Showing 87001 words to 90000 words out of 130248 words
jirgin mu zai ɗaga" haɗe fuska Arjun yay yace "Ni dai gasky wannan karan ba zani ba, wanda nai Allah ya bada lada" ta gefen ido Sheikh ya kalli Arjune ba tare da yace komai ba ya miƙe tsaye yace _"Tasbahii alaa khaaiir"_ miƙewa Arjun yay yace "Mace tasa kana neman zaucewa duk ka aro halin daba naka ba ka ɗura kanka" Murmushi kawai Sheikh yay kana ya nufi Masar part ɗinsa haka nan yaji gabansa na faɗuwa. Cikin dare Fannah ta farka da wani a zababban ciwon kai ga nauyin da kanta yay mata haka nan ta samu kanta cikin ɓacin rai da kuma damuwa wacce bata san ta mecece ba. Washe gari ya kama Friday (juma'a) tun wajan ƙarfe 11 Mutane suka cika babban *Abuja National Mosque* mata da maza manya da yara kowa burinsa bai huce yaga SHEIKH IMAM HAMDAN BALARABE ba, gidan Redio banda Sanarwa ba abinda suke t.v tuni sun fara haska cikin Masallacin.
Aslam ya kalli Ammi yace "Wlh yau ina cikin farin ciki wlh jiya har mafarki bawan Allan nan nayi" Tattausan Murmushi tayi tana kallon Mijin ta Deedat dake suba wasu files tace "Same to me, Ina son ganinsa a zahirance ba'a t.v, ko wacece ta haifesa babarsa ta iya haihuwa Ma sha Allah" kallonta Deedat yay yace "Da gaske kina son ganinsa?" Kai ta ɗaga tana ƙara kallon cikin t.v yace "Zan nemi Appointment dashi in sha Allah, badai zaije Oumara ba" Aslam yace "Papi nace ba zani Oumara ba amma dalilin Sheikh naji ina son zuwa" Anuska tace "Yaaaah Sheikh" Aslam yace "Kaga ƴar iya har ya zama yaya". Sheikh yana gaban mirror sanye da wata ɗan yar shadda Gezner ɗin kin wando da Jamper sai babbar riga, ya ɗura wata farar riga mai kamar Alƙyabba a saman shaddar, kana ya ɗura farin hirami saman hular kansa, sai ƙamshi ke tashi a jikinsa idan kaga Sheikh a lokacin zaka ɗauka wani babban mutum ne mai bala'in shekaru sbd tsarin halitta da kuma kamewarsa haɗi da cikar kamala, kallon kansa Sheikh a madubi cikin zazzaƙar muryarsa yace _"Ohh! Ya rabbi You look Good Sheikh Imam hamdan Balarabe"_ ya faɗa yana shafa fuskarsa, jim yay tare da kallon wayarsa yaga Arjun ke kiransa yasan Tabbas jiransa yake, katse kiran yayi kana ya faɗa saman kujera yana ɗan lumshe idanunsa a karon farko ya fara danna wayarsa cikin nutsuwa ya sanya lambobin ta wanda ya haddasa ce a kansa, dailing ta fara ringing, tsaki Fannah taja sbd ƙuncin dake ranta tana jin wayarta na ringing tai banza da ita, wayarsa yabi da kallo yana mmkin rashin ɗaga wayarta kuma yana da tabbacin tana da numbersa, ƙara kira a karo na biyu ware Idanunta ta kalli wayarta taga sunan _SHEIKH_ na yawo tsaki yaja kana tai answering call ɗin cikin ɗaga murya tace _"Pls who I'm i speaking with?"_ fiddo idanunsa waje yay sbd yanayin muryarta da yaji ta sauya kamar ba Zahraaansa ba, cikin ƙasa da murya kamar mai lallashi yace "Assalamu alaiki" ya faɗa a tattaushe ji tayi kamar an caka mata mashi a zcy a zuciye tace "Nace waye ne kamar ba'a fahimtar hausa" Dam!! Dam!! Zcyar Sheikh ta buga da mugun ƙarfi ɗauke tunanin komai yay yace "I'm Sheikh Imam hamdan Balarabe" Shiru tayi kafin tace "Mtwsss to meye haɗi na da kuma wani Imam, dan Allah malam Allow me to enjoy ka gane" miƙewa Sheikh yay ya fara zagaye Bedroom idanunsa yay jajirrr cikin damuwa yace _"Wake Up Zahraaah!!"_ miƙewa tayi tsaye tace "Uban Uban wake up ɗin, kai dallacan kai ka san wata Zahraaah ni Fannah nake, kuma kada ka sake kira na idan kuma ka kira wlh..." Sai kuma tai shiru wani Murmushi takaici yay dan baya tunanin wannan Zahraaah ce sai dai mutanan ta suka kawo mata ziyara yace "Or else?" Kai tsaye tace "wlh za kaga rashin mutuncin da tunda uwarka ta haifeka ba'a...," Bai tsaya yaji ƙasashen zan can ba yay saurin cire wayar a kunansa kai tsaye kashe wayar yay gaba ɗaya ya cilla cikin wardrobe, tsaki Fannah taja tace "Mai gemun banza kawai" kansa a ƙasa zcyarsa na mugun bugawa yay waje a Parlo ya samu Fareeq da Arjun suna ganinsa suka miƙe tsaye Mami kam da wani ƙayataccen kallo ta bishi har suka fita. Kai tsaye babban masallacin juma'a suka nufa securities sun fara binsu Sheikh yace baya buƙata, lokacin da suka isa kowa tuni masallacin ya ɗinke da al'ummar Musulmi, a tsaye ya tsaya saman digadigansa speakers babu adadi a saitin bakinsa, gyaran murya yay kaɗan hakan yasa gaba ɗaya hankalin jama'a na masallacin dana gida sukayo kansa, Ya Falta tace "Yasubuhanallah, tsarki ya tabbata ga wannan halittar, amma kamar na taɓa ganin sa, but where? And when?" Yana tace "ƙaryar banza ina za kuga wannan Balaraban?" Kai tsaye Ya Falta tace "Wlh a gidan Fannah na ganshi time ɗin yana Parlo ko inda nake ban kalla ba yabar waje amma kamar a Wheelchair na ganshi". Ammi tunda ta ɗura idanunta akan Sheikh ta kasa ɗaukewa, Fannah kam tashi daga Parlon ta koma cikin bedroom tana jin gidan yay mata zafi ko buɗe ido bata son tayi taga Sheikh ko taji an ambaci sunansa. Gyara tsaiwar sa yayi idanunsa a lumshe kana ya ƙara covering jikinsa da rigar daya ɗura ƙara saita lafiyayyar Muryarsa yay yace.
_السلام عليكم يا إخوة المسلمين كما عرفتم أن اسمي الشيخ إمام حمدا (بلا ربي) اليوم يوم الجمعة الذي يواق ١٥ في شهر رمضان سأذكر علي أشياء الذي شغلنا عليهم_
_(Assalamu alaikum ya ikwatul musulimina kamaa araftum anna ismii ashsheik imam hamdan balarabe alyaum yaumul juma'a yawaaqi 15 fi ramadhana sa'uzakkiru alaa ashiya'ul lazi shagalna alaihim)_ gaba ɗaya wajan yay tsiit kowa yana sauraran abinda Sheikh zai ce, numfashi ya sauke kana ya kure damuwar ransa ya fuskanci mutanan gabansa yaga kusan rabi hausawa ne dan haka ya sauya akalar harshen sa zuwa Hausa yace "In sha Allah! Zanyi tuni da abubuwa guda Uku da muke yawan mantawa dasu kana muka gafala akansu.." Shiru da sauri wani securities ya miƙa masa bottle ganin haka Arjun yabar wajan ba jimawa ya dawo ɗauke da ruwan da Sheikh yake sha ya buɗe ya bashi, cikin nutsuwa yasha ruwan kana ya matsar da bakinsa sai tin kunan Arjun yace "kar ka kuskura ka ƙara tashi" ya ƙare maganar yana ɗan sakin murmushi. Gyara tsaiwa yay yace.
*ZINA*
ﻭَﺻَﻠَﻰ ﺍَﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻣَﻦْ ﻵ ﻧَﺒِﻲِّ ﺑَﻌْﺪَﻩُ
Tsira da amincin ALLAH sutabbata ga ANNABIN dababu wani bayanshi
Salati da tsira da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (ﷺ)tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Maɗukaka.
ILoLin zina da kuma Hukuncinta
Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi
(ﷺ) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai
Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Shirka da Allah
alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce ‘sai
wane?’ Sai ya ce, “Sannan kashe ɗanka don
kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce “sannan
sai wane?” Sai ya ce, “Ka yi zina da matar
makwabcinka.” (Bukhari). yadda ruwaito
Allah Maɗaukakin sarki Ya sanya hukuncin
wanda duk ya yi zina kuma ya taɓa aure, a
jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taɓa
aure ba, sai a yi masa bulala ɗari, sannan a
baquntar da shi a wani gari daban tsawon
shekara guda.
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga
Allah Ya keɓance shi da wasu abubuwa masu
yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga
cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:
1. Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta
hanyar jefewa. Ko kuma bulala da
bakuntarwa shekara guda.
2. Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya
yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce :
ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِى فَٱجْلِدُوا۟ كُلَّ وَٰحِدٍ مِّنْهُمَا مِا۟ئَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِى دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْءَاخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِين
“Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.” . (Annur : 2). .
Yi musu ukuba a gaban mutane, ba a
yarda a yi musu a boye ba, Allah Ya ce :
Duk waɗannan abubuwa suna nuna mana
munin zina da rashin kyanta a Musulunci.
Imamul Bukhari ya kawo, a cikin ingantaccen
littafinsa, daga Maimun Al-audiy ya ce,
“A lokacin jahiliyya na taɓa ganin wani biri da
ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran suka taru suka jefe su”.
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar makwabcinsa. Allah Ya kare mu.
ILLoLin Zina: Babu shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, waɗanda suke shafar mazinacin ko
mazinaciyar, ko su shafi al’umma gaba daya.
1. Zubar da mutunci da jawo wa kai
qasqanci: Duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta ƙasƙanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta sami ciki ta haihu, sannan ta kashe ɗan, to ta haɗa laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai. In kuma ta bar shi, to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta, wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da taɓewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba daya.
2. Zina ta haɗa dukkan sharri gaba ɗaya: Saboda a cikin zina akwai rashin tsoron Allah; rashin kunya; rashin tsantseni; rashin cika alkawari; ƙarya da butulci da sauransu. Duk kuwa waɗannan munanan halaye a Musulunci.
Manzon Allah (ﷺ) yace Allah ya la’anci mai sake al’aura da mai kallon al’auran wani. Baihaqi ya ruwaitoshi
an karɓo daga muazu ɗan jabal (r.a) ya
karɓo daga manzon ALLAH (ﷺ) sai yace
ranar alqiyama ranar hasara ce da nadama
ALLAH zai ta da al’umma daga ƙabarburansu siffa goma sha biyu (12).
Siffa na biyar daga ciki.
Za’a tashesu daga cikin ƙabarinsu suna
wari kamar dunge Mai kira yayi kira da fuskar ubangiji waɗannan sune masu zina sun mutu batareda sun tuba ba, basuji kunyar Allah maɗaukaki ba wannan shine
sakamakonsu makomarsu zuwa ga wuta.
Gaba ɗaya wajan yay shiru wasu daga cikin matasa banda kuka babu abinda suke, sunkuyar dakai Sheikh yana jan numfashi a hankali wata zazzafar ƙwalla ta sakko daga cikin idanunsa zuwa saman fuskarsa, yana jin wani ɗaci a ransa ga wani zafi da zcyarsa ke masa, idanunsa a goge tass yana gyara tsaiwarsa, a hankali ya buɗe dararan idanunsa ya sauke saman camera da sauri Fannah ta janye idanunta sbd ganin kamar ita yake kallo tace "Anyi banzan Malami dai, kai har kana da bakin yin magana akan zina? Shiyasa ake cewa ka yarda da faɗar Malam kada kai aiki da abinda yake aikatawa" girgiza kai Sheikh yay kana yace "Ƙaddara!!! Ba abinda bata sanyawa wasu ba halinsu bane ƙaddara ce wasu bata da madafa idan ta hau kan ka sai lokacin lokacin ta yay, kuma ƙaddarar tana da nata lokacin wata rana zai zo kamar ba'ai ba, wasu iyayansu nada sila wajan abinda ɗan su yay, wasu kuma ƴan matan su keda sila haka dai, Bayan zina sai.
*ZAKKA*
WACE IRIN DUKIYA CE ZAKKA TAKE WAJABA A CIKINTA?
Zakka ba ta wajaba a cikin duk abin da Musulmi ya mallaka domin amfanin kansa, kawai, komai tsadarsa kuwa. Misalin wannan shi ne gidan da yake zaune a cikinsa. Ba ta kuma wajaba a cikin motarsa ta hawa komai alfarmarta. Haka nan kuma tufafi da abin ci, da abin shansa.
shiru Sheikh yay tare ɗaukan ruwa yasha idanunsa cikin camera yace.
Dukiyar da kawai, Allah Maxaukakin Sarki ya wajabta fitar da Zakka daga cikinta, ita ce wadda ta tabbata, ba ta daga cikin abin da yake biyan bukatun mai ita, na yau da kullum, tana kuma kan wata turba ta qaruwa da havaka da bubuta, kama:
Zinari da Azurfa:
Zakka ba ta wajaba a cikin zinari da azurfa, sai idan sun kai wani matsayi na ywa, wato, nisabi, sa’annan kuma sun cika shekara xaya cif ta shekarar Musulunci, wato kwana xari uku da hamsin da huxu.
Nisabin Zakkar Zinari da Azurfa Shi ne Kamar Haka:
Ba za a tava Zinari da nufin fitar masa da Zakka ba, sai idan nauyinsa ya tasar wa giram tamanin da biyar “85’’. Ita kuwa Azurfa sai nata nauyin ya tasar wa giram xari biyar da casa’in da bayar “595’’.
Dukiya da Kuxaxe: Dukiya da kuxaxe kowaxanne iri ne kuwa, da suke hannun mai su, ko ajiye a cikin bankuna.
Yadda Ake Fitar Musu da Zakka: Ana lissafa nisabin dukiya da kuxaxe dabra da kwatankwacinsu na Zinari. Idan qimarsu ta yi daidai da qimar Zinari ta Zakka, ko fiye da haka, wato nauyin kusan giram tamanin da biyar “85’’ xin can da aka ambata a kuma daidai lokacin da Zakkar ta zama wajibi; bayan ta cika shekara xaya ta Musulunci tana qanqashin mallakar mai ita. To, zai fitar da kasha biyu da xigo biyar 2,5% a matsayin Zakka.
Ga Misali: Kowa ya san farashin Zinari ba ya da tsayayyar alqibla; canzawa yake yi. To, da za mu qaddara cewa, farashin giram xaya na Zinari a daidai lokacin da fitar masa da Zakka ya wajaba, yana daidai da dalar Amerika ashirin da biyar “25’’. To, a haka nisabin Zakkar dukiyar zai zama kamar haka:
25 “farashin giram xaya na Zinari wanda yake canzawa lokaci-lokaci) x 85 “adadin giram da aka mallaka, wanda ba ya canzawa) = dalar Amerika 2125 “wannan shi ne nisabin dukiyar).
Dukiyar Kasuwanci:
Abin da ake nufi da dukiyar kasuwanci xin nan, shi ne duk wani abu da mutum ya tanada domin kasuwanci, wanda kuma ba a iya canza wa bagire, kamar filaye da gidaje manya da qanan. Kazálika, da kayan abinci da waxanda ake saye don wani amfani na daban.
Yadda Ake Fitar Musu da Zakka: Mutum zai gano tare da lissafa qimar gaba xayan dukiyar nan tasa, ta kasuwanci bayan shekara xaya cikakkiya. Zai kuma yi amfani da farashi mai ci; wanda yake gudana a kasuwa a daidai ranar da ya shirya fitar da Zakkar dukiyar. Idan dukiyar nan ta kai nisabi, to, sai ya fitar da kasha xaya bisa huxu na kasha goma daga cikin xari, wato 2,5%.
Abin da Yake Fitowa Daga Cikin Qasa: Tsirrai da ‘Yayn Itace da Hatsi:
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Ya ku waxanda suka yi imani! ku ciyar daga mai kyau abin da kuka sana’anta kuma daga abin da muka fitar saboda ku daga qasa” [Baqara:267].
Sai dai Zakka tana wajaba ne kawai a cikin wasu kevantattun tsirrai; ba gaba xayansu ba. Ko kuma da sharaxin sai sun kai wani adadi kevantacce a idon Shari’ah.
A wajen fitar da Zakkar wannan nau’i xin ma, ana la’akari tare da banbancewa tsakanin abin da aka noma ta hanyar ruwan sama, wato noman damana, da wanda aka noma ta hanyar shayarwa, wato, noman lambu. Haka kuma da tsakanin wanda aka shayar ta wasu hanyar amfani da wasu kayan aiki, da aikin kansa. Duk ana la’akari da waxannan abubuwa a cikin qimanta abin da yake wajibi na Zakka. Shari’ah kuma ta yi haka ne saboda kula da mutunta yanayi da halaye da al’adun mutane.
Sharuxxan Wajabcin Zakkar Tsirai da ‘Yayan Itace:
Cikar Nisábi:
Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya riga ya qayyade adadin da wannan Zakka take wajaba a cikinsa; qasa gare shi kuma walá. Ga abin da yake cewa: “Babu Zakka a cikin qasa da buhu biyar na dabino.” [Buhari:1447/Muslim:979].
Wannan miqidari na kilo ne. Sai dai alkama daa shinkafa ana kimanta nauyinsa da kilo giram 580-600. To, duk abin bai kai haka ba, babu Zakka a cikinsa.
Tsirrai Xin su Zama Daga Cikin Abubuwan da Zakka ke Wajaba a Cikinsu:
Zakka bat a wajaba sai a cikin amfanin gona wanda ake iya ajewa da taskancewa na tsawon lokaci, ba tare da ya lalace ba. Wannan, kamar alkama, da sha’iri, da zabíbí, da dabino, da shinkafa, da dawa. Amma abin da ya shafi ababen marmari, waxanda ba ta yiwuwa a ajiye sun a tsawon lokaci, kamar kankana, da Rumman, tumarur, da matara kama da su, Zakka ba ta wajaba a cikinsu.
Kammala Nomewa:
Zakka tana wajaba ne kawai a cikin kayan amfanin gona idan an nome an kuma girbe su gaba xaya.Sa’annan kuma zagayowar shekara a kansu, ba sharaxi ba ne. Idan akwai wani amfanin gonad a ake girba sau biyu a shekara. To, ya zama wajibi a fitar masa da Zakka duk lokacin da aka yi girbinsa.
Garukkan Dabbobo:
Abin ake nufin da Garukkan Dabbobi xin nan, shi ne kevantattun dabbobin da mutum yake amfani da su, da suka haxa da: Raqumma, da Shanu, da Bisashe.
Ta tabbata cewa, Allah Maxaukakin Sarki ya halicci waxannan dabbobi ne a matsayin wata ni’ima ga mutane, domin su ci namansu, su sha nononsu, su sarrafa fatunsu su yi tufafi, su kuma riqa xora musu kaya idan za su yi wasu tafiye-tafiye ko qaurace-qaurace. Ga abin da Allah Maxaukakin Sarki yake cewa a kan haka: “Da dabbobin ni’ima, ya halicce su dominku. A cikinsu akwai abin yin ximi da waxansu amfanoni, kuma daga gare su kuke ci. Kuma kuna da kyau a cikinsu a lokacin da suke komawa daga kiwo da marece da lokacin da suke sakuwa. Suna kuma xaukar kayanku masu nauyi zuwa wani gari, ba ku kasance masu isa gare shi ba, face da tsananin wahalar rayuka. Lalle ne Ubangijinka ne, haqiqa, mai tausayi, mai jinqayi” [Nahki:5-7].
Manyan Sharuxxan Zakkar dabbobi:
Nisábi: Wajibi ne adadin dabbobin nan ya kai nisabi karvavve a idon shari’ah, saboda Zakkar bat a wajaba sai a kan mawadata. A haka kenan wanda ya mallaki wani xan adadi na dabbobi, wanada biyan wasu bukatum rayuwarsa ya dogara a kansu, ba zai fitar musu da Zakka ba. Nisabin raqumma shi ne raqumi biyar “5’’, na bisashe kuma, tunkiya arba’in “40’’, na shanu kuma, shanuwa talatin. Duk adadin da bai kai wannan ba, babu Zakka a cikinsa.
Cikar Shekara: Ba za a tava garken dabbobi da nufin fitar masa da Zakka ba, sai bayan cikar shekara xaya ta kalamdar Musulunci, da mallakarsu.
Kiyo: Dabbobin da suke tafiya yawon kiwo, suna ci daga taskar Allah, su ake fitar wa Zakka. Amma, waxanda mai su yake saya wa abin