Showing 60001 words to 63000 words out of 130248 words
kowa ba ya shige back seat ya zauna yana mai duban agogon hannunsa Iwc Schaffhausen, kewar iyalansa ita tafi damunsa a yanzu, kai tsaye suka nufi Government House, bai daɗe a taron ba ya ƙara shiga mota ya nufi gidansa dake *Hamra Street* unguwar manyan masu kuɗi da kuma tarin ilimi wani tangamemen gida motocin suka fara tsayawa da gudu wani babban soldier ya buɗe gate ɗin gaba ɗaya motocin suka fara shiga cikin babban compound ɗin, bai tsaya jira an buɗe masa ya buɗe murfin motar ba ya buɗe da sassarfa ya nufi wani gate wanda yana dosar gate ɗin ya buɗe da kansa, cikin babban parlon ya shiga babu kowa ciki sai ƙarar A.c wajan sides biyar ne a tsakiyar parlon upstairs ƙaramin parlo'n dake upstairs ya tsaya fuskarsa cike da farin ciki yace "Your Dad is back my lovely daughters" da gudu Anushka da Aditya suka miƙe daga jikin mahaifiyarsu suka nufi wajan DEEDAT suna faɗin "yeee Dad Oyoyo" durƙosawa yay tare da rungome yaran nasa a jikinsa yana sakin Murmushi, kallon wacce take tsaye kasan yay ya miƙe tsaye yana sakar mata lallausan murmushi yace "Madam come closer" tana dry tace "Wlcm back Ur Excellence" jawota yay ya haɗa da twins ɗinsa ya rungome yana jin farin ciki na ratsa zcyarsa.
Granny ta kalli Fannah dake zaune gabanta tace "to banda ke ɗin wazai kulamin dashi dan Allah? Nidai Barista ya gaman komai daya kawoki gidan nan, gashi sai na kwanta na runtsa sbd kina kula da Imamu,bawai gulma ba wlh Sausaz take ko Sandala banda sata da yawo babu abinda ta iya, kinga ke na faɗawa balle ace gulma nayi" ita dai Fannah jinta kawai take domin tunda ta farka ba taji mutsin Malaminta ba,kamar Granny ta shiga ranta tace "Yooo shima baya zama gantalalle ba, ya tsiri zuwa ofis kamar dayi yake,ina dalili Ni Faɗimatu salan yaja min zagi ace na sallama ɗa a duniya, kuma...," Saurin yin shiru tayi sbd haɗa ido da sukai da Sheikh wanda yake murza Wheelchair ɗin sa, miƙewa tayi tana faɗin "Lalle marhabin da Imamu,yanzu nake faɗin shiru duk hankalina ya tashi" Murmushi kawai ya sakar mata ba tare da yace komai ba, ta gefen ido ya kalli Fannah dake zaune kanta a ƙasa, marai-raice fuska yay yace "Granny Am hungry ina jin yunwa sosai" tura Wheelchair tayi tace "Yoo ba dole ba, ace tun safe bakaci komai ba gashi kai baza kaci abincin kowa ba,sai yanzu dana samu kake cin na wannan ƴar albarkar shiyasa tun ɗazo nace ta shirya maka akan tire, muje ka watsa ruwa saita miƙa abincin ni zan leƙa gida Amina naji ance Huda ba lfy" ita kaɗai take mgnarta babu wanda ya tankata har suka isa cikin flat ɗinsa, a gurguje ya watsa ruwa Granny ta bashi Three gauthier ko singlet bai samu damar sawa ba, ya dawo ƙaramin parlonsa da zama wanda yake mai kyau da tsari, yana zaune saman carpet ya miƙar da ƙafafuwansa yana jin daɗin iskar dake kaɗasa har wani bacci² ne ya fara ɗibansa, tun kafin ta ƙarasa shigowa turarenta ya sanar masa da zuwanta, bakinta ɗauke da sallama kanta a ƙasa ta shigo, can ƙasa ya amsa ba tare daya kalleta ba, har gabansa ta tsaya kana ta ajjiye masa tray ɗin a gabansa dan ta lura yafi jin daɗin cin abinci a ƙasa, bata san lokacin da bakinta yace "Sannu da zuwa" ba sai jin Muryarsa tayi a kunnanta yana faɗin "thank you" buɗe ido yay ya sauke a kanta ganinta zata fita yace "Mummyna" turo baki tayi nan da nan Idanunta ya ciko da hawaye ta fara ɗaga ƙafa tana saukewa wacce ita kanta bata san tayi ba cike da shagwaɓa tace "Nifa bana so" muryarta ya kwaikwaya yace "Ni kuma ina so" zama tayi a wajan tare da saka masa kuka saurin danne dryarsa yay yace "Am sorry" tace "to bakai bane" waro idanunsa yay tace "Wayyoooo" ɗan haɗe fuska yay yace "what" turo baki tayi tace "ba kaine ka zaron ido ba" lumshe idanunsa yana jin kasala na saukar masa yace "kefa uwace a gareni why are you acting like child?" Tace "Nima ban sani ba amma ni ban haifeka ba" yana ɗan jan sajen fuskarsa yace "Uhm Zahraaah" shiru tai masa gaba ɗaya attention ɗinsa ya mayar kanta yace "Zahraaah!!" Ya kira sunanta a hankali kasa amsawa tayi yace "I think i fall in love" da sauri ta kallesa ya ɗaga mata kira Shiru tai masa yace "Amma ina jin tsoran ban iya soyayya ba ban sani ba ko zata soni" ji tayi zuciyarta na bada sauti ƙoƙarin daidaita nutsuwarta tayi tace "to" yana sauke numfashi yace "Ki ɗauka kece budurwa da nake so, zan gwada yin soyayya dake idan kince na iya then sai na faɗa mata" kanta a ƙasa tace "Tayaya ni bangane ba kuma mene haɗi na da budurwaka?" Murmushi yay yace "Akwai kefa uwace gareni sannan ita kuma sirikarki, kawai ki ɗauka ni saurayin ki ne ba ɗan ki ba, nima zan ɗauke ki matsayin budurwata ba uwa ba" tace "kana ganin ba matsala?" Yace "Yeah! Just 2week idan kikace na iya soyayyyar shkknan zanje na gayawa Rayuwar Sheikh Imam hamdan Balarabe" hawaye ne ya taro Idanunta tace "Your request accepted" yana rufe ido yace "انت جميلة وانت عقيلة
الله يدومك في السرور
كما تكون دائما في السرور في حياة "الشيخ إمام حمدا بلاربي"
Kallonsa tayi tace "me kace" ba tare daya kalleta ba yace
_"Kina da kyau da hankali, Allah ya dauwamar dake cikin farin ciki,kamar dai kika zama farin ciki a rayuwar SHEIKH IMAM HAMDAN BALARABE"_ ji tayi soyayyarsa ta ƙara nunkuwa a zcyarta anya zata iya wannan game ɗin, ba tare data ankara taji yasa hannu ya jawota jikinsa yana faɗin "Come closer my Kurratul aini....
It's 500 via 0116886423
Sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616
SIRRIN MU isn't free book..if you read for free🤷🏾♀️🤷🏾♀️🤷🏾♀️
Ai hutun ƙarshen mako lfy🌚🤕
22/10/2021, 10:30 - 🤔🤔: *SM💞*
Da sauri Fannah ta zare jikinta daga cikin nasa tana sauke numfashi tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana jin yadda zcyarta ke harbawa da sauri, ta rasa wanne irin so da ƙauna ta kewa Sheikh,mgn yake amma gaba ɗaya hankalinta baya tare da ita, sosai take jin zafi da baƙin cikin zancan budurwar da yay mata, bata jin zata iya wannan game ɗin sam ba zata iya abinda zai iya zama illah ga zcyarta ba, sunkuyar da kanta tayi ƙasa tana ƙara jan numfashi ji take kamar ta fashe masa da kuka ko hakan zai sanya ya janye batun budurwar,ko dai za tace masa yay hqr da budurwar ne? Amma mene hujjarta? Akan wanne dalili zata hanasa? ko dai ta faɗa masa abinda yake zcyrta game dashi, kai ina bazai yiwu ba ita ɗin ta haramta sam a garesa matsayin matar uba take a wajansa, ba tare data sani ba tace zube a ƙasan carpet ɗin ta shiga rera kuka kamar yarinyar goye, dukkan abinda take yana jinta kuma yana sauraran yadda take kukan, shi mmkin yadda kuka bai mata wahala yake ganin yadda take kukan da gaske yada yaji sam bazai iya jurewa ba idan yace zai jure jin kukanta to tabbatas zcyarsa zata iya bugawa, calmly yay yace "Zahraaah!!" Ƙin amsawa tayi sai shassheƙar kuka da take, yana kallon yadda ƙirjinta ke up and down alamar kukan yaci ƙarfinta,cikin ƙasa da Murya yace "What i have done to you?" Ya faɗa Sounding emotionally worried, girgiza masa kai tayi tana kuka shiru shima yay mata ba tare daya ƙara ce mata komai ba, almost 30scnds tana kuka kafin ta gaji dan kanta tai shiru ta shiga sauke ajjiyar zuciya, Kallonta ya ƙarayi, He don't actually know the meaning of the feelings Amma yasan cewa yanzu yasan komai yana jin zai iya jajircewa akan abinda ya keji game da ita,Amma yasan it deeply hurts some hidden parts da ke ƙarƙashin zcyarsa, ciki yanayi na sarewa yace "Idan mgnar game ɗin mu ne ke saki kuka, I'll cancelled it" girgiza masa kai tayi kuka na son ƙwace mata tace "No at all" "then why are cry?" Ya tambaya ba tare daya kalleta ba,kanta a ƙasa tace "Kawai ina jin tsoro ne, i think dani dakai kamar zamu tafka babban kuskure ne" ya gane me take nufi sarai sai ya share ba tare daya tanka waccen mgnar ba yace "You can go" kamar zatai kuka ta kallesa tace "Abincin fa?" Yana ya mutsa fuska yace "Ni! Am okey zaki iya tafiya dashi" share hawaye suka ƙara sakko mata tana sharewa tace "Amma ai ba kaci komai bafa" tashi yay ya zauna sosai ya kalli cikin Idanunta yace "Ai bakiso naci ba" girgiza masa kai tayi wani kukan na shirin ƙwace mata yay sauri cewa "Don't ever trying" haɗiye kukan tayi ta shiga sauke ajjiyar zuciya, ba zata gane ba da zata gane da batai wannan kukan ba domin ji yake kamar zcyarsa zata tarwatse sbd yadda kukanta yake taɓasa, Lumshe idanunsa yay kana ya ƙara buɗe su akanta cikin ƙasa da murya alamar rarrashi yace "Kin gama kukan?" Kamar wacce yace tai kuka haka ta ƙara fashewa da kuka numfashinta har wani maƙalewa yake, hannunsa yasa a hankali ya matsu da ita kusa dashi tare da ɗura kanta a saman shoulder sa yace "Cry! Cry! Yi kuka idan hakan zai sa kiji daɗi" hannu tasa ta riƙesa sosai ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita, yadda take kukan sauka rantse da Allah cewa wani nata ne ya mutu, bai kulata ba bai kuma hanata kukan ba sai bayan ta kawai da yake bubbugawa kamar ƙaramar yarinya, Shiru tayi ta shiga sauke ajjiyar zcy tana jan numfashi, ɗago kanta yay yaga inda hawaye suka ɓata mata fuska, a sanyaye yasa tattausan hannunsa ya shiga share mata hawaye yace "Kin gama? I mean kin gamsu da kukan da kikai?" Kaita gyaɗa masa yace "Sure?" Ta ƙara gyaɗa masa kanta, bai ƙara magana ba ya goge mata fuskarta tass,kana yay baya ya kwanta jikin kujerar yana fidda numfashi tana jan numfashi tace "kaci abinci" a hankali ya buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suka sauya kala yace "Kina so naci ne?" Da sauri ta ɗaga masa kanta yace "Ok Promise me?" Tace "Me?" Yana kallon fuskarta yadda ta ƙara yin jaaa sbd kukan da tayi yace "Har abada har gaban abada ba zaki ƙara yin kuka ba,har sanda Ubangiji zai ɗauki ranki baza ki ƙara zubar da hawayenki ba, Promise me Zahraaah!" Kallonsa kawai takeyi domin bata tsammaci abinda zai faɗa kenan ba, hanunsa taji a cikin tafin hannunta ya ƙara cewa "Promise me Zahraaah baza ki ƙara kuka ba? hawayenki bazai ƙara zuba komai daɗi komai wahala, You're not my Mom anymore you're my girlfriend,dan haka kimin al'ƙawari" bata san meke bin fuskarta ta ba ita dai kawai taji zafi da ɗumin abu na bin fuskarta hawayen daya goge ta ƙara tabbatarwa kanta cewa wani kukan take "Cry again" ya faɗa cikin damuwa da ƙonar rai me take nufi dashi ne? Ko kuma so take ta kashesa da kukanta sbd data san baya ƙaunar jin kukan nata, iska ya fesar Fannah kam ji tayi zcyarta ta tsinke har bata sanin sanda hawayen ke zuba daga cikin idanunta data tuna mgnar budurwar da yay sai taji hankalinta ya tashi Tabbas ita ɗin mai raunice a kansa tana masa son da baki bai isa ya faɗesa ba, Muryarsa taji yana faɗin "Ok Game ɗin ne baki so? To an fasa zanje da kaina na gayawa farin ciki na cewa ina sonta, be happy" kai ta fara girgizawa tana jaa baya sai kuma ta tashi da gudu tai waje tana toshe bakinta sbd sabon kukan da yazo mata, binta yay da ido yana jin babu daɗi a ransa yay zai da sabuwar ƙaddarar da taiwa rayuwarsa kotse ne? Mai yasa zcyarsa take son abinda bai dace dashi ba,mai yasa so da ƙaunar matar mahaifinsa nasa suke barazana da lfyar jikinsa ne, sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya yay tare dasa hannu ya ture tray ɗin abincin, kwanciya yay flat saman carpet tare da rufe idanunsa da tafin hanunsa sosai yake son yayi tunani akan sabon abin daya shifa'u rayuwarsa har yake son wargatsa masa dukkan wani jin daɗinsa. Fannah na fita ta shige bedroom ɗinta jikinta duk rawa yake a ranar kuka babu kalar wanda ba tayi ba, tunanin ya toshe ta gagara samawa kanta mafita bare ta samawa Malaminta mafita,zata iya tayashi neman abinda yake so indai zai farin ciki amma ita a wanne matsayi take haka zata ƙare Rayuwata bata wani ƴanci, shikenan ba zata taɓa samun abinda zcyarta keso ba?. Washe gari tun 7Am Arjun yazo suka nufi Company yana zaune akan kujera yana duba wasu files hannu yasa kana ya miƙawa wani P.A baya yay tare da kallon Arjun yace "Mene?" Shima Arjun yace "Naga har wajan 6 baka da niyyar tafiya shiyasa nazu naga ko lfy?" Taɓe baki yay baice komai ba dan bashi da abin cewa Arjun yace "Wannan halin naka shike ban haushi kai idan bakai kayi niyyar mgn babu wanda ya isa kai masa" idanunsa a rufe yace "idan sauri kake ajjiye min key ɗin" da rashin fahimta Arjun yace "As how? Bangane ba zaman me zakai a nan?" Banza yay masa yaci gaba da duba tarin files da suke gabansa cike da damuwa da kuma tuhuma Arjun yace "Akwai matsala ne a gidan?" Nan ma shiru yaywa Arjun tsaki Arjun yaja tare da miƙewa fuuuu ya fice daga office ɗin yana mai jin haushin halin Sheikh, kamar yadda Sheikh bai tafi gida ba haka Arjun ya kasa tafiya nasa gidan yana kallon wayarsa na ringing cikin sanyin jiki ya ɗauka daga can ɓangaren Aliyah tace "Me ajjiye min mijina a waje haka?" Murmushi yay mata kamar tana gabansa cikin son danne abinda ke ransa yace "My! Kinyi kewata ne?" Haɗe fuska tayi tace "faɗa ma ɓata baki ne now tell me mene ya tsayar dakai?" Ajjiyar zuciya ya sauke yace "Wlh buddy ne na kasa gane kansa,kallo ɗaya nai masa nasan cewa yana cikin damuwa,abinda yafi damuna yadda yaƙi tfy gida,bana son barinsa ban san mene zai iya faruwa dashi ba" jinjina kai Aliyah tayi tace "Ban san wanne irin haline da Sheikh ba,mutum sarai yana da damuwa amma ya ajjiye ta a cikinsa bai san cewa damuwa bata mgni ba?" Cikin damuwa Arjun yace "haka yake tun muna yara,yana tunanin zai iya handle dukkan abinda yake damunsa,na rabu dashi nasan idan abun yafi ƙarfin sa da kansa zai faɗa min" wahalallan numfashi Aliyah ta sauke tace "Allah sarki! Allah yaye masa abinda ke damunsa ya kawo masa sauƙi" cikin jin daɗi Arjun yace "Ameen² thank you My!" Tana dry tace "It's my pleasure abinda mijina keso shi nake so" "I love you so much you're the best ki shirya kimin wanka da kwalliya mai kyau" tace "I'll take care" kai tsaye yace "In sha Allah" da haka sukai sallama tare da katse kiran. Sai bayan Isshā Sannan Sheikh ya ajjiye komai ya murza Wheelchair ɗinsa zuwa waje a reception ya samu Arjun zaune yana shan Cork sai p.a miƙewa tsaye Arjun yayi tare da kama Wheelchair yana faɗin "Yap! Muna da aiki gobe sosai,dan haka ka fito da wuri zamu fidda sabbin designers na necklaces da ring da sauransu" cikin girmamawa p.a yace "In sha Allah before 7:30 ina nan" Arjun yace "Allah ya nuna mana goben" sanin halin Sheikh ko p.a yay mgn ba lallai ya amsa kawai yace "Sheikh na barka lfy" kamar yadda yay tsammani hakane ya kasance ko kallonsa bai ba bare ya sanya ran zai amsashi,a haka suka nufi motar Sheikh wacce Arjun keja, sai dai sukayi tafiya mai nisa a hankali Sheikh kamar bai son mgn yace "muje shopping" kallonsa kai yay ya ɗauke kai kana ya juya kan motar ya nufi Jabi Lake Mall, a harabar mall ɗin Arjun yay parking ya fito, kana ya buɗewa Sheikh ƙofa zai ɗauko wheelchair ɗin Sheikh yace "No! Bazai naje ba go and buy new phone for me" da mmki Arjun yace "Phone?" Kai tsaye Sheikh yace "haka nace" jinjina kai yay yace "Dame kuma?" Shiru yay alamar tunani sai kuma yace "With ice cream and Chocolate sai shortbread" Murmushi kawai Arjun yay yace "Zance zaka ne?" Banza yay masa yana dry yace "Something is fishing" ya faɗa yana yin cikin mall ɗin, lubb yay a jikin kujerar yana maida numfashin wahala yay ɗaya ya azabton da rashin ganinta anya zcyarsa zata jure rashinta? Zai iya hqr da ita kamar yadda ya tsara? A bai yane yace "Ni bazan iya ba, Airah is mine Always be mine forever and ever, ta zama jinin jikina rashinta a gareni babban illa ne,dole ya sauke wannan fushin da yake yaje ya ganta" ya faɗa yana jan ƙwantaccen beared ɗinsa. Arjun na shiga ya nufi side ɗin manyan wayoyi na zamani tashin farko ya zaɓar masa wata white ɗin Iphone 12 max pro, bayan ya ɗauka ya nufi wajan tarkacan chocolate ya lodar masa manya colours daban daban sai da ya cika basket Sannan ya nufi wajan biyan kuɗi, A.t.m ya baiyar suka sanya jikin pos suka ɗauki a dadin kuɗin su kana suka bashi receipt, kayan ya ɗauka zuwa mota yana zuwa Sheikh ya kallesa yace "Hauka dai? Wannan kayan fa?" Ajiye su yay a back seat kana ya nufi wajan zamansa yana yiwa mota key yana faɗin "kaita sha har sai ka gaji,kaga zasu ɗauke maka kewa tunda ka zaɓarwa kana ajjiye damuwa" jinjina kai kawai Sheikh yay kafin ya numfasa yace "me kake buƙatar ji SIRRIN ZUCIYATA? Ida hkne ka nemawa kanka sauƙi wajan hqr daji" Arjun cikin ɓacin rai yace "Daman nasan baka ɗauke ni a bakin komai ba,tunda haka ka zaɓa kowa yaje yay sabgar gabansa" ganin yadda Arjun duk ya sauya yasa Sheikh yay ƙasa da Murya yace "Idan abinda ke damun Sheikh za kaji to tabbatas kana gab dayimin kallon mahaukaci ko kuma zautacce,munin abin yasa na zaɓi barinsa a zcyta dan haka kaima ka hqr daji badan