Showing 69001 words to 72000 words out of 155717 words
Chapter 24 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
ba har kaima yau breakfast din mu yana hannun ta dan Allah sir kar ka nuna ban isa da kai ba kamin wannan alfarman mutafi yanzu".
tsaki yaja yace " bani da wani lokacin b'atawa akan wata macce kude da kuka daurawa kanku kuje kuyi tayi wancen shegen ma daga zuwa aikin da baifi na 1 week ba yace dole sai 1 months zayyi kuka duk kan macce ne nasani".
ajiyar zuciya Aliyu ya sak'e azuciyar sa yace inda kasan halinda yake ciki da bazaka ce haka ba
Afili kuma yace" to ai rayuwar duniya sai da mata shi kansa neman dan suwa mukeyi yanzu de zan samu wannan alfarman"?.
tattare fuska yayi yana mek'ewa yace " ba dole na ba inde ina son amin aiki da nusuwa bayi mata kawa".
"Thanks so much my friend".
ko ajirgi a zaton Aliyu Nasir zai nemi wayan sa amma ina ko tambaya bayyi ba kawai wantar da kansa yayi akan kujera tare da lumshe ido ya sauk'e numfashin a hankali
Nigeria
Bayan sauk'an su Nasir amamakince yake min mutanen da suke tare tun farkon layin su da kallo wanda dole su suka sauk'a dan mota bazai shoga ba amma dayake bashida kuzarin da zayi wani masifa kawai sai ya sauka tabbas agidan sune amma to meyake faruwa".
yayi maganan afilli hannun sa Aliyu ya sake damkewa yace "sorry MUHAMMAD mushiga ciki ko".
dak'er suke kur tsawa har suka samu nasaran k'arasawa wajen get din masu gadin suna ganin Nasara suka bude kofar ya shiga
da d'ai-d'ai yake kallon mutanen gidan Wanda su Hajja ma har yanzu suna compound duk ana waje a zaune a k'asa Hajja ce kawai take kukan da bama fitowa yake ba muryar ta yagama dashewa Ummu ko tuni ta suma anyi asbiti da ita
yana jefa idon sa kofar part din mommy yagan ta kwance sai faman shafa mata ruwa ake ahankali yake takawa gaban sa yana faduwa
ya k'arasa wajen mommyn zuba gwaiwogin sa yayi a k'asa lips din sa narawa yace "mommy meyake faduwa"""?
Mommy jin murya Nasir yasa tayi saurin mude idon ta kamo hannun Nasir ta damke cikin wahalallen murya tace'' sun tafi da ita Nasuru zasu kashe min y'ata zasu kashe ta Nasuru kaine gatan mu ka karbo min y'ata agaban Alhaji Abdulmajid aka jefa min ya a hilux police suka tafi da ita zasu kashe ta wllh Halima bazata kashe Fayyat da Khaldum da Agrif ba tana son su Dan Allah Nas........
"FAYYYYT KHALDUM
cikin wani irin k'ara da amonsa ya amsa duk gidan yasake cewa "mommy ina Fayyat ina Khaldum kafin mommy tayi magana Khafulan yace " Papa mamy ta shashe su har abbanmu yan sanda sun tafi dasu ni buya yani a toilet Ina ta kiran ka bakayin picking ba papa".
"ahankali Nasara yamek'a tsaye yana girgiza kai yace mutuwa "Ah Ah baza su mutu ba mommy ki min bayani ta yanda zan gane ya za ayi Khaldum da Fayyat su mutu ban nemi yafiyar suba ah ah mommy ki min bayani ya kalli Dr Hafsa yace Ummyn Ayman meya faru? ".
Mommy tace'' Nasuru nima ban san meyake faruwa ba bana gane komai Fayyat ya mutu khadum ya mutu jikokina dana daura dukkan burina akan su an kashe Aiban da guba banyi magana ba naga illan shiru yanzu gashi makiya sunci galaba a kaina an kashe min jikoki an daura al'hakin kisan akan y'ata mutuwa zanyi Nasir".
"Mommy da gaske yarana sun mutu abokina yamutu". Humairah ce tace'' wllh ya Nasir ta kashe su dama tun da rana tace'' sai ta kashe ya Agrif akan ya amince zai auri Izza ta kashe masa yara har biyu".
cikin wani irin amon murya yace
"tana ina tana Ina wllh idan rai goma Allah yaba bata to duk sai sun fita cikin a zaba wllh zatayi mutuwar wulak'ancin sai na daura ta ajikin mota na jata a kwalta sai nayi pieces pieces din naman jikinta tana ina yayi maganan yana cikumo Humairah yana wani irin gurnani kamar mahaukacin zaki".
Humairah kasa magana tayi dan yanda ya cukumota ko numfashi ta kasa ja Kamal da Ayman da Aliyu da sarkin gida dak'er suka ceto Humairah sai alokacin Izza tasamu shigowa dan tana asbiti tun dukan da Nasrim ta mata kwanciya tayi a k'asa tafara wani irin birgima tana rusa ihu haka Mama ma sai yanzu tasa kuka Kamal Abbaty da sauran mutane duk suka fasa kuka daddy da Abu jisuke kamar su kashe kansu duniya ta musu k'unci da gudu daddy yayi part din sana Mama ya haura sama rarufe kansa a d'aki yayi yak'i fitowa kawai shi jira yake ace tashin duniya ne kowa ma yamutu ahuta yakeji Abu ne yabiyo bayan sa yana
buga kofar yace "haba Abdul ka zama namiji mana ka daure kafito mu kwantar wa da matan nan da yaran nan hankali muje
station a karbo Nasrim muyi cuku cukun karban gawar wakin mu musu sutura".
cikin tashin hankali daddy yace "Ah ah Abdulrahaman bazan iya fitowa ba kawai kayi duk abin da yadace ba zan iya cigaba da kallon mutane ba y'ar da na haifa ita takashe d'an ka dan uwanta mijin ta Hajja tayi gaskiya kar kayi kuskuren bellin din Nasrim duk Wanda ya kashe ran mumuni da gan-gan shima a kashe sa".
Abu yace " yanzu kafito ni kadai bazan iya duk wannan ba ga Nasir ma yazo baya cikin hayyacinsa mu yaka mata mu kwantar musu da hankali".
dak'er daddy ya yarda yafito
suka dan kwantarwa da matan hankali suka shiga parlou su kuma suka tafi asbiti dan karbo gawa zasu fita yan sanda suma sukazo binciken gidan aka nuna musu part din da abin yafaru
sai da yan sanda suka gama nasu binciken akan gawar wakin doctors sukayi aka batu gawar wakin dan haka ba asamu daman suturan su a ranan ba Saida suka sake kwana
Nasir sai binciken wane station Nasrim take yakeyi amma yarasa dan bayan magaruba mommy da aminceciyar kawarta Dr Hafsa suka tafi Nasrim tana asbiti hannuwan ta dukka biyi a daure ajikin k'arafunan gadon asbiti a d'aki na musamman yan sanda ciki da wajen d'aki
Mommy girgiza kai tayi tana kallon yanda Nasrim take fitar da numfashin duk da bacci take amma ba na dad'i bane kallon ta tamaida kan Dr Hafsa tace'' Hafsa yanzu Nasrim ce ahaka y'ar dana haifa da cikina ce ahaka a daure ajikin gadon asbiti wllh Hajja ta cuceni Allah ya isa tsakani nadake Hajiya Maryam ke kika hura wannan wutan wllh ko duk abin dana mallaka zai k'are bawanda ya isa yasa a kashemin y'ata ita kadan nake da Nasir yajuya min baya ".
sosai ta fad'a jikin Nasrim take kuka
Hafsa tace'' wannan itace mummunan k'addaran ta amma dan Allah Fanna k'in tada hankalinki dayawa in sha Allah Nasrim zata fita cikin wannan yanayi koda biyan kudin diya zamuyi zamu dauki kwararrun lawyer da suka san aikinfu Nasrim ko ita tayi kisan in Sha Allah sai ta fita".
"Mommy mommy".
su kaji Nasrim tace da sauri mommy ta d'ago
" My daughter gani meye how you feeling now me kike ji yanzu ajikin ki".?
"Mommy ina Agrif ina Fayyat ina Khaldum".
"Nasrim kin kashe su kin kashe Fayyat da Khaldum da Agrif Nasrim meyasa kika mana haka idan kin kashe Agrif saboda kishi su yaran me suka miki me jikokina suka miki gashi kinsa zan rasaki ai da kin barmin su zanji sauk'i ".
"Mommy da gaske sun mutu? Mijina yarana duniya ta kuma ake zargin na k'ashe su meya ke faruwa dani da gaske ni na kashesu mommy".
Mommy tace'' Nasrim kece mana duk bincike ya tabbatar kece Khafulan yaganki kina wasa wuka kuma yace kafin sannan da kuma wukan da yaga kin wasa dashi kikayi kisan duk kuma dama kinyi furucin hakan".
mommy idan ni nakashe su mommy wane hukunci za ayanke min".
"Kisa mana Nasrim ke ba lawyer bace kinfini sani ai".
Murmushi Nasrim tayi tace'' mommy a yau ayanzu yaka mata ayanke min hukunci inason a kasheni yanzu inason naje inda Fayyat d'ana me sona yaje na tambaye shi waye ya kashesu Ina son naje naga mijina na tambaye shi waye ya kashe sa mommy a cikin daren jiyan bayan fitan ya Kamal saida Agrif yaje mukayi magana na fashimtar juna mun sasanta dashi munyi dashi zamu tafi mubar zaman Nigeria mommy meyasa to na k'ashe sa bayan mun sasanta ya yafemin yankan dana masa a hannu ya tabbatar min da mak'irci aha hada bashi ya d'aura hoton ba amma yaga Wanda yadaura hoton dan duk Wanda yayi amfani da wayan sa yana ganewa saboda wayan yana daukan hoton duk wanda ya taba amma nayi nayi ya gaya min yace" hakan bai dace ba amma yasamu munafikin ya tabbatar masa kuma ya nemi yafiyar sa yafe masa dan haka basai yagaya min ba mommy Dan Allah akai ni kotu yanzu zan amsa nina kashe su a kasheni gwara rad'adin mutuwa da kuncin yaruwar da zan fuskanta idan ba Agrif acikin yaruwa ta".
Mommy tace'' Al'hamdulillah kina nufin bake kika kashe suba ".
"Mommy kisa aranki ni banyi ba amma afili ki barshi anice".
Mommy ta girgiza kai tace'' Nasrim bazan bari ba bazan bari akashe minke ba kokina da lefi balle baki dashi sai kin fito sai me lefin yafito da kansa".
murmushi Nasrim tayi tace'' mommy wai meye acikin mutuwa ne duk gudun da zaka yiwa mutuwa zai zo duk tsawon shekarunda mutum zayyi a duniya baya wuce dubu to da mutuwar yanzu dana wata shekaran duk sunan su mutuwa kowane rai sai ya dan danni mutuwa ban damu na mutun ba mommy".
Doctor din da yake kula da Nasrim ne yashigo zubewa yayi har k'asa yace ranki shi dade an wuni lfy ya mukaji da wannan abin da yafaro".
mommy ta juya tana kallon sa tace
"Yawwa Dr suleman kaine akanta ko dan ALLAH akula sosai idan Muhammad Nasir yazo kar abari ya ganta inde ba Daddy ta ko yayanta Kamal ba banason kowa ya shigo".
"Ok ma'am amma muta ta fama da yan jarida". tace
na gayawa police din kar abari su shiga ayanzu bata cikin nutsuwar ta".
sai can dare Dr Hafsa da mommy suka bar asbiti har lokacin gidan tamkar nara kuma ba adena koke koken ba mommy part dinta ta yawuce direct ita kuma Dr Hafsa tace bari taje gunsu Hajja da dawo a falon sama ta samu Nasir ya daura Khafulan a cinya yana da aikin lalashin sa dan shide akawo masa su khadum kallo daya tayiwa inda suke tayi hanyar bedroom din ta
Khafulan yace " Papa Allah itace ta kashe su da kayan data shiga ta mana addua da zamu kwanta dashi ajikinta ta kashe su kuma ta rofe fuskan ta har hannun tasa safan hannu dogo baki da dogon shijab ina tsoron nima kar da kasheni tunda tayi ta buga kofar naki na bude tayi da turawa da karfi kofar yaki buduwa ta nemo key tayi ta gwadawa ni kuma sakata nasa ".
shiru Nasir yayi can yace sorry my son baza ta kashe kaba ina tare da kai kuma idan zan koma tare zamu tafi kaji".
yaci gaba da lalashin yaron har yasamu bacci ya daukeshi ya kaishi bedroom din sa ya kwantar dashi ya fita knocking yayi a bedroom din mommy batayi magana ba yashigo samun ta yayi atsakiyar godo tazuba uban takumi
hannun sa zube cikin aljuhon wadon ya karasa inda take
Mommy bata d'ago ba tace'' kai ma ka yarda Nasrim zata iya kisan kai ita ta kashe su ko".?
Cikin b'acin rai yace" to idan ba ita bace waye waya kashe su wayayayi FURUCIN zayyi kisan kai idan ba ita ba"'
Nasir ba ita bace ba ita bace Nasrim bata kashe su ba ta fadamin gaskiya".
" Eh mommy zakiyi kareta because y'arki ce amma nikuma jinin yarana bazai tafi abanza ba Ina nan Ina binciken asbitin da aka kaita wllh wllh awannan daren da zan ganta zan dinka yan kan naman jikin ta sai nayi piece piece dinta a tattara naman ta a binne danasu Fayyat".
Mommy sauk'owa tayi akan gadon tazuba gwaiwoyin ta a k'asa a gaban Nasir ta hada hannayin ta cikin tsananin damu tace'' Dan Allah muhammad katema kamin Nasrim ta fita cikin wannan k'alubalin zan iya shiga matsala idan narasa ta dan Allah Nasir kadubi soyayyar da yake tsakani na da kai kamin a dalci muhada karfi da karfi mu ceci rayuwar Nasrim uban da ya haifeta ma bai koyi bayan ta ba kuma bata dalefi".
"Juyawa yayi zai fita da sauri mommy ta kamo k'afafuwar sa tana kuka tace'' katema min".
girgiza kai yayi a hankali ya furta "impossible".
ya janye kafar sa mommy tana kuka tana k'iran sa "MUHAMMAD kai kadai ka ragemin Nasir kar kamin haka". Bai ko jiya ba yafice
washe gari k'arfe 9 nasafe akayi musu sutura ansha fama da Nasir da za afita da gawar wakin dan sunbatu yadin gayi dan Allah kar kukai min abokina wllh yafi kowa sona da rufamin asiri na Agrif ko mutum na kashe zai rufa min asirin dan Allah kar ku binne min Khaldum da Fayyat kubar su surayu su girma na nemi yafiyar su wllh idan muka hadu awajen Allah bazasu yafemin ba ni me lefini awajen su nasa sunzo duniya bata hallaceciyar hanya ba inaso sugirma in nemi yafiyar su".
Mutane basu wani tsaya sun fashimci abinda Nasir yake fada ba dan duk muryar sa adashe basa jinsa daddy yace a jan shi asani a d'aki ba aje mak'abarta dashi ba
Abu ya hana zaman makoki na mata da maza gaba daya wanda ya kama dole ya musu gaisuwa yana zuwa idan yayi musu soke sallaman shi
washi garin ranan
Izza da Baban ta
tace'' Baba wai dama wannan mutuwar kagani kace gidan zai hargitse wllh Baba gida ya hargitse gaba daya Hajja ta dauki lauyoyi ciki harda ni zamu gobza Shari'a kuma kasan me akotun daddy kasan shine na biyu a najeri daga shi sai high court babban kotu na k'asa dan haka Nasrim Baban ta ne zai yanke mata hukuncin kisa yanzu yau yan sanda zasuyi minciken su na k'ashe daga nan su mek'a cases din court insha Allah zamuyi wining".
Baba yace "ba nagaya miki ba akwai babban rigimar da zai taso wanda yafi karfin tsafina ba
yanzu ya cikin gidan yake dan naji shiru".
"Uummmmm Baba cikin gidan nan bakyau Abu da Ummu de basuce komai ba har yanzu amma Daddy yana bayan Hajja
Kamal Kai ma kasan ida yake gida ha hargitse yanzu yau Hajja zata sa daddy yasaki mommy ta bar gidan kai rigima fa gaba ta kama ita mommy tana Shirin daukan lauyoyi taci alwashin ba wanda ya isa ya yakewa Nasrim hukuncin kisa".
da yammacin yaran yan sanda suka zo gidan gaba daya a main parlour na Hajja suka taru dakka mutanen gidan tambayar farko Kamal sukayi wa suka ce
"Kamal bincike yanuna akwai tes message da Haruna marigayi ya tura maka da misalin 2 na pm ka boye baka nuna mana shiba a binciken farko da muka maga
ga tes din kamar haka
_kamal kazo dan Allah da gaggawa ashi Nasrim bata hakura ba gashinan zata kasheni tace ta kashe min raya_
fashewa da kuka Kamal yayi yana girgiza kai ya dafe goshi ya fara kuka
Sannan dan sandan yace " kayi ne Dan ka rufawa yar uwar ka asiri ko ita ma tayi kokarin haka dan ta CC TV yakamata muga komai amma an goge abinda yafuru daga 1 na dare zuwa karfe ukku darabi amma daga abinda muka gani na k'arfin hudu na yamma zuwa 12 na dare ya gamsar damu ita tayi kisan dan cc tv yanuna tun 12 taso ta kashe sa bata samu da ba ta kashe CC TV kafin taje tayi kisan saide marigayi Haruna yayi mata video a wayar sa alokacin da zata kashe sa tana sanye da likaf sai
Lokacin da zata Kashi yaran akwai yaron da yasamu ya tsira shima yayi video din a sanda ta kewa yan uwansa yan kan rogo amma abinda bamu gane ba shine meyasa ta kashe CC TV bayan da farko ta nuna bawani boye boye acikin aikin ta meyasa ta bari Haruna ya mata video meyasa ta sanya likaf bayan ita a bayyane take cewa sai ta kashe sa kuma yanzu ma duk tambayar daza amata cewa take ita ta kashe su dan haka gobe za a turaku kotu gomnati ta dauki nata lauyoyin sannan daga yan uwan mamatan ma sun dauka".
bayan tafiyar yan sanda Hajja tace " insha Allah gobe iwarhaka itama tazama gawa wllh sai de idan Legos din naki zaki kaita ayi jana'izar ta amma ba d'ana daya da zai mata sallah ban yafe ba".
Mommy tace'' in Allah ya yarda baza ma ta mutu ba nan da 50yrs Nasrim tana nan".
"Hajja tace'' ke tubebbiya ni zaki gayawa magana to abinki ya isheni ina gama da hadin bakin ki y'ar ta ki tayi aika Kai kan na
Abdulmajid idan na amsa sunan uwa a gurin ka ayanzu ba sai an jima ba kasaki wannan tobebbbiya taje can ta k'arata yanzu nake son ka saketa".
A tare Humairah Mama Ummu Abu suka mek'e har Kamal suna cewa subbahanalla Hajja abin har yakai haka
" yafi ma zaka sake ko sai na tsin.....
da sauri daddy yace "ni Abdulmajid Haruna nasaki matata Fanna emake saki daya".
"to kinji kifita kibar mana gidan mu ni idan kina ciki gidan hankalina bazai taba kwanciya ba".
dariya mommy tayi tace'' nafita fa kikace ai sai de nafitar daku kin manta gida nawa ne
Hajiya Maryam kinyi kuskure da kin bar auren d'an ki akai na dalilin auren d'an naki Ina iya raga miki amma yanzu nida ke ba komai a tsakanin mu yanzu zaki ga aikin tubebbiya kum.......
wani irin mari daddy ya zuba mata yace "ashe baki da mutumcin".
Mommy tace'' dani daku zaman shekara 32 bakusan bani da mutumcin ba sai yau akan y'ata ba abinda bazan iya ba".
Abu yace" au Dr Fanna duk kawai cinda nake miki agabana kikace haka to wllh za a hukunta Nasrim kamar kowa tunda duk bayanai sun nuna ita tayi