Showing 114001 words to 117000 words out of 155717 words
Chapter 39 - FURUCINA NE HAUSA NOVELS BY AISHA GALADIMA.txt
da kallo ta cikin mirror zuciyar kamar zai fashe jin abin take kamar a mafarki har batason tunowa wai ita ta bawa Bayahude haƙuri da bakin ta cikin ɓacin rai ta ɗauki rigan ta saka jin zuciyarta da gan gan jikin ta take a mungun jagule yake baza ta iya tukin ba yasa ta ƙira Usaini sarkin gida wanda ƙani ne ga Bala sarkin gida da bala yayi Retire ya kawo shi
tace ya turo mata driver daya ta kwatanta layin da take dan bazata iya tuƙiba
*Three brother*
Baba Nasuru ya nisa yace " Fanna na gaya miki nifa bazan iya tunkaran Emaka ba tare da na kai mata Nasir nace ga ɗan Halima ba kinsan halinta sarai ai irin taurin kan ku daya ke da ita shiyasa tafi son ki
Halima ce ta biyo sauƙin kaina kinga shima Nasir da alaman shi yana kafiya irin naki ita ma Nasrim duk irin halin EMAKA kuka dauko kinga Nasirm ta kafe bazata yafewa Nasir ba kema ban yarda kin yafe masa ba har yanzu da wannan shegen taurin kan naki".
nisawa tayi tace "Baba tunda kace na yafe masa na yafe amma kasani Nasir yana da lefi to yanzu zuwa jibin zamu wuce mai dugurin ne da Nasir da yaran zasu shiyasa tunda ana hutu".
"Eh hakan ya kamata amma har mijinki da surukar ki duk tare zamu wuce."
murmushi Mommy tayi tace "Eh Daddy yace dashi zamu tafi balle Hajja *Alah letu kude*
murmushi shima yayi sosai yace" Fanna kinji barbarci sosai idan munje ba zamuji kunya ba Hajjan ce *Alah letu kude*
yanzu ya labarin Nasir din har yanzu shiru."
ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tace " baya cikin garin nan amma bayanai sun nuna yana cikin ƙasan nan ka san a gidan wani yaron ɗaki na yafara zama Mudansir GUGA daga nan ta kwashe duk abinda yafaru da nasir kamar yanda guga ya mata bayani ta gaya masa
ta daura da
cewa fitan sa agidan Mudan gidan wani mutum yaje waishi ladan shine wanda Nasir ya dade awajen sa".
Baba Nasuru yace" taya kuka samu labarin ya zauna a gidan ladan din tunda Guga hoton sa ya gani ya baki labarin ya zauna a gidan sa".
Mommy tace " ai zoben sa yakai ya saida to wanda ya siyi zoben yana kaiwa company a kasheda zoben shine aka kama mutunin ya nemo wanda suka je sai dawan tare zoben ya saida ya tsayawa shi Ladan din gida amma muka tambayi shi Ladan din inda Nasir ya tafi sai yace mana shi bai sani ba ashe ƙarya yake alokacin da Nasir zai tafi ya tafi da waya agidan kuma suna waya sosai amma ya buye mana yanzu de ansa matakan tsaro ana binciken shi Ladan din".
shiru Baba Nasuru yayi yana gigiza kai can yace shiko wannan bawan Allahn ya faɗi inda jikana yake mana Nasrim da take dining area tana jinsu murmushi tayi a zuciyarta tace zai zo muku da fuska abin tsoro dan nasan Hajja Ta soro dole ta goroshi agobe insha Allah wani tunani tayi tace bai kamata ta watsa masa yanzu ba sai sunzo daga mai duguri saboda kar ya muso kancan din tafiya
Mommy tace "to ni Baba baka taba faɗamin abinda ya haɗaku da Mama ba dan Allah yau ka faɗamin".
numfasawa Baba Nasuru yayi yace kamar yanda na faɗa miki ni ɗan mai duguri ne ina da mata da yara biyu maza kuma ina zuwa lagos neman kuɗi kusa da inda Emaka da mahaifiyar suke ƙosai anan nake wanki da guga da gyaran ta kalmin idan ya samu to ana cikin haka emaka ta kawomin tallan kanta ita de tana sona kinsa alokacin nayi kyau sosai duk baƙine ni ina da hanci da tsowo da dogon fuska kuma shi kuka gado halima kam ma kamar kara aka tsaga dani sai yara na na mai duguri Girema bai biyoni ba mahaifiyarsa ya biyo amma Bana ya biyoni sosai
haka Emaka tayi ta shigemin har nima naji na fara son ta amma dama tana nuna ƙyama ga addini na bata son muslumci sosai soyayya mu har tayi ƙarfin da ta kaimu ga maganan aure Emaka masifafiya ce gani kasheni bata barin iyayenta ma balle yayunta ba wanda take tsoro a familyn su sai ita ake tsoro tana juya kowa a gidan yanda takeso dan haka ba wanda ya musa mata da tace ni zata aure wani limami ne ya tara musullamai aka daura mana aure ita tayi al adan su sukasha biki ita da ƴan uwanta muka tare ita tana fita sana arta nima ina fita nawa naso naja ra'ayin ta muyi planning amma ina gaskiya Emaka tafi ƙarfina ban son haifuwa da ita saboda muddin muka haifu to zata saka min yara cikin kafurci nikuma ba abinda na tsana irin addinin christian shi yasa banso mu haifu ba amma da tagane sai tafara fadan musulmai muna fukaine ina moran jikinta amma bana son haifuwa da ita sai nafito na gaya mata ga abin da nake gudu sai tace idan hakane ba damuwa zata bani dama idan muka haifu nima na nunawa yaran addini na ita ma tanuna nada duk wanda yayi rinjaye shikenan na amince da haka tunda nasan hujjan musulmi yafi na kafiri ƙarfi nasan nine da nasara mukayi wannan alƙawari shakara daya Allah yabamu ɗa namiji na saka masa Muhammed ina ƙiransa Mala ita kuma tana ƙiransa Friday Mala yana da shekara hudu aka haifeku to gaskiya Emaka ta samu nasaran akaina akan mala saboda tanayiwa yaron wani irin so da jansa ajiki sosai ko waƙa irin na coci yakeyi duk abinda nake koya masa baya dauka ni kuma ganin bazan iya barin ɗana ya shiga hanyar ɓata ba yasa nasa aka tsacemin shi zuwa maiduguri dama ƴan uwana sun san da maganan auren kafura da nayi tunda ina yawan zuwa ganin gida
sosai na tada fitunan Emaka ta ɓatar min ɗa nida ita har wajen yan sanda akan ita ta ɓatar min ɗa tane bo sosai na tada bori hankalin Emaka ya tashi sosai da tana mugun son MALA sonda ko keda Halima banayiwa haka de mukayi ta nema har ta haƙura gani na kawar da matsalan Mala yana inda zai tashi da Addini na yasa duk hankalina kuma yakoma kan ku sosai nake janku ajiki mude bakin kuma da BISMILLAH kuka fara saboda komai zanyi sai nace bismilla idan zan ajiyeku da bismilla idan zan ɗauƙe ku idan zamuci abinci kai har ni kaina ya zame min jiki alokacin ko magana zanyi sai nace bismilla komai yara suna bude baki suma suka fara shiga banɗaki addua fitowa addua ga na siri sallolin nafila agida tunda farali a masalaci nakeyi kullum nafila sosai nayi iya kokari na lokacin shekaran ku uku Matata Fanna wanda sunan ta nasaka miki wai ta gaji ta tako tazo lagos da yaran Girema da Bana dakuma MALA ɗan wajen Emaka to fa aranan ne babban tashin hankalin ya faru ban taba tsammannin masifan Emaka yaka haka ba ashe tana ragamin saboda son da take min aranan yan aguwar ma basu samu bacci ba ta tafi ƙiran yan sanda na dauƙi matata da yaran ta da Mala nakai tasha Allah ya temaka nasamu mota saura mutum daya ina sasu nace taje dasu ni ma idan na samu na dauki Fanna da Halima zan gudo
ina zuwa gida naga ta kawo yan sanda suka tafi dani nasha azaba sosai ahannun su amma duk tambayar suka min sai nake cewa ba ɗan ta bane ɗan gidan matata ce nace kuma kama suke dani shima mala dani yake kama gani ba yanda basuyi ban faɗa ba yasa dole suka rabu dani sosai nake lalaba Emaka akan tayi kaƙuri muci gaba da zaman mu kamar da fir taƙi wai naci amanan ta ban sanar da ita ina da mata ba ni kuma lallaɓa tan da nake dama nasamu na dauke kune na gudu amma tayi mugun sa ido akan ku saboda sace mata ɗa da akayi wata rana ke ta daukeki ta tafi coci na dauki Halima muka gudu kinji iya abin da ya hadamu da ita kenan
mukuma mukayi hatsari a hanya yanzu babban abinda nake damuna yanda zan fuskanci yara na maza uku da Matata Fanna sarkin haƙuri ƴar aljanna Allah yasa ma tana raye na nemi yafiyar ta ".
Na sauke ajiyar zuciya tace " , Insha Allah zata yafe maka Baba".
washe garin ranan birthday din Abdul Nasrim ta kalli Humairan da take ta shirin fita tace " amma de ba fita zakiyi bako Humairah tana gyara rolling din mayafin ta tace "fita kuwa akwai wani case da muke dashi gobe za ayi zama wllh wani tsohon banzane yayi wata yarinyan yar shakara 9 rapping shine nake son nasamu zama da iyayen yarinyar kafin goben".
ta ƙarashe maganan tana shirin daukan jakan
Nasrim tace " amma inaga kin manta da yau ne birthday din Abdul naga bakiyi kowane shiri ba ana su Muwadda iyanzu har an fara shirin party kuma ke kika shirya a ina za ayi cake din ne nasu Muwadda yayi kyau sosai ayi a inda akayi nasu dan Allah kinsan lokacin da akayi nasu Muwadda nawa cikin sukunin dina ai".
cikin rashin damuwa Humaira tace "ba wani birthday din da za a masa yaron da uban sa yake kulle meye nashi na birthday wllh ina mugun ta kaicin haɗa jini da Kamal".
hararan ta Nasrim tayi tace " ok yanzu kenan saboda Ya Kamal ba ƙe son Abdul kenan to nifa nayi yaya da Khaflan da yake ba ɗan sunna bane".?
Humairah tace '" ai wannan ƙaddara ce."
Nasrim tace shima Ya Kamal ƙaddara ce laifin da yayi kuma da makirci irin na uwar sa idan ki ka bari lefin ya kamal ya shafi Abdul baki masa adalci ba".
da yamma sosai Nasrim ta shiryawa Abdul birthday da ya ƙayata kowa saide sunyi kukan rashi Kamal sosai rashin Kamal yake damun mutanen gidan kodan dama can shine a gida sauran ba zama suke ba
ba shaƙuwa kamar na Kamal
washe gari akayi shirin mai duguri
Nasir ne ya shigo da sallama dan ya gaida Ta soro tana waya ya sameta
"yo ai Nasurim da kin gaya min da na miki rakiya dama ina son naje naga garin ƙamshi sai jin labarin sa nake".
saurarawa tayi can tace "Allah sarki to akawo mana kayan ƙamshi sosai anjima zan ƙiraki ga balarabe yazo zamu gaisa ai rannan kina fita ba jimawa ya shigo ashe wajen Jafaru ya leƙa kinsan dama Jafarun ne yayi hanyar haɗuwar mu Jafaru mai gadin kidan Alhaji yahaya".
sai da tabari ta saurara
ta sake cewa wllh kuwa ya miki baƙin cikin ganin wannan kyan nasa koda yake ai shima yayi a saran ganin naki kyan kin san ance abincin ido ganin abu me kyau shiyasa ni ko sanda na ke FADA wllh dan dole nake ɗaga ido na kalli gimbiya Murja nafi son na kalli gimbiya Balaraba ai wata zan kai ki fadan nan ki ga gimbiya Balaraba
to to a sauƙa lafiya".
Nasir yace
"HAJIYA waki ka samu ne"?.
" da mutumiya ta mana kaji wai tana hanyan mai dugurin garin kakan nin ta amma dayake in bata ga dama ba miskilan kanta ce zuwanta shekaran jiya bata gaya min zata tafi ba ko tana min baƙin cikin naje na kwashi ƙamshine waya sani ita mata ta ibi ƙugu kamar balam balam wllh duk mai rabon da ya kwashi wannan ƴa ummm zai kwashi kayan aiki ai shiyasa Ma'aruf ya rikice wai shi sai ita shegiyar uwar wai ya zai auri bazawara a auren fari yabari ya auri FIRDAUSIN in yazo ya ƙara da ita Nasrim ita kuma da yake da ruwan hanji aka wanketa zata tsaya jiran sa tana son ta mana a saran hada jini da gidan arziki yo idan jikana ya aure ƴar gidan jiri buroda ai fasa kaina ƙaruwa zayyi zan ƙara daraja a idon mutanen fada yo yanzu ma fa sun fara cewa dama mu dan gin sune idan jikana ya auri masu kudin duniya ai ƴan uwan su zamu zama ba dangi ba yo yanzu mafa idan na shiga fada kilishina daman ita nazama sirikar tiri buroda ai jerawa zanyi da mai babban ɗaki muzauna uwar sarkin gaba ɗaya baride Alhajin Allah yazo ya samu sarki da manyan mutane suje mana tambaya kaga ni baruwana da wani baza wara ce ai ANNABIN ALLAH ma da bazawar rar data girmeshi shekaru ma yafara yo ba sunna bane ai masu farawa da zawarawa sune a gaba gaba a wajen annabi ni nayi wasa da mutanen sai de muji labarin su agari yanzu gashi munsan jina".
Nasir de murmushi yayi yana tuno kalman ta na duk wanda ya ibi Nasrim ya ibi kayan aiki
gyada kansa yayi afili kuma yace
to Hajiya kuma ita ta amince zata auri Ma'aruf din?".
"kajini da wani zance yo kai kaga Ma'aruf dinne hai ko mace bata soshi da komai ba ta soshi dan ƙyansa uwar fa bafulatana ce kasan ni yara duk bana bari su auri mummunar mace shiyasa koda Isiya da Baban gida ba suyi kuɗi ba to yaran su ƙadaran mune balle ma gashi nan sunyi ƙudin zata soshi tunda tana kulashi yanzu ma".
Nasir de ya gaji dajin surutun hajja ya tashi ya fice tana ƙorafin miskilan cin sa yayi yawa baya tsayawa suna fira wllh sai ta rake masa albashi inde ba zaina zama tana bawa idon ta abincin saba
wani godon ajiyar zuciya ya sauƙe yace *YA ALLAH KAGA YANDA NACI BURIN ZUWA WAJEN FAMILYN MAHAIFIYA TA AMMA GASHI YAU ANTAFI BABU NI MOMMY YAUSHE ZAKI GANE GASKIYA KI SO GANI NA KI NE MENI ILOVE MY MOMMY*
ya ƙarashe maganan yanayin fuskan sa ya mugun canzawa ba ƙaramin missing din Mommyn nasa yayi ba
*Mai duguri Barno birnin shehu*
a gurguje
su Mommy sun sauƙa a cikin garin Alhadulillah Baba Nasuru ya samu dangi wanda suka rage wasu kuma Allah ya musu rasuwa akwai dan uwansa daya ADAMU ƙanan sane yayun sa duk sun rasu sai yaran sa da sauran dangi matar Fanna tanan da ranta yaran Bana shima yana mata biyu da yara sunka shashida Mala yayan Mommy matar daya da yara tara cikin yaran Mala abin mamaki harda zuhura yariyan da suka danyi sabo da Nasir har Mommy ta kecewa ya aure ta Girema ne bayanan yana lagos amma an ƙirashi yace gashinan zuwa aranan Mommy tayi mugun tausayawa dangin nata duk baza aƙirasu talaka ba amma de baza ace masu kuɗi ne sosai ba ashe Zuhura ma scholarship ta samu tafita DUBAI din karatu har suka hadu da Nasir din Mala principal ne nawani makarantan Secondary na mata sai Bana da shima de aikin gomnati yake bawani babban ma aikaci bane shima Girama ɗan kasuwa ne a lagos
Mommy sun sha kuka sosai duk suna zaune bayan cin abinci dare sai fira suke yara suka fara shigowa da kaya suna ihun ga Babakura ga Babakura
Girema shi ya shigo da saurin sa MOMMY ta miƙe tace SHARIF!!!!!!!
shima Girema yace Fanna!!!!??
Mommy tace" Sharif dama baka mutu ba ? .
ban mutu ba Fanna kece ƙanwata Fanna."?
itama nunasa tayi tace "kaine Yayana Girema da muke jiran zuwan ka
Baba Nasuru da su Hajjja sun nemi sanin me yake faruwa fanin Mommy ta fadi tana ta kuka Girema yace Fanna budurwa tace munkai kusan shekara 8 muna tare ni narabo ta daga cikin danginta na kawota mai duguri tayi karatu daganan na nema mata aiki akano amma sai da nasaka ranan auren mu da ita yarage sati ɗaya tak na aika mata da soƙon nayi hatsari na mutu sabo na fasa auren tane dalilin dogon nazari da nayi na ganin Baban mu yayi aure a lagos ya ƙimu ya watsar mu naji tsoron na auri ita Fanna ashe Allah yaso mu da rahama da ya zamuyi idan muka auri juna nida ƴar uwa ta Alhamdulila Allah mun gode maka da baka bari munyi wannan ƙazantaccen auren ba daga baya ina bibiyar fanna sosai ko da mijinta ya rasu naso naje amma naji tsoron yanda zata fassara abin da namata dan dama can ni zuciyata bai amince da auren fanna ba shiyasa ko sunana na gaskiya ban gaya mata ba kawai de ina son in rabata da addinin da take cikine".
Baba Nasuru yace Girema ku yafemin daga nan shima ya kwashe abin da yafaru dashi ya gaya musu
Hajja tace" ai dama shiyasa akeson bincike a aure Annabin Allah yace bincike a aure ya halasta".
su Mammy sun zaga dangi sosai kuma anata zuwa musu ka dauko kwana hudu sai da sukayi sati guda har Hajja aka zauna dan itama tace garin yamata daɗi sosai Dddy da Abbaty ne suka koma washe gari
aranan da zasu zo da kuka suka rabu shiko Baba yace ba komawa har yasa an baida masa auren sa da matar sa
su Baba an zama ango yasha tsokana ko awajen jikoki
Nasrim washe garin zuwan tafito da shirin ta sai gidan Ta soro nesa da gidan tayi parking ta fito a ƙafa ta taka knocking tayi yazo yana ganin ta
ya saki murmushi yace" lokaci yayi".?
bata masa magana ba sai murmushi da take jifan sa dashi tafara murda murfin kwalban da yake hannun ta
ta jefar da murfin still de tana jin sa da murmushi tace " da kunnen ka da idon ka zaɓi wanda zan rabaka dashi yanzu".
yayi murmushi cikin izzar sa ya tsaya a gabanta ƙyam yace "wannan zaɓin kine wanda baƙya so zaki zubawa".
tsayawa tayi tana kalon gefe da gefen alaman bata son wani ya ganta
idon sa a rufe yace " amma ko duk kina sone ba wanda baƙya so daga idon har kunnen duk kina so
cikin wani irin ƙarfin gwaiwa ta ɗaga kwalban ..................
*sis muhadu a pg 28 dan jin me zai faru da nasir NA GODE SOSAI DA COMMENT DINKU ALLAH YABAR KAUNA*
ƁJ
[4/8, 1:49 PM] Batul Adam Jattako: *FURUCI NA NE*
(```Rikicin Babban Gida```)
*NA*
*BATUL ADAM JATTKO*
```Marubuciyar```
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*