Showing 33001 words to 36000 words out of 130248 words

Chapter 12 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5993

bakinta,datse bakinsa yay duk da cewa bai san me take ba, yaƙi bata damar aikata abinda take so, ganin bazai mata ba yasa ta saki marayan kuka tana faɗin "help me please Imam wlh mutuwa zanyi idan baka kusance ni ba, ka taimake ki Maminka Sweet" sosai take kuka sbd azabar data keji ta sha maganin ba kaɗan ba hakan yasa take jinta a sama ga wani kumburi da mararta tai mata, cikin zafin nama kuma miƙe tare da ƙoƙarin shigar da Sheikh ɗinsa jikinta bata ankara ba taji an ɗaga ta sama tare da haɗata da jikin bangon ɗakin. Wata gigitacciyyar ƙarar a zaba ta sanya tana dafe goshinta da taji lokaci ɗaya ya kumbura ga jini na zuba a wajan, cikin wata iriyar murya taji ana faɗin "Tabbas kina son sanya kanki cikin halaka, zanyi maganinki tunda kikai kuskuren taɓa abinda yake halaliyata, zan nakasa abinda kike taƙama dashi, lallai bil'adama baku da kunya kuyi mu'amala da Uba Kunyi da ɗa,sai dai kinyi kuskuren taɓa mijina kinyi kuskuren taɓa abinda ba naki ba" cikin kuka Mami ta shiga juya kanta tana neman inda ake mgnar gaba ɗaya jikinta rawa yake, tuni ta fara gani dishi dishi sbd jinin dake zuba a kanta "Dan Allah kuyi hqr wlh bazan ƙara ba, na daina" wata dry aka sanya wacce ta cika ɗakin gaba ɗaya akace "Jiiii kuuujibaaa jituu Saudat" shiru akai sai kuma akace "Kina ƙwaɗayin Imam ba sonsa kike ba, kina tare da Uban Imam ba dan kina sonsa ba,duk abinda kike ɓoyewa mun sani, burinki ki haɗa zuri'a da Imam yadda zaki mallake dukkan wasu dukiya daya mallaka haka ne??" Shiru Mami tayi ta kasa cewa komai sai fitsari daya ƙwace mata ta shiga yin sa, tsawa mai ƙarfi aka daka mata akace "Ko ba haka bane?" Da sauri Mami tace "Haka ne" dry aka kuma yi akace "tashi ki ɓace daga nan kinci Sa'a bana cutar da ɗan Adam da kinsha Mmki yau,kema bawai barinki nai ba ina son naga iyakar iya warki ne,kuma duk sanda kikai ƙoƙarin taɓa wani abu a jikin Sheikh babu shakka zan bayar da gabanki irin na maza" kuka Mami tasa tace "wlh bazan ƙara ba,dan Allah kuyi hqr" wani mari taji an waka mata da sauri ta dafe fuskarta sbd zafin da taji, tsoro yasa Mami ko riga bata ɗauka ba tai waje da gudu nono yana up and down a cikinta.






Washegari da safe Sheikh na zaune a saman Wheelchair yana sauraren abinda Granny take cewa, shi dai jinta kawai yake a hankali yake shan coffee ɗin dake hannunsa, yana sanye da black ɗin yadi wanda akai masa ado da red ɗin zare yay masifar yi masa kyau, ya ɗura jar dara a saman sumarsa, idan kaga Sheikh a lokacin zaka ɗauka yay irin 35yrs ɗin nan a duniya sbd girmansa da kuma buɗewar jikinsa, bayan ya gaba shan coffee ɗin ya lumshe idanunsa, yana jin bacci na fisgarsa "To dai Ubanka yakai Toshi" idanunsa a rufe yace "meye hakan?" Tace "au kasan kanuri ya ɗauko ko barebari zance maka ne? To a yaransu ne suke cewa TOSHI kuɗin na gani ina so, nidai babu ruwana nace Allah ya sanya alkairi yasa muna raye za'ai,kaga aini ma haifesa bazan masa baki ba domin idan ya lalace ni ya lalacewa,to ba gwamma kawai nai masa addu'a ba" Murmushi Sheikh yay shidai baya baƙin ciki da auren at least ko Granny bata nan akwai wacce zaiji mutsinta a gidan, dan haka yabi Auren da addu'a yace "Allah yasa albarka" Granny tace Ameen dai,Ni da kai ya zaɓawa matar auren ba,amma Fisabilillahi guɗe guɗe dashi yace aure zaiyi" Murmushi kawai Sheikh yake yana shafa sajensa yace "Granny zani airport" taɓe baki tayi tace "meye eyapass kuma?" Yana wata ƙasaitacciyar dry mai ɗaukan hankali yace "yau su Fareeq da Bahaiyya zasu dawo jirginsu na gaf da sauka ma" ta washe baki tace "Laa! Kace yau zamu samu manyan baƙi daga Turai, to sun gama bastas ɗin ne?" Yana taune lips ɗinsa yace "In sha Allah!" Tace "To Allahamdulillah" tace "Au ban baka labari ba Barista har kuɗin K3re sart2ye (kayan sa Rana) aka kai masa, wai ana son yin bikin da gaggawa, babu ruwana nidai nace gaggawa aikin sheɗanne, kuma Ankul ɗinka yazo baka nan yace kaje ka samesa" da to kawai ya amsa mata. Yana zaune har Arjun ya shigo da addu'a Granny ta bisu har zuwa wajan mota Arjun yaja motar suka bar gidan, shirun da yay yawa yasa Granny faɗin "Ita kuma wannan lfy yau ko aikin bata fita? Badai kurarta akai ba" ta ƙare maganar ta nufar flat ɗin Mami a parlor ta samu Mami zaune,da sauri Mami taja gefen veil ɗinta ta rufe rabin fuskarta, haɓa Granny ta riƙe tace "yau naga abinda ya daman ni Faɗimatu,ya haka Saudala?" Mami tai ƙasa da Murya tace "Kin tashi lfy?" Granny tace "Kamarya? Nace Kamarya ganina kaɗai ya isa ya baki amsa, keda baki da lfy ba gashi nazo dubaki ba" Calmly Mami tayi domin bata son duguwar magana tace "A'a Mama lfy nake,kawai ina hutawa ne shiyasa" Granny tace "naga alama kam, kisan abun dace ne wai Auren mace da ciki, Allah ya ƙara lfy" tana faɗin haka tai waje tana ɓoye dryarta domin sarai taga kumburin dake fuskar Mami, Mami kam tun sanda abun ya faru cikin dare kasa bacci tayi data kwanta zata tashi a firgice hatta sallah sai da gari ya hawaye tayi ta, Granny na fita Mami ta ɗauki wayarta tare da kiran Fariha kiran farko ta ɗaga cikin kuka Mami tace "na shiga uku Fariha yaya zanyi da cikar muradina,kince nai hqr da batun Sheikh wlh ji nake ko Aljanun zasu kashe ni bazan zama iya hqr da Sheikh ba sai na cikar muradin zuciya ta a kansa" Fariha ta sauke ajjiyar zuciya tace "yanzu me kikeso ayi a kai? Ni gsky ban goyi bayan kije wajan wani boka ba,domin suma da Aljanu suke aiki to kuma wanda za kiyiwa yana da Aljanun, amma akwai shawara ina ganin idan kika bita za'a dace" da sauri Mami tace "wacce shawarar faɗi ina jinki" Fariha tace "a fara raba Sheikh da aljanar data aure sa" share hawayen ta Mami tayi tas tana sakin murmushi tace "Tayaya? Wa kike ganin zan faɗawa maganar Aljanun nan har su yarda da magana ta?" Fariha tace "Uncle ɗin Sheikh mana" Mami tai shiru tana na zarin maganar kafin tace "Kina ganin hakan babu matsala Uncle ɗin zai amince?" Fariha tayi dry tace "Why not? Ke matsalar idan kina son abu idanunki rufewa yake billahi, babu wanda Sheikh yake jin maganarsa kamar Uncle ɗin sa, kinga da zarar kinje masa da magnar kuma kikai masa bayanin komai zan yarda kuma zai nemi Sheikh ɗin" tsalle Mami tayi tace "Good idea gaba ɗaya kana ya toshe i don't know how to do, sai yanzu bari kiga na kirasa a waya domin ance da sanyin safe ake kama fara" Fariha tai saurin faɗin "Wait Hajiyata zuwa ya kamata kiyi idan kin ɗauki abun da muhimmanci, kinga ni jiya harna rasa yadda zanyi idan naji damuwarki sai naji ba komai bace a kan tawa" shiru Mami tayi tace "kamar ya?" Fariha ta share shawayen daya zubu mata tace "Saudat what should I do? Abban Taufiq ya mai dani sakarya a cikin gidansa,ina tsoran haƙƙi na ya kamashi wlh,bazan iya bin maza ba domin da ina budurwa banyi yanzu da nake da yara bazan iya ba,amma na kasa jurewa rabuna dana haɗa shimfiɗa da Abban Taufiq good 2yrs kenan,Nima fa mutum ce juya nai kuka harna gode Allah sai dai fa nayi azumi, wlh jiya da abin yaymin yawa da kaina na biyawa kai na buƙata" da sauri Mami tace "What da kanki fa?" Kuka Fariha tasa tace "Yaya kike so nayi Saudat abin yay min yawa zuciyata ga take da bugawa wlh" Calmly Mami tayi tace "it's okay! Kiyi hqr komai zaizo ƙarshe nasa ke ba irina bace dasai na faɗa maki wani abu,amma akwai number wani likita da zan baki kiyi masa bayani idan ba wata matsalar ce daga gareki saiki faɗa masa,ko kuma kikai ƙararsa idan ma auren za'a raba sai a raba mene a ciki?" Da sauri Fariha tace "A'a banda raba aure Saudat wlh ina son mijina, yana kyautata min babu abinda na nema na rasa sai haƙƙina na kwanciyar Aure" tsaki Mami tayi tace "kinga ina da abinyi idan fuskata ta sace nazo wajan aiki mayi magana" daga nan suka katse kiran da sauri Mami ta shirya zuwa gidan Uncle tana gama shiryawa ta sanya liƙab, fita tayi taga ba taga driver, mai kula da Flowers ta samu tace "Isa driver fa?" Kansa ya sunkuyar yace "Hajiya ai ya fita tare da Granny" baki ta taɓe ba tare kuma da tayi magana ba ta shiga motar ta mai ƙirar Mahindra XUV7000 black color taja da gudu tabar gidan.


Yana zaune a saman kujera ya maƙala abun ɗaukan sauti a kunansa kamar yadda ma'aikatan gidan Redio suke yayin program, lumshe idanunsa yay yana kallon yadda Arjun ke operating system cikin ƙwarewa gefe guda kuma yana sauraran tambayar da wata take masa akan muhimmanci lemon tsami,shin da gaske yana rage sha'awa? Ko baya ragewa? Juyawa idanunsa yay domin idan da samu ya saba da irin wannan tambayoyin,shiyasa mutane da yawa suke masa kallon magidancin mai aure wanda ya tara iyalai da yawa.


Zama ya gyara shima Arjun yabar abinda yake ya shiga kallon Sheikh domin shima yana buƙatar jin wannan amsar, sautari yakan yanka lemon tsami with black tea ya shafa domin kwantar da sha'awarsa, dan haka yanzu a shirye yake domin jin full impormation akan lemon tsamin, Sheikh yay domin yama rasa ta ina zai fara a karo na farko kenan yaji tambayar tai masa nauyin jin yay shiru yasa Arjun sanya waƙar larabci a tashar, kallonsa Sheikh yay da ido yay masa alamar mene yasa ka kashe? Dry Arjun yay yace "naga baka shirya ba, da alama lemon tsami yana da matuƙar tasiri ga hajiyarmu" ya faɗa yana shafa wandonsa tsaki Sheikh yay kamar bazai mgna ba sai kuma ya sauke numfashi tare da fesar da iska yace "Banza ɗan iska" dry Arjun yay yace "ba zaka gane ba sai ranar daka rakani ɗakin Amayarta zaka tabbatar da cewa niɗin cikakken ɗan iska ne" da sauri Sheikh ya saita speaker gabansa tare dayin stop na waƙar cikin ƙasa da muryar yana Lumshe idanunsa yace.


"Muhimmancin lemon tsami ga lafiyar maniyi
Lemon tsami yana gyara maniyi
Lemon tsami yana cikin muhimman ƴaƴan itace da likitoci suka ce suna da muhimmanci a jikin ɗan Adam saboda sinadaran da ke ƙunshe a cikinsa.
Akwai nau'in lemon tsami daban-daban a sassan duniya amma wanda aka fi sani shi ne ƙarami mai tsami musamman a Afirka da yankin Asiya.
Mujallar lafiya ta Healthline a wani cikakken bayani da ta wallafa game da lemon tsami da amfaninsa ta ce lemon tsami yana ɗauke da sinadarin Vitamin C sosai, kusan yana samar da kashi 20 na buƙatar mutum.
Yana kuma ƙunshe da sinadarai na iron da calcium da vitamin B da Potassium da magnesium" shiru yay yana maida numfashi da sauri Arjun ya ɗauki gorar ruwan sa daya tawo masa dashi ya tsiyaya masa a cup ya bashi a sanyaye ya karɓa tare da kafawa a bakinsa sai da ya shanye ruwan tas,sannan yaja kujerarsa baya ya shiga maida numfashi, gaba ɗaya matan gidan redio'n da mazan tsayawa sukai da abinda suke suna sauraran abinda zai ce,bayan ya maida numfashi ya ɗura da faɗin.


Sannan lemon tsami yana kunshe da sinadaran da ke hanawa ko rage lalacewar kwayoyin halitta a jikin dan adam da ake kira antioxidants a Ingilishi.
Binciken ya bayyana cewa ci ko shan lemun tsami yana ƙara ƙarfafa garkuwan jiki, yana kuma rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya da kansa da ciwon koda da kuma inganta lafiyar fata" lumshe idanunsa yay yana shafa sajensa wanda yake a ƙwance yace "Muhimmiyar tambayar Shin Lemon tsami na tsinka maniyi?" Zaro ido Arjun yay yana ɗan danne dryarsa gudun kada Sheikh yaji, kallon kai ɗan iska ne Sheikh yaywa Arjun kafin ya ɗura da faɗin.


"Wasu mutane sun dade suna ganin cewa shan lemon tsami yana illa ga rayuwarsu ta aure, tsakanin al'umma ko kuma a al'adance ake bayyana cewa lemon tsami yana tsinka maniyin namiji.
Wani lokaci ma akan faɗa wa mutum cewa shan lemon tsami yana rage ƙarfin sha'awa ga maza da mata da kuma rage ƙarfin mazakuta.
Sai dai Hajiya Jummai Hassan ƙwararriyar likita kan abinci da ke asibitin Wuce a Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya, ta shaida wa BBC cewa, baya ga amfanin lemon tsami a hanyoyi daban-daban na lafiya yana kuma ƙara inganci da gyara maniyin mutum.
Ta ce lemon tsami yana da amfani da yawa ana - amfani da shi ta hanyoyi daban-daban wurin sha da kuma abinci.


"Yadda mutane suka ɗauka cewa lemun tsami yana da matsala ga ma'aurata ba haka ba ne domin yana da amfani a jiki sosai. Domin wani bincike ya nuna cewa idan ana shan sa ba da yawa ba yana gyarawa da inganta maniyi."


"Ɗan ruwan lemun tsamin da ake matsawa a ruwa ko a shayi a sha bai kai yawan da zai tsinka maniyi ba- sai dai ya gyara da inganta shi."


"Nasan duk yadda ake shan lemun tsami ba a matsa shi har rabin kofi zallarsa a sha - amma ɗan matsawa kadan ba shi da wata matsala ga lafiya ko tsinka maniyi kamar yadda ake cewa," inji kwararriyar likitar abincin.


Sai dai kuma ƙwararriyar likitar ta ce shan lemun tsami da yawa a lokaci ɗaya yana iya tsinka maniyi musamman ga masu son ƙayyade iyali kamar waɗanda ba su son haihuwa.


Ta ce akwai bincike da aka yi a Australia wanda ya nuna cewa yawan shan Lemun tsami adadi mai yawa a lokaci guda yana iya tsinka maniyi.


"Idan an yi amfani da shi a jiki kafin jima'i ko kuma a matsa ruwansa sosai a sha zai iya tsunka maniyi."


Shan sa ne da yawa lokaci daya ne ba a so- Kuma duk abin da ya yi yawa yana da matsala amma baya da wata matsala ga ma'aurata.


Yana gama faɗin hakan yay saurin katse shirin ta hanyar sanya tallah, kallonsa Arjun yay yace "Malam ya haka bayan baka gama ba,Nima ina da tambaya" banza yay masa yaci gaba da duba takardun gabansa, Arjun yace "Ya kamata gsky kai min lecture ta musamman yadda san sumar da My Aliyah kaga in one time ta ɗauki cikina yadda zan samu damar haihuwa da wuri na baka abinda na haifa" wani duka Sheikh ya kaiwa Arjun yana kwaɓe fuska yace "stop buddy ban so, kasan komai lokaci ne fa dan haka bana fidda ran wata rana zan shiga duniyar da kake ƙwaɗayin shigarta, kawai dan ban san tayaya ƙaddara zata zomin da abun ba" Shiru Arjun yay sai kuma yace "kaga tunda ka katse mana shiri tashi muje ka rakani wajan my Aliyah ina son naji abinda take so" "God forbid dani za'a shirya bidi'a? Kasan Allah ka rage rawar kai babu abinda za'ai daga walima sai ɗaurin auren walimar ma sai anyi ɗaurin auren" ɓata fuska Arjun yay yace "Haba buddy nidai gsky ka shiga haƙƙina" shafa ƙirjinsa yay yana sakin Murmushi mai sauti yace "to wannan zamanin mata da aljanu sukai masu yawa ana fara kiɗa kaga ƴar ƴan mutane suna zubewa a ƙasa kamar wasu tattabaru, nikam bana so" tura Wheelchair Arjun yay yace "ok nama fasa zuwa muje kawai gidan Uncle kaji kiran da yake maka" jama'ar gidan redio'n suka dinga gaisar da Sheikh suna masa gdy da ido kawai yake kallonsu domin bai fiya sakewa da mutane ba,daga Arjun sai yaran gidansu. Bayan sun hau kan titi Sheikh yay ƙasa da murya yace "mu huce airport after y maje gidan Uncle" murmushi Arjun yay yace "Duk yadda kace haka za'ai Sheikh Imam hamdan Balarabe.


Sosai Fannah tasa Barrister a gaba tana kuka tare da begen ɗinsa akan ya janye maganar auren, murmushi yay mata yace "mene yasa baki so?" Kai tsaye tana sauke ajjiyar y tace "Nifa bana sonka" har ransa yaji ɗacin maganarta dan haka ya miƙe tsaye yace "But ni ina so ina ƙaunar Auren yay za'ai?" Kuka ta ƙara sawa kamar ƙaramar yarinya tace "wlh bana so ran kuwa zai ɓaci da wannan auren, ka ɗauka sabur ƙaddarar muce zata fara dani dakai, badai kace sati biyu kakeso ba" yana ƙare mata kallo yace "eh haka ne,amma yaymin tsayi wlh naso ace 1week ne amma yana iya dole zan hqr, kinga ana auren zan ɗauke ki zuwa honeymoon" idanunta ta share tas tace "Shikenan zanyi Auren amma ka sani auren nan na nufi abubuwa da yawa, wlh wlh idan har aure akai aka haifan baza ka taba samun abinda kake muradi ba kana ji kana gani wani zai amfana dani kuma da auren ka a kaina.....










*SARAUTA 👑*
20/10/2021, 20:46 - 🤔🤔: *_NLUV💞_*
2️⃣9️⃣-3️⃣0️⃣
"Badai budurwar zuciyarka ta dake Ƴar cikanka take so ba? Ok fine idan ni kake so tabbas zaka saman idan kuma gangar jikina kake muradi zaka mutu da wannan muradin domin baza ka taɓa samun sa ba, wlh ni bana sonka dan Allah try to understand my feelings,zuciyata akwai wanda take ƙauna da muradin kasancewa dashi tun kafin na san menene so da kuma daɗin sa,ina jin kamar zan kasance dashi amma ƙaddarar aurenka na shirin wargatsa min all my plans" with much surprised yake bin bakinta da kallo gaba ɗaya bata huce good 17yrs a duniya ba amma har soyayya tai mata wannan mugun kamun? Tabbas ya shirya faɗa da dukkan wanda zai kawo masa cikas a zaman aurensa da Fatimansa,ya shirya ƙalubatanar ko uban waye wanda take so da kuma ƙauna kuma a shirye yake da shafe babinsa a duniyar baki ɗaya, juyawa tai da sauri zata bar wajan yay saurin riƙe gefen hijab ɗinta yana faɗin "Wait Fatima.." tsayawa tai ba tare data kallesa ba sai ajjiyar zuciya kawai take saukewa, from head to toe ɗinta yake ƙare mata kallo sai yanzu ya kula da zallar ƙuruciyarta domin ko a fuska ka kalleta kasan yarinya ce ɗaya sharaf.
Kamar daga sama yaji muryar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login