Showing 99001 words to 102000 words out of 155717 words
Chapter 34 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
me rai yana kallo ni mairo".
Dr Hafsa tace'' Hajja to ya akayi kika gano ta".?
"Ummm ai tun ran da nace sai na hada auren Izza da Haruna naga murna a tattare da ita kuma abin da yafi dauremin kai yanda Nasrim tacigaba da haukan bataso amma Aisha shiru kakeji bata ce komai ba bayan Nasrim maganan ta kad'ai takeji da kaina na Kira Aisha nace tabawa Nasrim hakuri ayi abinnan yariyar nan Izza tana da biyayya kuma wllh tana mutuwar son Haruna tun tana takaba na gano hakan har mafarkin sa take duk Ina sane to kawai dan jikata ce agidan sai nazama meson kai bayan ALLAH yace kayi temako a inda kakeda ikonyi musamman sunnan manzon Allah ba Lada zan samu ba amma Aisha da alaman ma zuge Nasrim take daga nan nagano sai abin da yasa zargina yasake k'aruwa kuma ranan da Haruna ya mutu Nasir yazo yake gayamin shifa yana tunanin ba Nasrim bace tayi kisan shiyasan duk Wanda yayi kisan akai abinda yake son
kuma ganin bayan Nasrim yake son yayi shine yayi kisan a kan gab'an FURUCIN ta
nace masa to wakake zargi kai tsaye yace Kamal tare dabani hujjojin da misalai sai yace inde da gaske Kamal ne
to Hajja ba makawa akan dukiya zayyi hakan dan Kamal b'arawo ne sosai bashida Amana bama ganin dai-dai a
ai'kin sa kawai muna kyaleshi ne sabo da ai yafi wani abin duniya awajen mu sannan idan Kamal ya tara dukiya mezayyi dasu ba three brother zai kawo ba zuba basa idon da mukayi yasa yana yanda yake so gsky Hajja ina mugun zargin sa da boyeyen hali yanzu de nasaka an saka CC TV na boye da farko dole sai mun sako daddy a binciken ke kuma abin da nakeso dake kinuna bakya goyon bayan Nasrim da Mommy ki dage akai abin kotu sannan ki tunzura Mommy ta fadi wani abun sai kawai daddy ya saki Mommy kinga idan shi yakeyi idan aka saki mommy jikin sa zanyi sanyi idan dan dukiyar Mommy yakeyi zamu gane
Tode haka akayi kuma yana kunna bin CC TV din Ina ganin duk munafurcin da Aisha da dan ta suke kullawa
sati 3 da rasuwan su Agrif Humairah tazo min da kuka tana cemin wai Kamal ne yayi kisan kayan ta yasaka yayi kisan gasunan yanzu Faiza mai'aikinta tafito dasu anan muka sake tambatarwa Nasir yace takoma tayi zaman ta kamar bata gani ba komai yazo k'arshe amma sheda mukeso dumu-dumu
anan Nasir yace to muma Hajja murikita musu tunani ta hanya amfani da FURUCIN Mommy muce tabaki guba a gefe daya akasaka guban aka bani naci gefin da ba guban sannan na gauraya na fara birgima
ai kunga yanda hankali Kamal da uwar ya tashi suka fara tunanin basu kad'ai bane masu kulla kullan kuma kunga ita Fanna ta tsira da bamuyi saurin amfani da FURUCIN nata ba su zasuyi dashi kuma ni zasu kashe alokacin tunda nice Fanna tayiwa FURUCI a kaina
NASIR da iyawan sa da Basiran sa saida yabi diddigi ya kawo wani babban malami mai suna malam K'aura ashe bokane shi yake koya musu komai ashe tun Aisha tana budurwa take aiki akan gidan nan tayi ta asa sosai amma mun rufawa malamin a Siri tunda yamana alk'awarin ya tuba yana da yaran shine Nasir yace mu rufa masa asiri".
Mommy tace'' kenan ku kuka sa Barira aiki kenan".?
"Eh mune muka sata amma daga baya ta zama abin farautar su dan su samu wanda yasakata aikin Saida Nasuru yasa aka d'auke ta agidan ko Dr Hafsa ma dagan gan ya saka aka kulleta duk dan yabata kariya dan sunyi niyar hallakata sabo tasan komai na Fanna shima Baba Nasuru ai ni nasa aka fita dashi dama Nasir ya gaya min Baban Fanna ne amma idan suka gano zasu iya illatashi saboda magajin Mommy ne ita kuma Fanna ta kwashe ta gayawa Kamal shine baban ta shikuma dan hauka aranan yazo kashe Baba Nasuru Wanda adaukan sa mahaukaci ne bayan ya warke ras kuma idan baki man taba ai nashigo aranan nida yaron alk'ali har nace na canza k'aran ai bayan nan nashigo nacewa Baba Nasuru karyayi bacci zai iyayin b'oko cikin dare kuma yanda na zarga din ne Kamal yazo kashe sa
Amma aikin mu daga k'arshe yaso ya b'aci saboda rashin Nasir karfin addua ne kawai yasa aka samu nasara Fanna kina da saurin yarda yanzu gashi mun rasa Nasir anyi neman duniya ba a gan Shiba burina yanzu naga Nasir sai mu daukeshi muje wajen kakar sa Emaka muje maiduguri musan asalin Nasuru shima".
Dr Hafsa tace'' Hajja Allah ya temaka yanzu ba inda aka samu labarin Nasir ".
Hajja ta nuna Aliyu da Ayman tace''kinga agun Wanda nake jin labarin nima
Ayman yace'' wllh mamy babu labarin sa amma muna nan muna bincigawa insha Allah za a ganshe".
Kotu ta yankewa Baban Izza hukuncin kisa ta hanyan rataya bisa kwararun hujja da Izza ta gabatar shikam bayyi mutuwar salihai ba dan Asher yake ta kutsawa Izza har yacika
*Allah kasa k'arshen kalman mu aduniya yazama kalmatus shahada ne Allah kacitan ta aikin mu na alkairi ya rinjayi sherrinmu duniya duniya cike take taf da rud'adi*
washe gari dan aike yazo daga prison wai Mama tana son magana da duk yan gidan kafin arataye ta dak'er Abbaty ya lalaba Daddy ya y'arda zai zo haka Ummu da Hajja da Mommy ma dak'er ya shawon kan su
Prison
Mama zubewa tayi agaban su cikin kuka
tace'' Abdulmajid gobe za a ratayeni gobe zan mutu yafiyar ka nake buk'ata duk da ban can canci hakan ba nacuce ka nacuci rayuwar y'arka nacuci rayuwar duk family ku badan komai ba sai son zuciya da hassada da nagina zuciya ta dashi a tunani na zanci riba haka na Gina zuciyar tilon d'ana dashi sai yanzu nagane duk wani mai bin boka da malaman tsubu to burin sa baya taba cika duk inda ka toshe wani b'angare to wani zai balle
lalle Gina zuciya da tsoron Allah yafi komai riba yanzu kam na yarda babu meyi sai Allah shi yake yaye matsala kamar yanda Nasrim taji tsoron Allah gashi Allah ya fitar da ita
Abdulmajid farkon hassada dana akan d'an uwan kane Abdulsamad tun kuna zuwa zance wajenan na gano dukiyar gidan duk nasane daga nan najuya nace shi nake so babu juyin da bokana bayyi ba yace Sam ba aure atsakanin mu shine na hakura na aure ka Koda nazo gidan naga yanda Halima tafi kowa iko Hajja tafi sonta shima na gayawa K'aura yace zai min maganin ta zata mutu a haifuwar fari alokacin kaura gidan yake zuwa da sunan driven gidan Yaya mairo ne aiko sa take wajena ashe Halima taji duk wannan maganan da mukayi da K'aura amma k'aura ya mata barazana da idan ta fad'a zai kasheta kuma ya kashe mahaukacin uban ta wannan shine dalilin da yasa Halima tabawa Fanna d'anta shine dalilin da yasa tasan zata mutu a haifuwa
Sai gashi nida nayi dalilin tafiyar ta lahira amma nima a haihuwa farin aka ciremin mahaifa duk inda nayi mugunta to sai nima naga ba dai-dai ba nayi abu dan Nasir yazama dan iska mashayi Wanda bazai amfani kansa da wani ba ta wani gun nayi nasara tawani gun banyi ba
ya shafi d'an shegen yazama mashayin amma nima
sai gashi nawa yazama hakan yanzu Kamal ma Yana da y'ar shege
nayi nayi Nasrim tazama y'ar isa karuwa ta yanda mutumin kirki bazai aure taba abin ya gagara sai ranan auren ta K'aura yabani babban dama Kamal yasakawa Nasir maganin karfin sha'awa ya kus......
dasaure Mommy tace'' dakata Aisha ya isa".
ta kalli Abbaty tace'' Abbaty kafita da Nasrim ka kaita gida kadawo".
Nasrim tana kuka tana cewa Mama ki k'arasa
amma Abbaty yajata suka fita bayan sun fita
Hajja tace'' ai da bari kikayi taji komai da bazata zargi Nasir ba har yaushe zamu cigaba da boye mata wannan babban al'amarin da dole sai taji komin dadewa kwara taji tun yanzu ta hada ciwon dukka ta ciye su".
Mama tacigaba
" Kamal nasa yasaka masa maganin k'arfin sha'awa dan dama mungano ba maccen da Nasir yake so fiye da Nasir muna saka maganin karfin sha'awa kuma sai mukayi sa'a shed'an ya k'awata masa Nasrim abin ya sauk'a kanta dan duk yanda mukayi da Nasir asiri baya kamashi har ita Nasrim har Fanna K'aura yace suna da k'arfin jini da addua basa sake da addua asiri ko yakamasu baya tasiri akan su nayi asiri dan kar Nasrim tayi haifuwa dayawa sai gashi Humairah matar d'ana ta tsaya a d'an daya duk wani aikin boka k'arya ne tasirin sa kad'an ne sai jiya da yau nayi dogon tunani
sannan mai bin boka kullum cikin zargi da rud'ani yake sannan Allah yana dauke masa kwarjini ta yanda mutane bazasu na ganin kamalan saba so dayawa Nasrim tana min nasiha da cewa
_Mama ki diga yawaita salatin Annabi yana k'arawa mutum kwarjini_
to Mai bin bokaye kuma k'warjinin sa yana disha shewa duk sai dana makara na gano hakan inama
Inada daman k'ara rayuwa dana gyara kuskure na nacuci kaina nacuci rayuwar d'ana kullum Ina burin nawani ya lalace duk yaran gidan ba Wanda banyiwa asiri ba amma yanzu gashi ni nawa d'an zayyi zaman gidan prison na shekara 25 rabin rayuwar sa zai cinyeta a gidan yari
dan Allah ku yafemin Dr Fanna keda mijina sai Hajiya Amina da mijin ta sunfi kowa daukan ciwo d'an suna fari nakashe musu Hajiya Amina bani da bak'in neman yafiyar ki
ku yakamata ku fara yafemin wllh rabin rabin abin da nayi a gidan ba fada ba wanima idan kukaji tsinemin zakuyi dan Allah ku yafemin".
Hajja tace'' Allah ya yafemiki muma muna neman yafiyar Allah duk sukace sun yafe mata dalilin kukan data keyi sosai kamar zata cire ranta haka suka tafi suka barta.
*washe gari*
haka aka rataye Mama kuka de yan uwanta dasu Hajja sun shata dan Koda za arataye ta ba abinda take ambato sai kalman shahada tanayi tana k'iran sunayin mutane three brother daya bayan daya tana cewa kuyafemin
Allah sarki Zahra tasha kuka dan ita Mama tasani a uwa Nasrim Mommy hana ta fitowa wajen zaman makoki tayi dan tana tsoron kar Nasrim taji gaskiyar lamarin akan su Khafulan daga k'arshe de Dr Hafsa ta dauketa zuwa gidan ta bata dawo ba sai bayan sati 2
aranan kuma su daddy suka zo Allah sarki Abu dama ance jinya lokaci daya yake shigar mutum sauk'i sai ahankali amma yana magana sannan idan ya dan dafa kafadan mutum yana dan iya daga da k'afar sa abin ka da Naira har injin din gasa jikin da doctor aka hadasu dashi Wanda zai dinga masa gashin k'ashin
Bayan sati Hajja ta tarasu dukka harda baba Nasuru Banda Nasrim data auri d'aki kullum kuka ita tunda tazo jitake kamar za ace mata ga Agrif nan yazo takeji
gyaran murya tayi
tace'' Ina fatan de kowa yana cigaba da adduar Allah ya bayyana Nasir ko?
Duk suka amsa ta Eh
"to yayi kyau Allah ya bayyana shi
da farko de Abdulmajid kai nake son ka karbowa Humairah takardan sakinta dan Babana yace nan duniya bazai saki matar sa ba nima zuwana firzin yayi ukku amma yaki yabani".
Daddy yace'' insha Allah zai bada".
Hajja tace''
sai abu na ukku abude company afara aiki kamar yanda aka saba".
Daddy yace'' ai Hajja nikam ba wani abin da nasani game da business ga Abbaty nan shi zaici gaba kafin Allah ya bayyana Nasir".
Hajja ta kalli Abbaty tace'' Adamu meyasa ba abude company ba".?
ajiyar zuciya ya sauk'e yace
"Hajja yazanyi ta Ina zan fara aikin Aiban da Kamal da Agrif da Nasir ma Yana musu yawa balle ni daya yanzu shikenan yan uwa dakka hudu ba sanan Hajja ta Ina zan fara dawane k'asa zan fara"?
Hajja tace'' Aliyu yana Dubai zai nemi ma'aikatan da suka dace Ayman Yana America shima zai nemi ma'aikata kaga kai Chaina yaka mata ka fuskanta tunda nan de akwai Muhusin zai kula shima ya nemi ma'aikata sannan itama Fanna zata koma bakin aikin ta Izza da Humairah da Nasrim duk zasu temaka mata duk da suna aikin su na lawyer hakan bazai hanasu aikin gida ba ni badan sun nace sai sunyiwa k'asar su aiki bama banga abin wahalar da kai ba".
cikin karayar murya Abbaty yace shikenan Hajja amma Muhusin zan tura Chaina ni anan Nigeria zanyi aiki na tun gida ba yaro babba".
Hajja tace''to Allah yayi albarka sai batu na gaba wai mutanen gidan matar da zaka aura sun ce tunda ka fasa aure aje adauki kaya hakane".?
"Eh Hajja nasamu wata Wanda tamin ne fiyeda wancan amma ai kaya nace na bar musu".
Hajja tace''wacece kasamu har ka canza Nabilan taka daka kwallafawa rai".?
murmushi yayi yana sosa k'eya yace "zaki santa ai y'ar gida cema".
Hajja tace'' gidan three brother nan"?.
Abbaty gyad'a mata kai yayi
salati Hajja tashiga yi
tace "idan Izza ko Nasrim kake nufi ma to kwalelen ka su matan manyane".
Abbaty sai da yatashi yaje tsakiyar parlourn yajuyo yace'' Hajiya ni kuma azanin goyo nake ko yayi maganan yana fita da gudu kamar wani yaro
Hajja tace'' ashe rikici bai k'areba ni Maryama Abdulrahaman kuyi min maganin matsala nan kunji ni da yaro da shegen ka ranbani".
*NASIR*
Doctor ya kalli Nasir yace " Muhammad zamu dauki hoton ka mu watsa a Media saboda asamu kudin da za a maka aikin nan idan wannan k'afar taka ta sake kwanaki ukku Wllh saide a yanketa ai kanajin yanda yake wari ko
hannun kade normal ya dauru Amma kafa akwai matsala kuma kudi ake buk'ata yanzu kaga kudin asbiti ma ba abiya ba balle na aikin ka".
cikin dauriya da hade fuska Nasir yace'' doctor nace a yankemin zanfi son haka amma kada ayadani a media".
shima doctor cikin b'acin rain da k'osawa da taurin kai irin na Nasir yace "saboda kai din mai lefine baka son ayada ka duniya ta ganka to nagaji zan saka afitar dakai a watsar a titi mungaji da wannan warin da kake magana anan".
yakarashe maganan yana kiran ma'aikatan da suzo su fita dashi".
*Prison*
Cikin kuka Kamal yace'' Daddy idan sakin Humairah zai saka farin ciki shikenan na saketa amma daddy wllh da son Humairah zan mutu cikin k'ank'ani lokaci wani wahalallen son ta yashigeni".
daddy ya kalle shi cikin wani irin tausayi irin na d'a da mahaifi yace''
"Kamaluddeen na yafe maka Ina fadan Allah yabaka shekarun da zaka Kai fita awannan gida kasamu mata Wanda tafi Humairah kuma ka gyara zaman ta k'ewar ka".
"cikin kuka tace'' Amin Daddy nagode amma daddy ko kasan *Agrif* bai *mutu* ba".?
daddy yace'' ta yaya kasan Bai mutu ba".
Daddy ya aikomin da wasika Daddy tambbas wasikan rubutun Agrif ne ko Ina cikin baccin Daddy aka tasheni zan shada writing din sa Daddy wllh yana nan araye wllh bai mutu ba kaga wasikan".
ya k'arashe maganan yana mek'awa daddy wasikar
Daddy karba yayi yafara karan tawa har yagama yamek'a masa yace'' to yanzu Kai yarda kayi da wannan wasikan kenan".
Daddy na yarda ai kaji abinda yace
Kuma daddy abinda yasa nima na tabbatar da bai mutum ba ranan da ake wankan sa da idona naga dan yatsan sa yamotsa nayi sauri na danne dan kar mutane sugani
Dama kuma Mama tace so biyu tana caka masa wuk'an Yana rikewa wuk'an bai shigeshi Sosai ba
Kuma sannan Daddy damu kaje mak'abarta a gaban idon kowa aka binne Khaldum da Fayyat amma Agrif kai da Abu kukace a watse kuma naga shigowar motan asbiti cikin mak'abarta bayan fitan motan bajimawa kuma kuka fito kaida Abu da Baba suleman da Baba Hamza
washe gani da nakoma mak'abartan zanyi sheda akan kabarin su sai naga Wanda aka tona dan asa Agrif danyen k'asa ne bai bushe kamar na su Fayyat ba na tambayi mai gadin nace ya akayi wannan dan uwan nawa k'asan har yanzu danye yacemin wai ai yanzu aka kawota kuma macce ce".
nide nasa sheda nabar wajen
Duk alokacin ban dauki abin da mushin manci ba duk da naga k'afar sa ta motsa amma tunda an binne sa ai zaimutu acikin rami sai yanzu da ya aikomin da tabbacin bai mutu ba".
Daddy yace'' Habubakar bana son sake jin wannan abakin ka ko Agrif bai mutu ba ai uwar ka ta kashe Khaldum da Fayyat kuma karikewa Agrif Amana kamar yanda yace idan kasake wannan maganan yafito ban yafe maka ba".
"Daddy zan rike Amana dan uwana bazan gayawa kowa ba amma............
*Sorry sis mu hadu a 24*
*Humairah an zama bazawara Izza bazawara Nasrim bazawara dir k'ashi muje zuwa*
*Wane irin wasika AGRIF ya aiko? Muje zuwa rikicin babban gida*
*Bj*
*FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*INA GODIYA SOSAI DA COMMENTS*
*24*
zan reƙe amana Daddy amma dan Allah kasan inda Agrif yake".?
daddy yace " idan nasan inda yake menene".?
"Daddy ƙiramin shi zakayi ina da abinda zan gaya masa dan Allah daddy".
kallon sa daddy yayi sosai ya girgiza kai yace'' bansan inda yake ba sai wani lokacin ka kula da kanka nasa an dauke maka duk wani wahala dan haka kana da lokacin ibada kayi ta istigfari da karatun Qur'an".
hannun daddy ya riƙem yana girgiza kai shima daddy bai san sada hawaye ya suraro masa ba ahankali yaja hannun sa yaraba dana kamal yafara takawa da sauri sauri
cikin ƙara kamal
yace "daddy karka tafi
ka barni daddy inason narayu cikin yan uwana daddy daddy.......
Daddy a cikin mota sai da yasha kuka yaja tissue yagoge hawayen sa sannan yabawa driver umarnin yaja wai kamar shi justice Abdulmajid ne yau yazo ziyaran ɗansa a prison gyaɗa kai yayi afili yafurta Allah humma'ajirni fimusifati".
juyowa driver yayi yace "Alhaji ALLAH de yafito mana da kamal lafiya Allah dan cikar sunayen sa tsarkaka".
"Ameen Lamido". jinji Daddy
*Nasir asbiti*
shigowar wani babban Alhaji wanda da gani yagama taka ƙasa ne ya dakatar sa doctor Ibrashim daga barazanan daga Nasir daga doctor din har