Showing 111001 words to 114000 words out of 130248 words

Chapter 38 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5997

Sheikh akan ko yana da hujja dazai kare kansa tunda bashi da lawyer, banza Sheikh yay masa sai buɗe idanunsa kawai da yay, yana buɗe idanunsa ya sauke a kanta wani tattausan murmushi ya sakar mata yana nuna mata cikinsa sai kuma yay mata nuni da tayi Shiru tsit tayi ta shiga sauke ajjiyar zuciya idanunsa ya juya kamar ance ya juya ya hangi Muhammad Jalal Kabeer bobo shida Jalilerh zaune suna kallonsa.
Guduma Al'ƙalin ya buga kana ya mayar da glass ɗin idanunsa ya shirya takardun gabansa yace "Bisa ƙwararan hujjojin da suka mata da kuma amsa aikin da mai laifin yayi wannan Court mai adalci ta yankewa Sheikh Imam hamdan Balarabe hukuncin....," Shiru yay sbd jin murya daga baƙin ƙofa bana faɗin "Adakata!!!" Gaba ɗaya mutanan suka maida hankalinsu Miƙewa Barrister yay Sheikh kuma ya ɗan furzar da iska daga cikin bakinsa yana juyawa a hankali Arjun ne a farko, sai Anut Amina hannunta riƙe ta dairy, sai kuma Mama kolo da Yagana, daga can baya kuma wani farin mutum ne da alama shima prvt investigation ne, gefe guda kuma wata farar mata ce wacce tasha ado da wani farin lace amma gefen kanta a fashe yake yana zubda jini, sai Deen dake riƙe da hannunta fuskarsa tai jajir, da sauri aka ware mata rigar ta Deen ya amsa ya sanya mata, hakan na nuni da cewa itace Queen Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen, kuma lawyer mai kare Sheikh Imam hamdan Balarabe...






SIRRIN MU isn't free contact to subscribe
08119237616




NIMCYLUV✍🏽
22/10/2021, 10:38 - 🤔🤔: Who Is The Killer
83-84


Gaba ɗaya cikin Court ɗin yay shiru idanun jama'a suka dawo kansu Deen, da Arjun da Anut Amina tare Mama kolo haɗi da Yagana.
Gyaran murya kaɗan Moon tayi wanda yasa Deen fahimtar abinda take nufi, zame hannunsa yay a nata daf da kunanta yace "All the best My Queen" yana faɗin hakan yaja baya tare da nufar inda Muhammad Jalal Kabeer bobo yake zaune tare da Jalilerh.
Cikin nutsuwa Moon ta ƙarasa kallo guda tayiwa Alhj Kamal ta ɗauke kai, kafin ta maida kallonta ga Sheikh, kusan numfashinta ne ya kusa tfy, duk yadda Mijinta yake da kyau da kwarjini amma ƙafar Sheikh Imam hamdan Balarabe Deen bai kama ba, ga wata nutsuwa kamala, da haiba uwa uba kwarjini wanda kallo ɗaya Mutum zai masa ya cika masa idanu.
Shiru ne ya biyo baya, Arjun da Anut Amina suka nemi wajan zama, Mama kolo da Yagana suka zauna suma, Al'ƙali ya buga guduma Court tayi shiru, jin shiru yay yawa yasa Moon ta miƙe kamar yadda Al'ƙalin ya bata dama, gyaran murya tayi irin tasu ta matan manya da kuma sarauta tace.
"Sunana Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen, nice lawyern wanda ake a ƙara Ngd"
Rubuce² Al'ƙali yay kafin ya ɗago kai yace "Shin Lawyern wanda ake ƙara tana da hujjar da zata kare wanda Court take tuhuma akan yima matar mahaifinsa ciki?"
Miƙewa Moon tayi tana gyara zaman rigar jikinta kanta a ƙasa tana duba wasu takardu kafin tace "Ya mai girma mai Shari'a kamar yadda kace tun farko tuhumarsa ake ba'a tabbatar ba, kuma wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa da dukkan gskyar zcyarsa, to anawa ɓangaren haka abin yake Tabbas cikin jikin Fannah Baba Baa'na cikin Sheikh Imam hamdan Balarabe ne..," ihun Court ta ɗauka aka shiga surutai, Barrister kallon Moon kawai yake hakama Alhj Kamal suna jiran suji ta inda zata kare Sheikh daga wannan abun, guduma Al'ƙalin ya buga akai shiru da idanunsa ya kalli Moon yace "Muna jinki" gyara tsaiwa tayi tace "Uhm! Hujja ta farko tabbatar da cewa cikin jikinta na Sheikh ne" wata paper ta ɗauko wani ya karɓa kana wani ya amsa ya miƙawa Al'ƙali, dubawa ya fara yaga gwajin halitta ne, kuma ya tabbatar da jinin Sheikh dana babyn cikin Fannah abu guda ne, ajjiyewa yay kana tace "Sai abu na biyu, wanda ake tuhuma bashi da laifin komai hasali ma ya samar da cikinne ta hanyar da ake so,hanyar da Addinin Musulunci ya sharaɗanta" nan ma shiru tayi kafin ta juyawa sukai ido huɗu da Barrister sai kawai ta ɗauke ganin yadda zufa ke wanke masa jiki, hakama Mami da Alhj Kamal, juyawa tayi idanunta ya sauka akan Deen ya kashe mata idanu, tare da jinjina mata hannunsa, murmushi tayi tace "Bisa dugun binciken dana fara tun jiya zuwa yau, to Allahamdulillah duk wani binciken da nayi ya tabbatar min da cewa Fannah Baba Baa'na halaliyar Sheikh Imam hamdan Balarabe ce, Ma'ana Matarsa ce ta sunna" a hankali ya shiga ware idanunsa yana sauke numfashi kaɗan² bakinsa na mutsawa yana faɗin _"Astagafirullah wa'atubu ilaik!! Astagafirullah wa'atubu ilaik!! Astagafirullah wa'atubu ilaik!!"_
Jajayen idanunsa ya sauke akan Fannah wacce itama shi take kallo zuciyoyinsu suka shiga bugawa a lokaci ɗaya, yayinda numfashinsu ya fara daidaituwa dana juna, idannunsu a manne, suna jin mgnar kamar dirar mikiya, Sheikh taune leɓansa yay yana son ya tabbatar da abinda kunnuwansa suke faɗa masa amma ya kasa, wani ƙyakƙyawan shock ya kama Sheikh, ya kasa koda mutsi ya zama kamar wani statue.
Moon da take kallonsu tace "You have a right to that, kana da ikon kallanta as much as you can, Fannah is your wife" da sauri Barrister ya miƙe tsaye yace "Ƙarya ne, wlh matata ce, ƙarya ne, nina na bada sadakin ta, Ni nace ina sonta ba shi ba, matatace dani aka ɗaura mata Aure bada Sheikh ba" Barrister ya faɗa cike da tashin hankali jikinsa gaba ɗaya gumi ya wanke sa, Al'ƙali ya buga guduma nan take Court tai shiru cikin bada umarni yace "Is an order Kada wanda ya sake mana magna idan ba haka ba yanzu hukunci ya hau kansa"
Gyara tsaiwa Moon tayi Idanunta na kan Sheikh tace "Ina son Court ta bani damar tambayar Sheikh Imam hamdan Balarabe wasu tambayoyi" kai tsaye Al'ƙali yace "Court ta baki dama" cike da ƙwarin qwiwwa Moon tace "Sheikh da gske cikin dake jikin Fannah naka ne?" Jajayen idanunsa ya buɗe yana kallon ta kafin ya janye idanunsa ya mayar kan Fannah wacce tai lamo jikin Ya Falta tana sakin ajjiyar zcy sbd kukan da taci ta ƙoshi, ganin da gske bashi da niyyar mgn yasa a hankali Moon tace "Amsar ita zata tabbatar da abinda nake son faɗa a gaban jama'a" fesar da numfashi a hankali yasa tattausan hannunsa ya shafa fuskarsa zuwa gemunsa wanda yake ta ƙyalli, kamar bazai mgn ba sai kuma ya janye idanunsa yana faɗin _"Ya Allah"_ a zcyarsa, a fili kuma ya fidda wani emotional sound kafin a hankali yace "Da cikin da mai cikin duk Mallakin Sheikh ne" jinjina kai Moon kana ta buƙaci ganin Fannah, a hankali ta tashi cike da tsoro sbd sam bata sama tsaiwa gaban mutane irin haka ba, bayan ta tsaya kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta jikinta duk rawa yake, Moon tace "Shin akwai wata halaƙa ta auratayya data taɓa shiga tsakaninki da Barrister Hamdan Balarabe?" Kasa mgn Fannah tayi sbd tambayar tayi mata girma, tsora mata shanyayyun idanunsa yay shima yana so yaji me za tace, domin shi gaba ɗaya ya manta da wannan tunanin ya manta da cewa wani abu zai iya shiga tsakaninta da Abbansa, a karo na farko tsoro da fargabar abinda zata faɗa ya kamasa, addu'a yake idan wani abun ya fara kada Allah ya nufeta da faɗa, dan sam zcyarsa ba zata ɗauka ba, a hankali Fannah ta girgiza kanta cikin sanyin murya wacce ta kama dishewa sbd kuka tace "Babu komai, tun zuwana gidan kawo yanzu" wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zcy Sheikh ya sauke yana rufe idanunsa wani sanyi ya fara ratsa masa zcy, jinjina kai Moon tayi tace "Idan Court ta amince zan fara gabatar da shaidun da zasu tabbatar da cewa Fannah matar Sheikh ce" Al'ƙali ya bada dama Moon ta buƙaci ganin Arjun, cike da ƙarfin quiwwa Arjun ya tsaya kana ya gabatar da kansa a gaban Court matsayin mai bada shaida, wayarsa wacce ta samu matsala ya ɗauko yace "A ranar da Allah yaywa Uncle Sham Kawon Sheikh rasuwa wayata ta samu matsala, kafin rasuwarsa ta riskemu ina tare da matata a kitchen naji shigowar saƙo wayata, ban samu damar dubawa sbd wayar ta faɗa cikin hug ɗin tea, tun daga rana na cire sim ɗin na ajjiye ta, na duba ko zanga wanne saƙo ne ya rage a cikin sim ɗin amma ba komai duk sun zauna a wayar, to cikin ikon Allah yau na ɗauko hanyata ta zuwa Court na fara biyawa police station kamar yadda Queen Maimunatou ta buƙata, bayan muntattauna da ita, zamu tawo Court ɗin na samu kira daga matata, tace nai sauri nazo akwai hujja mai ƙarfi dazai kare Sheikh,jin hakan yasa na tafi Queen Maimunatou kuma ta shiga mota ta nufi Court, ina zuwa na samu wayata ta dawo dai-dai kai tsaye kuma ta nuna min saƙon dake jiki" jinjina kai Moon tayi tace "Ko Arjun zai iya karanta mana saƙon yadda kowa zai fahimta?" .
Wayar ya buɗe yace "ga saƙon kamar haka;"


_Assalamu Alaikum, Mohd na turo maka wannan saƙon ne a lokacin da nake jin kamar bazan iya samu damar faɗar wani Sirrin da baki na ba, da farko ka kula da Imam bashi da wanda ya fika, sai Granny ita kuma wannan a Kullum ƙarfinta ƙara jaa yake, Sheikh yana cikin magauta da maƙiya, na san halinsa mai ɗaukan ƙaddara da rashi Yadda da mutum, amma kai tsaye bazai fahimci wanda suke son kaisa ƙasa ba, abu mai muhimmanci shi ne FANNAH ba Matar BARRISTER bace, matar SHEIKH, na buƙaci abun ya zama sirri sbd na fahimci ita zata zama silar samun ƙafafuwansa Kuma Thank God ya samu lfy, haka kuma ya tabbatar min da Sheikh yayi tarayya da mace ne, ka gaggauta sanarwa da Imam wannan mgnar domin akwai gobarar da take shirin tunkaro sa, bayanin Auran sa da FANNAH da kuma bayanin cikakken Tarihin rayuwar Sheikh yana cikin Dairy na kasa Anut Amina ta ɗauko maka, ka bata hqr sosai ta kula da Huda, ta ɗauki ƙaddarar rashi na, abu na ƙarshe kuma kamar yadda jama'a da kuma ko kuke tunani Sheikh ba ɗan Barrister ba ne, na barku lfy realy miss you so much Arjun ka kula da Sheikh na baka amanarsa!_


Shiru Court tayi, Barrister ya susuci ga samu ga rashi, tayaya? Yaya akai Uncle Sham ya san da wannan Mgnar? Meyasa bai tunanin ɗaukan mataki akan Uncle Sham tun tuni ba? Yanzu duk shekarun daya ɓata ya tashi a banza kenan ko mene? Da ƙarfi ya furta "Ina it can be possible" kallonsa akai a wannan karan hadda Sheikh a kallonsa, tunanin Sheikh da yawa amma ya rasa wanne zai fara, idan ba Barrister bane mahaifinsa to wanene mahaifinsa, mai yasa Fannah ta zama matarsa bayan bai taɓa ganinta ba bare yace yana sonta? Ko kuma ƙaddarar haɗuwa da Airah ita ta haɗasa da Fannah, ada no one replace Airah in his heart, amma yanzu Fannah ta maye gurbin Airah ta samu matsayin da Airah bata samu, wannan da burin samu Allah ya ɗauki ranta.
Al'ƙali ya buƙaci ganin Anut Amina tare da Dairy, gabatar da kanta tayi kana ta fara buɗe shafin Farko na Dairy inda aka rubuta. _“TUSHE”_


Deedat da Hamdan yaya da ƙani ne, amma sun haɗu ne ta hanyar Uba uwa kowa da tashi, Hamdan ɗan stepmom ɗin Deedat ne, tun suna yara Allah ya bawa Deedat baya ta tsara art ga kuma son mulki, dan haka tun a secondary school aka fara bawa Deedat muƙami, hakan ya fara damun Hamdan sbd shi mutum ne mai hassada da kuma ƙyashi, amma baya taɓa nuna tsanar Deedat yana barin komai cikinsa ya iya takunsa, mahaifiyar Deedat ta mallaki Property da yawa wajan iyayenta da suka rasu ya rage daga ita sai ni Shamsudeen da nake rubuta wannan bayanin, ni ƙanin mahaifiyar Deedat nan wato Khadijertou, a haka rayuwa ta fara tsayi Deedat ya manyanta, a haka iyayen sukai tafiya babu wanda ya dawo da rasa sosai Deedat ya shiga tashin hankali bashi da kowa saini, daman familyn ba yawa garemu ba, yawanci ba'a ƙasar suke ba, haka dukkan ƙadarorin Khadijertou ya dawo mallakin Deedat Balarabe, ya fara juya kuɗi a lokacin ni kuma ina da aure matata ta fari amma ban taɓa haihuwa ba, ganin Deedat ya mallaki hankalinsa yasa nabar ƙasar, kwanci tashi Deedat ya zama shararran mai kuɗi, hakan yasa ya nemi wata matashiya dangin Kanuri ya aura, watan ta biyu ciff da Aure, akaiwa Deedat ƙuruciya yabar garin baki ɗaya, a hankali kuma aka sanya mota ta takashi, amma sam Deedat bai mutu ina ji a jikina yana raye, ya tafi yabar matarsa da ciki wanda bai san dashi ba, a lokacin ne kuma na dawo Nigeria da zama tare da sabuwar matata Amina sbd Allah yayiwa ɗaya matar tasa rasuwa, ba tare da binciken komai ba aka sanarwa Hamdan cewa Deedat yay hatsari ya mutu motar da ƙone tare dashi, hakan yasa ya ɗauki ragamar komai na Deedat ya barni kaɗan daga ciki nake juyawa, kulawar matar Deedat ya dawo ƙarƙashin Hamdan ba wanda ya san tana da ciki, sai ita da Hamdan ɗin, domin koni basu yarda na sani ba, kullum yana nuna mata sai ta haifesa lfy za'a sanar, lokacin da cikinta ya cika watan haihuwa a lokacin ta fara tsanar cikin sbd asirin da Hamdan yasa akai mata, dan haka tana haifar Imam ta tsallake ta barsa aka ransa inda tayi, sai Hamdan yay farin ciki ya bawa Saudat riƙon Imam, daman tunda ya aureta ya shaida mata cewa Mahaifiyar Imam matarsa ce, daga nan kuma yaje ya ɗauko Granny mahaifiyar Balarabe wato kaka wajan Deedat kenan, kana ya ɗaure mata baki, bokan Hamdan ya tabbatar da cewa idan har bai ɗauki mataki akan Sheikh ba to Tabbas shi ne zai kawo ƙarshen sa, sai ƙwace komai na dukiyar mahaifinsa Deedat, dalilin haka idanun Hamdan ya rufe yasa aka mayar da Imam gurgu tun yana zanin goyo, Saudat Granny sukaci gaba da kula da Imam cikin Aminci"


Shiru Court tayi kowa ya fara surutu, Granny kam kasa mutsawa tayi, kanta ya fara sarawa ta shiga tunanin abubuwa da yawa, Sheikh kam kansa motsi yayi, ya sunkuyar ƙasa tare da sulalewa a wajan ya shiga fidda numfashi idanunsa na janyewa tari na son kawo masa ziyara, da ƙyar yake fisgar numfashinsa sbd nauyin da zcyarsa yake masa, tabbatas an zalunci kamaninsa da mahaifansa.
Share hawaye Anut Amina tayi kana tace
_“MAFARI”_ lokacin da Saudat ta fahimci kaf Dukiyar Barrister ba tasa bace itama ta shiga ƙoƙarin ganin yadda zatai ta samu kasu fiye da rabi na Dukiyar, har kawo lokacin kuma bata son cewa Shaikh ba ɗan Barrister bane.
Rashin, Barrister yayi abu baya tuna baya Deedat lfyarsa ƙalau, Yayinda kuma matarsa ta koma daginmu dake Niger da zama, wata rana naje Dubai yin oder sabbin kaya na company Sheikh kamar daga samu naga Deedat nai mmki sosai domin har lokacin bai tagayyara ba, kuɗi da hutu sun zauna masa, daga nan kuma na fahimci yana da babban matsayi sai dai ban san matsayin mene ba,muna haɗuwa matarsa ya fara tambaya ko da nace muje ya koma Nigeria sai ransa ya ɓaci hakan ya tabbatar da kurciyar da akai masa ta nan, ya amshi number na daga ya huce, kwana biyu tsakani ya dira a Niger sunyi farin cikin ganin juna sosai, babu wanda ya tambayi Imam, Deedat bai san da Sheikh matarsa kuma an saya mata mantuwa, daga nan suka sauyawa sabuwar Rayuwa haka kuma ban sake ganinsu ba har kawo yanzu dana rubuta wannan abun"


Nan ma shiru Anut y tana share shawaye, Deen kam jin abun yake wani iri ace ɗan uwanka na jini shine bai ƙaunarka, mai yasa kuɗi keson hallaka jama'a ne, murmushi kawai yay sbd tunawa da Oga Damus da yay, Muhammad Jalal Kabeer bobo yay ƙasa da murya dai-dai kunan Deen yace "kana tunawa da tashin bom ne?" Harara Deen ya watsa masa yace "Yeah! Of course, kamar yadda kake tunawa da Governor Mubarak Yahya cibo, Jafar, right?" Taune baki Jalal Kabeer bobo yay yana Rungome Jalilerh yace "Forget the past amma serious sun cutar min da my Jalery?" Ya faɗa yana matse Jalilerh, Anut Amina ta ɗura da faɗin
_“REVENGE”_
A lokacin da Barrister ya gane cewa a koda yaushe abubuwa na iya juya masa, kuma ya fahimci halin Saudat da abinda take niyya, kuma ya gane cewa ɗa ɗaya shi ne nasa a cikin yaran da Saudat ta haifa, sai ya ɗauki niyyar ɗaukan fansa ta hanyar ƙarin Aure ya samu wacce zata haifa masa yara masu yawa, cikin Sa'a kuma ya haɗu da Fannah, a lokacin da Barrister ya buƙaci naje wajan Kawo Madu domin mu tattauna dashi nayi mmki sosai, ɗan uwan wajan mijin ƙanwar mahaifiyar matarw Deedat ne, hkne nima ƙanwar mahaifiyar Mamana ta ce, Shira mukai sosai, kafin Kawo Madu ya gayamin cewa Fannah bata son Auren hakan yasa na gaya masa ra'ayi na ina son a juyar da auran kan Sheikh, daga nan nai masa bayanin komai, haka Kawo Madu ya Sanarwa da Baba Baa'na ranar ɗaurin auren aka shaida ɗaurin auren Sheikh Deedat Balarabe, da Fannah Baba Baa'na, domin nace kada a bayyanar da sunan wanda aka ɗaura auran dasu, babban farin ciki na kuma babu abokan Barrister suna can waje shi kuma ya gidan Kawo Madu, aka ɗaura aura na bada kuɗin sadaki a aljihu na, kuɗin Barrister kuma sunan a ajjiyewa kamar yadda ya bani, Abu guda ya ragewa Sheikh a yanzu shine sanin inda iyayensa suke, sannan kaf Dukiyar da Barrister ya tara ba kuɗin sa bane haƙƙin mallakar Sheikh ne, a nan na kawo ƙarshen Rubutu na Allah ya yafe min bisa ɓoye wannan abun da nayi na barshi matsayin SIRRIN MU nida Kawo Madu da Baba Baa'na"
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai mutane suke faɗa, Barrister kam tuni ya fara zaucewa, murmushi Moon tace Anut Amina tace ta zauna, Alhj Kamal ya miƙe tsaye yace "Ina da mgn yamai girma mai Shari'a" Al'ƙali yace "an baka dama"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login