Showing 78001 words to 81000 words out of 155717 words

Chapter 27 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt

29 Oct 2025

658

itama shi zatayi uban ta ma ya yanke mata hukuncin balle mu kuma ya rubuta horo me tsanani ajiki da bai rubuta ba da bazamu saka taba".
ta k'arashe maganan tana ficewa

can Nasrim ta bude Ido arazane ta mek'e ta zauna zata cire dripe dinda yake hannuta sister Safeeyya ta rik'eta tace'' please Halima kar ki cire".
"Doctor dan Allah da gaskene mommy na ma ankama ta dan Allah meyasa rayuwa ta juya mana baya meyasa hakan take faruwa damu wllh mommy tama shirri aka mata kamar yanda aka min nasani mommy bazata kashe Hajja ba".
"Please Halima saurara waye yace miki mommyn ki tayi kisan kai karya ne mommy ki ko dazu tazo to abinda yasa bata ganki ba duk Wanda aka yanke masa hukuncin irin naki ana jimawa ba azo masa visiting ba kinga ke yayanki Kamal jiya yazo kuma Dr Hafsa tazo shine aka hana mommy ganin ki amma tazo".
Nasrim tace "wllh wancan maam din ce take gayamin yanzu".
sister Safeeyya tace'' auke dama wancen mahaukaciyar ce ta gaya miki kuma kika yarda kinga alamun hankali a tattare da ita ai mahaukaciya ce".
shiru Nasrim tayi tabbas da alaman hauka ajikin matar kam ko dan ba sabawa tayi da ganin irin wannan mutanen ba ita hatta masu aikin gidan su sunfi wannan fasali wai ahakan ita ma aikaciyar gomnati ajiyar zuciya ta sauke tace'' shikenan Allah yakere mommy da Khafulan da Zainab".
Sister Safeeyya tace'' Amin harda abinda yake jikin ki ko"?
da sauri Nasrim ta shafa cikin ta tabbas tayi wata biyu bata ga period din ta ba wannan hargitsin ne ya hana ta gane ahankali ta shafa cikin na ta koma ta kanta tana ambaton Agrif haka zakamin
katafi ka barni awannan duniya Allah kadau Raina ka kai inda ka kai na mijina towai ni mema ya faru har yamutu ah ah na tuna Izza ce tace zata shigo rayuwar mu amma ban kashe shiba fa mijina nefa yanka kane fa kawai kawai dan kaji tsoro kace kafasa ai da zan kashe da tun lokacin dana yan kekan zan kashe ka amma hannu ka fa kawai na yanka kuma ai kaya femin zamu gudu fa kace ni dakai mun saba yafewa junan mu fa .....
Sister Safeeyya tace'' dan Allah Halima kiyi hakuri ki bawa Brain dinki huto kinga fa har yanzu arikice kike ai da tun farko kin bawa lawyer ki hadin Kai da tun azaman farko baza akayo ki nan ba dan bawani hujja sashishi da yatabbatar da cewa kece ki kayi kisan in kece a video din da yaron ki yamiki ai bakiyi magana anji muryar ki ba kuma fuska arufe ida kece meyasa zaki rufe fuska tunda da faro fuska abude kikayi barazanan kuma meyasa akayi deleted din CC TV na gidan daga karfe daya na dare zuwa k'arfe biyu inda kece meysa bazaki yi delete din daga inda kika wasa
wuka harzuwa inda kike masa farazana ba kai wannan abinma ba na dauka bane kibawa Brain naka hutu insha Allah za adauka k'ara gaskiya zai fito akama melefi a dauwa mijin ki da yaran ki fansa kiyi kodan yarinyar ki macce idan kika bar abin ahaka zai shafi yaruwar y'arki idan ta girma me auran tama sai ta rasa za ace ai uwar ta ita takashe uban ta akan kishi kinga zaki jefa rayuwar ta cikin matsala ki daure ki zama jaruma ko dan yaruwar y'arki shi namiji bashi da matsala Sosai kamar maccen".
girgiza kai Nasrim tayi tace "a a akasheni ni dan Allah bana son na kashe kaina na tashi kafura bayan Agrif musulmine kinga bazamu haduba nafison akasheni dan Allah Ina son na mutu".
hannu ta sister Safeeyya ta sake kamawa tace" kinsan wani abu Halima idan kika kuskura aka daukaka k'ara kika amsa ke kika kashe su bayan kina da daman da zaki kubutar da kan ki wllh da keda Wanda ta rataya kanta ta kashe kanta daya bazaki taba ko hada hanya da Haruna ba amma idan kika fadi gaskiya wllh akwai hujjojin k'arfafa da zaki fita cikin sauk'i a zaman farko ma dan haka ki daure ni kuma idan lawyer ki yazo nace masa yanemi k'arin lokaci dan ki sake samun nutsuwa dan saura kwana ashirin da ukku ayi zaman amma zance yanemin k'arin lokaci baki da lafiya zan bashi katin ki yakai dan asan kina da ciki kafin lokacin kin gama shiga hankalinki Agrif da yaran ki yanzu sunfiki samun nutsuwa nuna gidan aljannan ki kwantar da hankalin ki kinji wata rana zaku hadu tunda dole kowane rai sai ya d'an d'ani mutuwa".
Nasrim tace" aunty Agrif dan aljannan ne duk halinsa irin na yan aljannan ne hakuri saurin yafiya sauk'in Kai tsoron Allah biyayya ka iyaye tausayi Kai wayo gidan marayun sa na Zaria ko wa zai na kula dasu yanzu
bayan haka akwai kuragu da makafi da sauran nakasassu da yake biyan su albashi duk wata dubu talatin wa zaici gaba da biyan su dama ni yake sakawa ko baya k'asan nake vocher duk wata sai ansamu k'arin mutane yanzu waye zanyi duk wannan".
Sister Safeeyya tace'' ke Nasrim amma sai kin yarda kin rayu ke zaki cikaba da yimasa sadakatun jariya duk abinda mutum yafara amma Allah bai bashi ikon gamashi ba ya mutu akai to duk wanda yazo ya daura daga inda yatsaya Allah zai bawa wancan ma ladan sa shima Wanda yafara yai bashi batare da yaragewa kowa ba wannan Yana daga cikin adalcin Allah da rahaman sa yanzu ko shekara nawa kikayi kinayi shi Yana da lada kema haka idan kika koma ga Allah duk Wanda yazo yasake farawa kina da Lada shiwanda yafaran Yana dashi shima Haruna Yana da shi dan sada katunl'jariya ba karamin abu bane Allah kamamu ikon yin sa ko da kadan ne".
numfasawa tayi tace'' insha Allah Aunty inde da Raina sai sai na k'ara daga inda ya tsaya yanzu haka inda za aduba account din Agrif wllh baza asamu kyakkyawar Million talatin ba duk yayi kyau dasu kullum bayar wa yake su ya Kamal har company ne dasu Abbaty ma k'anin sa amma shi kullum idan nace meyasa ba zayyi tatali ba tunda dukiyar ba dashi bace dukiyar mutum ba abin dogaro bane sai yace'' shima rai ba abin dogaro mane Wanda kabayar shine naka acan inda ran zaije ashe da gaske tanadin yakeyiwa kansa Allah yasa halayen sa masu kyau subishi wayoo Haruna meyake faruwa".
b'ata rai sister Safeeyya tayi tace''zaki fara ko bari ma na miki alluran bacci kada wancan azzalumin tazo taga idon ki biyu ta ce kikoma ciki".

**********************
*Three brother house*

da alama meeting akayi Hajja an salamota tana zaune Nasir cikin b'acin rai yace " to idan ba atsakanin mu abin ya fito ba waye yafito da magana bayan nace abar abin a hannu na ni zan dauki mataki nasa anzo an kama mommy amma kuka fitoda maganan nan a duniya kowa yaji duk inda kalek'a a duniya hoton mommy ne koma wane danshegiyar ne ya fitar to zan bincika na tabbatar a cikin gidan nan abin yafito wllh ko waye idan nasamu dasa hannun sa wllh abin bazayyi dad'i ba kuma a kansa zan dasa binciken abin da yake faruwa".
Abbaty yace'' yes boss wllh nima abinda nake son aduba kenan wllh boss Ina tausayin Nasrim". haka de kowa ya tashi gida kam kowa yanzu jikin sa lak'os Hajja ma tunda abin yafaru da ita shiru kake ji tayi k'im tana tsoron ran

Izza ma samun Baban tayi tayi masa tatas da cewa idan ma shine yake kashe kashe to wllh itan yakashe Hajja burin na auren Kamal bazai cika ba
Dariya yayi yace tasu ma ta ishe su Dan har yanzu rikici gaba daka ma zata b'are musu

*Bayan sati 2*
*rayuwar Nasrim a gidan yari*
balefi ta dan sake har tana shiga cikin abokai
sannan aikin wahalan ma yanzu an dan rage mata saboda ciki ta bata wankin barguna bata faskaren itacce
sai surfe shara guga da dan k'ananun abubuwa kallon Halima da take dinke uniform nata na firsunoni tayi yarinyar k'arama Sosai cikin tausayawa tace'' niko takwara dan Allah me ki kayi aka yanke miki hukuncin rai da rai ina sausaya muku keda Lawisa da Maryama bazaku wuce shekara ashirin ba kuma gaku makarantan Al'kurani kuna son ibada sai nake ga kamar akasi aka samu balefin ku bane kwata kwata bakuyi suffan masu kisa ba".
tashi shiru tana jiran taji daga Haliman
Halima ajiye alluran hannun ta tayi ta fuskanci Nasrim Sosai tace'' Aunty Halima wllh bani da lefi kullum Ina gayawa Allah yafito dani kodan mahaifiya ta ni kadaice macce Allah ya daura mata Sona yanzu haka hawan jini ya kamata kullum ana jigila asbiti da ita wllh inason na rayu kodan ita amma gashi har na shekara anan".
gyad'a kai Nasrim tayi tace" to wakika kashe".
cikin kuka tace'' kamar yanda kika gani arubuce ajikin rigana sunana Halima Ibrahim ni haifefeyar cikin garin nan Kano ce ni daya ce mace acikin yan uwa na maza goma nice ta hudu wato Ina da yayu ukku ina da kanne bakwai maza
a cikin anguwar dawanau Ina da uwar d'aki aunty amarya Wanda tana da uwar gidan ta me yara Tara ita kuma uwar dakin tawa amarya ce dan haifuwar fari ma tayi in zata shiga wanka dasafe ni take K'ira na rike mata jaririn ta idan tayi wankan tukun zan shirya natafi makaranta haka da yamma ranan da tsausayin zai fadamin danaje da safe sai nace wa aunty dan Allah zan kaiwa Umma Mubashir ta gansa sai tayi dariya tace'' to Halima da yammma sai ki kai shi kinga yanzu Abban Rashid bai fita ba bazai bari ba nace to da yamma kuma Musa saurayina ya nace sai naje na duba yayar sa gidan ta kuma danisa idan nagaya Umma baza ta barni ba shine nayi shirin islamiya naje gidan yayar Musa ban ma same taba haka nadawo a k'afana sai da magaru ba nazo sai na tsaya a gidan anuty amarya dan nasamu nacewa Ummu anan na tsaya rike mata mubashir nasamu aunty tana wanka sai kishiyar ta tana sallah yaran kishiyar ta kuma duk maza ne suna masallaci
na samu yaron akwance acikin katifar a baranda sai kishiyar ita ma tana sallah a kofar barandan ganin lokaci yakure yasa na wallah nace Aunty amarya nazo kuma kina bandaki ni natafi na fice da saurina naje nacire kayan islamiya nayi sallan magaru ba bayan Isha Zakar dan gidan kishiyar aunty Amarya yazo wai Halima inji aunty ki kawo Mubashir Abba yakusa zuwa
sai nace ai banzo dashi ba wasa wasa shikenan sama da k'asa aka nemi Mubashir aka rasa gowa sai yace nice karshe fita kuma shijab ne ajikina sai jakata ta leda da yasinke na runguma to nan fa kowa sai yace ai yaganni rungume da rayo itama aunty Amarya tace'' aidama ni nace da yamma zan kaishi wajen Umma haka kishiyar aunty ta bada shida a kotu na taga lokacin da na dauki yaro kinji dalilinn da yasa aka yanke min hukunci zama gidan yari
Ta k'arashe maganan tana fashewa dakuka
Nasrim tace shikenan kiyi hakuri ni sunana Barrister Halima Abdulmajid insha Allah zan temaka miki saura na Maryama da Lawisa
bayan magaruba Nasrim ta samu lawisa ta mata tambaya cikin shikima tasu ta lawyer kuka Lawisa ta fashe dashi tace'' tabbas nayi kisan kai amma wllh ban zata zai mutu ba
Sunana Lawisa Hasan iyayena cikakkun yan shi'a ne wata rana muka kaiwa wani abokin Babana ziyara jigawa state a wani k'aramar hukumar malummadori kwanan mu biyu amma ban gamsu da yanayin kallon da abokin baban nan nawa yakemin ba bayan sati biyu kawai sai abokin Babana ya kawo mana ziyara shima da dare yayi kawai sai yacewa Baban mu shi bazai iya kwana ba macce ba dama da matar sa yake tafiya yanzu kuma tana da tsohon ciki bazata iya bulaguro ba kawai sai Baban mu yace sai kayi auren mutu'A da Lawisa ko da Baba yagayawa mamar mu yarda tayi tace Allah yabada lada malam ai bak'on ka annabin ka
Baba yasame ni wai naje d'aki bak'i nace mezanyi yace yamin auren mutu'A da abokin sa dan haka natashi muje Baba ya sokoni agaba har d'aki ya barni kulle koba abokin Babana yayi zai kwace min budurci da k'arfin dan naki amincewa dan ni bana ra ayin shi'a inada akidata aboye akwai wani saurayina dan izzala ne na gani kasheni kullum yana gargadina da auren mutu'A shine muke ta fafatawa har yakusa cin galaba a kaina Allah ya temake ni naga wani Reza ak'asan kujera shikuma yariga ya shagala da abin da yake bai san ma na dauki Reza ba dana kama gaban sa yazaci na bada kaine yafara sakamin albarka Yana cewa yawwa shafamin kawai ni kuma tun k'arfina na gusza Reza a gaban sa wanda najimasa ciwo Sosai yafara ihu nan take jini yafara zuba su Baba jin ihun ba iyaka yasa sukazo bakin kofar suna tambaya lafiya kasa bada amsa nayi har Baba ya tura kofan yashiga kafin akai abokin Babana asbiti har rai yayi halin sa wlllh banyi da niyar kashesa ba nayi ne da niyar na kare kaina Allah ya k'addara hakan dan ni nariga nayiwa kaina alk'awarin Habu zan bawa kaina kinji dalilin".

shiru Nasrim tayi tana girgiza kai can tace ''Lawisa insha Allah zaki fita ai kinyi ne dan ki kare kanki bawai niyar kiyi kisan kai bane kuma ko a Constitution na k'asa ba ayarda namiji yace zai nemi macce da k'arfin yaji ba inde ba matar saba ko abinda yafaru dashi shi yaja kuma auren mutu'A sahabban anbabi sunyi da sukazo Annabin duk da bai ce meyasa sukayi ba amma ya hanesu dasu kiyaye gaba dan haka auren mutu'A Annabi bayyi ba ba sunna bane Isha Allah zaki kubuta iyakar ki kiyi azumi kaffara".

Nasrim da tunanin wannan ta kwanda dasafe tasamu Maryama tana tambayar tabata tarishin ta Maryama tace'' wai me zakiyi da tarishina tarishina bashida kyau Nasrim tayi ta naci amma taki rabuwa tayi da ita
Nasrim wajen sister Safeeyya taje ta lallabata ta bata wayan ta ta kira daddy sai da sister Safeeyya ta duba sosai taga bakowa ta bata tace " to minti 1 cikin sauri hannu na rawa Nasrim tasa number daddy wanda private ne bajimawa ya dauka
"hello hello yace
shiru Nasrim tayi tana sauk'e ajiyar zuciya yace "waye akan layi kuka Nasrim ta fashe dashi Daddy da yake zaune tashi yayi tsaye Yana cewa NASRIN''
cikin kuka tace'' nice daddy "
Nasrim meyasa zaki min haka meyasa duk lawyer da yaje miki sai ki k'i bashi hadin kai kode da gasken kin aikata ne".
"Daddy bani da amsan badawa ne nide nasan ban kashe suba amma daddy Dan Allah ga wata alfarma nasamu wasu yaran da aka yanke musu hukuncin irin nawa amma bataren da bincike ba daddy inason kasamu tsayayyun lawyer su fitar dasu wllh yarane kanane basu Kai nima duk yan mata ne".
Daddy yace ok idan akayi nadu zaki yarda ayi naki kema cikin sauri tace'' Eh daddy".
"Ok zan tura Barrister shashid ya binciki ka filet din su afara aikin akansu amma yakike my daughter
" kina cin abinci Sosai naki shariyar ma sai kin haifu mun nemi alfarma an d'aga".

"Ok daddy kadinga turawa Aunty safiyya kudi ita zata dinka siyamin abinda nake so daddy Ina son naganka naga mommy naga Zainab da Khaldum".
"Ok my daughter ni ba halin na ganki mommy ki ta tafi ummara dan ta gayawa Allah kema ki dage da addua kinji".

**********************
ako kaman wasa aka fara Shari'ar su Lawisa kuma Al'hamdulillah anyi Na sara na Halima kishiyar aunty Amarya ce ta dauke yaron tsabar kishi amma de bata kashe Shiba wata kawar ta bawa kyauta a Bauchi an yanke wa kishiyar anuty amarya zaman gidan yari na shekara daya bisa adalci tunda aunty Amarya tace ta yafe
To fa wannan abin yasake jayo hankalin mutane kan Nasrim kowa sai tofa al'barkacin bakin sa yake wasu suce duk neman sunane wasu suce tana da tausayi Umma Halima zubewa tayi agaban Nasrim sai fatan alkairi take mata tana cewa insha Allah kema sai kin fita

Nasrim ta maida hankalin ta akan addua da kuma kula da cikin ta ajefi tana bibiyar Maryama dan tana mugun son jin labarin ta ko meye

**********************
*bayan kwana biyu*

Kamal da daddy
Kamal yace " daddy me yasa gidan nan daga wannan sai wannan ya za ayi ace wai anje anyi belling din mommy kuma batare da sa hannun kowa a gidan nan ba sannan ba asan inda take ba daddy hakkkin kane ka neme ta amma kayi shiru".
Daddy yace to Kamal ya kake son nayi Ina zan same ta nasani ".

"Daddy ni na bincika ance Nasir ne ya dauke da a police officer din amma tsabar ana tsoron sa ankasa tuntubar sa Ina yakai ta aiko ba komai har yanzu mommy bata gama idda ba amatsayin matar ka take".
girgiza kai daddy yayi yace" Kamal kana damuwa da abinda bawani abin damuwa ba Fanna ba karamar yarinyar bace nasan Nasir bazai cutar da ita ba in ma shi din ne ya dauketa kuma kayi lisafi mana ta gama idda furuwan abin wata ukku ne cuf yanzu so ban sani ba ko ta canza wajen zamane ".

"Daddy Nasir shi ya dauketa an tabbas min da haka amma da na tambaye shi cewa fa yayi shi bai dauki mommy ba sannan ana gani yafita da su Khafulan da Zainab sati biyu an rasa inda suke ni wllh duk motsin Nasir tsoro yake bani Ina zargin abubuwa dayawa".
Daddy yace'' me yake maka tsoron"?.
numfasawa Kamal yayi yace gani nake dukiyar mommy yake so kar ya hallakata ga yaran Nasrim ba asan inda yayi dasu ba".

gyaran murya daddy yayi yace'' Kamal ka dena irin wanna magan ganun ai idan cutar dasu zayyi bazai fita dasu a idon jama'a ba bana zargin Nasir na komai saboda bai kasance cikin masu boye abu ba komai nashi afili ya keyi ".

haka de Kamal ya tashi shi yarasa inda zai bulowa wannan lamarin k
gaba daya kansa ya gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login