zaka zaɓa ahine shikiman fita da kai din".

cikin isa yace
" bana bukatar su" .

cikin mamaki Alhaji yace ". ikon Allah kai ɗin waye a ƙasan nan ɗan waye kai wanda ni ALHAJI MUDANSIR GUGA zanyi magana kaja dani kasan ni kowaye".

cikin mamaki Nasir ya maimaita MUDDANSIRI GUGA acikin ransa cikin mamaki ya daga yana kallon sa tabbas shine shine me *WANKI* da *GUGA* a gidan su kafin rasuwan Abban sa to ya akayi yayi wannan kuɗin duk da yasan tsofin ma ai 'katan gidan su duk masu kuɗi ne cikin ahekaru kaɗan duk wani ma aikaci a Three brother yakeyin kuɗi amma wannan ai nashi yayi over tun dadewa Mommy take cewa Muddansir Guga yana son ya kanshi amma Allah bayyi zai ganshin ba tasha kiran sa tace ga Guga a Dubai zaije su gaisa sai kuma wani uzzurin ya shigo masa Mommy tasha cewa yana yawan tambayar sa dama shine Guga mai company *roba*

Alhaji ne ya katsar masa da tunanin da cewa "nace kai ɗin waye ne da kaƙe mayarda hannun ƙyauta baya ni kaina da kake gani ƴauta ne ɗalilin arzikina

ni sunana Mudansir ni bafulatanin Gombe ne almajiran ta neya kawoni nan kano sai nasamu wata uwar ɗaki ma aikaciyar asbiti ina mata wanki da guga dr Fanna bata da kowa sai ƙawar ta dr Hafsa saboda yanda na iya wanki da guga har dr tasamu miji mai kuɗi miji na nunawa a duniya
da tayi auren dani da tare gidan ta lokacin bazan guce shekara 14 ba naci gaba dayi mata wanki har uwar masu gidan HAJJA ta yarda da nagartan aikina daganan na samu cigaba sosai dan duk wanda Hajja take so to zai zana ɗan gatan Alhaji ABDULSAMAD bayan shakaru bakwai da tarewar mu gidan wata rana Alhaji zaiyi tafiya yamana wani irin ƙyau wanda shine tsilan wannan arzikin nawa
amma babban abin baƙin cikin kuma a ranan da yamana wannan ƙyau tan aranan yarasu ɗan sa daya Mahammed Nasir yarasu yabar uwar ɗakina da ciki amma Allah bai sa abinda ta haifa sun rayu ba wannan hospital da ka kwanda *GUGA ClLNIC* dan Alhaji Abdulsamad nayi saddakatul jarin
sannan uwar ɗaki na Hajiya fanna tamkar uwa take aguna kaga matata ma ita tazaɓa min kanwar ƙawar ta dr Hafsa shakaran mu asirin da aure Hanifa itace babba kuma sunan HAJIYA FANNA ne da ita sai ƙannen ta 5 duk maza ne suna US suna karatu a wajen ƙanina wanda yake kulamin da harkoki na nacan
so temako ya kaini duk matakin da nake yanzu
nima na temaki mutane dayawa amma meya sa kaida Hanifa tace tanaso zakaƙi karɓan tayin ta bayan zan iya mallaka maka rabin abinda nake dashi".

Nasir ajiyar zuciya ya sauƙe ya dan gago ya kalli momyn Hanifa tabbar suna yanayi da MAMY HAFSA kuma sai yanzu ya sake ganeta ta zauna a gidan su kuma itama Hanifa sai yau ya tsaya ya kalleta sosai suke kama da Amiran dr hafsat
lalle rashin daukan hoto da bayayi rahamane a wajen sa da yanzu ko da ƙarfin an baida shi Three brother
asanyaye ya meƙe tsaye yace "Alhaji nagode da temakon da kayi min nima ina yuwa Uban gidan ka Alhaji Abdulsamad addua amma ni dama nazo na maka sallama ne zan wuce".
cikin sauri Alhaji ya meƴe yace "ban gane sallama ba kai da kace bakada family?".

"bani da family yana nufin ba inda nake rayuwa kenan".
ya ƙarashe magana yana matsawa kusa da hanifa yace am so soory my Fatima".
ya kama ɗaya hannu ta ya hada danashi idon sa cikin nata yasake cewa sorry sis".
ahankali yasaki hannu yajuya zai fita
da sauri tabi bayan sa tace " zaka *aure ni*?
bai juyo ba ya girgiza mata hannu alaman no

ya fita cikin takun isa

wani irin ƙara Hanifa tasaka ta fadi awajen sumammiya
da sauri dad da mom dinta sukayi kanta dad yaleƙa yace SAidu kada kabar wannan gaye ya fita wllh idan na rasa ƴata kai ma sai karasa ranka Sa'idu tsaremin shi
Sa'idu yayi kan Nasir gadan kadan amma nasir yana watsa masa wani irin kallo ya tsaya cak yana ganin sa yafice

Nasir sai da yafita a get din gidan ya tsaya yayi murmushi afili
yace " duniya kenan ni Nasir wata kucaka zata gani a araha ta shige min lalle Fatima kinci darajan sunan Mommy
hmmm wai yarinya harda taba min jikina me daraja
ALLAH sarki Alhaji baka can canci namaka haka ba amma nayiwa kaina al’ƙawarin bazan sake rayuwa a inuwar Three brother ba da gumina zan rayu dukiyar gado masifa ne.....

juyawa yayi yafara takawa cikin sauri dan jun an fara kiciniyar bude get


*Three brother house*


Daddy ya kalli Nasrim yace " daughter kina kaiwa dan uwan naki ziyara kuwa?".

gaba daya yanayin Nasrim ya canza cikin damuwa ta girgiza masa kai
gyara zama Daddy yayi yace Halima ko baki yafewa ɗan uwan naki bane yajima yana cewa yana son ganinki kije mana ya ganki akwai abinda yake son gaya miki".

cikin kuka Nasrim tace "daddy bazan iya ba bazan iya zuwa naga Ya Kamal a prison ba lefin sa bai kai wanda za ayanke masa wannan hukuncin ba Mama ce mai lefi kuma an kasheta Dadd dama inason gaya maka ina shirin shigar da ƘARA akan a sassauta masa".

girgiza kai Daddy yayi yace" impossible Nasrim hakan zai iya ragemin daraja a idon duniya bayan kowa yana yabon da sha'awar abin da nayi na yankewa ƴar cikina hukunci da kaina kuma anyankewa ɗana hukunci ina da ikon fitar dashi amma na bari saboda iya adalcin kena sannan anyakewa matata hukunci banja ba har aka kasheta wannan abin ya ɗaga darajata a idon duniya hakan yaja an bani wakilancin alƙalan ƙasan nan baki ɗaya yanzu nine hugabansu idan kika sake tada wannan zaki sa aga rashin girmana".

"Daddy saboda mutane zaka bar ɗan ka kada kasa baki ni zan fitar da ya Kamal bazai shikara a gidan prison ba".

taƙarashe maganan tana ficewa

hajja da mommy

"Hajja dan Allah kiyiwa Baba magana wai shi ya nace bazamu je maiduguri da lagos ba sai anga Nasir Hajja yanzu tsawon wata 5 ba nasir ba alaman sa gaskiya ni inason ganin uwata".

murmushi Hajja tayi tana kallon momy
tace "Fatima Zahra damo sarkin hakuri ki ƙara haƙuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login