Showing 6001 words to 9000 words out of 155717 words

Chapter 3 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

672

take balle su Kamal da Agrif ko abu aka ba da baya wajen to ba za su dauka ba sai sun jira ya zo ya gama jan ajinsa ya d'auki nashi su d'auka
har ga Allah Abdulsamad ba ya son halin d'an nasa sai de ba shi da lokacin zama da shi wani halin nasa ma bai sansu ba tunda bai fiye zama a k'asan ba. Baba yabubu me gadi kam yaron tausayi yake bashi kuma bayan mommysa ba wanda yasan halin Nasir sai Hajja da yabubu me gadi.

Yau ma kamar kullum sun taso daga islamiya duk kansu ukku kowa akan kekensa a tare suke tuk'awa Bodyguard dinsu ne a gefensu sun sanya su a tsakiya Agrif kam wani fisari yake ji sosai tun a makaranta amma bai isa ya wuce Nasir a gaba ba dan ahankali suke tuk'awa kuma a tare ko ataku daya wani bai isa wuce wani ba har suka zo bakin get Baba Yakubu yana ganin sa yafara masa kirarin da yasa ba
"A a barka da zuwa NASARA nasara ko gani kafi mutum NASARA me wuyar badanci Nasara goshin jirgi me wuyar karo kafe kekensa ya yi daidai inda Baba Yakubu yake Kamal ma yatsaya cak shida bodyguard din shi ko Agrif fisari ya gama matsansa dan haka da sauri ya masa kan keken alaman ya yi gaba cikin wani irin tsawa Nasir yace
"What Agrif".................

Ba Agrif da ya gama jika jikinsa da fitsarin b hatta bodyguard din da Baba yabubu sai da suka tsorata dan yanda yayi tsawan kaman ba yaro ba



*To masoya mu je zuwa don ganin FURUCINA da wane salo yake tafe kar ku manta taku Batul mai baku kala ce*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURRUCI NA NE*

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*


```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURRUCI NA NE*


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_Domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


*Page 2*



"Agrif fitsari kake yiwa mutane a wando? Banza, wawa, jaki, dabba. Wani irin kuka Agrif ya fashe dashi ga kunya ga tozarcin zagin Nasir, yayi jifa da keken ya shiga part ɗinsu da gudu cikin tsananin kuka.
Kamal ya fashe da dariya irin na yara shima ya sauka a keken ya barta a nan shi ko uban-gayya wani dogon tsaki yaja shima yabar nasa keken ya shiga part ɗinsu. Su kuma bodyguard ɗinsu suka dauki kekunan suka kai ma'adanar sa
kamar yanda al'adan gidan yake
bayan Isha kowa ya haɗu a dining table har Alhaji Abdulsamad da yaran suke kira da Abban mu yana wajen, dan idan yana ƙasar yana kokarin yaga ya zauna cikin familyn sa. Abdulraham kuma suna kiransa Abu sai Abdulmajid Dady, Amina ummu Aisha Mama Fanna mommy. Mommy ce ta hanga ta ga ba Agrif a wajen cikin mamaki tace "Ummu yau ina Agrif ne".
"Amina tace "ai yau abin akayi a hanyar makaranta da kuka ya shigo nayi nayi yayi shiru yaƙi yanzu haka har zazzabi yazo masa nabashi tea da magani ya sha ya samu bacci."
Mommy ta kai kallonta wajen Nasir da ko ajikin sa har ya fara cin abincin sa tana son tayi masa magana dan tasan dashi akayi faɗa amma tasan tana masa magana yanzu zaiyi zuciya yabar abincin, kuma Abdulsamad yana wajen tasan shima faɗa sosai zai masa dan haka ta rufa asirin, dan haka tayi murmushi tace ayya Allah sarki yarona lalle yau gidan nan ba lafiya, Baban gida guda akwance?"
Aiban yace "Mommy ya Nasir ne ya masa duka yayi fitsari a wando".
Abba yace" duka kuma? Nasir ban hanaka faɗa da yan uwan kaba dama baka daina ba?".
Ko ɗaga kan sa baiyi ba kamar ba dashi ake ba Alhaji Abdulsamad ya fusata sosai yace"Kai NASURUDDEEN ba da Kai nake ba?"
Abu yace "haba Alhaji ka bisa a hankali mana kasan fa Nasir baya son hayaniya kuma ni nasan baya faɗan rashin gaskiya, san nan ko kashe shi zakayi tunda baiyi niyar magana ba to ba zai yi ba abin da ya faru ya wuce."
Abba yace" haba Malam bakwa ganin yanayi yaron nan ne idan yatashi a haka bazai mana daɗi ba. Yakamata a din ga tsawatar masa dan dai ni ba mazauni bane.
Ya juya ya kalli Dady Abdulmajid yace "alk'ali ya kamata kusa ido akan yaron nan fa wlh akwai abubun da yake sam bana gamsuwa dasu akan sa. Yaro sai yanda yayi damu? Yakamata yasan mu ne gaba dashi."

Murmushi Dady yayi yace "zai daina."
wani dogon tsaki Nasir ya ja tare da ture cup ɗin tea ɗin tare da gangara shi hannun Aiban. Da yake yana saman tablen ɗin yasamu yanda yake so dan dama yayi ne dan ya ƙona Aiban da shi ne ya gayawa Abba abinda ya haɗasu da Agrif.
Wani irin ihu Aiban ya callara yana yarfa hannu da sauri Abba ya cafko Nasir ya figo wayan da yake jikin DBD yadinga sula masa ko tari baiyi ba bale yayi kuka kawai wani irin huci yake da sauri Hajiya tashiga tsakanin su. "Abdulsamad kashe tilon ɗanka zaka yi akan abinda ba laifinsa bane? Ai shi Aiban din shine munafiki ai duk inda mutum biyu sukayi faɗa sai ansamu laifin kowa. Da yake Agrif ɗan uwan sane yaki faɗan laifin sa, sai na Nasir ai gwara da ya ƙona munafikin, ai ni da nasan haka Aiban zai zama munafiki da ban sa masa sunan ubana ba suna mai daraja Habubakar w....
Abba yace ''haba Hajja bai kamata ana barin yaron nan yana taka kowa a sanda yaga dama ba, ni idan aka min haka ba'aman adalci ba, ni ina can wajen da zan rufamana asiri ni da ku da dangin mu. Ɗana yana cikin matsala yanzu ne Nasir yake lokacin da za'a nuna masa dai_dai da ba dai _dai ba saboda gaban sa."

Hajja tace" amma sai ka kamashi da duka sai kace kisa yayi?"
Abba numfasawa yayi ya jefar da wayar, yayi hanyan waje Mommy da Mama suka kama hannu Aiban suna ganin kawai shagwaɓa ne da gulma irin nasa ba wani ƙonewa da yayi. Dan shayi ya huce mommy tace "sannu Aiban yanzu zai daina ciwon ko?"
Ummu tace "kai Dr. kinsan fa halin Aiban dama son asani ne bawani. Kuma nima ruwan tea din ya taɓani ba wani zafi".
Ai ko Hajja tafara masifan to azo a kai mata jikanta asbiti, Abdulsamad ya fasa masa jiki. Mommy ma da taga jikin nasa ranta ba karamin bacci yayi ba tace "Hajja kawoshi muje na shafa masa magani".

Cikin bacin rai tace "gafara can ba a gaban ki yarinƙa jibgar sa kamar an aikoshi daga sama ba? Ai da ke kika haifeshi da baza ki bari hakan ta faru ba baki san ciwon haifuwa ba. Ɗan da shikenan a wajen Abdulsamad har yasa hannu ya dake sa, nima nasan hanyar asbitin ba dole sai ke ba. Idan kinga Nasir ya koma ɓangaren ku to Abdulsamad ne yabar ƙasan nan." Ba Mommy ba hatta Mama da Ummu basu ji daɗin abinda Hajja tace ba duk da ba wai yau ta fara faɗa ba.
Mommy idon ta ne ya wani irin cicciko wa ita ba wai gorin haifuwar ne damuwarta ba yanda Hajja take nunawa kamar ta gaza a kula da Nasir shine damuwar ta, bayan yanzu ita a duniya ba abin da take so fiye da Nasir ko da yara ɗari zata haifa dukkan su batajin zasukai darajan Nasir, kuma indai ciki ne yanzu ma tana dashi kuma bata jin aranta ya kai Nasir. Saurin ficewa tayi dan bata son hawayen da take ɓoyewa ya zubo.

Taɓe baki Hajja tayi tace" jita gwalmaɗaɗɗiya dama wannan ƙugun naki ina zai iya daukan ciki mace kamar muciya duk ƙashi, abincin cikin ta ma a ƙa'ide yake wai ita likita. Aure kusan shekara bakwai bako ɓari. Yo ina ta tsaya taci ta koshi balle cikin ya zauna awan nan shafaffen cikin nata tubabbiya kawai"
suma sauran mata haka suka zame rai a ɓace suka fice suka bar Hajja tana ƙolotun kiran sule driver yazo ya kai mata jikan ta asbiti.
Ita kuma mommy tana shiga part ɗinsu direct bathroom ta shiga ganin Alhaji a zaune da laptop ɗinsa akan gado bata bari ya gane yanayin fuskar ta ba, kai tsaye ta wuce bedroom kwanciya tayi lub cikin bathroom ta dai_daita shower a dai-dai kanta, ta jima tana tariyo rayuwar ta, to ina mahaifin ta? Ina dangin sa tasan dai duk inda suke musulmai ne me yasa shi bai ɗauke ta ba? Da duk wannan abin bai faru da ita ba, da ba'a kira ta tubabbiya ba.

Allah sarki mommyn ta Emeka tasan tana cikin damuwar rashinta tunda bata da wani ɗa sai ita anya lokacin zuwanta wajen uwar ta baiyi ba kuwa? ko ya take uwa uwa ce kuma tana da haƙƙi akanta, taja dogon lokacin tana tunanin tana shafa cikin ta tasaki murmushi a fili tace Hajja "Fanna ba juya bace kwanan nan zaki sheda hakan.
Ajiyar zuciya ta saue lokacin da taji knocking ɗin kofan bathroom ɗin ya tsanan ta tasan Alhaji ne dama tasan dole zai biyota yace zasuyi wankan tare ita kuma tana son keɓantuwa shiyasa tasa sakata, bude ruwan tayi ya fita ta tara na dauraye jiki ta dauraye jikinta ta ɗaura towel ta bude kofar, tsaye ta samesa daga shi sai boxer yana tsaye.Suna haɗa ido ya kama kunnen sa alaman ya tuba".
murmushi tayi tace"kayi wani laifin ne ai kai baka laifi in makayi abisa kuskure to tun kafin kayi laifin an yafe my heart hubby".
Murmushi yayi ya kamo hannan ta suka ƙarasa wajen mirror ya zaunar da ita akan seat ɗin gaban mirror yana kallota ta cikin mirror yana murmushi yace "dan me akayi mudubi".
murmushi tayi tace dan ya haska kyau ko muni".
Murmushi yayi yana shafa fuskanta sannan yana kallonta
ta cikin mudubin yace "amma gaskiya nasan shikansa budubi yafi tsoron masu hasken fata irinku saboda kinga ke kika haskaka mudubin nan ba shi ya haska ki ba. Ni Abdulsamad inason wannan fuska me cike da Kamala da annuri damuwa ko ɓacin rai da fushi bai isa yasa annurin sa gushewa ba. A yanzu fa nasan kina cikin fushin dukar miki ɗa amma gashi fuskar bai nuna ba nagane ne kawai a aikace mun saba wanka tare shine da kina fushi kin barni kin shiga kinyi".
Ita ma murmushi tayi tare da daura hannuta akan nasa dayake shafa mata fuska cikin salonta na jan hankali tace''
nagaya maka bana fushi amma kai ma kasan dukan yayi yawa ko".
kujera ya jawo yazauna yana kallon idonta
'"idan akayi duba da laifinsa baiyi yawa ba Dr inda ya ƙona Aiban fa".?
"ai laifin Aiban ne shi ina ruwanshi ko uwar shi batayi magana ba Kamal da akayi gabansa baiyi magana ba sai shi yaron ya rena Son sosai shiyasa ma Son yace sun dena tafiya tare yanzu ko boko Aiban motar sa daban kullum shari'a. Shi ne nagaji na raba su duk da basa taren ma bazai daina haɗin faɗan ba waye baisan tsakanin Nasir da Agrif ba ko sunyi faɗa basa 10minutes sun shirya. Yanzu da Agrif ya fito dining da sun shirya bawanda ya sani ba...

Ya ce" to shikenan doctor shidama me ɗa fa baya ganin laifin ɗansa. Koni da nake dukan sa ji nake kamar jikina nake duka balle keda aka baki amanan sa".
Murmushi tayi tace '
"ai kaima amanan aka bar maka shi".
Ya ce"ba kamar ke ba, ni wllh Halima bata cemin Nasir amana ba kullum sai nayi tunanin meyasa tayi hakan amma inaji a jiki na kamar nima bazanyi rayuwa me tsawo tare dashi ba shiyasa batace min amana ba. Dan Allah FATIMA ki riƙe min amanan Nasir kamar yanda kika saba sannan naji duk kalaman da Hajja ta jefeki dashi, Hajja ta manta da rashin haifuwa da yawa ko a haifi daya ko biyu a zuri armu ne ba laifin ki bane. Babana shi kadai iyayen sa suka haifa sannan shima Baban sa wato kakan mu su biyu ne. Kakan mu da Kawu Haruna me sunan Baban haka muma daga kanmu ba kari kinga daga mu ne...."

"A a my hubby daina cewa haka yanzu haka ina ɗauke da jinin ka na watanni 2 da sati biyu naso nayi surprise dinka ne." Dr
Are you sure?"
"Very sure my heart".
"Dr Dan Allah ki cire maganan wasa"
Murmushi tayi tace shekara bakwai ka taɓa jin irin wannan wasan a baki na duk yanda kake nuna son kaga mun samu ka manta nakai maka ziyara a China, wata biyu kawuce paris ni nazo gida idan kayi lisafi dai_dai da lokacin cikin zai nuna maka wllh tun a chana na gane amma nayi shiru dan nayi surprise ɗin ku gabaɗaya".
A hankali ya sunkuyo ya manne ta a jikin sa yace" fatima batul kin bani farin ciki tabbas ke ɗin haske ce a rayuwata dole nayiwa Allah godiya. a gobe dayawan ma buƙatan da suke cikin garin kano zasu kwana da farin cikin Alhamdulillah! Allah yamin komai Allah yabani matar da nafi so a rayuwata wanda tun ina yaro nake kwatanta irinta a Raina, yabani dukiyar da ban san iyakar taba yanzu kuma yara Alhamdulillah! ni kam ba dan kar nayi sabo ba da sai nace ina ma ba a wajif ta mutuwa ba dan nikam Allah ya shimfidamin rayuwa a duniya kamar bazan mutu ba amma nasan hakan saɓo ne yarabbi ka Gina min lakhirata fiye da duniya ta. Ya rabbi ka dora ni kan hanya madai daiciya, dukiyar da na tara kasa yazama silar ciyo na zuwa aljana ba ya kai ni ga wuta ba. Allah yasa yara na da zan bari su tafiyar dashi ta hanya madaidaiciya."

"Ameen tace tare da ɗaura hannuta kan nasa da yake yawo a cikin ta
ta ce "my Son yana wajen Hajja nasan kuma bazai yarda ya kwana a can ba duk hankali na yana can".

Murmushi yayi yana shafa cikinta
yace"niko hankalina yana nan."
da sauri ta ɗago kai tana kallon sa da alaman ɓaccin rai, harshin sa ya kai kunneta yana lasa yace "kina yaudaran kanki fuskan ki fa baya nuna ɓacin rai ko damuwa a kullum cikin annurin take".
In dai zaka taɓa my Son to sai na fasa kawo maka ɗan adawar namu".
dariya yayi ya ce" faɗan Allah ne ai ba ikon ku bane ai kwara a kawo masa ɗan a dawar ko ya daina taɓara. Wllh taɓaran Nasir dan ganin shi ɗaya ne yanzu Agrif dayake da ƙannai Aiban da Abbaty ai bayayi ga Aisha ma data ɗauko ƴar riko Zahra ai Kamal bayayi, shi ko kullum abin jarirai yakeyi har shekara bakwai sai dai kimasa wanka da kanki kuma baya yarda yan aiki su masa ko wando bai iya sawa ba nasan idan ya samu ƙane zai san ya girma".

A ɓangare hajja kuwa daƙyar ta lallaɓa mutumin ya yarda yayi bacci. Bacci yayi rigimar a kaishi wajen Mommyn sa.

Da safe duk an haɗu a dining za ayi breakfast, su Mommy da Abba sun makara har anfara ci suka karaso cikin raha. Abdulmajid yace" kai Abba amma ko dai jiyan nan....
sai kuma yayi shiru yana dariya.

Abba ma darinyan yayi yana gyarawa mommy kujeran ta yace ƙarasa mana karamin marar kunya."
Duk akayi dariya, mommy ko idonta akan kowa ganin bata ga ɗan taba har tabuɗe baki zatayi magana taji Agrif yace" mommy Abba Ina kwana Ina my bro?".

Mommy amsa gaisuwan tayi tare da kallon Hajja da alaman tambaya kafin Hajja tayi magana sukaji Nasir yana cewa "to ni ina ruwana da kai naga Mama ce tace kar musake shigowa arabe shine dan na tsaya na gaida baba Yakubu yayi gaba, dan zan maga magan kawai ka saki fitsari shi ne Aiban yacewa Abba wai nayi faɗa dakai ya min duka".
Agrif yace " to bakai kayimin tsawa ba fisarin yafito ban sani."

dariya duk sukayi ban da Nasir da yaci kunu Ummu tace "Allah sarki NASARA ai dama nasan ba laifinka bane shima Abba dan ba ma zauni bane baisan halinka ba baka fadan rashin gaskiya haka ne kam kamar yanda Mama tace kudun ga shigowa tare ku haɗa kan ku kar a ganku a rarrabe mugayen mutane zasu iya samun nasara akan ku kuji ƴan albarka".
Yes! suka ce
Shi kuma Nasir durƙusawa yayi har ƙasa kamar yanda suka saba yace "Daddy Abu Ina kwanan ku".?

Lafiya suka amsa suna tambayar ya jikinsa bayyi magana ba yaci kunu
yana cewa "Mama ummu ina kwana?
Mama tace "Nasara ko gani kafi mutum NASARA me wuyar ɓatanci ya jikin naka?"
ya sake yamusa fuska yayi bai yi magana ba,
Mommy ganin Nasir ko inda take bai kalla ba yasa cikin sanyi murya tace
"my Son".
ɗagowa yayi ya zuba mata dara-daran idon sa da suka gama cikowa da kwallah yayi
yana juya idon alaman yana son mai da kwallan, bai amsa ba har ya maida kansa ƙasa
ta sake cewa "my Son fushi kake damu".?
girgiza mata kai yayi
tace" to me yasa baka gaida mu ba nida Abba".
miƙewa yayi ya ƙarasa inda take yayi saurin faɗawa jikinta ya saki kukan da yake dannewa tun jiya ya ƙwace masa cikin kuka yace "mommy ba ke bace kika barni kika tafi na kasa bacci, baki min wanka ba, baki min addu'a ba, baki bani tea ba, banyi bacci ba, nayi ta mafarkin ki
Ga ciwon da Abba yajimin sai zafi yakemin kin gani".ya ƙarashe maganan yana ɗaga rigan uniform din sa abinka da farin fata duk birdi yayi jajir wani ma ya fashe".
Alhaji Abdulsamad da sauri ya ɗauke idon sa akan ɗan nasa wani irin tausayin ɗan nasa ne ya ziyarci zuciyar sa amma ya dake mai kawaici ne, sai kawai ya ɗauki pork yafara caccankan dankali.
Mommy itama idon tane ya cicciko tace "sorry my love. Soon zaka warke nima nayi missing naka banyi bacci ba zo kayi breakfast karku makara idan kazo zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login