Showing 36001 words to 39000 words out of 130248 words
ta tana faɗin "kima ɗauke rayuwa take, Soyayya kuma bada rayuwa take" Murmushi ya sakar mata yace "of course my dear,idan kin shiga ciki ki cema Abba gobe Uncle zaizo" ko ƙara kallonsa ba tai ba ta shige cikin gida tana share shawayen da suka taro a cikin idanunta, juyawa yay zuwa cikin motarsa mai ƙirar Audi RS5 mai blue black, kai tsaye hanya ya ɗauka domin a yau yake son komawa Abuja.
Nnamdi Azikiwe International Airport
Nnamdi Azikiwe International Airport is the prime international airport of the capital city of Nigeria, Abuja. Situated, shine airport ɗin dasu Sheikh suke jiran zuwan su Fareeq da Bahaiyya, cikin nutsuwa passengers suka fara sauka daga cikin jirgin wanda ya sauka a filin tashi da saukar jirgi na Nnamdi Azikiwe International Airport, kusan sune na ƙarshen fitowa kowa ka gani yana cike da farin ciki da murna, kusan rabin mutanan cikin jirgin students ne wanda suka samu hutu sakamakon kammala exam ɗin 3rd semister da sukai, kowa yana ɗauke da jakar matafiya, wata farar yarinya ce wacce ba zata huce age mate ɗin Fannah ta fara ce tass ta fara sauka daga stairs ɗin jirgin fuskarta ɗauke da zallar murmushi, tana sanye da duguwar milk wacce akaiwa ado da red ɗin stones rigar ta tsage daga gaba kana hango dugun crazy jeans data sanya,tai rolling kanta da red ɗin veil, hannunta riƙe da trolly ɗin ta, fuskarta ta cika da farin ciki gaba ɗayan ta ba zata huce 17 to 18 yrs ba, daga bayanta kuma wani chocolate ɗin sarauyi ne bashi da tsayi sosai but he's handsome guy yana kyau mai tasiri a zuciyar mace, da sauri shima yake sauka daga stairs ɗin jirgin bazai huce 20yrs zuwa 22 ba amma gaba ɗaya suna da girman jiki wanda hutu da jin daɗi da kuma kwanciyar hankali sune sukai tasiri a jikin nasu har ya haddasa masu girman jikin, kasa jurewa sukai a kusan tare suka kwaso da gudu suna faɗin "Yayahhhh Sheikh, Yayahhhh Sheikh" faɗaɗa fuskarsa yay da Murmushi tare da gyara zamansa da kyau a saman kujerar da yake domin yasan suna iya ka dashi wajan kokawar hawa jikinsa, rige rige zuwa wajan sukai da sauri kuma Fareeq ya ture Bahaiyya ya faɗa jikin Sheikh yana faɗin "Yayahhhh Sheikh we missed you a lot missed wlh,kamar nai fiffike na dawo Naija haka nake jina" lumshe idanunsa yay tare da bawa ɗan uwan nasa side hug yace "Wlcm back Fareeq Hamdan Balarabe wlcm Bahaiyya Hamdan Balarabe" Bahaiyya kuka tasa tana turo baki gaba, da sauri Sheikh ya ture Fareeq daya shige jikinsa yace "Ƙaton banza" dry Fareeq yay yana kallon Arjun yace "Yaah Arjun mun sameku lafiya?" Arjun ya ɗauke kai yace "A'a ban sani ba tunda ni ba za'a rungome ni ba" da sauri Fareeq ya rungome Arjun yana faɗin "double sorry Yayana" kansa ya shafa yace "Ohh Fareeq an zama manyan samari ma sha Allah" dry Fareeq yay yace "kai Yaah Arjun" Kallonta yay yace "Sorry Habibty" tana ƙara matsu hawayen idanunta tace "Ba Yaah Fareeq ba ne kuma na riga shi zuwa wajanka shine ya ture ni" Murmushin da baya barin fuskarsa a ƴan kwanakin nan yay yace "yanzu baya baki wajan ba?" Kai ta gyaɗa masa yana sauke ajjiyar zuciya yace "Barakallahu fikiii how was your study?" Tace "Yaah ba sauƙi wlh" Murmusawa yay kaɗan ba tare da yay mgna ba yaja idanunsa ya rufe ruf kamar mai shirin yin bacci.
Wayar Arjun ce ta fara ringing da sauri yay answering call ɗin sbd ganin sunan Uncle Sham yana kira, cikin ladabi yace "Ina yini Uncle" daga can ɓangaren Uncle ya gyara zama idanunsa akan Mami yace "kai da Imam kuzo yanzu" Arjun yace "Uncle bamu kaɗai bane munje ɗauko su Fareeq ne" jinjina Uncle Sham yay yace "ok ki fara drng nasu a gida then zai kuzo nan is that clear?" Arjun yace "Yeah" daga nan gaba ɗaya suka nufi gida bayan sun sauke su Fareeq suka juya zuwa gidan Uncle Sham, haka nan Sheikh ya samu kansa da faɗuwar gaba amma sai bai nuna a saman fuskarsa ba, yana zaune ya lumshe idanunsa yana yana sauraran bugun zcyarsa wacce bata fita sai da tunanin Aljanarsa.
A zaune suka samu Uncle a saman kujera idanunsa sanye cikin farin glass, ga laptop a gabansa yana operating akan aikin da yake wanda ya wancin dukiyar da yake kula da ita bata kowa bace face Sheikh, kusan fiye da rabi na Dukiyar Sheikh tana hannun Uncle Sham yana kula da ita, sam Sheikh bai kula da Mami dake gefe ɗaya zaune a saman kujera ba,sai matar Uncle Sham mai suna Aunty Amina, Arjun ne ya zauna saman carpet bayan ya gaida Uncle da Aunt Amina, sbd shima bai kula da Mami wacce take ta rufe gefen fuskarta wanda ya haye lokaci ɗaya ba. A sanyaye cikin kasalar data saukar masa yana ɗan fidda numfashi a hankali ya ɗaga kansa tare da duban Uncle da zararan gashin idanunsa,ya sauke ajjiyar zuciya tafi a irga kafin ya samu damar buɗe baki cikin ƙasa kuma da murya yace "Evening Uncle" Murmushin Uncle Sham yay zuciyarsa fass da ganin Sheikh cikin nutsuwa ba kamar sauran shekaru da watannin da kuma satittikan zuwa kwanakin daya ɗi ba bashi da walwala.
"Imam my son kana lafiya?" Ƙasa Sheikh yay da gansa sbd sarawar da yaji yay masa yana sauke ajjiyar zcy yace "Allahamdulillah!" Ya ƙare maganar yana jan manyan idanunsa wanda suke cike da bacci ya rufe, gyara zama Uncle Sham yay yace "Me kake shiryawa rayuwarka Didat?" Da sauri Mami ta kalli Uncle Sham sbd sunan da taji ya amsa na Didat sai kawai ta ɗauke kai tana tunani kala², shiru Sheikh yay domin bashi da amsar tambayar da Uncle ɗin ke masa, up ɗin laptop ɗin yay yace "what i mean mene hujjarka taƙin am Amincewa Auren yarinyar da Barrister yake faɗa maka?" Ɗan haɗe fuska Sheikh yay ba tare kuma da yay magana ba sai kuma ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya wacce ta cika ɗakin, Uncle Sham yace "it's okay! Na fahimta, amma kasan zama haka a gareka bamai yiwuwa ba ne ko? Idan taƙamar ka Mama na kula da kai wata rana dole zata gaza yayinda tsufa ya gama cinta,ko yanzu dauriya kawai take amma responsibilities ɗinka ya kusa fin ƙarfinta" shiru kowa yay yana sauraran abinda Uncle Sham ke faɗa kana yace "me yasa baka son Auren ita Nanan?" Runtsa idanunsa yay da ƙarfi ya shiga sauke ajjiyar zuciya dan seriously baya ƙaunar ai masa mgnar wata ƴar idan ba Aljanarsa ba, Uncle Sham ne ya ƙara maimaita masa tambayar kansa a ƙasa idanunsa a lumshe yana yatsuna fuskarsa cikin ƙasa da Murya very slow yace "ban so ne Uncle" jinjina kai kawai Uncle yay cike da gamsuwa yace "ko kana so ba lallai ya yiwu ba" Anut Amina tace "why?" Yace "I don't think a Governor will give him his daughter hands in marriage, Duk dukiyar daya tara, cos shi kansa baya da labarin auren shima Young brother ɗinsa wanda suke uba ɗaya ne yake son abun sbd lura da yadda yaga yarinyar tana ƙaunar Sheikh, dan haka ka manta da wannan mgnar, just forgot the past kawai ka fuskanci ƙalulaban dake gabanka ko zai sameka" cikin rashin fahimta suka kallesa gaba ɗaya kafaɗa ya ɗaga yana maida idanunsa kan jaridar darly trust dake gabansa.
Tun daga bakin ƙofa Granny ta sanya kuka tare da cire gefen mahaifinta tana faɗin "Assha, Assha Allah dai ya shiga tsakanin na gari da bugu" idannunsu suka bayar zuwa bakin ƙofar harta shigo ta nemi waje ta zauna tana matsar ƙwalla, Aunt Amina ce tace "Mama lfy dai ko?" Ƙara matsu hawayen tayi tana share hanci tace "inafa lfy Aminatou?" Uncle Sham ya ɗaga kansa ya kalli Granny wacce take matsayin yayar mahaifiyarsa yace "Mama wanine ya mutu ne?" Kamar wacce aka faɗawa wani abu ta ƙara rushewa da kuka tana matsar ƙwalla tace "Inafa Shansu, wani abun alamara na gani a talabijin wai wani ƙaton mutum fisabilillahi ya ɗaga uwar ƙafar sa ya danne mutum ana ji ana gani babu wanda yay mgn saima ihu suke,amma ai dai babu kyau cin zali na gaya maka gsky wancan har baki aka fasa masa nikam ina zan zauna gidan Sadia ina ganin wannan lukutar masifar fisabilillahi? Itama dai Sadia zama kawai ake da ita ba'a gama sanin ƙarfin imaninta ba wlh, nidai na bar mata gidanta babu ruwana" kusan rabin parlon sai da suka murmusa Uncle Sham yace "Hajiata kodai Resling film Kika kallah ne?" Da sauri Granny tace "Yawwa ɗan albarka sisilin amma dai ko gantalallu wlh ita kuma Sadia badai na bar mata gidanta ba?" Jinjina kai Uncle Sham yay yace "haka ne" Arjun dai na zaune yana jin yadda ake gantalar da uwarsa murmushi kawai yake, Gyara zama Uncle Sham yay yace "Allahamdulillah daman su nake kowa ya taro nasu kiran Baffanka a waya to baya ƙasar baki ɗaya,ina son na sani da gaske abinda Saudat ta faɗa gsky ne ko menene?" Tun zuwan Granny sai yanzu ya ɗaga kansa ya kalli Uncle Sham ba tare kuma da yace komai ba yaja idanunsa ya rufe.
Granny dake kuka tai tsit tana son taji abinda Uncle Sham zai faɗa "Saudat tace akwai mutanan ɓoye a jikinka haka ne" da sauri ya ɗaga kai ya kalli Uncle ɗin nasa kasa mgna yay sai ajjiyar zcy da yake saukewa, Granny ce ta muskuta tace "Wace Saudat kuma? Wacce gayyar ce?" Uncle Sham yace "gata nan gabanki ai Mama ita ta faɗa gama ciwon da suka ji mata nan, kuma tace kema an taɓa tsorata ki da mai kamarki" shiru Granny tai tana kallon Mami shima Sheikh sai lokacin ya juya ya kalli Mami suna haɗa ido ta janye nata idon tace "Eh Uncle gsky ne, shima kansa Sweet yasan da hakan kuma ina da tabbacin sune suka hanashi Aure domin a mgnarsu ta jiya sun tabbatar min da haka" kafin kowa yay mgna Granny ta fashe da kuka tana faɗin "kiji tsoran Allah Saudala kema uwa ce ki rasa sharrin da zakiwa jikana sai na Aljanun fisabilillahi? Kuma dai wlh Nima ina zargin haka sanin cewa Imamu malami ne yasa ban taɓa kawo tunanin wannan ba, to tayaya zanyi wannan tunanin do Allah? Tunda sai babu kyau zargi kuma wutar mai zargi daban take, amma nasha zuwa nemansa sai naga baya nan sai na koma ɗakinsa na ganshi shida Ranjun yace wai fita sukai,wani lokacin ma harda Barista nake ganinsa,naita Mmki sbd nasan Barista ba zama yake ba, nasha zuwa ina samunsa yana bacci yana surutai shi ɗaya yayta ɗaga ƙafa kamar dai wanda akaiwa kaciya, to haka nan naje ɗakinsa a ranar da nake gaya maka ya yini baya gida to wlh ina zuwa naga ƙatuwar macijiya a jikinsa, ina dalili ina mafari zaka jawa kanka masifa tunda kana da hanyar rabuwa dasu" Sheikh ji yay ransa ya ɓaci haka nan jikinsa ya ɗauki rawa jijiyoyin kansa suka fito a saman goshinsa lokaci ɗaya duk gargasar jikinsa suka mimmiƙe tsaye, ya shiga fesar da numfashi yana jan ajjiyar zcy, sosai Uncle Sham ya kaɗo da jin zancan Granny idanunsa akan Sheikh yace "is that true?" Shiru Sheikh yay idanunsa na sauya launi Granny tuni tai bayan kujera ganin abinda Sheikh yake, cikin tsawa Uncle Sham yace "dakai nake Imam haka ne? Gsky ne abinda Mama take faɗa ko mene? Da gaske ne akwai Aljana jikinka" idanun Sheikh akan Mami yaja ajjiyar zuciya ba tare daya kalli Uncle Sham ba yace "haka ne, kuma ina sane da ita a jikina rayuwa da ita ya fimin rayuwa da Iyayena tunda ta fisu ƙauna ta,bana jin kuma akwai abinda zai rabani da ita sai dai wata sabuwar ƙaddarar" kasa mgna Uncle Sham yay sai kallon Sheikh kawai da yake, Arjun ma with much surprised yake bin Sheikh da kallo, sai yanzu abubuwa da dama suka fara dawowa kansa, wato Airahn da yake yawan faɗa ba kowa bace face Aljanar dake jikinsa, zanan da yay ba kowa bace a jiki face Aljanarsa, da yawan lokuta yana ganin Granny a jikin Sheikh ashe ba kowa bace face Aljanar dake jikin Sheikh, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wanne irin abu ne haka? Ta maza Uncle Sham yay yace "ita aljanar da ita zaka zauna har ƙarshen rayuwarka kenan?" Kai tsaye Sheikh ya bashi amsa da "Eh" Jinjina kai Uncle Sham yay ba tare da yay mgna ba ya ɗauki wayarsa ya shiga latsawa harya fice daga parlon not too long time ya dawo ya zauna ba tare kuma da yace komai ba, cikin ɓacin rai Sheikh ya kalli Mami ya jinjina kansa ita dai ko a jikinta tasan sai an cire Aljanar jikinsa sannan zata samu damar kasancewa da sweet Imam ɗinta.
Ƙara miƙewa Uncle yay babu jimawa ya dawo da wani babban Malami wanda yake ɗauke da babbar jaka da kuma Kur'ani a hannunsa, zama Uncle yay fuskarsa a sake ya kalli malamin yace "Sit Malam" Zama Malamin yay kamar yadda Uncle Sham ya buƙata kallon tsaf yaywa Sheikh ya ganu gskyar lamarin, Sheikh wanda ya durƙosar da kansa ya kalli Arjun yace "let's go" kafin Arjun yay mgna Granny dake bayan sofa tace "me kace?" "Malam ina son a cire Mutanan dake jikinsa yanzun nan" zama Malam ya gyara yana kallon Sheikh wanda yake zaune ko mutsi ba yayi sai sakin ajjiyar zuciya da yake.
A can cikin jeji kam Airah ce kwance tana fitar da numfashi sai Tijama dake gefenta tare da Tuɓe, cikin mawuyacin hali ta kalli Tijama tace "Nasan bazan tashi ba, na san kin fini sanin suwaye suke farautar rayuwar Sheikh da kuma abinda suke so game dashi, Nakasar Sheikh ba daga Ubangiji take ba magauta ne suka samar da ita tun yana Ƙarami,sannan ba Saudat ce kaɗai take buƙatar wani abu game dashi ba,bayan ita akwai wasu, Ya kakata ina son ƙaddarar Imam yazo masa da sauƙi, bazai iya ɗauka ba naso na kasance dashi amma nima bani nake da kai na ba,akwai wanda ya halicci ne wanda a koda yaushe zai iya ɗaukan rai na,amma ina son kimin wata alfarma Yake Kakata" Tijama da jikin Airah ya fara bata tsoro kuma ta tabbatar wannan karan ba zata tashi ba ta daɗe da sanin Airah ba zai duguwar rayuwa kamar yadda ake faɗa sauran aljanu nayi,rashin Airah a jikin Sheikh ba ƙaramar tawaya bace amma dole tasan abin yi, kallon Airah tayi tace "Me kikeso ya jikanyata?" Sauke ajjiyar zuciya tayi idanunta na janye wa tace "kalli Tijama yadda Rayuwata yake baƙin cikin rabuwa da ni? Basu san ko basu rabani dashi ba Ubangijin daya haɗamu yana gaf da rabamu ba, Tijama ina son Sheikh Imam hamdan Balarabe yay farin ciki a rayuwarsa bana son yay kuka akan rashina kiyi abinda zaki akan cikar muradina, kiyi ƙoƙarin ɗaukan fansar da nace zanyi akan wanda ya lalata Rayuwar Sheikh Imam hamdan Balarabe, Tijama a koda yaushe numfashi na iya tsawaya ina son ki gayamin abinda kike ɓoyewa game da Sheikh wanda kikace SIRRIN MU ne ina son sani yanzu" shafa kanta Tijama tayi tace "Tabbas nakasar Sheikh ba lalura bace samar da ita akai ta hanayar a siri tun yana cikin mahaifiyarsa abu guda ne zai dawo masa da ƙafafuwansa har ya fara tafiya kamar sauran mutane" Airah na jan numfashi idanunta na tsiyayar da hawayen baƙin ciki da kuma takaicin rabuwa da Mijinta tace "Menene shi Yake Kakata?" Tijama ta kalli Tuɓe tace "Sheikh bazai taɓa taka ƙafafuwansa da zumar tafiya ba har sai ya kusanci mace....
🤕Hello nace idan an fitar da wannan sai a nemi sanitizer a wanke hannu asa face mars aci gaba da zaman jira
SIRRIN MU isn't free book
Contact to subscribe 08119237616 ga Niger 84506476
20/10/2021, 20:47 - 🤔🤔: *_NLUV💞_*
3️⃣1️⃣-3️⃣2️⃣
Zare ido Airah tayi tana ƙara kallon kakarta ta "Tabbas sai ya kusanci mace yay tarayya ta auratayya da ita sannan ƙafafuwansa zasu warke ya fara tafiya kamar sauran mutane,haka tsarin karyewar asirin yake, komu bamu da ikon da zamu karya wannan sihirin sai dai mu taimaka masa wajan samun macen da zata bashi wannan damar" kuka Airah tasa tace "Mene yasa sai an sama min kishiya kafin Rayuwata ya samu lfyarsa? Bazan iya jurar ganinsa da wata ba koda babu raina please Tijama do something" riƙeta Tijama tayi sosai sbd rawar da jikinta ya fara cikin ƙaramin lokaci ta fara kokawa da numfashinta, riƙe hannun Tijama tayi da kyau tace " please i need your help Tijama" shafa kanta tayi tare da danne mata ƙirji tace "zan maki komai zan ƙarasa cika maki muradin ki ko bayan babu ranki, amma dole ki rabu da Imam a dai-dai wannan lokacin domin hakan shima wata damace a garemu, ki fita a jikin Sheikh yanzun nan Airah" kuka Airah tasa tare da juya idanunsa zuwa gefe guda tana hango Sheikh dage gaban Uncle Sham kansa a ƙasa, girgiza kai tayi tace "i can't Tijama dan ki rabu dani na mutu a jikinsa ko zan samu sauƙin abinda na keji a raina, ki barshi yaga mutuwa dan Allah Tijama" tsawa Tijama ta buga mata mai ƙarfin gaske tace "idan baki fita a jikinsa ba yanzu tayaya zan samu damar kawo maki shi nan? Ya zama dole ki hqr da jikin Imam tunda ba tare Ubangiji ya kawo ku duniyar ba, idan kuma taimakon nasa da gaske kike sonyi dole ne ki ɗauki taki ƙaddarar kamar yadda shima sabuwar ƙaddara zata riskeshi a tasa rayuwar, rabuwa da Sheikh Imam hamdan Balarabe ya zama dole domin hakan kaɗai zai sanya mubawa matar Ubansa kunya a gaban muta nan da suka amince mata,kinga ko gaba ta kai wani zancen ba zasu yarda da ita ba" ƙanƙame jikinta tayi tana karkarwa tare da danne ƙirjinta dake mata ciwo tace "shikenan zan rabu dashi Tijama amma kimin al'ƙawarin babu wata ƴar macen da zai raɓa soyayyata ce kawai zatai ta tasiri a zuciyarsa, da soyayyata zai dauwama ita zata zamu abokin shirarsa, zata zame masa mata ɗa Aboki, dan Allah kada ki bari wani abu ya raba