Showing 15001 words to 18000 words out of 130248 words
mu'amala da Aljanu,domin wasu Aljanun har Auren mutum suke, za'a ga mutum baya sha'awar aure ko kuma bashi da sha'awa gaba ɗaya,abinda nake nufi da sha'awa shine; ko yaga wani shashe na jikin mace ba zai taɓa ji mazantakarsa ta mutsa ba, bare har yay tunanin kasancewa da mace, zamu kawo misalan yadda ake gane Aljani ya auri Mutum ko kuma yana jikin mutum a haɗu bar mu ta gaba.
Ajjiyar zuciya Sheikh ya sauke mai ƙarfin gaske,kafin yaja baya kaɗan shi kaɗai ya shiga sauke tattausan Murmushi ya nayi yana jan ƙwantaccen bear ɗinsa, cikin ƙasa da Muryar kamar mai raɗa idanunsa akan camera yace "Baiwar Allah fatan kinji amsar tambayar ki kuma kin gamsu? Allah ya kyauta ya kuma tsare mu daga sharin kafiran Aljanu".
Gaba ɗaya cikin Masjeed ɗin suka amsa da Ameen. Suna cikin mota Sheikh yana driving cikin ƙwarewa ba tare daya saurar abinda Arjun yake magana akai ba, ganin Sheikh ya ɗauki hanyar zuwa gida yasa Arjun marai-raice fuska yace "Haba Buddy bana ce zaka rakani zance wajan Aliyah ba?" Ɓata fuska Sheikh yay yace "Nifa ba za'a kai ni wajan da za'a dinga zabga ƙarya ba" dry Arjun yay yace "Au ƙarya ake a zancen? Malam just wait and see za kaji yadda ake faɗar kalamar soyayya" shiru Imam yay Arjun ya ce "fara kai ni gida na ɗauko mata gift ɗinta" kallonsa Sheikh yay kamar zai magana sai kawai ya karya gwana, a compound ɗin gidansu Arjun yay parking Arjun ya ce "ba zaka shiga wajan Ummi ba?" Girgiza kai Sheikh yay yace "kace ina gaisheta,nasan za ta ce sai na ci abinci ni kuma am full" kafin Arjun yay magana Ummi dake bayansa ta ce "Daman always you're full,kawai kace furar Granny za kasha"
Murmushi kawai yay mata kafin ya lumshe idanunsa yace "Evening Ummi" "how are you?" Ya ce "Allahamdulillah!" Daga nan ta shige cikin gidan, Arjun yabi bayanta yana riƙe da hannunta, da kallon sha'awa Sheikh ya biso yana ji inama mahaifiyarsa ce Ummi.
Bayan sun isa gidan su Aliyah Arjun yay mata waya daga can ɓangaren ta sauke ajjiyar zuciya kafin ta ce "fatan mijina ya sauka lfy?" Murmushi yay mata har cikin zuciyarsa yake jin ƙaunar Aliyah yana mutuwar sonta kamar ransa "Surprised?" Ware ido tayi ta ce "What a good news?" Cikin jin daɗi ya ce "Tare muke da Buddy" saurin faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" tayi sbd yadda taji gabanta ya faɗi,cikin ƙarfin hali tace "Sure?" Da sauri ya ce "I mean my words Matata" miƙewa tayi tsaye tana gyara zaman rigar jikinta wacce ta amshi jikinta sosai, Aliyah fara ce sosai tana da ɗan tsayi ba sosai Mahaifinta shine senator na lokacal government ɗin su, ita kaɗai ce wajansa,sun haɗu da Arjun taje shopping shi kuma yaje siyowa Sheikh sabbin jalabiyoyi, a nan sukai exchange na number "come in" daga can ɓangaren Arjun ya ce "No muna sauri lokacin shan furar Buddy yayi" ok kawai tace masa kana ta kashe wayar, parfume tasa masu ƙamshi ta gyara zaman veil ɗinta, but ƙasan zuciyarta taoroy da far gaba ne, tun daga nesa Arjun yake kallonta yana jin kamar yaje ya rungome ta sbd yadda ya kejin ƙaunarta a ransa, fuskarta ɗauke da Murmushi tai masu sallama, Amsawa Arjun yay yace "Ma sha Allah tawan kinyi kyau fiye da ko yaushe" cikin ƙasa da Murya tace "Fatan kana lfy kamar yadda zuciyata ta sanar dani?" Kallon Sheikh yay dake cikin mota ya lafe jikin kujera idanunsa a rufe sai ƙirjinsa dake ɗagawa da sauri yace "Wow ashe haka zuciyarki take da faɗin gsky?" Shira suka taɓa kafin yace "Ga Buddy ko gaisa zamu huce" kallon cikin motar tayi a zuciyarta tana faɗin Tubarkallah ma sha Allah barakallahu ahhasanal kaliƙin Ubangiji yay halitta a nan, da sauri Aliyah ta ɗauke idanunta ta ce "kamar bacci yake" dry Arjun yay yace "haka yake fa, ƙilan zaman ya damesa" cikin motar ya leƙa tare da bubbuga murfin motar yace "Buddy! Buddy!" Ware firgitattun idanunsa yay "What again?" Arjun ya ce "Ruhina ke gaidaka" kallon bayan Arjun yay kallo guda yay mata yay saurin janye idanunsa tare murza zoben hanunsa ka ɗan yace "Ykk?" A fili tace "tab" Arjun ya kalleta ya ce "me" girgiza kai tayi tace "Ina lfy ya jiki?" Ware fararan idanunsa yay kafin yace "Lafiya" Wannan idan bai ji dakai da kuma miskilanci ba ai sai Allah ya tambaye sa da sauri Sheikh yace "me kika ce?" Rufe bakinta tayi tace "No ba dakai nake ba" a zuciyarsa yace "Ƴar ficika kawai" bayan sun gaisa Arjun ya bata tarkacan chocolate daya siyo mata, Sheikh yace ya gaji dole suka sauya waje Arjun yay driving nasu zuwa gida. Misalin 10:30 na dare Sheikh na zaune a parlour'n sa daga shi sai 3gauther fresh skin ɗinsa sai Shinny take ga yadda 6packs ɗinsa suka ƙara buɗewa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa yana ta gyalli hanunsa riƙe da mug yana shan coffee, idanunsa ba kan cenema yana Kallon Tafsir a Sunna t.v, bayan an gama tafsir ɗin ya sauya channel zuwa zee world, samu yay ana film ɗin johda &Akbar bai taɓa tsayawa yayi kallo ba,amma ganin film ɗin na musulmai kuma na sarauta sai abun ya birgesa, lumshe idanunsa yay lokacin da yaga Akbar yay kissed ɗin Johda, cikin ransa yake faɗin ko meye abin daɗi a nan ohhhu? Yana nan zaune yana shan coffee kamar bai so amma gaba ɗaya tunaninsa yana kan Airah shi kaɗai yasan yadda yake a zabtuwa da rashinta a ɗan wannan lokacin da yay sabo da ita, tana ɗebe masa kewa fiye da tunanin mutum yana samu kwanciyar hankali da ita, at least ya samu wacce za tana rarrasbinsa zata rungomesa idan yay kewar Amininsa,tana ƙoƙarin bashi farin ciki shiyasa ya yarda da ita sosai ya bata dukkan yar darsa, ta riga ta samu gurbi a zuciyarsa baya jin akwai halin da zai shiga bai tuna da Aljanarsa ba, Aljana ta fi masa sauran mutane da yawa, Aljanarsa ta fi masa Amminsa ta fiye masa Abbansa, tayaya zai iya mantawa da ita, lumshe idanunsa yay yana jin ɗaci a ransa yaushe zai samu freedom ne kamar yadda kowa yake dashi? Yaushe zai zama cikakken Namiji mai lfy? Yaushe zaiji feelings akan mace kamar yadda Arjun yake gaya masa a kullum, cije lips ɗinsa yay tare da fesar da numfashi, hanunsa ya shiga miƙawa wajan table yana son ajjiye cup ɗin hannunsa cikin rashin Sa'a ƙafarsa ta zame daga jikin Wheelchair, ƙara ya ɗan saki saboda tsoratar da yayi kafin ya ƙarasa ƙasa Airah tayi saurin taresa ya faɗa jikinta.....
20/10/2021, 20:42 - 🤔🤔: *SIRRIN MU*
*BY*
_✍🏾 NIMCYLUV_
_it's #500 via 0116886423 Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 ga ƴan Niger suyi mgn ta nan 84506476_
🆓P
EPISODE1️⃣5️⃣-1️⃣6️⃣
Murmushi Airah tayi tace "Meyasa kake punishing kanka?" banza yay mata shi a dole yayi fushi da ita why zata tafi ta barsa a lokacin daya saba da ita? Ganin yadda ya marai-raice fuska yasa ta shafi fuskarsa cikin lallashi tace "Am sorry ban ƙarawa ka ji" kai ya ɗaga mata kafin ya zame a hankali ya ɗaura kansa saman cinyarta tare da lumshe idanunsa wanda suka sauya launi, yana jin kansa cikin farin ciki a duk sanda ya kasance da ita, amma mai yasa baya jin feelings ɗin da Arjun ke faɗa masa? Ko dai da gaske bashi da lfy ne luff yayi a jikinta kamar ƙaramin yaro, duk da cewa yana da shekaru Amma Imam shagwaɓaɓɓe ne na bugawa a jarida, yana da haƙuri, juriya, da wahala kaga damuwarsa yana da ɗaga ƙafa akan laifukan da mutum zai masa, Amma idan haƙirinsa ya gaza sam bai iya fushi ba, kaifi ɗaya ne idan yace Yes! babu wanda ya isa ya sauya masa ra'ayin da zai sa shi faɗin No!, Kaifi ɗaya ne yana tsayawa akan Dukkan abinda ya keso baya nuna gazawar sa ko kaɗan, yana da taurin kai idan yace yana son abu baya taɓa haƙuri dashi sai ya same sa, shi kansa sometimes yana mamakin halinsa ya ci ace yadda yake Malami ba komai zai zama halinsa ba, amma idan ya duba yaga hali ba kai kake samawa kanka Allah ke yo mutum a haka, sai ya ji sauƙi a ransa."yau ka gaji da yawa ko?" Hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa yana ɗan murzawa yace "Yeah! Na raka Arjun zance" kansa ta shafa tace "I knew, hope da sauƙi jikin naka" juya idanunsa yay yana kallonta yace "Wane yace bana da lafiya ?" "Au sai wani ya gayan bazan iya sani ba? Nasan cewa yau ɗin ba daɗinta ka ke ji ba kawai dauriya ce irinta ta jaruman maza kuma sadaukai", miƙewa yay zaune yace "tell me something, Arjun yace duk sanda ka kasance da mace kana jin feelings da sha'awarta, har yanayinka ya sauya Manhood ɗinka ta fara harbawa" shiru tai sai kuma tace "Of course ,hakan na nuna cewa Mutum nada cikakkiyar lafiya ai, ko a mata haka ne bawai iya maza ba" marai-raice fuska yayi yace "kenan bani da lafiya?" Itama tace "who tell you that?" Komawa yayi saman cinyarta ita kuma ta cigaba da massaging kansa yace "na fahimta ne, saboda jikina baya bani abubuwan nan idan na kasance da mace" gemunsa taja tace "au har mata kake kasancewa dasu?" Kai tsaye yace "You're the first person and last dana taɓa sani har na amince da ita" Airah ta kallesa tace "Kai cikakken mai lafiya ne fiye da sauran mazan da suke da lfy, you have a beautiful and big dick, kana da lafiya kai lafiyayye ne Rayuwata I don't know how to explain saboda SIRRIN MU ne wannan but wata rana zaka ce na faɗa maka" kamar zai mata kuka yace "i don't have any feelings a kanki" dariya tayi tace "it's complicated ka ji fellings akai ne" buɗe baki yay zai mgn tai saurin rufe masa baki tace "You need to rest now" miƙewa yayi zaune ita ma ta miƙe tsaye gyara masa bedroom ɗin tayi in few seconds bama minutes ba abinka da aikin aljanu, bayan ta gama ta haɗa masa warm water a cikin jakuzzie, ta taimaka masa tai wajan zuwa bathroom ɗin, Lokaci da ruwan zafin ya ratsa jikinsa lumshe idanunsa yay yana ƙara nutsewa cikin jakuzzie, yana ta zaune kamar bazai wankan ba sai kuma ya fara yanayi yana fesar da numfashi, bayan ya kammala ya haɗe cinyoyinsa sosai ta yadda babu mai ganin jikinsa kana ya ɗan fara buga gefen bango, babu jimawa ta shigo tare da miƙa masa towel kana ta buɗe Wheelchair ta taimaka masa ya zauna dariya tayi masa tace "Why are you hidding your naked body for me?" Banza yay mata tare da ɗaukan brush ya wanke bakinsa kana ya ɗaura alwala duk akan idanunta, daya ɗaga kai ya kalli mirror sai ya ɗauke kansa saboda ganin Airah da yake ta cikin mirror'n rabi Mutum rabi jikin maciji, abu ne mai wahala madubi ya ɓoye asalin halittar su ko yaya ne sai yayi showing.
Shirin kwanciya yayi bayan ya gyara jikinsa ta shafa masa mai just like Granny use to do, gaba ɗaya jikinsa ƙamshi yake lungu da saƙo, Imam yana mutuwar son parfume ko shopping ya je abinda yake ɗauka kenan, sai glass, boxer ta bashi ya saka kana ya maida komai wajan sa, wasu fararan night wears ta ɗauko masa "No! am not interested bana sa kaya idan zanyi bacci, am okey a hakan" ya faɗa yana karanta addu'ar bacci yana gamawa ya shafa ta ko ina.
Kwanciya yayi ya lumshe idanunsa ya shiga sauke ajjiyar zuciya jikinsa ta shige bai trying na hanata ba cos yana buƙatar ɗumin jikin mace na sawa ya ƙara samun nutsuwa, Murmushi Airah tayi saboda yadda ya shige jikinta a hakan ma wai baya jin komai game da mace duk sanda ya fara jin daɗin mace sai Allah a haka bacci ya ɗauke sa yana maƙale jikin Airah yana jin yadda take shafa lips ɗinsa.....
Washe gari da safe Mami ce zaune da ƙawarta mai suna Fariha suna hira akan bank nasu, numfashi Mami ta sauke tace "Wlh ina cikin damuwa, i don't know how to explain , bana samun nutsuwa da mijina gaba ɗaya" Fariha tace "kamar ya kenan?" Mami tace "rabon dana kwanta da Barrister na manta, kamar yadda bana zama shima baya zama, daga Granny sai Sweet Imam, amma end of this month Su Fareeq da Bahaiyya zasu dawo holiday", tsaki Fariha tayi tace "ke fa baki da fahimta wallahi, bari ki ji yanzu kai ya buɗe idan zaki fuskanci mijinki ki gaya masa bakya gamsuwa da shi to, wallahi kina kallo zaki cuci kanki, ƙilan shi garesa zam yake jikinki amma ai ke baza kiso ki zauna haka ba tunda ba dutse ba ce ke, so go and meet your husband ya je Islamic chemist ya amshi magani ƙilan kuma infection ne yasa haka", wani wawan tsaki Mami ta ja tace "God forbid! Ni na je wajan Barrister nace masa ya nemi magani? Sorry Am classy woman I can't do that", "kenan haka zaki zauna? Ko dai baki da lafiya ne?" Ware ido tai tace "kul ki ƙara faɗa lafiya lau nake wallahi , kullum sai na gyara kaina da sabbin magunguna ina matse kaina yadda babu wanda zai raina ni, ke ni fa ko tsufa nai banga abinda zan sauya ba, domin gyara daɗi gare sa" jinjina kai Fariha tayi tace "ikon Allah kowa da abinda ya dame sa ni Abban Taufiq kullum cikin ƙorafi yake a kaina, ban san mene yasa ba amma kamar baya gamsuwa da ni" riƙe baki Mami tayi tace "Allah dai ya kyauta kema kina gyara, baki son gyara kanki, namiji kuma duk tsufansa da kika gani yasan daɗi, yanzu dai goben za ki zo ko yaya?" Miƙewa su kai a tare Fariha tace "By the grace of God" dry Mami tai tace "kizo akwai magana"....
A zaune ta samu Sheikh shida Arjun suna hira ƙasa ƙasa da alama hirar cigaban da Company Sheikh yayi suke, shi dai Sheikh hankalinsa na ga zane da yake a jikin white paper Sheikh na son zane tun yana yaro ya iya zane, domin har zanan gida makaranta, masallatai yana fiddawa, yanzu tunda suka fara magana ya fara zane da pencil ga wasu different colors da yake using dasu "A week ɗin nan mun samu ƙaruwar kuɗi more than 5.1m nai mamaki sosai fa, amma ganin manager bana wasa ba ne yasan aikinsa yasa ban tsayawa wani bincike ba" shiru Sheikh yat domin idan ka tambayesa mai Arjun yake cewa shi kansa bai sani ba, kula da hakan yasa Arjun leƙa paper wata budurwa mai matukar kyau da tsari yake zanawa, ga gashi da ido farare tass, ga shape mai tsari, murmushi Arjun yayi yace "Wannan alama ce take nuna Buddy ya faɗa soyayya", manyan idanunsa ya ɗaga bayan ya kammala zana Airah babu abinda ya bambanta tsakanin Airah fairy da zanen, lumshe idanunsa yayi kana ya buɗe a kan, taune lips ɗinsa yayi kaɗan tare da tsotsa "you're very beautiful Airah,i never see a beautiful lady like you, you make me happy, wlh billahi am proud of you Aljanata i love You more than anything, your love and care mean a lot to me, I love you My Aljana" farin ciki ne ya cika zuciyar Arjun da sauri ya kama hannun Sheikh yace "Who is that Airah da kaketa magana a kanta time to time" haɗe fuska Sheikh yay yace "kamar ya? Wace wata Airah kuma?" Kallonka rainawa kanka hankali Arjun yay masa yace "kada ka mai dani wani sakarai mana, yanzu ka fara mgn kana Airah waye-waye kace wai wace ce Airah, idan ka fara son mace ni nafi kowa farin ciki saboda ko babu komai zaka samu farin cikin daka daɗe kana nema wajan mace" taɓe baki Sheikh yay yace "Duniya ta lalace tunda su Arjun aka fara wa'azi", "ohh da kai kaɗai ka iya wa'azi?" Idanun Sheikh a saman zanensa yace "A'a fa" fushi Arjun yayi yace "ok fine sai anjima" da sauri Sheikh ya riƙe hannun Arjun yace "Sit" zama yay yace "zagina zakai yanzu kuma?" Ware idanunsa yay yace "Laaa! Bana son ka matsa kanka wajan sanin abinda ba hurumin ka ba ne Buddy, kowa yana da private life ɗinsa, nasan ka cancanci kasan komai nawa amma bana da ikon faɗa maka SIRRIN MU but time will tell us everything" miƙewa tsaye Arjun yay kafin yay mgn Granny ta ƙarasu tana faɗin "Haka fa! ya gaya maka meke damunsa? To dai Ranjun abun kullum lalacewa yake kamar wanda iska ta aura, jiya fa ban faɗa maka ba naje tashinsa da asuba na samesa yana ihu da surutai, nidai babu ruwana idan ya jawa kansa masifa ina dalili ina mafari fisabilillahi?" Girgiza kai kawai Arjun yayi yace "something is fishy" yana faɗin hakan ya fice abunsa daga cikin gidan... Mami dake tsaye ta saki wani sound da sauri Granny ta juya tana faɗin "Mahammadur Rasulullah ashe kema gantalalliya ce? Wannan ɗaukan zunubi har ina fisabilillahi? Sai kace ana yaƙi kawai zaki faɗo kamar dai a sabon gari, daman kwana biyu duk a tsorace nake, gaskiya idan baki nemi yafiya ta ba sai Ubangiji ya kamaki babu ruwana wallahi, kawai dai sbd son jin zance sai ai tsaye akan mutane kamar wata ƴar dama??" Murmushi Mami tayi tare da ƙarasa shigowa parlourn ta zauna saman kujera idanunta na kan Sheikh tace "Afuwa Granny nai sallama ba ki ji ba kina ta faɗa" a fusace Granny tace "yaushe na zama sallamammiya da zanyi faɗa, da Imamu zanyi faɗa ko da Arjun? Yau naga lukutar masifa" Mami tace "kiyi haƙuri Granny", Granny tana keɓe baki tace "shiya kashe Jaki" zaro ido Sheikh yayi still idanunsa na kan zanen da yay "Yooo an loda masa kaya yau, gobe an loda masa babu ruwa bare abinci duk wahalar daya sha babu mai gani, ba dole haƙurinsa ya gaza ba dan Allah?" Mami tace "haka ne fa" miƙewa Granny tayi tace "bari na dama masa wannan furar ta gado yaro