Showing 3001 words to 6000 words out of 155717 words

Chapter 2 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

665

Abdulraham.


Asalinmu iyayena duk 'yan nan kano ne a sani yan kofar na'isa amma Hajja wato mahaifiyata tana da dangin mahaifiya a Dardum wani k'wauye a jahar zamfara iya mu ukku nan suka haifa shakara daya da auren su Allah basu mu yara ukku maza a lokaci daya daga kanmu kuma ba ta Kara ba ni Abdulsamad, Abdulraham, Abdulmajid.

Mahaifinmu malam Haruna baza a kira shi me kudi ba sai rufin asiri dan sana ar dinkin maza kawai yakeyi ni Allah yamin nasibin tun ina shekara 9 nake bin Hamza wani abokina shagon Babansa muna taya shi auna kayan masarufi alokacin muna primary ne Allah yayi wa Baban Hamza rasuwa kasancewan suna da yan uba suka raba gado daga nan kasuwa ta rushe adan kudin da nake Tarawa awajen Hajja na ce tabani na sari kayan aleyoyin na yara idan nazo daga makaranta zan dinga kasawa a kofar gida hakan ko akayi Allah Ya sawa abin da na fara kamar wasa albarka har kofar gidanmu ya zama matattaran tara yara saboda ina da fara'a da saurin sabo tun ina bazawa a barantin Hajja har Baba yasa aka bugamin yar benci ina bazawa tun a lokacin ko ina a jikin bencin na rubuta
3brothers ajiki wanda yanzu haka shine 3brothers company a fadin duniya ni kasuwancin bai barni nayi karatu me zurfi ba amma kinga yan uwa na sunyi Abdulraham Lecturer a B. U. K.


Abdulmajid kuma alk'ali abin da yasa zan gaya miki dukiyar gidan mu nawa ne saboda shi sha'anin aure ba a boye-boye na san zama ya yi zama zaki gane to ina son na sheda miki yan'uwana suna da mahimmanci a wajenana kuma sun fiye min komai a rayuwa ba na son ki dauki kanki amatsayi kin fi matansu ki dauka duk kanku ɗaya idan Allah Ya yi aurenmu da ke."

Ta ce "in Sha Allah amma ba ka karasamin ba ya akayi kayi kudi me yawa a cikin k'ananun shekarun naka Wanda har yanzu bazaka wuce shekara talatin ba amma duk Nigeria ba wanda bai san 3.brothers ba".

Murmushi ya yi ya ce "Akwai wani lokaci a lokacin ba zamu wuce shekaru sha bakwai ba, na raka Hamza abokina garin su innarsa kauyen zamfara mun dan fita bayan kari guraren tarihi na ji nayi tuntube da wani abu kamar dusi haka ya dan dulloko da nakalli dutsin sai naga yana shek'i kuma shi ba fari ba shi ba ja ba na tsugunna na bara tonoshi ina mamakin yanda yake shek'i kuma gashi da girma amma a cikin k'asa yake har Hamza da Yakubu suka zo suka karaso Hamza yace 'yade A.3full kake tonan k'asa haka".?

nace ''wllh Hamza wani dutse ne abin sha'awa kunga shi".

Yahaya dayake dan garin ne wani irin zabura yayi yace " kunsan meye wannan kuwa gol nefa ance yanzu sama da shekara 20 ba wanda ya tsinta nima a hoto nagani tabbas wannan shine kuma wllh gomnati ne za su kwace".
Na ce wllh ba zai yuwu ba ni zan tona kayana kuma naje na saida ba wani gomnati da zan bawa ni Allah Ya bawa.

Yahaya ya ce ta yaya? Ina ka san ana sayar da shi wllh kwacewa za suyi su dan baka wani abu ai harmu ma munyi arzik'i tunda ai za a dan ba mu.
Na ce ka san Allah ba wani wanda zan bawa ya min wayo saidawa zan yi mu raba kudin ku tayani tono shi mun sha wahala dama da buhu a wajen mu za mu zuba goruba wanda zamuyi saraba da shi bamu ciko goruba ba muka sinto gol. Yahaya ya ce kai amma kai Abdulsamad kana da sa'a ka san yanda mutare suka hawalan neman wannan sama da shekaru amma kai ka samu nima na sheda wajen ko zai sake tsurowa".

da kyar suka dauramin a ka ban ma koma cikin gari ba suka rakoni tasha ba wani wanda ya kawo wai gol ne a buhuna haka har na samu motan kano su kuma suka koma cikin gari na musu alk'awarin idan na saida zan raba kashi biyu na basu daya
ina zuwa nayiwa su baba da brother bayani Baba yace kar mu gayawa kowa kafin a san abin yi muka cusashi k'ark'ashin gadon Hajja
amma da safe danaje shagon me alewa na wanda nake sari nasan yana da amana kawai naji zuciya ta ta aminta dana gaya masa ina gaya masa yace" to kar ka sake gayawa kowa a take yabarwa yaran sa jiran shago muka shiga motarsa mukaje sabon gari wajen wani abokinsa yana zuwa Dubai sarin gol ya masa bayani da farko bai yarda ba sai da oga Kabiru yayi da gaske alh sa'idu mai gol yace mu je ya gani ai ya san danyen gol da yana da hotonsa ma amma yanzu ya rasa muna zuwa gida Baba bai tafi shagon dinki ba saboda ba ya dan jin dadi brother suna makaranta dan alokacin suna level one 100 da ganin yanda Hajja da Baba suke harara na na san basu so na zo musu da mutane nide dama haka Allah ya yi ni da wutan ciki inde a gun kudi ne Alhaji sa'idu da oga Kabiru sun gaisa da baba san nan suka masa bayanin abin da suka zo gani Baba yace" na dauko dak'er na mirgino shi dan sai a sannan naji nauyinsa nake ta mamakin meyasa jiya ban ji wannan nauyin ba abakin kofa na barshi Alh Sa'idu ya tashi yazo ya gani wani irin ja da baya yayi yana rufe bakin sa yana salati sai da yagama mamakin sa ya zauna yana fitar dashi na temaka masa muka fitar yace malam Haruna wannan fa ba karamin abu bane anya zamu iya fitar dashi a k'asan nan kuwa?."
Baba yace "to yaza ayi kenan".?
shiru alh sa'idu yayi can yace "shikenan bari na kira wani balarabe abokin kasuwancina a Dubai yabamu shawaran yanda za ayi atake yafito da wayarsa ya kira shi yace shima abokin nashi yace to bari yakira wani uban gidansa me company k'era gol yana kiransa bayan ya kashe wayan ba jimawa aka kira wayan Abdallah ne daga Dubai yace sun gama magana da uban gidansa gobe zasubi jirgin India sabo anan ne kadai yake da register na bita da danyen gol ta India idan yashigo na Nigeria zai iyacewa da abinsa yashigo bawanda zai tuhumeshi hakan ko akayi bayan kwana biyu sai gashi
shi ma da yagani tsora yayi da girman gol din musamman ma da fari ya fi yawa atake yayi mana bayani ai wannan dukiyar zai sayi campanyn sama gaba daya bashi da kudin da zai iya sayan sa amma idan mun yarda tunda yana da company sarrafawa sai asarrafa in yaso sai mu ba shi ladan sa mu saida kayan mu ladan da zamu ba shi ma ya isa ya K'ara k'arfin jari shima kasancewar da turanci yake maganan sai da yagama nayiwa Baba bayani yace ba damuwa Allah ya sa me albarka ne
bayan su Abdallah sun koma masaukin su a dare Baba yamin nasiha sosai ashe wasiya yake min bayan mun gama cin abinci ya ce

"Abdulsamad ina son magana dakai Abdulsamad duk da kai da yan uwan ka rana daya aka haifeku amma karigasu zuwa duniya dan kai anan gida aka haifeka su kuma ya gagara muka je asbiti shiyasa nake cewa kaine BABBAN GIDA kuma alama ne da Allah ya nuna kai ne jagoran su
to ina son kayi hakuri da yan uwan ka kamakar yanda na sanka kar ka canza wannan daukaka da Allah yake shirin yi maka na mallakan dukiya kar yasa ka dauki kan ka daban dasu ka rike zumunci ku kamar yanda kasaba tun kana yaro ka sadaukar da naka karatun kake nemaka kawo musu sun shiga karatun kai kuma gashi baka shiga ba
karike zumunci kar abin duniya ya rudaka ka canza daga Abdulsamad dina me sadaukar da farin cikin sa akan na yan uwan sa Allah yasa albarka cikin rayuwar ku."

nace" Amin Baba in sha Allah zaka sameni fiye da yanda kafada."
Baba yace" nasani Abdulsamad ba kai nake jiba sherin macce nake tsoro matar da zaka aura ni a son samu nama ka auri Halima itace zatafi dacewa da rayuwan ka" .
na juya na kalli Halima da take wanke wanke a kusa damu wanda alokacin bazata wuce shekara 10 ko 9 ba
nace "Baba Halima kuma."
yace"eh ita ina tusayawa yarinyar bata da kowa sai mu kaga Baban ta har yanzu bai dawo hankalin sa ba kai nake son ka auri y'ar nan kariketa amana na yarda dakai Halima tarbiyar muce nasan zata dace da kai ".
cikin kunya nace amma Baba kaman tayi min yarinta nifa nan da shekara 3 zanyi aure kaga lokacin nacika shekara 20 kenan".
Murmushi yayi yace"kabari nan da shekaru ukku kagani idan zata ma yarintan amma na nemi alfarman karin shikara 2 kaga ta isa aure a wannan lokaci".
nima murmushi nayi nace "to Baba na gode".

A washegari muka kama hanyan Dubai nida Abdallah da ogan sa Albaty da kuma alh sa'idu mun isa lafiya ba jimawa aka fara aikin sarrafa gold wanda ya yi matukar ba da mamaki dan farin diamond din da yafita ciki me daraja ne wanda a lokacin anci shekaru ba a samu irinsa ba kuma kinsan turawa da larabawa da shi suka amfani ana bugawa a jarida ba jimawa yan sari daga k'asashe da dama suka fara rububin companyn dinmun samu riba fiye da zaton mu, wanda yanzu tun muna hade da Albaity yanzu mun raba kuma Allah da ikon sa nawa company shine akan gaba bayan company na babba na bubai ina da reshe a
America ina da reshe a Englan ina da reshe a saudia a an Nigeria ne nake jin tsoron budewa amma ni na aikin gina babban companyn k'era mota mashin da yawanci kayan da akeyin sa da k'arfe
Dr Fanna nayi mamakin yanda dukiya ta yake ta hayayyafa agareni kinji yanda akayi nayi yaro yayi kudi kinji tarishi na kenan a tak'aice".

Murmushi ta yi ta ce" saura abu biyu ne ban sani ba yanda aka yi Halima ta zo gidan ku da mutuwar Baba".

Sai da yayi shiru na yan second yace " Dr tun zuwana na daga Dubai na farko ban samu Baba ba sai tarin wasiyoyinsa duk wannan dukiyar Baba bai san dashi ba, ita kuma Halima ai inaji ta gaya miki da bakinta hatsari mota sukayi da babatan wanda yayi loosing memory akwai wani Alh Musa a tsohon anguwarmu kofar na'isa a gabansa suka yi hatsarin mutum ne me tausayi komai da shi akayi na ceton ransu Alh Musa ya kashe kudi sosai akan Halima dan saida aka canza mata fuska alokacin baza ta wuce shekara 2 a duniya ba shiko Babanta aka ce zai warke ahankali dalilin dawowar Halima gidanmu mutuwar Alh musa ne wanda wasu mutane da ba a san su waye bane suka dirka gidan sa suka kashe shi shida matarsa bayan sadakan bakwai yan'uwansa suka zo suka koro Baban Halima da Halima da alokaci bata wuce shekara 5 ba waje suka ja gidan suka rufe shi Baban a nan kofar gidan ya zauna ita kuma Halima dama tana shigowa wajen Hajja da yake Hajja bata da ya macce tana son y'ay'a mata shiyasa ta jata sosai ajiki ta tasa ba tana shigowa shine da aka korosu ta shigo gidanmu tana cewa Hajja ai wasu mutane sun rufe musu gida Hajja tana jin haka ta san yan uwan Alhaji Musa ne shiga d'akin Baba ta yi ta gaya masa Baba ya je ya sanar da Mai anguwa aka zo daukan Halima da Babanta Hajja ta ce ita zata rike Halima har sanda tunanin babanta zai dawo haka ko aka yi Mai anguwa yawuce da Babanta ita kuma Halima ta zama yar Hajja".

Dr Fanna tace "Allah sarki Allah ya jikan Halima ya raya Nasir yanzu ina shi Baban nata".?

Abdulmajid yace"yana nan acikin gidanmu dama da zamu taso Hajja tace mutaso dashi yana part din sa damasu kula dashi".
Dr Fanna kallon agogon hannuta tayi tace "to Alhaji zan wuce sai da yamma a kula min da yarona kar ganin sabon yaro adena yayin nawa dan naga Hajja sai doki take"
Murmushi yayi yace"keko ba dole tayi doki ba saifa yanzu aka mana k'anne Allah ya sa Aishan Abdulmajid mata haifi namiji kin ga
3 brothers ya samu kenan,
sai ke kuma idan kika tashi kifara da macce sai ku sake Haifa mana mata masu kai daya to ya zaki aureni?
zaki zauna da yan uwa na zuciya daya?

Murmushi Dr Fanna yayi tace "wacce macce 3 brother's zai yiwa tayin aure taki Koda na wuni daya ne amma kasa a ranka wllh ba kudin ka nake soba wasiya Halima ne da kuma son ka da yamin shigan ba zata dan tun rasa Sharif ban yi zaton zan samu wanda zan so kamar shi ba sai gashi harma fiye dashi Allah yasa kai kamin ko da rabin s.......
Sai kuma tayi shiru tana mai da kanta daya gefen a hankali yatashi yafita a motan yana murmushi ya kama murfin motan zuciyar Dr Fanna sai bugawa yake adduar nasara take ta karantowa ta ji kamar daga sama

yace "zuciyar ABDUL tun yana yaro yake son auren yar barebari mai irin zanen ki me irin sanyin halinki me irin sanyin muryan ki amma nabi zabin Baba na auri Halima sai gashi a karo na biyu Allah Ya bani fiye da zabina gaskiya na san dalilin biyayya da umarni iyaye ne ya sa Allah yamin wannan babban kyautan amma ba wai dan na cancanta ba tun kallon farko dana miki naji kece matar mafarkina FATIMA ZAHRA kisa aranki Abdulsamad naki ne".

Yana gama fadan hakan ya mata murmushin sa me tsada tare da kashe mata ido daya ya rufo kofan ya juya cikin takunsa na ingarma ya fara tafiya kasa rufe baki tayi wai ita Fanna emeka 3 brother's yake gayawa wannan kalaman anya ba mafarki take ba mutumin da saide taga sunansa ajikin gidajen Mai ko kwalin taliya ko muhun sugar omo shikafa dade sauran su 3brother's dafe kirjinta tayi yanda yake bugawa kawai jira take taji ta farka daga baccin da takeyi

shi ma Abdulsamad yana shiga yayiwa Hajja da yan uwan sa bayanin wacece Fanna da farko Hajja ta nuna kamar bata gamsu da d'anta ya auri tubebbiya ba amma da taga yanayinsa ta gane yana sonta kuma ta tuna da asalin saurayin Fanna din Sharif yanda yayi soyayya na shekaru da ita kuma suka shiya shirin aure batare da sanin iyayen saba shine ta tsorata kar shima Abdul yayi tunanin haka tunda yana da daman da zai ajiye mata dari gashi ba mazauni bane tsoron haka yasa ta amince ayi auren amma har ga Allah ba dan taso ba.

A ranan suna jaririn Amina ya ci sunan Haruna Baban su A'A'A Hajja zo kaga mu a gun hajja a take tace akirashi da Agrif Hajja tsohuwar makaranciyar litatafan hausa ce dan haka tasan suna kala_kala dan har yanzu hajja karatun hausa novel takeyi har irin na online duk tasan marubuta shiyasa ko kallon yaranta sukayi tasan me suke nufi ita take koya musu yanda zasuyi soyayya ma

A ranan da Nasir ya cika wata ukku a ranan aka daura auren Dr Fanna da Abdulsamad ba wani shagali akayi ba a washegarin ranan ne kuma Aisha matar Abdulmajid ta tashi da nak'usa tasha wahala Dr Fanna tace amata cs amma Hajja da yan'uwan Aisha suka hana wahala tayi wahala har suma Aisha takeyi sai da sukaga abin bazai yuwuba suka saka hannu aka turata d'akin theater ansamu nasara ceto uwa da jaririta amma ansamu babbar matsala a mahaifarta wanda yariga ya fashe ba wani dama sai de a fitar dashi Allah saki Aisha kowa sai da tausaya mata haifuwar fari a cire mahaifa kowa ya ji sai yace Allah sarki Allah yasa albarka arayuwan d'an data haifa. Ranan suna yaro ya ci sunan Muhammad Albaity ogan gidan Abdulsamad dan Hajja haka ta ce ba abin da za a saka wa albaity dashi sai de susaka masa me suna ana kiransa da Kamal

bayan warkewar Aisha gida ya koma yanda yake kowacce tana kula da nata ɗan yanda ya namata Fanna ta ajiye aiki saboda kula da d'anta da mijinta duk da yawanci bayanan yau yana can gobe yana can wani abin mamaki Nasir yana kara girma kaman nisa da Dr Fanna yana bayyana abin yana bawa kowa tsoro dan Abdulsamad de b'aki ne ita ma marigayi Halima kak'ace sosai amma Fanna fara ce sosai irin sol din nan farin ibo din nan idon sa hancinsa duk rin na Fanna ne kullum Hajja cewa take ikon Allah tsabar son da Fanna take yi wa Nasir ya sa har kamanninsu yana son ya zo daya in dai ba ido na ba ne wllh sak

*Bayan shakara biyu*

Amina ta sake haifuwa wannan karon ma danta namiji sunnan Baban Hajja Habubakar sadik aka masa alkunya da AIBAN . AIBAN na da shakara biyu Amina tasake haifuwa shima namiji sunan Baban Amina aka sa wato Adamu ana kiran shi Abbaty har wannan lokacin Fanna ko batan wata ba tayi ba tun abin baya damunta har ya fara damunta dan Hajja tafara k'ananun magan ganu
tunda yaran suka fara wayo suka gane Nasir ya fita daban acikin su yana da wani irin zafin zuciya ga rashin tsoro da rashin kunya idan ba mommynsa ba
ba wanda yake ragawa ba wanda ya isa da shi inde yana gu to sai de kome ayi yanda yake so dan shikara 6 amma tamkar dan shekaru 20 haka yake diler kowa a gidan iyayensa ma ba ya raga musu balle ma aikatan gidan hatta Hajja shayin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login