Showing 33001 words to 36000 words out of 155717 words
Chapter 12 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
ba mai iya juya shi_
"kinga me take nufi da wannan su wa abin ya dama bamu k'adai ba har iyayen mu wllh hadin ku suke so bana Izza ba musamman Ummu wllh kowa yagan ta yasan ta damu da abin
Ita kuma Izza taci gaba ni me iya zuwa na zuga Hajja ce wllh takafa k'aramin yak'i afasa".
dariya Zahra tayi tace kin manta wacece Izza agun Hajja ko"?
Nasrim tace''nace kubari".
sai asannan Izza ta tura kofar ta shiga bakin ta dauke da sallama cikin nutsuwar ta jefa kanta tayi akan bed a rufda ciki tana murmushi ta d'ago kai tana kallon Nasrim da tarame sosai cikin kwanaki biyu
tace" Nassi kije inji my heart".
taja my heart din da siririn murya irin yanda Nasrim takeyi a da tana lumshe idon tare da cigaba da murmushin ta
Nasrim
bata juyo ba tace'' gaskiya bacci nake jifa nasan ma aiki zai sani kawai kice baki ganni ba".
"Okay".
tace tare da mek'ewa ta fita wayar Nasrim ne yayi ringing da sauri ta dauka ganin my best bro ne wato Kamal cikin sanyin murya ta amsa sallaman sa tace "Yaya yaushe zaka zo"?. My best sister ina Camaro yanzu haka insha Allah yau zan zo daddy ya gaya min komai abin da yafaru da har nayi shirin daukan mataki daddy yace a a ina miki fadan alkairi sis farin cikin ki shine nawa bani da y'ar uwa ko dan uwa ciki daya sai ke abin yabani mamaki shikan sa Agrif dazu dana kirashi har da kukan sa yana cikin damuwa sosai ni sheda ne akan son da yake miki ban san meya sameshi ba amma insha Allah k'anwata kece da nasara babu rashin sa'a ko rashin nasara a 3brother kinji zakiyi nasara ki kwantar min da hankalin ki kafin nazo".
ba tasan sanda ta fashe da kuka ba dan dama ta sabayiwa Kamal shagwab'a sosai lallashin ta yayi tayi
tana zaune cikin gerdeng akan wani kujeran k'arfe tana sanye da goguwar riga yellow an masa ado da bak'in duwasu ta d'anyi nisa cikin karatun da takeyi dan sunkusa fara exam jin k'amshin turaren sa yasa ta dan shafi hancin ta da hannu amma bata d'ago ba shima kujera yaja ya zauna yana cigaba da kallon ta kusan mintuna 2 sannan ya sauk'e wani ajiyar zuciya me nauyi cinki cool voice dinsa yace
" Halima. bata d'agoba amma tabar karatun da take kuma da alaman shi take sauraro yasake cewa "Halima".
ahankali ta d'ago fararen idonta ta zuba cikin nasa still yasake cewa "Halima where is you phone".?
batayi magana ba amma ta dauko wayar da yake cinyar ta
ta nuna masa
"Ok ok horon har yakai ga haka kin sani a
black list why ? kin san yan da kika azaftar da zuciya ta a tunanina ko meye zaki gaya min bani da kamar ki a duniya bayan uwar data haifeni kisa aranki a mata ba wanda zata kai ki daraja zaki iya sarrafa rayuwata yanda kike so ko zaki min horo da komai kar kimin na rashin ganin ki ko jin muryar ki wllh shine abinci na bana son ganin ki cikin k'unci da rashin walwala shine dalilin da yasa bazan iya auren kiba saboda nasan in akace nine mijin ki wataran zan sab'a miki ayanzu nafison kiyi ingantaccen rayuwa ta yanda duk mijin da kika aure inya tsaba miji zan zame miki garkuwa hakan zaifi duk da kowa yasan ke cousins dina ce kuma ina da daman fitowa auren ki kowa yasan there is marriage between us so confusing people
Amma but sai de nace kiyi hakuri dan Allah ni ba amatsayin cousins na dauke kiba tamkar yanda kuke da Kamal haka nake daukar ki tamkar Humairah please amma...
"Stop ya Agrif ai nima ban taba cewa ina son ka da aure ba".
ta dakatar dashi dan Magan ganun sa sunfara isar ta shuri yayi yana kallon ta
ta numfasa
cikin sanyin murya tace" hope de ba Izza ta amince ba to ai fatan mu kenan kuma nagode sosai da soyayyar ka nima Ina son ka kuma bazan canza ba ina matsayin cousins din ka zanyi duk yanda kace.....
tana cikin maganan taji kawai yayi wani irin hugging dinta yana wani irin kuka cikin tsoro take kogarin kwacewa amma abin ya gagara "Nasrim ki barni naji dimin jikin ki abin da najima ina rayawa ne ashe na kasance bani da rabo Nasrim tunda na furta bake nake soba ban samu sauk'i ba sai yanzu da najini a jikin ki sai yanzu naji hawaye na yazubu abinda nake mutuk'ar buk'ata kenan na samu nayi kuka ashe kuka ma rahama ne Allah kabani karfin gwaiwar sadaukar ta".?
jin yafara shafata yasa taji wani irin k'arfi yazo mata tunk'ud'ashi tayi kefe da gudu tayi cikin gida
cikin yan kwanakin Hajja ta matsa sai da aka zo neman auren Zahra da Humairah Zahra Aliyun tane da suke soyyya sai humairah Ayman d'an gidan Dr hafsa Abbaty yayi tsalle yadire shide bai isa aure ba Aiban ko k'asar ma yakasa zuwa agogon sarkin aiki kenan
Hajja sai data matsawa mommy tace tasa Nasara yasa ranan zuwu
*********************
zuwan Nasir da kwana ukku Hajja ta kasa cemasa komai ganin har yana shiren komawa bayyi maganan Nasrim ba yasa Agrif yasame shi da batun yafito yanemi soyayyar ta kafin yatafi tunda Hajja ta kafe dole da Nasrim za ahada auren Humairah da Zahra da Izza
zaune suke cikin gerdeng su biyu da alamun de tattaunawar tasu batayi musu dadi duk kan su biyun cikin b'acin rai Agrif yace " to wllh baka isa ba wai me Nasrim tai maka a rayuwa har haka da kake son rayuwar ta
ta dauwwama cikin bak'in ciki".?
Nasir cikin isa yace " tamin abubuwa da dama kuma idan kaga Nasrim taji dad'in rayuwar duniya to nikuma bana raye wllh bata isa ta auri mutum sak kamar kai ko wani gaye da ya amsa sunan sa guy ba shine dalilin da yasa na dakatar dakai kuma na baka umarnin ka nemi Izza dan nasan itace aminiyar ta ko da kagane ba auren ta zanyi ba to baka isa kadawo kana son Nasrim ba amma bawai ni zan aureta ba kafin na gama nazarin wanda ya dace da mummunar rayuwar ta da gan-gan na turaka gun k'awata
ka gane ko ina son kane kuma ko mak'iyina bazan masa fatan auren Nasrim ba saboda ni nasan me na kullawa rayuwar ta balle kai dan duk wanda yayi kuskuren auren ta to ya gurbata rayuwar sa gaba daya ".
dariya Agrif yayi yace " baka isaba kuma ka dena kiran rayuwar Nasrim da mummunar rayuwa domin ita din bata masan kanayi ba kuma ni Haruna nine mijin ta in Sha Allah ai ba dauramin aure da Izza akayi ba na fasa kuma zaka ga yanda zan canza aure na yakoma kan Nasrim".
Nasir murmushin sa na gefen baki yayi wanda ya keyin sa idan yaso mugunta ya mek'e tsaye ya dafa kafadan Agrif yace " okay ban hana ka ba amma kasani muddin ka auri wannan yarinyar bakai ba kiran kanka a cikin 3brother bayan nayi fired dinka zan maka sherin da zaka dauwama a gidan prison na har abadan kaga sai tabika kuyi soyayyar a can amma har yanzu Ina warning din ka kafita daga har kanta ba baraza na kena maka ba na kuma Mai maita wa wannan FURRUC NA NE".
shima Agrif cikin fushi yace
"bazan fita a har kan nata ba Nasuru ka koreni a aiki mana ai ba tun yau ba nasan kana ta k'ama da dukiya to kasani Nasrim tafiye min komai na duniyar nan kuma zaka gani ba abin da zai samemu da sherrinka".
Yana gama fadan haka ya kwashi wayoyin sa yayi hanyar fice a gerdeng din
Murmushi Nasir yayi yace "zan baka mamaki ai ba aiki zan koreka ba dena amsa sunan 3 A full zakayi".
shide Agrif bai juyo ba ya k'arasa ficewa
******************
a hankali take takawa daga part din mommy zuwa nasu daga sama taji sauk'ar ruwa me sanyi a kanta cikin sauri ta d'aga ido ta ga wane isheshen ne zaune ta gansa kafa daya akan taya yana aikin zuk'ar taba tsigari gefe da gefen sa yan mata ne fararen fata a tsaye cikin bad dress
kafin ta gama tan_tan ce waye taji an jeho guntun sigar cikin bakin ta da sauri ta tofushi tana murza leben ta inda ya k'one cikin fusata taja baya dan tagan shi da kyau to waye shi kaman taso ganiwa amma bata ganin fuskan sa sosai gashi yana sama kuma idon sa acikin bak'in glass Wannan din waye shi? tace afili kawai sai tajuya takoma part din mommyn banko kofar tayi mommy tagani a dining room batayi mata magana ba ta fara taka steps mommy tace'' ke Nasrim ina zaki hakan?".
"Mommy wani d'an iska ne a sama ya zubo min ruwa ya jefa min guntu sigari shine zanje na duba d'an uban waye shi".?
cikin tsoro mommy tace'' Nasrim Yayan ki nefa".
"Mommy Yayana kuma? ni kaf cikin yayuna ba mahayin taba ba mane min mata wasu turawa nagani da bad dress a sama....
sauran maganan ne ya mak'ale mata saboda wani irin shak'a da taji a mak'ok'oron ta
"mommy cikin in in na tace'' dan Allah my Son kayi hakuri bata san kai bane afuwan".
"cikin dakiyar murya irin tasa yace "ai shine yanzu nake son ta sani tasan ni d'an uban waye na kuma tabbatar dani D'an iska ne"..
Mommy tace dan Allah kayi hakuri nace".?
"Wllh mommy yau sai tasha giya tasha taba sannan na hadata da alade ta kwana dashi kinga ta zama cikekkiyar y'ar iska ko".
da k'er har Saida mommy tasa kuka ya hakura ya barta amma yace zasu sake haduwa ta guji haduwa na biyu dan baya yafiya".
Mommy tace'' insha Allah baza ku haduba yanzu mafa data shigo sai da nacewa Barira tace bana nan kar ta bari ta shigo ai idan kana gida bana bari ta shigo kayi hakuri kaji my Son".
sakin ta yayi ya juya ya haye upstairs cikin b'acin rai
Nasrim ma cikin b'acin rain tace "mommy dama kina gida kika ce ace bakya nan saboda wani banza mommy na bar masa ke nikuma har abadan bazan k'ara ahigowa part din ku ba".
dagudu ta juya ta fice
**************
Aiban da Agrif
"Aiban dan Allah kaine kadai zaka iya temakona kamin wannan alfarman".
shiru Aiban yayi can ya sauk'e numfashi yace'' haba Agrif meyasa da kasan Nasrim kake so kace Izza yanzu Koda nace inason Izza ai iyayen mu bazasu yarda ba kuma yazama kamar wasa da hankalin sune ai".
Agrif yace"ni amin cewar ka kawai nake buk'ata nasu me sauki ne zuwa zakayi gaban Hajja kazube kana kuka kace ai Izza kake so nasan tana sonka zata amince kuma amincewar ta shine amincewar kowa nikuma idan aka tambayeni zance na sadaukar maka da ita zan tafi karatu course na watanni tara kafin nazo kunyi aure kuma kafin nazo nasan yanda zanyi na shawo kan Nasrim".
Aiban ya girgiza kai
yace "zanyi hakan saboda farin ciki ka amma ba dan Izza tamin ba".
**************
Hakan ko akayi Aiban yazube gwaiwoyin sa a gaban Hajja yana kukan shi idan bai aure Izza ba zai mutum Hajja uwar son jikoji kodan basu da yawa nan danan ta gigice ta tara mutanen gida ta tambayi Agrif zai iya hakura ya barwa k'anin sa da gudu ya amsa eh
Hajja tayi ta sawa Agrif albarka akan sadaukar
Izza zaune a d'akin Baban ta tace'' Baba kaji shawaran da suka yanke ko".?
Mustapha yayi shiru
can yace " eh Izza amma abin da yafi bani mamaki akwai maganan aure tsakanin ki da Agrif ga kuma shima Aiban za ayi auren abin yana rudani har yanzu na kasa tan tance wa gashi de ina gani har da rabon haifuwa a tsakanin ki da Aiban to na kasa gane yanda Agrif ma yake ta k'iftawa ta tsakani".
Izza tace " Baba kawai Ina ga maganan da d'in kake gani".
gir giza kai baban Izza yayi yace' ah ah bana baya bane akwai rud'adi sosai amma kar ki damu zanji da komai".
Izza tace" nifa Baba hakan yafiye min ma Aiban yanzu na gama gane Aiban yafi kowa aiki dukkan account din dukiyar gaba daya yana hannun sa dan shine aban garen kudi sai yagani yake turawa Nasara ma ni shakan ma yafi dan kana ganin Aiban gaka Naira".
dariya Baban yayi yace' ai ni nayi aiki akan Wanda yafi kudi yazama shine mijin ki yanzu de abin da yafi damuna wannan maganan Agrif din".
Izza tace'' kai Baba rabu dashi ayi abin da zai fita a rayuwata in ma sona take".
***************
a ranan aka sa ranan daurin auren Aiban da Izza Humairah da Kamal zahra da Aliyu sati biyu kacal dan Aiban yace bazai bar k'asan ba har sai an daura auren
Nasir yakoma Agrif ma haka fadan shagalin da akayi a bikin b'ata lokacine Agrif yazo bikin amma Nasir bai zoba Agrif tun a na shagarin yake ta faman tura kansa wajen Nasrim amma ba fuska acikin gidan aka ajiye Izza da Humaira dayake Hajja tace duk ka jikokin ta 5 anan zasu zauna da matan su dan haka gidan Izza da Humairah ajere suke Aiban bayan gama cin amarci yakoma India yabar Izza saboda makaranta Izza kam ta taka matakin da take so aburin ta dan Aiban me bushasha ne motocin da ya saya mata ma abin kallon ne tana fasa kai yanda take so cikin k'awaye fiye da yanda Nasrim takeyi
******************
*bayan wata 2*
Izza ta kalli Nasrim tace'' haba my sister amma idan kikace haka bakiyiwa ya Agrif adalci ba kuma akaran kan ki maki duba mun tashi mu hudu duk kan mu ukku munyi aure ban da ke."
Nasrim tace'' lokacin kune yayi nikuma ahalin yanzu bani da wani space da zan ajiye namiji kingane musamman Agrif bana buk'ar sake jin wannan ke da mijin ki kune masu yimin wannan dan ya Kamal tun so daya da yakawo min yaga ba fuska bai kara ba amma ya Aiban da ya Abbaty sun nace min har nadena mude message din su".
Izza tace
"to naji dan Allah tunda yace alfarma ya nema kimasa alfarma Koda na iya gaisuwar ne gashi ma a falo dan Allah ki fito".
da k'er Izza ta shawo kan Nasrim ta samu Agrif a falo Agrif kam awanan Karan da k'arfin sa da kalamai masu zafi yazo bai sha wani wahalan shawo kan Nasrim ba duk taurin kai irin nata
Numfasawa tayi tace'' shikenan amma kasani ina da dokoki".
'ki fadi ko wacce iri yace inde zaki yarda ni Agrif ina son ki".
tace
"na farko deni ina da kishi duk mijin da ya auri Nasrim to yasa a ransa tamkar ya auri mata hudu ne dan daga ni ba k'ari ina da kishin azaba wanda ni kaina ban san iyakar sa ba".
Murmushi yayi ya sauka daga kujeran yazuba guiwowin sa k'asa yace" inde wannan ne mai sauki ne ba mata hudu ba na sawa Raina ke a masayin mata dubu kike a rai na ke daya ce azuciya ki rik'e ki aje ".
murmushi tayi tace'' Allah ya Ag wllh ba dan ina mutuwar son kaba wllh ba zan sake yarda da kai ba dan ina da kishi sosai a gabana kece kai Izza k.....
rufe mata baki yayi da tafukan hannu sa yana dariya
*************
Hajja tace'' ikon Allah ai ni dama nasan iskanci ne irin na yaran zamani amma Agrif ai na Nasrim ne kunji irin iskancin da yadinga min ne wai wllh shi de cikin satin nan ya keson adaura masa aure daddy yace "gaskiya Hajja ba wani abin da yarage banda a daura auren me za a saya jira a take aka sa ranan auren wata 1
Nasir bai ji ba sai a status din Kamal ya gani alokacin ma ko suna tare da Agrif din a Dubai cikin riki cewar yanani yake kallon Agrif yace
"Agrif bakaji gargadin dana maka akan yarinyar nan ba ko Wllh auren yariyar nan shine mummunar k'addaran ka na gaya maka ba matar ka bace ka nace".
Agrif cikin b'acin rai yace'' ni kuma na gaya maka baka isa ba Ina son Nasrim kuma baka isa hanani auren taba".
Nasir
mek'ewa yayi tsaye cikin b'acin rai yayi taku ukku ya k'arasa Inda Agrif yake cikin sanyi murya yace Wannan shine Warning na k'arshe da zan maka Haruna kar ka auri Halima rayuwar ta ba shida kyu idan kasa taurin kai abin ba zai muku yau ba".
"Ai kai ba ubana bane da zaka sani gaba kana gayamin wannan Nasrim ce nan da sati biyu tazama matata".
gyad'a kai Nasir yayi yana
murmushi yafara takawa na barin gun
tun daga wannan rana Nasir bai k'ara nuna cewa baya son aure ba har taya Agrif shidimar biki yake saura kwanaki biyun adaura suka sauk'a a k'asar da dinbin abokan su
Dr Fanna kam awanan Karan tafito tanuna eh Nasrim y'arta ce kuma tayi rawan gani
Safiyar jumma'a dinbin al'uma suka sheda auren
Haruna Agrif Abdulrahaman da Halima Abdulmajid Nasrim
Justice Abdulmajid yatara mutane sosai
da dare bayan sun kwanta Humaira da Izza yau a part din Mama zasu kwana saboda shidiman biki zahra ma tazo shine suka samu daman cewa anan zasu kwana dama daga ita har Izza laulayin ciki sukeyi shiyasa duk suka gaji
Humairah tace'' nasy K'iran fa ake
Nasrim da har tafara bacci tace'' kai wllh Ya Agrif bashi da hakuri tashi tayi zaune tace wai ni dukka aure haka yake ko nawa mijin ne bashida hakuri wllh dazu da mukazo a wajen diner dak'er na kwaci kaina awajen sa acikin mota ba dan nayi da gaske ba wllh komai zai iya faruwa shine fa yanace wai yanzu yanason ganina kuma wai a part din mu da akayi jere ina tsoro wllh me yasa bazayyi hakuri a kaini goben ba".
dariya Humairah da Zahra da Amira da Izza sukayi Zahra tace'' ai ko dole kije kinsan ya Agrif da rashin hakuri wllh zaki iya ganin sa anan ba da jimawa ba".
ma'rairaicewa Nasrim tayi ta kalli Amira da yake