Showing 45001 words to 48000 words out of 155717 words
Chapter 16 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
wllh baka fi karfin komai ba ciki harda hukunci ".
Nasir dariya yayi yace" karfin ramawa ai zanfi son haka dan zakafi bani k'arfin gwuiwan sanin inayi da namiji Agrif tun farko nafito na nuna maka akwai illa a rayuwar ka muddin ka aure ta amma ka aure ba tare da daukan wani matakin ba Kai kan ka san ni babban bak'iyin kane tun daga randa ka aure ta meyasa baka dauki mataki ba dama baka shiyawa hakan ba ai nayi zaton ka shiya ne wawanci ne Allah Ta'ala ya nuna maka mak'iyin ka amma baka nemi hanyar ts'ira daga sherrin saba na gaya maka tun farko ni nafison katona min asirin sabo da cikar wata DAMA TA tawa barin abin ahaka wllh ni ba rufa man asiri kayi ba zaifi min dadi idan kowa yasan cewa cikin jikin Nasir ba naka bane nawa ne kuma nafison ka fada da bakin ka za afi yarda ".
Agrif yace" ai nasan kafi son a haramtanin ita shiyasa bazan taba tona asirin hakan ba zanjira har sai sanda Allah ya sauketa lafiya na mayar da ita cikekkiyar matata zamuyi rayuwan da ba wasu ma auratan da sukayi".
cikin wani irin dariyar mugunta Nasir yace " ni Nasir na maka alk'awarin inde ina numfashi a duniya Nasrim bazata taba jin dadi ba wanda ya rab'u da ita ma bazai ji dadi ba kai meyasa ka kasance me taurin kai ne mommy da cikin ta ta hafi Nasrim amma da nace bana son ganin ta da Nasrim rabuwa tayi da ita takoma wajen Maman Kamal da zama sai kai kayi taurin kai ka aure ta ba abin da ban gaya maka ba dan haka wllh yanzu ma nafara k'unta ta maka Wannan kad'an ne manyan na nan zuwa
duk da yanzu ma Al'hamdulillah Allah yabani sa a biyu na farko dauke budurcin ta wanda nasan har iya karshen rayuwar ka sai de kayi manage da ita amma fanko ce ita bazawara ce sai na biyu Allah yabani daman ajiye d'a a maran ta wanda hakan na nufin ni zata fara haifawa d'a ba kai ba duk san da zakayi sex da ita sai ka tuno ni na fara shan romon farko duk sanda ta Haifa maka d'a sai katuno nawa ne babba
murmushi yayi tareda dafa kafadan Agrif yaci gaba dacewa
Yanzu dama ta ukku nake rokon Allah yabani wanda dashi zanyi AMFANIN Nasrim ta haifamin d'a namiji me kama dani.....
hhhhhhhh yayi dariya tare da jefa kan sa cikin kujera yaci gaba wllh Agrif zanyi abin da dakan ka zaka fito kanunawa Nasrim ni ta haifawa d'a ba kai ba zanyi AMFANIN da DAMATA wanda kai kanka kasan bana sake dashi kuma kasan duk abin da na furta to sai nayi shi ko yayi kyau ko kar yayi nide ba Wanda ya isa ya dakatar dani Agrif ba a tsabawa umarnin Nasir da kab'atawa Nasir gwara ka sab'awa ubangijin ka yana sonka zai iya yafe maka ka bari mu hadu gobe a 3brother kaga abin da zan iya da wanda bazan iya ba ko zan baka mamaki....
hada yatsun sa yayi ya bada sauti k'as k'as yace " Agrif ka sani NASARA baya yafiya baya furta abin da ba zayyi ba kajira saka mako".
ya tashi yashige bedroom din sa
dafe kansa Agrif yayi yana ta mai maita Hasbunallahu wa ni' imal wakin
Kwana a k'asan nan bai kama shiba dole yariga Nasir zuwa Nigeria yanzu ya zauk'a akasan Dubai din dama dan ya dauki wani documents din sa a gidan Nasir din sai yasame sa yana wannan wayan azabure ya tayi yayi han yar waje...
gida kuma Hajja cikin mamakin kalaman Nasir na cewa _Nasrim ta samu ciki adaren mu na farko dan Allah kulamin da ita kafin gobe nazo_
cikin mamaki tace "Abdulmajid me hakan yake nufi me kalamun Nasir yake nufi ko de................
*dir k'ashi To masoyya ankusa fa shiga RIKICIN BABBAN GIDA ya Nasir da Agrif zasu kasance wake da nasara sai naji comments din ku mu hadu a page 8 insha Allah sosai nake jin dadin comment din ku Allah yabar kauna*
*Bj*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
```NOW```
*FURUCI NA NE*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*_________________________________*
*Page 9*
Dama wannan bayahuden shi yamin haka shi ya rabani dakai na shawon sati shida alokacin da nake buk'atan ka akusa dani shiyasa ni dama banga lefin ka ba dan Allah Yaya kane mi wani ai'kin a wani'gu tunda baya sona ka aureni bazai bari muji dadin rayuwar mu ba ai kagani tunda ga yanzu ya turaka aiki adaren furkon mu mun jure yaga ba riba shine yanzu yafito a file yake maka barazana daka sake ni ko".?
ajiyar zuciya Agrif ya sauk'e afile bakin sa yana furta "Al'hamdulillah" tunda bataji kan zancen ba duk da shima hankalin sa atashe yake amma cikin son wantar da nata hankalin yace " come down ki fashin ta my dear ni nafi kowa sani waye Nasir ba zance yana farin ciki da auren mu ba kuma bazance yana b'akin ciki ba dan da baya so wllh yasan hanyar da zai biya yaha auren amma Nasir mutumin kirki ne ba yanda kike daukan sabane".
cikin rashin yarda da maganan nasa tace'' mutumin kirkin ne zai umarceka daka sakeni har kana cemasa zaka d'auki duk sharadin sa ni kawai kagaya min wane sharadi ya gindiya maka har kake masa alk'awarin ko yatsa na bazata taba ba?".
cikin in'ina
yace
" amm amm dama randa zan tafi Bai San na karbi budurcin ki bane kawai Hajja tasa mommy ta kirashi tana tambayar sa ni anan tagaya masa kina da ciki shine yake fadan na zaliceki wai jikin ki nake so nak'asa hakura har naje na dawo haka na turmujeki da gajiyar biki to danaga ya zauki zafi dayawa sosai har yana gani kamar wata rana zan iya juya miki baya shine na masa alk'awarin dana miki randa zan tafi ai namiki alk'awarin bazan sake neman wani abu ajikin kiba har sai kin shekara agida na dan ki yarda ba jikin ki nake soba abin da yafaru k'addaran ce
to wannan shine saradin Nasir shi yana fadane akan ki
ki yarda dani Nasir yak'i yake akanki Nasir masoyin kine na boye ke kike nuna masa k'iyayya".
tabe baki tayi tace'' ummm to Ina ruwan sada rayuwar mu nide wllh ban karbi wannan sharad'in ba".
Agrif yace" nima bawai na karbi sharad'in sa bane ah ah yazo akan gab'an alk'awarin da na miki ne bazan kusan ceki ba in Sha Allah har sai lokacin da na dauka yayi danna nuna miki ke nake so bawani abunaki ba".
Nasrim wani irin kallo ta masa tana tabe baki ta wuceshi
sai data haye kado taja blanket ta rufe rabin jikin ta tace'' ni kuma ban yarda da wannan alk'awarin ba ni kayiwa lefi kuma nayafe maka saboda isanka a waje na kai harma kafi".
tana gama fadan haka ta k'arasa jan bargon ta ta shige ciki
Agrif dube dube yafara da alaman yana nemam inda aka tsak'ala CCcamera ne amma bai gani ba
cikin muryar shagwab'a tace''
"wai me kake nema ne ".?
diri diri yayi yace
"amm sweetheart ki kwanta kinga kina buk'atan hutu bari ingama shiryawa ina zuwa".
yace tare da ficewa daga shi sai towels akugun sa
yana taka steps wani message din yasake shigowa Nasir din ne de da sauri ya bude gaban sa yana fuduwa yafara karantawa
_banason kabawa kan ka wahala wajen neman CCVT Dan zaka b'ata lokaci kane dan ko da ido dubu aka halicceka bazaka gani ba_
a slow yake takawa
d'akin k'asa yashiga ya zauna abacin gadon yana dafe kansan
shima
Nasir abangaren sa rufe laptop din sa yayi ya mek'e yana murmushi yafita da saurin sa yafice direct part din su Agrif ya nufa cikin rashin far gaba saikace gidan sa haka ya haye har sama direct bedroom din da yake zaton anan Agrif din yake yanufa murda handle din yayi ya shika Agrif duk da bai d'ago ba amma yasan Nasir ne dan idan ya doshi gu k'amshin turaren sane yake sallama
karasawa yayi har inda Agrif yake abakin gadon shima zama yayi abakin gadon yasa hannu ya cire tagumin Agrif cikin sanyi murya yace"
My friend banso muka zo wannan matakin da Kai ba naso ka dauki shawara ta tun farko kara bu da ita amma ka nace banso kyakkyawar halak'ar mu takoma haka ba dan kasan kaine abokin shawarata kai kafi kowa sani na duk damu ukku muka tashi Amma kasan bamu shak'u da Kamal kamar kai ba agani na na isa dakai ni me baka shawara ne san nan nafi k'arfin komai awajen ka".?
Agrif sake matse hannun sada yake cikin na Nasir yayi cikin k'unan zuciya yace "Nasir kafi karfin komai awajena nasani shine dalilin na na barmaka NASRIM tun farka a zatona da gaske son ta kake duk da nasan bazan jure rashin taba nima amma na bar maka dan kafi karfin komai awajena ashe kai bason Nasrim kake ba nikuma ina sonta bilhakk'i bazan yarda da abin da zai cutar da ita ba dan Allah Nasir Nasrim taci darajan son da kake min kabari mu zauna lafiya".
girgiza kai Nasir yayi yace' ah ah wllh bazan iya ba Agrif bazan iya kwatan ta maka yanda zuciya ta take min barasaza a kowacce second game da Nasrim bane tayi mugun shiga yaruwata yanda bazan iya kwatan tawa ba wllh bazan taba barin ta
ta huta ba".
numfasawa Agrif yayi yace
"Nasir ka bani mamaki duk da nasan halinka duk abin da kace zakayi zakayi da kace bazaka bari nazauna lafiya ba ban zaci ta wannan hanyar zaka bullo ba duk atunani na k'untatawar taka zata tsaya a iya korata a aiki ne tunda Kai ne me campanyn amma ashe abin naka ya zarce nan Nasir ina tausayin ka aranan da zakayi nadaman abinda ka aikata kana musulmi ka aikata zina da matar aure kuma baka sirran tashi ba kanunawa wanda yake auren ta saboda ka isa kasani wllh Allah shine ishehhe Nasir wani irin zuciya Allah yabaka da baka sawa aranka akwai ranan shisabi awai randa ikon ka kudin ka baza su maka amfani ba Nasir ban zaci isar taka har takai ka dauki CC camera kasaka a d'akin aure ba har kana barazana dashi kasani mala'ikun Allah ma idan ma'aurata suka keb'e kansu juya musu baya sukeyi basa ganewa idon su tsiraicin ma'aurata Nasir me namaka ?me Nasrim tamaka? Wllh Nasir ka jefani cikin wani irin k'uci wanda ko fitar rai bana jin yafishi ciwo why".?
ya k'arashe maganan yana dafe goshin sa saboda kansa da yake masa zugin ciwo
Nasir mek'ewa yayi tsaye yana juya baya yana murmushi me dauke da b'acin rai yace
"Agrif duk yanda zaka kwatan ta zuciyar ka bata kai tawa ba wllh nafika shiga cikin k'unci
Dan Allah ka temaka kar kayi yunk'urin bawa Nasrim kowane
irin farin ciki a karo na biyu zan zo maka da buk'ata idan kabi insha Allah zaka tsira da mutumci ka idan kayi gardama irin na baya to saka makon zaifi haka muni".
cikin dauriya Agrif yace" me kake buk'ata"?.
sunkuyawa yayi cikin taushin murya yace
" Ina son ko dan yatsar ta kar ka taba har ta haifamin yaro na sannan ina son mahaifar ta yazama a tsarkake yake shine dalilin saka cc camera idan ka k'arya alk'awarin nasani".
Agrif yace
"wannan sharad'in ai nariga na dauka amma dan Allah kacire CC TV a bedroom din mu bazan kusan ceta ba sannan ba maganan na baka yaro Dan koni nabada ayanda Nasrim ta tsane ka bazata baka d'an taba sannan shara'a musulumci ta halak tamin cikin jikin Nasrim".
wani irin kallo Nasir yabi Agrif dashi ya d'aga kafada yace' ai dama Kai zumane sai da wuta to wllh ni dakai zanga me nasara zan tona asiri komai ma yafaru ba uban kowa zanji kunya ko tsoro ba".
shima Agrif cikin b'acin rai yace "amma ai na yarda da sharad'in kana farko bazan hada shimfida da ita ba dan haka kamin uzurin ta haifun idan ta amince zata maka shikenan amma da sunan ni zan maka kyautan sa dan Allah idan kana kaunar iyayen ka kar ka fallasa zaka zubar da mutumcin gidan mu hakan babban abin kuyane zaka janyowa three brother abin fad'a aduniya kasani gidan mu shaharatren gidane aduniya ".
cikin rashin damuwa yace
"ni duk wannan bai dame ni ba na tsabawa mahaliccina ma balle wani abu da wani bawa me zunubi aka zai fada akai na ba wannan ne damuwa taba damuwa ta ka kula da sharadina kawai".
Agrif yace"shikenan naji zan kiyaye amma dan Allah ina son na d'an kwanta na huta".
murmushi Nasir yayi ya nufi kofa atunanin Agrif fita zayyi sai yaga yasakawa kofar key kuma yazare ya jefa acikin aljihun sa ya tako yana murmushi ya fada bed din yana jan blanket yace "good night".
ba aja dogon lokaci ba bacci ya dauke Nasir
Juyowa Agrif yayi Yana kallon fuskan Nasir afili ya furta "anya ko Nasir kai mutum ne kana nufin kwana zakayi a part din mu wannan wacce iri yar rayuwa ce"?
tashi yayi yafara safada marwa a d'akin ba abinda yake tunawa irin Nasrim tabbas yaga sha'awar kasance wa dashi acikin idon ta mezai ce mata bai gama wannan tunanin ba yaji ana murda handle din kofar da k'arfi gaban sane yaji yafadi sanda yaji muryar ta tana cewa Yaya "Agrif anan kake ne dan Allah kabude min wllh bana iya kwana ni kadai tsoro nakeji".
ta k'arashe maganan tana dafe maranta dan wani irin murdawa yakeyi duk kwana kin nan hakuri takeyi ta rasa wane irin abune yake damunta tabbas cikin jikin ta yana da son a sadu ga magunnuna da aka dura mata yau ma Mama sai da tabata wani shiyasa take jin mugun sha'awa
Ji shiru yasa tace'' dan Allah Yaya kabude"?
tayi maganan tana jij-jiga kofar da k'arfi
bude Ido Nasir yayi yana murmushi yace "kaji jarababbiya ko"?
Nasrim da sauri ta koma d'akin ta
ta dauko wayan ta Saida tazo dai-dai kofar da Agrif yake ciki ta danna k'ira dan azaton ta kobaya d'akin ne aiko taji waya yana Ringing aciki amma har ya katse ba adauka ba
tabbas tasan duk baccin da yake zai ji wannan bugun k'ofar da k'ira da take masa
Afili ta furta "yaya Agrif me hakan kenufi"?.
Nasir yace'' ka bata amsa da cewa kai kana tare da wata yau ba zaka samu daman budewa ba kana da buk'uwa".
cikin razana Agrif yace" ah ah bazan iya ba Nasir cikin sharad'in mu ba wannan'.
mek'ewa yayi tsaye yana cigaba da murmushi sa
yace "ni zan iya yayi bakin k'ofar
Agrif bai ankara ba yaji Nasir ya canza muryar sa ya koma irin na mata sak sai ka rantse macece yace "ke balla gaza da baki san waye mijin naki bane to ki koma da jaraban ki tunda har ya gaiyatoni har gida ba zan hakura ba ban saba da kwana ba namiji ba".
cikin k'araji nasrim tace'' wacece ke......?
sakeyin muryar matan yayi yace' keni bani da wannan lokacin idan nagama aikina na tafi ki tambayi mijin ki".
Agrif zayyi maganan Nasir ya fisgoshi yayi bathroom dashi sai da suka shiga yaturo kofar yace "kasan ni ba tsoro nake jiba idan kayi magana ko kamusa to dai dai yake da tonan asirin komai dama ni shi nake jira........
ji sukayi Nasrim tana wani irin buga k'ofar kamar zata karya tana cewa " ya Agrif kasan wacece Nasrim awajen kishi amma kamin haka kashigo min da k'aruwa har d'akin aure na ka manta nace duk randa kaso wata to za ayi biyu babu wllh kashe ku zanyi".
Agrif yana ji yana gani har muryar Nasrim ya dashe amma ba halin yafita lekawa yayi ta bulin mukuli yaga hannun Nasrim har yakumbura dan bugu jinginuwa yayi jikin kofar yana maida numfashi shi kam Ina ma zai mutu yahuta da wannan rayuwar Ina ma zai iya kisa za zai kashe Nasir kawai ya huta in yaso shima akashe shi sai de shi ko Marin mutum bayason yi balle ya illata mutum ko cinnaka bai taba kashewa ba".
azabure Agrif ya mek'e jin wani irif yana cewa wllh nas...…...
*To masoya mu kasance cikin pages na gaba 10 Ina jin dadin comment din ku ngd sosai da soyayyar ku*
*Taku b JATTKO*
[4/8, 1:47 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
*BATUL ADAM JATTKO*
*Marubuciyar*
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYAR*
*NOW*
*FURUCI NA NE*
*10*
jin shiru yasa Agrif lekawa ganin Nasrim yayi akwance plates kamar bata numfashi cikin wani irin razana yayi kan Nasir yana cewa "wllh Nasir ni zan zama ajalin yaruwar ka idan har Nasrim ta mutum wllh Kai ma zaka mutu ka kasheta ka kasheta Nasir.....
Nasir fizgewa yayi a hannun Agrif yabude k'ofar ba alaman numfashi atare da ita ga hannun ta duka biyu jini yakeyi dan yatsar roban tama ya cire acan gefe da sauri ya d'agata cak yayi gaba da ita cikin hanzari yake tafi ya Agrif naya binsa abaya har wajen parking spot duk da dare ne a kwai driver da yake idon sa biyu dan duty duty sukeyi ganin Nasara yasa da sauri ya mek'e jikin sa na rawa ya bude a katin a jiyan mukullayen motan yana ganin motar da yaga Nasir ya tsaya ajikin sa cikin saurin ya dauko key din da sauri ya nufi motar Yana budewa Nasir jiki na rawa yasa Nasrim aciki Agrif zai shiga Nasir ya masa kallon sama da k'asa alaman dubi halin da kake ciki sai a sannan Agrif yaduba jikin sa ashe daga shi sai towels ne komawa yayi da baya cikin sauri.
duk gudun da drive yakeyi amma Nasir sai fada yake masa yana danna k'irjin Nasrim dan yabata temakon gaggawa shi yamafi jin abin cikin ta idan akace cikin nan ya zube to