Showing 105001 words to 108000 words out of 130248 words

Chapter 36 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5971

a yanzu bata sonsa gaba ɗaya, amma mene yasa wannan tunuwar Sirrin ya girgiza tunaninta ne? Meyasa taji sam bata ƙaunar Sheikh ya tuzarta idan mgnar ciki ne zata zubar dashi kowa ya huta, amma mgnar da ake cikin wajan watansa uku zuwa huɗu.
Barrister ya ƙarasa inda Sheikh yake tsaye yana ɗan lumshe idanunsa, yana zuwa yace "Imam da gaske ne abinda na keji? Ko kuma sharri ne?" Gajiyayyun idanunsa Sheikh ya buɗe ba tare da tsoron fargabar komai ba yace "Gata can ai saita ƙarasa maka bayani with her evedance" yana faɗin haka ya shige bathroom ɗin dake maƙale a jikin bedroom ɗinsa, Juyawa Mami tayi ta ɗauki wayarta ta shiga gallery ta shiga nunawa Barrister photons da video, rufe idanunsa yay Yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi, da sauri kuma ya saki wayar ya nufi inda Fannah take zaune.
Tana ganinsa ta miƙe tsaye da raguwar kuzarinta Ta fara ja baya sbd wutar masifar data gano cikin ƙwayar idanunsa.
Yana zuwa ya cafki hannunta tare fisgarta zuwa waje, gaba ɗaya binsa take kawai sbd tasan ita ɗin me laifin ce ta kuma cancanci Duk wani hukunci da Za'ai mata.
Suna fita Mami ta saki wani shu'umin murmushi cikin zcyarta take faɗin "You're the best Saudat, u did a great job Wow! Finally Duk yadda za'ai Sheikh sai ya amshi cikina matsayin nasa, daga nan kuma zan san duk yadda nayi na raba Fannah da nata cikin, at the end all his property will become mine, Wow Saudat you're lucky" ta faɗa tana girgiza kanta tana jin komai ya kusa zuwar mata ƙarshe all her dreaming is going to be true.
SHEIKH na shiga bathroom ya kifa kansa a tsakiyar shower ruwa ya fara dukansa, ganin abin yake kamar a mafarki but komai dake faruwa is in real life, _"Ya rabb!"_ ya faɗa a taushashe yana furzar da wani zazzafan huci daga cikin bakinsa, ganin ruwan shower bazai masa sbd sosai yake jin zafin zcyarsa na dawowa saman fatarsa, zame kayan jikinsa yay ya ɗura saman hanger kana ya cika jacuzzi da ruwa mai sanyi ya shiga ciki.
A hankali ya janye idanunsa tare da Numfashinsa, ya fara shigewa cikin tafkeken jacuzzi wanda ya cika da ruwa, yadda baya fidda numfashi hakan yasa ruwan ya samu damar shigewa cikin hancinsa da kunansa.
Granny na fita ta samu Anut Amina tai jigum tace "Maza kira min ƴan sanda yanzun nan wannan munafukar sai ta kwana a gidan ƴan sanda"
Anut Amina tace "Granny abin bakai nan ba, nasan Sheikh he'll never do that, amma mubi komai a sannu har a gane Gsky, a bar abun a sirrince sbd bayyanar Sheikh Matsayin babban Malami wanda ake ganin girma da kuma darajar sa, kinga idan aka fitar da mgnar waje everyone zai kalli Sheikh Matsayin bad man and hakan kamar anyi cin zarafin sa ne, an tuzarta tashi a idanun jama'a"
Granny tace "Kefa ba ruwana babu abinda zai samu Imamu kamar yadda nake matsa addu'a amma dole ƴan sanda suzo yan zun nan, idan ba zaki kiramin su ba ki faɗa nai waje na nemu taimako wajan jama'a bokan nan babu wanda bai iyata ba"
Girgiza kai kawai Anut Amina tayi domin tasan abune mai wahala Granny ta fahimci matsayin Sheikh a idanun jama'a
Wayar ta amsa ta kira mata number as she said! Barrister na zuwa part ɗinsa ya cilla Fannah saman kujerar yana mata kallon tsaf kafin cikin ɗaga murya yace "Wannan cikin na waye, nawa ne or Imam?"
Shiru Fannah tayi sai Idanunta daya cika da hawaye ta fara shassheƙar kuka jikinta ya ɗauki rawa, hannu yasa ya miƙar da ita tsaye cikin tsawa yace "Am not talking to you? Cikin waye Fatima da gaske wannan cikin na Imam ne? How long Kika ɗauka kina cin amanata? Ace ciki a jikinki kuma cikin ɗa wanne kalar jakanta ne wannan,wlh idan baki gayan cikin waye wannan ba sai na yanka ki ɗakin nan"
Zubewa tayi a ƙasan wajan ƙafafuwansa ta saki kuka mai tsuma zcy tace
"Na sani i made a very big mistake, amma wlh is not my fault, na gaya maka bana sonka i don't love you anymore amma u don't understand all my feelings, meyasa yanzu zaka tsare ni akan abinda bana da ikon hanashi faruwa? Meyasa tun farko baka janye qudirinka na Aure na ba ka barni da wanda zcyta take so kuma take ƙauna, dan Allah kada ka matsa akan abinda kai zai iya sawa a ɗaure ka"
Kallon tsaf yay mata yana wani jinjina kai kafin yace "Wa me? Ni za'a ɗaure bama a ɗaure ki da wanda yay maki cikin ba? Ke Ni ba wannan ba ina magana akan wannan cikin na jikin ki na waye? Wane Ubansa ni Hamdan ko kuma ɗan cikina za ki haifawa ɗa? Wannan cikin ɗa na ne ko kuma jikana tell me Fatima".
Kuka tasa sosai ta kasa mgna ƙasan zcyarta kuma tsoro da tsanar abinda tayi haɗi da tsanare Sheikh suka ƙara dirar mata, amma bata ƙaunar Sheikh ya tuzarta bata fatan hakan, belet ɗin jikinsa ya zare yace "zaki gayan ko sai na farfasa maki jiki yanzun nan" kasa mgna tayi sai kuka da take tana jin gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi duk kukan da take tana jin abin cikinta na mutsawa kamar yasan akansa ake wannan masifar.
Zarara mata belet ɗin yay wanda tsabar gigitar da tayi yasa ta faɗi ta fasa wani uban ihu tare da birgima domin sosai belet ɗin ya sauka a fatar jikinta sbd ƙananan kaya dake jikinta.
"Wlh idan baki faɗa min cikin waye ba you'll regret for what you did"
Ya faɗa yana ƙara sakar mata wani dukan zafin daya ƙara shigarta yasa numfashinta ya fara sama sbd rabon da wani ya daketa a rayuwa harta manta, azaba tai mata yawa tana jine yana faɗin "Ok, wannan dalilin yasa kike gujemin ko? Bari nai yadda nasu a nan daga nan kuma sai na zubar da cikin kowa ya huta" jin haka yasa Fannah ta buɗe Dukkan muryarta ta ƙwalawa Sheikh kira.
Yana cikin jacuzzi ɗin babu alamar numfashi na fita a tare dashi sbd yadda yay kwance luff cikin ruwan, kamar a gabansa yaji saukar muryarta tana kiran sunansa, fisgo Numfashinsa yay da ƙarfi wanda yake ƙoƙarin barin gangar jikinsa nan da nan ruwan ya fara mutsi amma har yanzu ya gagara fitowa daga cikin ruwan sbd yadda ruwan ya shige masa cikin jikinsa.
A karo na biyu ya ƙara jin muryarta sai dai a yanzu a rarrabe ta kira sunansa da _"She....ikhhhh!!"_ wani irin zabura yay yana jin yadda santsin jacuzzi yake ƙoƙarin yadda shi amma ya tattaro dukkan wani karfinsa da jarumtarsa ya miƙe tsaye, idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa saman goshinsa.
Jikinsa na zubda ruwa musamman gashin ƙirjinsa dana kansa, haka ya jawo bathrobe ya sanya jikinsa, yana layi kamar ɗan ƙwaya idanunsa na rufewa ya nufi waje yana dafe bango a yadda ƙirjinsa da zcyarsa ke bugawa kawai yasan tana cikin matsala wani abu ya faru da _Zahraaansa_.
Fannah ganin da gske Barrister yake sbd ta miƙe a hankali ta tattaro dukkan ƙarfinsa ta hankaɗa sa baya, ta fita da gudu zuwa downstairs.
Mami waya take da dukkan alamu wayar mai muhimmanci ce tace "kar kaji komai, badai Barrister yay sign a file ɗin nan ba? To da wannan za muyi amfani mu tirkesa, kuma munyi amfani da motar Company Sheikh ne, amma hakan ba yana nufin zamu ɗura alhakin kisa a kansa bane, a'a komai zai tafi akan Barrister wannan contract na yarjejeniyar kisan bashi ka bashi yay sign akai ba?"
Daga can ɓangaren Mutumin ya ɗan saki dry yana murza kan motar yace "Exactly! Abin farin cikin files ɗin Property Sheikh dake wajan Uncle e shine na kawowa Barrister matsayin contract ɗin da yake nema, kinga muna da evedance wanda zamu tirke Barrister ya kaisa har gidan yari"
Farin ciki fal ranta tace "Kana da brain wlh, Yayinda Barrister ya shiga hannu a nan ni kuma zan fara nawa aikin wajan ganin na mallaki komai na Sheikh, amma kayi duk yadda zakai Sheikh kada yasha super ok"
Mutumin yace "Kada ki damu kin san waye ni, akan dukiya zan iya komai, amma kiyi duk yadda za kiyi Sheikh ya amshi cikin jikinki hakan shi zai bamu damar yin komai cikin sauƙi"
Miƙewa tsaye tayi lokacin da ihun Fannah ya daki kunnanta tace "Ok kada ka damu kaji komai zai tafi successful"
Jinjina kai yay yace "Where is my Cutie hope tana Lfy" tace "Yeah! She's fine I'll catch you later bye"
Tana faɗin haka tayi hanging up na kiran. Sheikh na zuwa parlon Fannah na sakkowa daga upstairs idanunta a rufe abin mmkin kuma gaba ɗaya kansa tayo hakan yasa ya daidaita tsaiwarsa gudan faɗuwa, Anut Amina gyara zama tayi tana kallon ikon Allah, Granny ta saki sbd Fannah hijab ɗin jikinta ya cire daga ita sai wani crazy jeans iya cinyoyinta wanda suka ƙara girma, ga half vest cibiyar ta a bayyana ne, wanda cikin jikinta ke sawa tai wannan shigar sbd bata son zafi ko kaɗan, idanun Sheikh a rufe ya shiga mutsa bakinsa yana tasbihi da neman kariyar Ubangiji, sbd gaba ɗaya kansa ya toshe.
Fannah na zuwa ta faɗa jikin Sheikh wanda yay dai-dai da tsayawar numfashinta, haka kuma yay dai-dai ta isuwar Arjun da kuma Police ɗin da Granny ta kira wanda mata ne suka shigo mazan suna waje.
Barrister shima ya sakko downstairs ɗin yayinda Mami ta fito idanunta yay faca-faca da hawaye.
Shigar da ita jikinsa yay a ruɗe kuma ya fara girgiza ta yana ɗan buga kumatunta yana faɗin _"Wake up Zahraaah, don't do this to me ki tashi nothing will happen to you ok!"_
Ganin haka yasa Anut Amina miƙewa ta nufi wajan fridge ta ɗauki ruwa mai sanyi, karɓa Sheikh yay yana ɗaukan ta cak zuwa duguwar kujera, gaba ɗaya suka tsora masa ido Arjun mmki ya hana shi tambayar abinda yake going on! Buɗe ruwan yay tare da shafa mata a fuska, amma ko mutsi ta ƙiyi hakan yasa Sheikh tsorata baya son nuna gazawar sa at all amma Sheikh itace weakness nasa, zai iya loosing control ɗinsa akan ta.
Uwa ba gudan jininsa dake jikinta baya son rasa ɗaya daga jikinsu domin su biyun yake kalla ya samu nutsuwa a zcy, miƙewa yay da ita a jikinsa da sauri Barrister yace "Stop Imam, Fatima is my wife not urs ka gane, kada ka sake ƙoƙarin yin wani abu a gareta, duk ko biyun you'll pay for what you have done".
Ko tsayawa Sheikh bai yi ba yaci gaba da tafiya Barrister yace "Wlh Imam idan baka sauketa ta faɗa min cikin waye a jikinta ba zan tsine maka, ka bari na ƙarasa kasheta idan yasu tayi bayani a lahira"
Cak Sheikh ya tsaya jin kalmar Abban nasa, a hankali ya sauke numfashi yana ɗan taune leɓansa kafin ya juyawa gaba ɗaya ya kalli mutanan Parlon har da police ɗin cikin jarumta da cikar haibarsa da zallar murmushi a fuskarsa yace.
"Ok Abba! Amma bari na fara taimakon ta ta samu numfashinta I'll explain you everything" yana faɗin haka ya sanya tattausan bakinsa a saman nata wanda ya jiƙe da yawo gaba ɗaya Parlon suka ɗauke kansu banda Mami wacce take jin zcyarta na bugawa, a sanyaye ya zare ribbon ɗin kanta gashin ya bazo a saman fuskarta wanda ya haddasa rufewar bakinsu dake haɗe jikin na juna, cikin nutsuwa ya maida dukkan hankalinsa ya fara hura mata iskar bakinsa zuwa cikin bakinta yana Murza tsakiyar tafin hannunta, babu jimawa taja wani wahalallan numfashi tana ƙoƙarin sanya wani kukan yay saurin danne mata baki da nasa, cikin ƙamshi da kuma ɗanɗanon bakinsa yasa ta haɗe bakinsu domin ta tabbatar da abinda ta keji, a wahalarce ta buɗe idanunta wanda sukai ta sauke saman Kamila fuskarsa mai cike da haiba, idanunsu ya sarƙe cikin na juna, a hankali ya dinga juya tongue ɗinsa cikin bakinta Wheel idanunsa na cikin nata yana hango zallar soyayyarsa a cikinsa amma wani banzan dalili nata ya hana ta fahimci abinda yake ranta.
Idanunta taja zata rufe ya ɗan daki kumatunta hakan yasa ta ƙara ware su a hankali ya fara bata wani hot kisses wanda ya daɗe bai samu ba, Yadda yake mata kaɗai zai sanya ta fahimci yadda yay missed ɗinta.
Bakinta ta ware hakan yasa nata bakin ya ƙara shiga cikin nata ciki so da ƙaunarsa wanda yake ƙasan zcyarta ta fara bashi wani lafiyayyan kiss mai tsayawa a zcy Sheikh ji yay yana ƙoƙarin zubewa sbd ƙafafuwansa dake rawa gaba ɗaya ya manta da Mutanan wajan _Zahraaaah_ kawai yake kallo a gabansa dama bayansa, zai ɗauki ko wanne abu wajan kareta bai damu a kansa ba indai Zahraaah zata samu kwanciyar hankali da nutsuwa harta kula da abinda yake cikinta.
Arjun ya ɗan saita murya kana yace "Buddy" sai kuma ya buga kujerar wajan, da sauri Fannah ta zare bakinta ta sauka jikinsa tana ƙoƙarin guduwa yay saurin haɗata da jikinsa yana kifa fuskarsa a cikin gashin kanta.
Granny bata son lokacin da tace "Muhammadur Rasulullah (S.A.W)" sai kuma ta sanya kuka.
Arjun yace "Sheikh me kake haka ne? Kana cikin hankalinka kowa?" Fesar da iska yay idanunsa ya ware ya kalli Barrister hakan nan yaji baya jin nauyinsa kamar da, Barrister wanda ya kejin zcyarsa kamar zata fashe ƙarar yake ƙoƙarin rasa damarsa yace "Are you done? Yanzu explain cikin waye a jikinta?"
Fannah kunya ta kamata tana jin kamar ta nutse a wajan, bata san me Sheikh ke taƙa ma dashi ba, amma gaba ɗaya ta nemi tsanar da tayi masa a yanzun ta rasa, jin Sheikh ya shafa jikinta tare da ɗauko mayafin Anut Amina ya naɗe mata jikinta dashi.
Tsaiwarsa ya gyara yace "Da Zahraaah da abinda yake cikinta duk nawa ne, i love her kamar yadda nake son kaina da Rayuwata, zan iya bada raina da dukkan abinda na Mallaka akanta, mai Soyayyar gsky fansar rai yake bayarwa akan wanda ya keso bawai ya ɗauki ran wanda yake so ba".
Barrister wanda har huci yake yace "Imam ni mahaifinka kake faɗawa haka? Ni kake tarayya da matata ta sunna har kai mata ciki?"
Lumshe idanunsa yay ya ƙara buɗewa akan Barrister yace
"cikin Zahraaah, nawa ne kamar yadda tun a sali na sameta a kamilalliyar mace, wacce bata san kowanne Namiji ba sai Ni"
Kan Barrister ya sara da ƙarfi saman ya daɗe da zarga ashe Fannah ce dalilin samuwar ƙafar Sheikh? Kenan bai taɓa kusantar ta ba ko me? Kasa mgn yay sai cewa yay da yay Maam "arrest him, zanyiwa lawyer na mgn" yana faɗin haka yay upstairs yana dafe kai, Kasancewar Ƴan sandan mata ne hakan yasa ɗaya ta fita ta kira sauran mazan suka nufi inda Sheikh yake tsaye.
Arjun da Granny sukai saurin yin wajan Arjun yace "Officer stop muyi mgn anan basai anje gaba ba" wani kallo Officer yay Arjun yace "Malam kai zaka faɗa aikin mune? Babu wanda ya isa ya hana mu tafi dashi sai wanda akaiwa laifin" Fannah ta rikice a yanzu idan aka tafi dashi wa take dashi? Ta rasa mahaifinta ta rasa kawonta kenan bata da sauran wanda zai taimaka mata kuka ta saki Sheikh ya kalleta da idanunsa wanda suka ɗan tara ruwa yace _"I promise to be everything to you! I will take care of you! I will stand by you a ko'ina a kuma ko Yaushe, zan maye maki gurbin koma you've lost, sannan i promise to be your family Duk da kina dasu, Don't cry Again come here Zahraaah Jewel"_
Da sauri ta nufi wajansa tana zuwa ta shige jikinsa ta saki kuka tana rirriƙesa mgn take son yi tace ya tafi da ita duk inda za'a kaishi kada ya barta za tafi samun nutsuwa idan yana wajan, Arjun ganin abun Babba ne ya fita waje idanunsa cike da waye tausayin su Sheikh wannan Soyayyar tasu Forbidden love ce wacce tarayya da junansu haramun ne, kai tsaye number Aliyou Eneye Ahuoyza Deen ya kira domin yay masa hanyar samun babbar lawyer nan Queen Maimunatou Moon.
Officer ya fara janye Sheikh, da saurin Anut tace "Dan Allah Officer ku rabu dashi ka bari ai mgn a wajan nan ko me kuke so za'a baku" Officer yace "Mgnar babbace and nasan Sheikh yana da kuɗin da zai babu da komai Amma Uban daya haifesa shi ne ya bada umurnin kamasa" Sheikh rungome Fannah yay sosai idanunsa na ɗan tsiyayar da hawaye kana yay kissing bakinta da hancinta da goshinta da wuyanta, ya ɗura bakinsa a kunanta yace "I love You Zahraaah i love You! I love you so much please take good care of yourself and my unborn child"
Yana faɗin hakan ya saketa yana jin Anut Amina na zura masa jallabiya tana sakin kuka, Officer ya maƙalawa Sheikh sarƙa a hannu, ya fara jansa Granny ta kalli Officer tace "Allah ya tsine maka La'ananne mugu azzalumi, kai dai ba zakai albarka ba kuma wlh saika sakar min jikana" kuka Fannah take kamar ranta zai fita tana kiran sunan Sheikh Anut Amina ta riƙeta mutuwar Uncle Sham ta dawo mata sabuwa da yana nan da wannan duk bai faru bazai taɓa bari a tafi da Sheikh ba.
Suna zuwa baƙin ƙofa ya tsaya tare da juyawa ya kalli Fannah dake kuka yace "Just wait for me Jewel" yana faɗin hakan ya fita kai tsaye motarsu suka sashi Allah yasa motar a rufe take Arjun yabi motar yana faɗin "Don't worry Sheikh you'll be safe" yana faɗin hakan motar ta fita da gudu zuwa police station....






SIRRIN MU
Contact to subscribe
08119237616




NIMCYLUV✍🏽
22/10/2021, 10:38 - 🤔🤔: The Evedance
81-82


Da sauri Arjun ya juya tare da komawa cikin gidan yana zuwa ya samu Granny a Parlo tana faɗin "Haihuwar asara, to gidan na kawonka ne da zaka shigo mana? Yau naga sabuwar gantalewa fisabilillahi ni Faɗimatu, wlh gidan zan bari ba zan iya tsiya tunda ake ƙoƙarin kashe min jika nima kashe ni za'ai".
Anut Amina ta kalli Arjun tace "Arjun yanzu da gaske sun tafi da Sheikh? Innalillahi wa'inna ilaihir" Arjun yace "Kada ki damu everything will be ok Anut Amina,bari na kira wata lawyer in sha Allah zata tsaya masa".
Anut Amina tace "In sha bazai taɓa tuzarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login