Showing 42001 words to 45000 words out of 130248 words

Chapter 15 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

6002

gida haka kuma ka gabatar da sallah" girgiza kai Arjun yay yace "Bana jin zan iya barin buddy a wannan halin da yake ciki,ko na tafi bazan samu nutsuwa ba" "Olright i understand your feelings, yanzu kaje kai sallah sai kazo kaci abinci" kansa ya shafa yace "bari nai sallar am full" yana faɗin hakan ya nufi Mosque ɗin dake cikin hospital ɗin. Bayan tafiyar Arjun wani Dr ya buɗe ƙofa ya fito yana fitowa sauran suka fito ɗauke da gadon da Sheikh yake yana kwance samɓal kamar ma tacce hannunsa manne da drip lokaci ɗaya ya faɗa sai fari daya ƙarayi, kai tsaye wani special room aka nufa dashi Dr ya kalli Barrister yace "ina buƙatar magana dakai" sunkuyar da kai Barrister yay yace "Ok ga Uncle ɗinsa ma ni dashi duk ɗaya" kafin Dr yay mgna tuni Uncle Sham ya miƙe ya barawa Dr baya, jinjina da jikin bango yay zuciyarsa fal da tunani gefe guda yana tunanin Sheikh ɗinsa wani gefen na zuciyarsa na tunanin Fatimansa, wayarsa ya ɗauka tare da dailing number busy yaji wayar alamar an danna masa rejecting, sau wajan biyar yana kira babu response hakan yasa ya hqr da kiran a zuciyarsa kuma yana ƙara niya da kuma ɗaukan ƙudirin auren Fannah koda zai ƙarar da dukkan abinda ya mallaka Fannah kimarsa ce ta kuma mutuncinsa dan haka dole ya mallaketa a matsayin mata. Dr ya kalli Uncle Sham yace "he's critical condition I don't know how to explain you but Imam na cikin muhuyacin hali, akwai abinda zuciyarsa ke muradi da kuma fatan samu tun yana yaro ƙarami, nasan ba abun mmki bane idan nace baku san cewa yana da hawan jini da kuma ciwon zuciya ba, ciwon baiyi tsamari ba sbd kwanciyar hankalin daya samu a kwanakin nan, ciwon nasa yay tsamari daga jiya zuwa yau wanda harya sanya zuciyarsa ta kumbura" share zufar data keto masa yay yana ƙara nanata innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wacce kalar lukutar masifa ce wannan mutum kamar Sheikh yana da kuɗi yana da lfy yana da iyaye wanne irin abu yasa a zuciyarsa har zuciyarsa ta kumbura, kodai Nakasar dake jikinsa kai! Ina Sheikh yana da yarda da ƙaddarar a duk sanda tazo masa yasan da wahala ace lalurarsa ke damunsa harya sanya abun a zuciyarsa wanda yay affecting zuciyarsa, ajjiyar zuciya ya sauke yace "Dr mene yaja ciwon yanzu, muna da kuɗin da zamu samawa Sheikh dukkan abinda yake so kuma yake ƙauna idan har kuɗi na maganin abu tabbas a yau Sheikh zai samu lfy" Murmushi kawai Dr yay yace "Anya kowa? Idan kuɗi na mganin lalura ai da tuni ya daɗe da samun ƙafafuwan sa, yanzu magana ake ta ABINDA ZUCIYA KE MURADI, Tabbas akwai abinda zuciyar ke so kuma take muradi ban sanshi ba kaima ina da tabbacin baka sanshi ba, Allan daya halacce sa ne kaɗai dashi suka san komai amma samuwar abun ga Sheikh shine samun daidaito a cikin zuciyarsa, namu bashi taimako amma ba zamu iya cire masa damuwar dake ransa ba" tunanin abubuwan da suka faru shekaru masu yawa Uncle Sham ya fara har kawo yau da safe da kuma mgnar Aljanar Sheikh kai tsaye kuma zanan da Sheikh yay a jikin white paper ya faɗo masa, miƙewa yay tare da bawa Dr hannu yace "zan iya ganinsa yanzu ai?" "Bana jin hakan sbd yanayin yadda zuciyarsa take a kumbure abu kaɗan zai iya haddasa matsala,da zan maku shawara da kawai kun fita dashi waje ya samu cikakken hutu zuciyarsa ta samu sauƙi da sukunin ƙuntarar da take ciki" Uncle Sham yace "Ok I'll think about that Ngd Dr" Dr yace "your wlcm" yana fitowa ya samu Arjun da Anut Amina sai Fareeq da Mami wacce zuwanta kenan idanunta ya kumbura sbd kukan munafurci idan har Sheikh ya mutu ita kam ta tashi a tutar babu shiyasa take kuka kamar ranta zai fita, Granny kam duk yadda tayi masifar a tawo da ita taga jiƙanta ƙi Fareeq yay domin yasan saita cika masu asibitin da jama'a, Barrister ya kalli Uncle Sham yace "Yaya me Dr yace, wlh I'm scared shiyasa nace kaje bazan iya jure ganin Yarona a haka ba i luv him a lot" kallon gefe Uncle Sham yay masa yace "zai samu lfy in sha Allah just pray for him" jim sukai kafin Barrister yace "maganar Abban Fannah fa?" Idanunsa akan matarsa yace "zuwa gobe sani nima i want to talk to him" Barrister yace "Okey! Allah ya nuna mana" "Ameen" Uncle Sham ya faɗa yana yin gaba, babu wanda ya samu damar ganin Sheikh sbd ya under kulawar Dr Ilyas. Washe gari da yamma Arjun ya dawo Shida Aliyah sai ɓoye fuskarta take sbd kunyar dake cikinta Musamman da taga Umma a wajan, haka nan suka Karachi zamansu babu wanda ya samu damar ganinsa. Tijama ta kalli Tuɓe tace "yanzu aiki yana gareka domin kai ne zaka maye gurbin Airah kai ne takubin da zai sanya mu cika mata muradin data mutu dashi" shiru yay kana yace "Tijama mene nawa? Me zanyi wanda ƴar uwata zatai alfahari dani?" Murmushi tayi tace "zan faɗa maka komai da zarar lokaci yayi ina faɗa maka ne ka shirya domin a yanzu babu gudu babu jada da baya". Kwanaki suna tafiya kamar fitar numfashin Mutum yau kusan satin Sheikh biyu a cikin asibiti ya dawo hayyacinsa amma ko mgn ba yayi sai dai kallon da ido wani lokacin kuma zai fara masifar da ba'a sanshi da ita ba haka zai ce kowa ya fice ya bashi waje, ji yake zuciyarsa kamar zata fashe yasan yay rashi rashin da kafin ya samu wanda zai maye masa gurbinsa zai sha wahalar gaske ji yake ƙasar ma gaba ɗaya ta ishesa dan haka ya ƙudirci niyyar barin ƙasar da zarar an kammala bikin Abbansa da Arjun ɗinsa. Ƙofar baka buɗe tare da shigowa dake dare ne Yana sanye cikin sleep wears na parda white colour, idanunsa farare tass har wani fitta ruwa suke sbd fari, ga faffaɗan ƙirjinsa daya ƙara buɗewa sbd yanayin zaman da yay a saman bed ɗin, sumar kansa sai Shinny take sbd gyaran da Arjun ke mata, Arjun ne ya shigo tare da Aliyah wacce take biye a bayansa ta haske sosai sbd gyaran amarci da aka farayi mata sbd gaba ɗaya bikin bai huce 1week ba, kallo guda Sheikh yay mata ya janye idanunsa ya rufe sbd shi bai ƙaunar ganin mace ma wlh, duk da sauyin da yake jin a jikinsa amma hakan bai hana yaji sha'awar mace ba, kujera Arjun yaja mata ta zauna shi kuma ya koma kusa da Sheikh ya zauna a bakin bed ɗin, kallonsa yay yana Murmushi yace "Allahamdulillah! Nafi kowa jin daɗin samun sauƙin ka" shiru yay masa Arjun yace "kaga stop all this nazo mgnar biki ne tunda kace babu wani event shiyasa nazo ka tsara mana abinda kakeso ayi" ware idanunsa yay sosai akan Arjun kafin ya sauke numfashi ya shiga murza zoben hanunsa, Aliyah ce tace "Ina wuni buddy?" Shiru yay mata sanin halinsa yasa sam bata damu ba ta ƙara faɗin "Yaya jikin?" Kai tsaye tace mata "Allahamdulillah" yana faɗin hakan ya juya idanunsa ya kalli Arjun yace "mayan mace mai data gida saika dawo anjima" dry Arjun yay yace "Rai dai wlh zan rama duk abinda kai min" cije ba kinsa yay domin bai hango ranar da Arjun yake mgna akanta ba, rungomesa Arjun yay yace "I'll be back, Allah ya ƙara maka lfy Buddy na" da ido kawai ya bisu yana mmkin yadda Arjun yake rawar jiki akan mace. A ranar aka sallami Sheikh da daddare an gyara masa komai na ɗakin domin nan da 5days zasu koma sabun gidan da aka gama gyarawa. Ɓangaren su Fannah Barrister yakai kuɗin turaren huta da kayan gyaran jiki suka fara biki sam bata farin ciki da bikin amma ko a fuskarta baza kaga alama ba, Barrister ya haɗa lefe na amarya da iyayen amarya da ƙanwar uwa,da ƙanan uban amarya da uwar ɗakin amarya ko wanne sai da aka sanya gold a ciki, kaya na gani na faɗa iya Amarya wajan set uku akai mata,Sannan Uncle Sham ya ƙara da key ɗin mota. Yau ta kama ranar (WUSHE WUSHE) Amarya Fannah tasa kwailliya anyi mata kitso na gaba, wanda ya sauka har wuyanta sbd tsayin da gashinta yake dashi, anyi mata jan lalle tana sanye da Ghana kauwa da gyalen mindil na kanuri, ƙawayen Amarya sunsha ado kusan rabin ƴan uwa ne sbd bata da wasu ƙawaye na kuzo mu gani, bayan nan washe gari sukai KUNO wankin kan Amarya wanda ƙanin ango dana amarya suke mata, kasancewar Barrister yanzu bashi da wani ƙani sai kawai ya tura Arjun yin Duniya Arjun yay su tafi da Sheikh yace Allah ya sauwaƙe a bari ya zama ɗan daudo saiya fara zuwa biki tukun, dry kawai Uncle Sham yay domin ya basa dry wai ɗan daudo kenan duk mazan da suke zuwa biki ƴan daudo ne bana da labari, shidai shiru kawai yay yana spending tea ɗin dake gabansa, yana kallon Arjun ya tafi, domin shi Arjun ba wani event daya haɗa sai an ɗaura auren tukun za'ai walimar da Sheikh ya haɗa masu shida Barrister, haka dangin Fannah sukai bikinsu Ranar asabar aka fara ɗaura Auren Arjun suka ɗauki Hanyar zuwa Barno wajan ɗaurin auren Barrister Hamdan Balarabe da Fatima Baa'na. Gyara zamansa yay a cikin motar yana lumshe idanunsa yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda white colour mai ɗinkin riga jamfer da wando sai babbar riga, ya sanya hula mai zanna bukar, hannunsa sanye bada Rolex Balancpain, yana kishin giɗe a bayan motar Arjun na gama yana driving ya gama mitar driver da Sheikh ya mai dasa shidai yana jinsa yay masa banza sbd lugudan da zuciyarsa ke masa, saurin buɗe ido yay tare da dafe ƙirjinsa a kuma dai-dai lokacin Arjun ya karya kwana tun daga bakin kwanar suka fara ganin taron jama'a wanda suka halarci ɗaurin auren Barrister, Sheikh ji yay kamar zuciyarsa zata fito sbd harbawar da take masa, runtsa idanunsa yay da ƙarfi ya runtsa idanunsa ƙara buɗe idannunsu yay kai tsaye idonsa ya sauka akan wasu ƴan da suke riƙe da wata ƙaramar yarinya an lulluɓe ta lafaya yarinya zai ce dan gaba ɗaya bata huce age ɗin Bahaiyya ba, da sauri ya cewa Arjun "Reverse the car" kallonsa Arjun yay ta cikin motar yace "why?" Da ƙarfi yace "ka juya motar Arjun....








SIRRIN MU isn't free book contact to subscribe 08119237616 ga ƴan Niger 84506476






*Nimcyluv*
20/10/2021, 20:47 - 🤔🤔: *_NLUV💞_*
3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣
Da wani irin speed Arjun ya juya kan motar zuwa wani lungu nada ban wanda ya ɓulle har babban titi, ganin sun bar area'n yasa Sheikh ya saki wata wahalalliyar ajjiyar zcy yana dafe saitin zcyarsa, haka nan fargaba ta riskesa ba tare daya san dalilin faruwar ta ba, baya yay tare da lumshe idanunsa a ransa yana ambaton Allah, sai da Arjun yay tafiya mai tsayi sannan ya samu gefen titi tare da parking motar, ta cikin madubi motar yake kallon Sheikh yaga ko a jikinsa jin kuma shirun yay yawa yasa Sheikh fesar da numfashi tare da ware narkakkun idanunsa wanda suka ɗan janye kaɗan sbd baccin safe da bai samu yayi ba,tsaki Arjun yaja hakan yasa Sheikh kallon madubin motar suka haɗa ido kallon da Arjun yake aika masa kaɗai yasa ya fahimci yana son yaji dalilin daya sanya yace su juya, ɗauke idanunsa yay dan bashi da amsar da zai bawa Arjun, a karo na biyu Arjun ya ƙara sakin tsaki hakan yasa Sheikh ya ɗan ware laɓɓansa da ƙyar ya samu damar faɗin "wlh ka ƙara zaka fita,idan bani da ƙafa kasan ina da hannu i know how to drive" ta cikin madubin ya kallesa yasa yace "Ohhh! Really" yana fito da fararen idanunsa waje yace "sure" juyawa yay gaba ɗaya zuwa back seat ɗin da Sheikh ɗin yake a kishin giɗe yace "why?" Shoulders ɗinsa ya ɗaga yace "haka nan Buddy kawai hankali nane bai kwanta da zuwan ba" Murmushi Arjun yay da kallon ka rainawa kanka hankali arjun ya miƙawa Sheikh yace "Why are you acting like a child Sheikh? Kasan me kayi? Why tun farko kazo kasan hankalinka bai kwanta ba?" Banza yay masa dan yasan abune mai wahala Arjun ya fahimci halin da yake ciki. Koda wasa Uncle Sham bai san cewa su Arjun sun juya ba har suka isa ƙofar gidansu Fannah time ɗin ango kawai ake jira da kuma danginsa, bayan sun yi parking Uncle Sham ya kalli Barrister yace "shall we go?" Ajjiyar zcy Barrister ya sauke yace "why not Uncle?" Buɗe ƙofa Uncle Sham yay ya fito daga cikin motar shima Barrister ya fito daga cikin motar idanunsa a rufe sbd jirin dake ɗibansa, har wani duhu yake gani yana sanya da light blue ɗin gezner yay kyau sosai kana ganinsa ba sai anyi mgn ba kasan cewa shine angon. Yanayin yadda ya kejin kansa wani iri ya sanya ya fara taka ƙafafuwan sa a hankali cike kuma da nutsuwa but bottom of his heart fargaba ce zallah ga kuma wani Irin bad Mood daya samu kansa ciki a daddafe yaci gama da tafiya shida Uncle Sham sai kuma wasu manyan abokansa, cikin jama'ar suka shiga nan aka fara miƙa hannu ana gaisuwa, lokacin da suke gaf da isa tsakiyar rumfar da Za'ai ɗaurin auren wani jiri ya kwashi Barrister yay Baya luuu zai faɗi da sauri Uncle Sham da wani Sha'aban suka tare Barrister tare da faɗin "Subuhanallah!" Da kyau Uncle Sham ya riƙe Barrister yace "be careful" ya faɗa yana miƙar dashi ganin idanun jama'a na son dawowa garesu yasa Uncle Sham faɗin "ka shiga mota ka zauna you will feel better" Kawo Madu ne yace "A'a muje cikin gida dashi akwai special room sai ya huta a can" bai musu wani gardama ya amince har cikin gidan Kawo Madu aka shigar da Barrister cikin parlo mai kyau da kuma tsari ga t.v.da fridge da kuma a.c dake faman bada iska, bayan ya zauna Kawo Madu ya ɗauko masa gorar ruwa mai sanyi tare da glass cup ya ajjiye masa saman table yana faɗin "Bari naje lokaci na hucewa kuma munfi son baka matarka ka huce da ita domin ko ɗan rakiya baza mu baku sbd tafiyar nesa ce" da ƙyar Barrister yace "Ngd da karamci" waje Kawo Madu yay yana faɗin "haba an zama ɗaya kai kuma Allah ya jisshe mu alkairi" wajan taron jama'a ya koma yana fita Barrister yaji wani sanyi ya fara ratsa jikinsa sai ya kejin kansa fresh ba kamar ɗazo daya samu kansa a jiri ba, harya miƙe zai fita wajan ɗaurin auren sai yaji sanarwar har an ɗaura Auren akan sadaki dubu 100k with sisin gold. Ajjiyar zuciya ya sauke a taƙaice wani rabi daga cikin burinsa ya fara cika cikin ƙaramin lokaci kuma yaji so da ƙaunar Fannah na ƙara shiga cikin zuciyarsa. Sheikh ne yace "The you have any problem with that?" Taɓe baki Arjun yay yace "kaga canta matse maka shegen iyayinka yay maka yawa, nidai dan Allah muyi mu koma kai wa'azin a kaimin matana am anger to see my wife wlh" banza Sheikh yay masa sanin halin Sheikh ba irin mgnar nan yake so ba yasa Arjun ƙara faɗin "Finally zan kwana a jikin matata yau Wow akwai bacci mai daɗi" a cikin ran Sheikh yaja tsaki yana faɗin "Meye ajikin matar har kake rawar jiki Allah yasa ba yarinya bace masu kwararaton tsiya" wata dry Arjun yay yace "ehyeee har kasan mace nada raki? Idan yarinyar ce ni bani naji na gani ba? Ka jimu da mutum kai da ka tare da Aljana fa" haɗe rai tamau Sheikh yay Arjun na shirin yin mgna wayarsa ya fara ringing ganin sunan Uncle Sham yasa Arjun faɗin "ka nemi amsar bayarwa" kana yay picking call ɗin Uncle Sham na zaune a parlo shida wasu mutane sai kuma Barrister wanda yay garau sai wurga ido yake yaga ta inda matarsa zata fito "Mohd kuna ina ne haka?" Shiru Arjun yay kafin yace "Uncle ba ruwana Buddy ne yace mu juya" jim Uncle Sham yay kana yace "Ok bashi wayar" wayar ya miƙawa Sheikh kamar wanda ba dashi ake ba ya ɗauke kai yana kallon can sama ta cikin motar, sbd yanayin gari daya fara sauyawa hadiri ya shiga haɗuwa hakan yasa Sheikh ya fara tsorata sam bai son ruwa haka nan Allah yayi sa, calmly yay yace "sata speaker" sai lokacin ya tuna Sheikh bai taɓa riƙe waya ba hakan yasa cikin sauri yasa a handsfree muryar Uncle Sham ta cika motar yana faɗin "Why Imam?" Shiru Sheikh yay yana bin wayar da kallo sai da Uncle Sham yace "Speak up" sannan ya sauke numfashi Murya bata fita sosai yace "Uncle kawai naji bana son zuwa" Uncle Sham yace "akwai wani abu ne?" A taƙaice Sheikh yace "A'a" sanin halin Sheikh baya ƙarya yasa Uncle ya yarda da abinda yace kana yace "Ok ya kamata kuzo ko ruwa kusha kuma ko gaida Kawon Fatima" taɓe baki Sheikh yay yace "Who is she?" Murmushi Uncle Sham yay yace "Your Mother i mean your stepmother" lumshe idanunsa yay ba tare kuma da yace komai wai mother to Allah yasa ta zame masa uwar da yake fatan samu a kullum, Amma gani yake sam itama ba lallai ta bashi kulawar da yake buƙata ba komansa ya wargatse he missed his Airah ya rasa matarsa shiyasa ya kejin sa kamar ba mutum mai ƴan ci ba, ya rasa farin cikin sa a lokacin da zcy da kuma gangar jikin ta amince da ita, ya ɗauki hakan a matsayin wata ƙaddara amma meyasa tasa ƙaddarar zata zo masa a haka? Mai yasa a duk sanda yayi sake ya samu abu sai ya tafi ya barsa? Wanne laifi ya aikata haka? Da sauri yay astagafirullah a zcyarsa kana ya ɗaga kansa tare da sauke ganinsa akan Arjun yace "What again?" Arjun yace "burinka ya cika sai mu ɗauki hanyar Abuja ko?" Fesar da huci yay daga cikin bakinsa kafin yaja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login