Showing 27001 words to 30000 words out of 155717 words
Chapter 10 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
de idan bata motsa jikin taba dan sai sun k'ada komai na Nasrim me kyau ne
Zahra ce ta shigo ihu tayi tana cewa "kai Nasy kingan ki kuwa".
sake kallon kanta tayi a mirror tayi murmushi tace yawwa "Zar dan Allah kizo ki zabani kayan da yadace dani nasa doguwar riga yar Dubai da saudia da sinigal yafi kala goma duk basu min ba gashi Mama ta hana ni saka English wears kawai atakura mutum da manya kaya"..ta k'are maganan tana turo baki
dariya Zahra tayi tace "mu meyasa bata hana mu ai yanayin halittar kine ya janyo miki shi yasa a kullum nake taya Ya Agrif murna wllh yayi mugun tsintar dami akale wai ni da ake cewa mutum tara yake bai ciki goma ba to ni kullum tambayar da nakewa kaina ke meye naki bai cika ba".
kallon ta Nasrim tayi tana cire yatsan roban da yake hannun ta tanuna mata tace "kinga abin da bai cika ba kuma bayan shima akwai da yawa".
Zahra ta kalli hannu tace " wllh bayan shi bawani abun in kuma akwai nuna".
murmushi Nasrim tayi tana maida yatsan kan manu niyar yatsan ta na hagu tace'' yanzu de time ya kusa ki ki bani shawaran".
Zahra tace'' ni wanne ma zaki sane yawwa kisa wannan
Swice lace din nan wanda mommy ta siyo mana a Dubai yellow ki d'aura masa wannan blue after idan bayyi ba sai mu duba wani".
hakan ko ahayi sosai kayan ya mata kyau Humairah ta shigo tana ganin ta tafara mata wak'a ayee riii zobiya naira zo biya naira zalla Yaya na kaji dadin ka".
juyi Nasrim tayi tace '' nayi bazai kushe ba".
Zahra tace'' wane shi ni ina tsoron ma ki masa kwarjinin da zai kasa cewa yana So".
take yanayin moment dinta ya canza
ta juya tana d'aura agogon ta na farin gol
Humairah tace'' ke wasa take miki kisa aranki za abaki wanda ki keso".
"bana son irin wannan wasan ai ni yau kam ko bai furta ba ni zan furta wai ni yawwa Ina Izza ta shiga yau ".?
ta k'arashe maganan da tambaya
Zahra tace'' ai jiya da taje wajen Baban ta bata zo da wuri ba har mukayi bacci ina ga ramuwar baccin take".?
tabe baki Humairah tayi tace'' can ta matse mata ba wani bacci da take shegen zurfin cikin na ta ne ya motsa tana nan akwance sai juyi take ko breakfast bata fito ba".
dama Nasrim tun asuba tabar d'akin data gama kuma direct dressing room ta shigo
basu Ankara ba suka ji tsayuwar motocin
da sauri Nasrim ta k'arasa jikin window tana ganin drive ya fito ya zaga ya bude back seat din wani irin dafa k'irjinta tayi tana jin yanda yake bugawa kamar tayi fuka fuki ta dira ta finciko sa take ji shiko kamar yasan tana jiran sa sai da yadan b'ata lokaci ya ziro k'afar sa daya wanda yake cikin b'akin socks me shak'i sake ziro dayan ma yayi daga nan kuma ya mek'e gaba daya yafito da gan-gan jikin sa wow ba Nasrim ba ko wacce macce dole ta so wannan guy din dan bashi da makusa sa ta ko ina dogone b'aki amma ba bak'i can ba kalan fatar sa irin na Nasrim ne har kusan kaman suma suna yanayi sosai kusan duk gidan sunfi kama dashi da ganin yanda fatar sa take shek'i kasan ba k'ananun kudi ake kashe masa ba bakin kilas ne a idon sa saide yanayin sa ba kamar na da ba yau ba far'a'an nan da haba haba da mutane kana ganin sa kaga me damuwa Baba Yakubu ne yafara masa kirarin da yasaba yace "barka da zuwa Alhaji Haruna sarkin tsafta Haruna kan d'aki bane hannu daya ya dauka ba a kaida d'a nabiyu a gidan 3.A. full nd'ororo an baka kabawa yaran baya Haruna kafi k'asan randa yawan wanka kai jarumi kake meson mutum kake".
hannun kawai ya jinjina masa ya fara takawa wanda da dane yadin ka wahe baki kenan yana nagode Baba Yakubu dan ko Nasara idan baba Yakubu ya fara masa kirari sai yasa shi murmushi balle Agrif sarkin fara'a ahankali yake takawa
Nasrim tayi saurin damk'e hannun
Zahra da hannun ta daya dayan kuma ta dafe k'irjin ta tace'' Zar gaba na faduwa yake"!
Zahra tace''
"Kinji kifa meye abin faduwar gaba bayan gashi gaki yazo lafiya zo musauk'a ya shigo".
Nasrim tace''kema kinsan part din Hajja zai wuce kibari sai ya shiga sai muje".
Agrif direct part din Hajja ya wuce kamar yanda al'adan gidan yake duk wanda yazo daga tafiya a nan yake sauk'a tun kafin ya k'arasa shiga parlourn ya fara rage suit din sa yarik'e a hannu sai farin riga da yabari
Hajja tana zaune akan wani lallausar kilishin ta idon ta cikin farin glass ta sunkuyar da kai tana karatun wani littafin da yagama tafiya da hankalin ta k'afar ta akan tum-tum Barira tana shafa mata man zafi ya shigo ciki-ciki yayi sallaman dan haka ba wanda yaji balle Hajja da tayi nisa a karatun ta har ya k'araso ya cilla kansa kan kujera there'siter bata jiba sai da Barira tace" barka dazuwa yallabai Agrif".
hannun kawai ya d'aga mata
sai asannan Hajja ta d'ago ta kalleshi ta tabe baki tace'' zama da mad'aukin kanwa dama ance shiyake kawo farin kai karasa halin d'auka sai na wannan bayahuden sallama ya gagare ka Haruna".
ta k'arashe maganan tana cire glass din idon ta tare da ajiye littafin
tsaki yayi yace". ko nayi sallaman amfani me zai miki dan Allah Hajja me kike nema a duniyar nan ne yanzu littattafan addini yaka mata agani a hannu ki ba wai novel ba ko mu jikokin ki bama karantawa".
"Haruna ka kiyayeni kar kaga ina raga maka saboda girman sunan ka awajena haka nace maka bana karanta littafin addini kalli can duk sune yoni ban dama Hajiya sabuwa tacemin littafin yayi dadi da ma'ana Wllh rabona da nayi karatu har na manta idan bana addini ba".
sake jan tsaki yayi yace kinji fa Hajiya sabuwa fa baza ta wuce sa ar Ummu ba amma da ita kike k'awancen karatun litafin soyayya".?
"Eh fadi kan ka tsaye ta dalilin littafin ma kuka san juna ko haramun ne labari nefa tamkar ta tsuniya yake gashi kuma kewa yake daukewa mutum meye a cikin jin labari inba nishad'i ba Hjy Bilkisu Funtuwa ta girmeni ma ba littafin ma take rubutawa ba k'arewa ma wata rana ai sai labari kuma zan bari gaba daya ma".
Agrif kwantar da kansa yayi ya lumshe idon sa yana sauraron yanda zuciyar sa take bugawa anya ? bayyi kuskuren barwa Nasir soyayyar da yarayu da shi shekaru shatara ba kuwa anya yayiwa zuciyar sa adalci kuwa to ma meyakai shi wannan gan gancin
Hajja yaji ta katse masa tunanin da cewa "to ai sai katashi min kaje inda ake zabbarin ganin ka an hada maka duniya kaje kai kam ai kaga ta kan ka yarinya rawan kai da kisisina tamkar uwar mata wannan ai idan Amina bata tashi atsaye ba ita ta haifawa d'a nasan juyaka zatayi sosai kamar waina acikin tanda".
shide bai kula taba ya mek'e dama hakan yake buk'ata dan adole yashigo dan kar ya tsaba doka dan yasan sai ta tara family meeting akan yazo bai sauk'a a ban garen taba
ahankali ya mek'e yafara tafiya yaji nata cewa"ikon Allah ni Lami Haruna da abinda yake damun ka je kagama cin abincin kazo kasameni".
Direct part din mommy yayi Yana tafiya very slow ma'aika suna ta masa sannu amma ko hannu yakasa d'aga musu har ya shige ciki
a hankalin ya murda handle din kofar ajiyar zuciya ya sauk'e da wani irin k'amshin d'akin ya ziyaci hancin sa idon sa yafara warewa akan komai na d'akin ko a ina yaga gyaran Nasrim zai gane tsaftan ta ya ban banta dana kowa afili yace "anya idan na cireki acikin rayuwa ta zan iya sarrafa shi tabbas inde zan cigaba da jin abin da nake ji yanzu to nan gaba kad'an za arasani ni nasan rayuwata na sadukar ba soyayyar kiba
jikin sane ya k'ara very slow a lokacin da ya tura kofar bedroom din nan ma k'amshin sa da ban dana parlourn kai tsaye bathroom ya wuce ya sakar wa kansa shower ya dafe bango yana sauraron yanda ruwan yake ratsa jikin sa yajima a haka sannan ya d'aura towels yafito adan gurguje ya shirya cikin k'ananan kaya t-shirt bak'i me dogon hannu da wando maroon ya dauki wayan sa ahankali yake taka steps idon sa akan wayan sa yana karanta message din Nasara yana sake jadda da masa alk'awarin su dan tun yana jirgi yake ta tura masa tsak'o baya Ripley ga ya dameshi da kira ba ya d'agawa bai taba ganin Nasir ya damu akan abu haka ba wannan shi ya tabbatar masa da lalle Nasir ya damu da Nasrim wannan shi yake k'ara k'arfafa masa gwuiwar ya bar masa kawai Allah yasa hakan shi yafi alkairi
zai shiga part din Ummun sa yaji anan shirin ta da i'k'aman sallan zuhur bayan yadowo daga masalaci yashiga yasamu Ummu zaune akan sallaya sai da yajira ta shafa ya tsak'o k'asa cikin ladabi yace "Ummu an wuni lafiya".?
"lafiya lau kadawo lafiya"?.
jin jina kai yayi
"tace'' to yayi kyau abinci fa.?
sosa k'eyar sa yayi yana murmushin da kana gani kasan a iya fuska ne
itama murmushi tayi tace'' dama nima na fad'a ne kaje inda aka hada maka delicious".
mek'ewa yayi yana cigaba da murmushi
Ummu tace'' amma kamar akwai damuwa ko kafin kazo kunyi abin da kuka saba ne kai da mutumin naka ko?". bai juyo ba ya girgiza kai yana cewa
"a a Ummu bakomai".
jin jina kai tayi tace'' ai dama kai da Nasara ba mejin kan ku kuma hakan yafi duk rintsi kuyi kokarin rik'e tsrrin junan ku dan idan kuka tona a sirin juna tanan shed'a'nun mutane zasu samu nasaran raba kan ku".?
"to Ummu mun gode in sha Allah ba komai kuci gaba dayi mana addua".
tace'' muna cikin yinta kullum Allah ya hada mana kan ku ya muku albarka yabaku zurua ta gari".?
"Ameen".
yace tareda k'arasa ficewa yana karanto addua azuciyar sa ta yanda zai tunkari Nasrim da salon
bakin sa d'auke da sallama ya shigo main parlourn Mama durk'usawa yayi ya gaida Mama ta amsa tana masa kirari "lafiya lau Baba Haruna gafi k'asan randa yawan wanka".
hawa kujera yayi yana murmushi yace", Hjy Mama me dinbin iyayi a ina kika zamu yaro haka''?
ya k'arashe maganan yana shafa kan wani yaro da baifi shekara shida ba
tace "la Agrif daman baka san Haydar ba ai d'an wajen marigayya Zainab ne yafi sheka 3 agidan nan ni aka bawa".
Agrif ya bude baki zayyi magana yaji sautin takalma kos kos ahankali bakin sa d'auke da addua ya d'aga kai wani irin bugawa gaban sa yayi tana tsakiyar Zahra da Humairah ajere suke takawa wajen sauk'owa daga steps din cikin sauri bai san sanda ya mek'e tsaye ba baki bude da gudu Humairah ta rungume shi yana murmushin bai san lokacin da yace "wahhh my heart kinga zata karya miki ni ko".
Nasrim tace'' Allah Yaya tunfa dazu muke ta faman jiran ka".?
"Tode yanzu ba gani gaban kiba ai sai yanda kikayi dani".
ya k'arashe maganan yana cire Humairah ajikin sa
yace "Hummee ke bakya girma kinga Nasrim ta dena fodowa mutane jiki ita dau girman".
dariya akayi har Mama
sannu dazuwa suka masa ya amsa yana shafa cikin sa idon sa akan Nasrim yasake cewa nifa welcomen din abinci kawai mutum zai min ya burgeni".
Nasrim tace'' ai Yaya baka da matsala da wannan".
tayi maganan tana jan hannun sa wani slowly kasala yaji ya rufeshi a sanda sanyaye kamshe turaren ta ya doki hancin sa jin tattausar tafin hannuta cikin nayi yasa gashin jikin sa wani irin mek'ewa har sai da yaji kamar yafadi a hankali yazame hannun nasa cikin nata ya sunkuyo dai-dai kunneta yace my sweet sister idan kina irin wannan gan gancin na rab'an mutum fa za'a iya samun matsala ke baki san daban kike da kowacce mace ba".
ya mutsa fuska tayi tayi gaba a slow yabita abaya gyara masa kujera tayi tace'' Bismillah ko".
har yanzu face dinta ba walwala
zama yayi idon sa akan ta ita kuma ta fara budude masa tana zuwa kan tuwon *d'alayi* yace" yawwa sis sannu da kokari Allah yabiya ki zubamin *d'alayi* ko sai kunun *mordom* sai *garabiyya* da dendero yan komin *denderon* na fara da dashi".
Humairah da Zahra dariya suka fara sukace dama ai munsan duk wannan shidimar baifi kaci kala biyar ba".
shide bai ma jisu ba ya shagala da kallon santala santalan y'an yatsun Nasrim wanda yasha jan lalle
sosai yaci tuwon d'alayi da miyar ganyen daddawwo kusan shi yacika masa cikin
ya d'ogo yana kallon Nasrim yace my heart missing you so much nayi missing girkin ki".
har yanzu ba walwala a face dinta tace' "ok girkina kawai kayi missing bani ba ko".
yana murmushi yace" am sorry I really nafi yin missing din girkin ki ai ke kullum muna tare a waya ai kema bakiyi missing din nawa ba tunda daga zuwana kin fara min fushi".
cikin turor baki tace ''ba kai ne kace ni ina da ban banci da sauran mata ba towai ni meye ban bancin nawa haka fa Yaya Kamal da ya Abbaty da ya Aiban ma suke min zasuyi hugging kowa ban dani ko kusa dasu nazo sai sudin ga ja baya".
cikin sanyin murya yace"bazaki gane bane Nasrim".
yajuya yana kallon su Humairah ta suke ta ciye-ciye yace to sarakunan ci mu zamu wuce ya mek'e tsaye yana cewa sister zokiji
direct parlourn sa suka suce
bayan ta zauna akan kujera one'siter shikuma ya zauna a wanda yake fuskan tarta there'siter cikin dauriya yace" da gaske bakiyi missing dina ba ko.'
yayi maganan can cikin mak'ok'oron sa cikin wani irin amon da ya ruguza duk kan garkuwar jikinta
ido ta zuba masa bata san yanda zata masa bayani yanda yake acikin yarayuwar taba
cikin sanyin murya tace" Yaya I really missing wllh bana second 10 ban tunoka cikin rayuwata ba bacci nishad'i duk sai da tunanin ka yake tasiri ba sai nace kai daya ne a Raina ba nasan kasan da haka tun jimawa bani da burin da yawuce n....
da katar da ita yayi dacewa
nasan da haka NASRIM ni anawa ban garen har yafi yanda kike jina ina ga nafi mommy da daddy sonki shiyasa ma nake son yazama kece ta farkon Wanda zan furtawa farin cikin abinda yajima a rayuwata Nasrim najima ina cemiki inason na gaya miki abu mai mushimmanci to yanzu lokacin yayi Nasrim ina neman soyayyar y'ar uwar ki k'awar ki wato IZZATU ke nake son ki sayo min soyayyar ta dan kinfi kowa kusanci da ita Nasrim Ina son Izza ta zama matata uwar y'ay'a na dan All......
awani irin razane ta m'eke jitayi kunnuwar ta da kwakwawan ta sunto she dif
shima me k'ewar yayi yana sun kuyar da kansa
cikin rawan murya yace" what happens to u
kamar bakiyi barin ciki da abin da nazo miki dashi ba ko batayi ba? Wllh idan kika ce batayi bana barta har abadan ki canza min da duk wacce ki kaga tayi".
itama cikin rawar murya lip dinta na rawa tace'' seriously Izza kake son"?
cikin cool voice yace " sure".
"Yaya kasan me kace kuwa Izza fa".
baya yayi ya jefa kansa cikin cushion ya lumshe idon sa yana danne wani abu da yake taso masa can
yace" Nasrim shifa baki dan aike ne duk abinda ya furta to daga zuciya ne
Sure ina son ta".
Nasrim ja tayi da baya da baya har taje tsakiyar parloun tajuya dawani irin sauri ta fita shiko daya ke idon sa alumshe yake bai san ta fita ba dan yasan a yanda zuciyar sa take idan yaci gaba da kallonta komai zai iya faruwa jiyake kawar yajata ya gungumo ta yake keji
Nasrim a dai-dai babban parlourn suka kusan cin karo da mommy da shigowar ta gidan kenan daga wajen aiki da gudu ta k'arasa ficewa ko mommy bata gani ba amma taji murya ta tana cewa lafiya
bata juyo ba kai tsyaye part din Hajja ta nufa bata tsaya a k'asa ba tawuce sama Hajja da take zaune da wasu bak'i tana ta fad'an ke marar hankali wannan gudun fa kin ibi k'ugu kamar wata uwar mata".
bata kula taba ta wuce bedroom din Hajja direct zubewa tayi akan gadon Hajjan
har yanzu kuka yak'i zuwa mata wani irin bugawa zuciyar ta take mata gaba daya tunanin ta ya d'auke cikin k'an k'anin lokaci kanta da jikin ta yad'au wani irin zafi wani irin kar karwa takeyi
Hajja da tama manta da Nasrim ta shigo sai da tashigo alwalan magariba taga mutum kwance akan gadon ta sai wani irin karkarwa takeyi ja Hajja tayi da baya tace
"la'ilaha'ilallahu me zan gani ni Mariya dama wannan y'a tana da mutane boye ban sani ba nabari ta shigo min dasu d'aki dan mugun ta har kan gadon bacci na yau nashiga ukku a gidan nan inane gun kwana na na gadona tun na Abdulsamad na hana acan zamin wani dan idan nazo kwanciya kullum sai na tuna dashi na masa addua Allah sarki da hannun saya kafamin gadon nan kafin ya kwanta dama shine zaki shigomin da mutanen boyen ki
Ina Barira Barira".!
ta k'arashe maganan tana kwallah wa me'aikin ta k'ira amma tana sake ja dabaya wai tana tsoro
da sauri Barira ta shigo tana
cewa " Hajja Mama lafiya".?
''ina ko lafiya an shigo min da masifa".
ta nuna Nasrim da bata cikin hayyacin ta
da sauri Barira ta hau gadon tana dafa Nasrim ta zaro ido cikin tsoro tace'' Hajja wani irin zazzabi ne ajikin ta kamar garwashin wuta" .
Hajja tace'' zazzabi ko far fadiya kiga yanda take girgiza gadon nan ba ita daya bace Kira uban ta ya nemo me ruk'iya".
da sauri Barira ta fita takira Mama atare suka shigo dasu Humairah Mama kuka tasa a sanda ta dafa jikin nata haka zahra da Humairah jiki na rawa Habiba takira family doctor din su
Dr yana auna BP dinta yace" subbahanalla Hajiya ya akayi jinin