Showing 114001 words to 117000 words out of 130248 words
Alhj Kamal ya kalli Fannah yace "Shin daman dai kina da ra'ayin tarayya da Sheikh, kuma mgnar baki taɓa haɗa shimfiɗa da Barrister ba ƙarya ne, Sannan..," shiru yay sbd salatin da yaji Granny ta tafka, zumbur Granny ta miƙe ta nufi inda Alhj Kamal yake ta shiga tafa hannu tana faɗin "Muhammadur Rasulullah (S.A.W) wlh kai dai babu kai a ganin Annabi, ba kaji Imamu yace da cikin da mai cikin duk nasa bane? Kai dai anyi a sarar haihuwa ka zauna kaita giggilla ƙarya, to babu gantalalle irinka a nan" tana faɗin hakan ta juya ta kalli Al'ƙali tace "Don Muhammadur Rasulullah maza a nan ka yanke masu hukuncin kisa, a fille kan salllamammu" Da sauri Saudat ta kalli Granny Alhj Kamal yace "Wa muka kashe da za'a kashe mu kuma? Ni meye nawa a ciki?" Moon tai Murmushi tace "Ka shirya kare kanka bawai kare wani abuba" guduma Al'ƙalin ya buga kowa yay shiru kana yay rubuce² zuwa wani lokaci kafin ya ɗago kai yace "Bisa ƙwararan hujjojin da wannan Court mai adalci ta samu ta wanke Sheikh Imam hamdan Balarabe bisa zargin sa da akai, sannan Court ta buƙaci Barrister ya bawa Sheikh kuɗi bisa ɓata masa suna da akai" Kuka Fannah tasa tana rungome Yakura farin ciki fal ranta sai shafa cikinta take, da zata iya da babu shakka wajansa za taje ta rungomesa.
Gyaran murya Moon tayi tace "Bayan nan Matar Uncle Sham na ƙarar Barrister bisa zarginsa da kashe mata miji da yay" da wani irin sabon tashin y Barrister yace "What? Wlh bani bane ban kashe kowa nayi niyya amma bani bane" gaba ɗaya aka kallesa Al'ƙali yace "Kace bakai bane, kuma kace kayi niyya mekenan?" Sunkuyar dakai kansa yay kafin yace "Tabbas nayi niyyar kashe Uncle Sham, lokacin da zargina ya tabbata a kansa, na shirya yadda za'ai a kashe sa cikin ruwan sanyi a ranar da ya tafi Barno, amma wanda nasa yay kisan ya dawo yace ai sunyi Accident amma wlh bani bane" gyara tsaiwa Moon tayi tace "Idan akai bane kenan Matar kace Saudat tayi kisan kamar yadda ta faɗa jiya" Mami ji tayi cikinta ya juya da ƙarfi zcyrta ta buga bata son lokacin da tace "Kai Ni kuma yaushe na faɗa kuma?" Ka faɗa Moon ta watsa tace "Ai ko abin naku wasa ne, kun iya haɗa abu amma baku san Yadda zaku kare kanku ba, tun jiya na fara shiri na, jiya kinje Police station wajan Sheikh kin faɗa masa maganganu da yawa" daga nan Moon ta ciro wata na'ura ta bawa wani shi kuma ya bawa Al'ƙali, ana kunnawa Muryar Mami ta bayyana duk abinda ta faɗa jiya sai da kaji, Moon tace "Ɗan sandan daya rakaki wajanki ba ɗan sanda bane, shiri na ne, ni Barrister/Queen Maimunatou Aliyou Eneye Ahuoyza Deen" wani fito Deen yay tare jinjina mata, dole Mami ta fito gaban jama'a tace "Zahiri ina son Mallakar Dukiyar da Barrister yake ƙwaɗayi, fahimtar kuɗin bana kowa bane sai na Sheikh yasa na fara tunanin yadda zan mallaki komai nasa, shiyasa na fara shirin ƙulla tarayya dashi amma duk yadda nasu yaƙi, sai na rabo dashi na fara binciken yadda zan samu komai cikin sauƙi, wata rana naje gidan Uncle Sham yana Tsaka da rubutu sai ya tashi yabar rubutun da yake ban tsaya tunanin komai ba na fara karantawa, a nan nagane cewa Fannah matar Sheikh ce, sai na shirya yadda zan lalata ƙusanci dake tsakaninsu bayan nayi haka kuma, na fahimci ina da ciki sai na shirya ɗorawa SHEIKH cikin, ganin Fannah nada ciki sai hankali ya tashi naga kuma a koda yaushe asiri na shirin tunuwa sai na shirya yadda za'a kashe Uncle Sham, amma kafin hakan wani ya rigani domin Barrister yasa an sace motar Company Sheikh, bayan ya bada file ga wanda zai kisan ya sanya hannu, amma wlh Allah bani na kashe su, wlh bani bace Allah ko yarda dani" Barrister ba ya shiga rantsuwa, daga nan Moon ta kalli Alhj Kamal tace "Idan ba Saudat bace, ba kuma Barrister Hamdan bane, kenan Barrister Kamal ne ya kashe su kamar yadda ya daɗe yana cin amanar abokin nasa, harta kaisu ka samun yarinya shi ne yanzu kaci Amanar Abokiyar hurɗar taka kuma kaci Amanar Abokin naka?" Rarraba idanu Alhj Kamal ya fara ya shiga rantsuwa dafe kai Moon tace "Ok Securities za kuga wani a outside ku shigo dashi" ba taɓa lokaci aka fita aka shigo da wani matashi saurayi Barrister! Mami! Alhj Kamal suna ganinsa suka miƙe tsaye aka shiga kallon kallo...
Finally dai na warware dukkan wani ƙulli da yake a littafi😨 let's see who is the killer.
SIRRIN MU isn't free contact to subscribe
08119237616
NIMCYLUV✍🏽
22/10/2021, 10:38 - 🤔🤔: Released From Jail
85-86
Gabatar da kansa saurayin yayi, kana yay Shiru yana sauraran tambayoyin da Za'ai masa, Al'ƙali yace "Malam Adam, ka shirya faɗin gsky ba tare da tsoro ko fargaba ba? Ka shirya zaka faɗi gsky tsakaninka da Allah?"
Wanda ake kira da Adam ya ɗaga hakan yasa Moon tace "Adam a tura ka ka saci motar Company Sheikh haka ne?" Kai tsaye ya amsa mata da "Eh" sai ta kuma cewa "A cikin wannan mutanan wanene ya saka wannan aikin?" Adam ya kalli Mami ya dawo ya kalli Barrister kana ya kalli Alhj Kamal, ɗauke ido yay yace "Duk cikinsu ba wanda banwa aiki ba, sai dai duk nai masu aiki ba tare da sanin cewa inawa wani daga cikinsu ba, Hjy Saudat tasa na sace motar bayan haka, Barrister yasa na ɗauko masa motar bisa dararjar kuɗi masu yawa, dalilin hakan kuma na amince nace na ɗauko masa motar, Amma shi ya amshi motar ne yana son a ɗauko masa drugs a ciki (Muyagun ƙwayoyi) daga nan ban san komai ba sai da Alhj Kamal ya rikani ya bani motar ya gaya min abinda ya keso, wato naje na kashe masa wasu mutane, nayi shiru sbd ban san me zance masa, daga nan nace yaban lokaci ina ta tunani sai kawai nace masa bazan iya ba, dan haka na bar masa office ɗinsa" kallo ya dawo kan Alhj Kamal nan Court ta buƙaci ganinsa, tsayawa yay yana sunkuyar da kai kafin yace "Barrister aboki na ne, wanda bani da kamarsa, tunda na fahimci munufarsa na gane irin manyan kadarorin da yake hari na sauya tunani na, Nima na fara farautar abinda yake so, hakan sa muka haɗa ƙarfi guda Shida matarsa Saudat,ita ta fara zuwa waje na a faɗar ta, tasan nasan komai naka, na Aminci mata sai na kawo mata buƙatata, muka fara zumunci har aka samar da Bahaiyya, wacce ita ɗin jinina ce kuma ƴarta ce, lokaci guda na fahimci Saudat bata da imani tun sanda ta gaya min nufinta akan Sheikh, dan haka Nima na janye daga gare ta na fara aikina ni ɗaya, bayan an kawowa Barrister mota naje nace ya bani aro za'a shigo min da kaya, ba musu ya aramin,har yake bani file ɗin drugs ɗin da za'a kawo masa, kuma burinsa a yanzu ya amshi wani file dake wajan Uncle Sham, daga nan na nemi wani bayan Adam yaƙi na bashi kuɗi wajan 5.6m haka yaje da motar yabi ta kansu Uncle Sham, daga nan ya ɗauko min file ɗin, ni kuma na bawa Barrister file ɗin ya samin hannu, domin na shirya ɗura masa laifin kisan, tun daga ranar makashin da yay kisan ya fita hayyacinsa ya zama kamar mahaukaci, yana ta faɗin ya shiga uku, Tabbas ni na sanya a kashe Uncle Sham da sauran Mutanan domin idona ya rufe kunne na ya toshe kuɗi kawai nake gani da jin daɗin rayuwa" nan aka shiga Allah wadai da Alhj Kamal Al'ƙali yay rubuce² kafin yay gyaran murya yace "Bisa dugun nazari da kuma hujjojin da Court suka samu akan wanda yay kisan dan haka bisa adalci a yadda hukunci yake a Muslunci Al nafs bin nafs, a hukuncin Shari'a kenan, In kuma a kotun turanci ne, Section 221 of Penal Code duk wanda ya kashe wani shine kashe shi ake yi inde da gangan ne, dan haka wannan Court ta yankewa Alhj Kamal da Barrister Hamdan Balarabe hukumcin kisa ta hanyar rataya, Barrister hukuncinsa akan Iyayensa daya kashe Alhj Kamal kuma akan kisan so Uncle Sham, wanda yay kisan kuma Allah ya fara yi masa hukuncin tun daga yanzu, Ina fatan wannan abun zai zama izini ga masu son ransu da son duniya fiye da lahira, ace idanun mutum ya rufe akan kuɗi har ya kashe iyayensa, wannan duniya ina zata damu, Allah ya kyauta ya kuma shirya mana zuri'a" gaba ɗaya aka amsa da Amin wata Ɓoyayyiyar ajjiyar zcy Mami ta sauke a zcyrta tana Allah wadai da hali irin na Alhj Kamal gefe guda kuma tana baƙin rasa shi sbd Bahaiyya, Fareeq kasa zama yay lokacin da ƴan sanda suka nufi wajan Barrister yasu tafi dashi. Dishi² Sheikh ya fara ganin sbd wani bugu da zcyarsa ke masa, a hankali ya fara tari ba tare da kowa ya sani ba, Fannah ji tayi dama babu kowa a wajan tana son ta haɗa ido da Malaminta taga irin farin cikin da zai yi, juya idanunta tayi taga bata ganshi ba hakan yasa ta sulale daga wajan tana dubawa a hankali, Anut Amina ma wajan Sheikh ta nufa sbd ganin yaƙi fitowa kusan a tare har suna karo da juna suka ƙarasa wajan, gaban Fannah ya bada sauti sbd ganinsa da tayi durƙoshe yana tari cikin sarƙewar numfashi, ga jini na zuba daga hancinsa, jikinta na rawa da wani irin sauri har tana ture Anut Amina kafin ta ƙarasa wajan jikin Sheikh ya saki Numfashinsa ya tsaya hannunsa dafe da ƙirjinsa dake masa zafi da raɗaɗi, baya Anut Amina tayi tana sakin salati gaba ɗaya hankalin jama'a ya dawo kanta da sauri Arjun ya ƙara so ganin Sheikh haka ya firgita sa, Fannah kam zubewa kawai tayi a wajan ta kasa aikata komai sai rarraba idanu da take, motsin da taji yasa ta buɗe idanunta hannunsa taga yana rawa yana Shirin taɓa fuskarta, sai a lokacin ta gane bai gama ficewa a hayyacinsa ba, runtsa idanunta tayi tana jin yadda yake son jan jikinsa kusa da ita amma ya kasa, buɗe ido tayi sbd tattausan hannunsa da taji saman fuskarta sai a lokacin ta fashimci hawaye ke zuba daga cikin idanunta, dugun yatsarsa ya sanya ya sharce mata hawayen yana ɗan jawo fuskarta dab da tashi, cije lips ɗinsa yay sbd wani irin azabar ciwo daya keji a zcyarsa, dab da kunanta yana ɗan fesa mata Numfashinsa mai ɗumi cikin ƙasa da murya da sarƙewar numfashi yace _"Matata!!"_ shi kawai ya samu damar furtawa ya riƙe hannunta gam yana faɗin sunan Allah, daga nan Sheikh bai sake fahimtar komai ba, sai farkawa yay ya gansa a saman bed ɗin asibiti.
Duhu ya fara gani hakan yasa ya maida idanunsa ya rufe a hankali ya shiga motsa bakinsa yana tasbihi ga Allah daya ƙara farkar dashi a duniya, saukar numfashinta ya ji yana dukan saitin ƙirjinsa wanda yake a buɗe slowly ya ƙara try na buɗe idanunsa sosai hasken room ɗin ke damunsa amma bisa dole ya buɗe idanunsa tare da saukesu a saman drip ɗin dake maƙale a hannunsa.
Sosai yay mmki domin bai tunanin a asibiti yake ba, kenan duk yadda yaso danne abun sai da yafi ƙarfinsa kenan, cikin ransa yake faɗin _"Zahraaah my wife_, ɓoye min ya ƙare, zaki kasance da Malaminki, yanzu ne ya dace kisan cewa soyayyyar Malami fiye take data sauran maza" a zahiri kuma wani ƙawataccen Murmushi ne ya suɓo ce masa.
Saukar numfashinta ya ƙara dukan ƙirjinsa hakan yasa yay ƙasa da idanunsa,ƙuri yay mata idanu ganin yadda take bacci amma sai marai-raice fuska take ga wasu gudun tun hawaye na bin idanunta wanda suka bushe.
Ƙyakkyawar fuskarta ya tsorawa idanu yana jin yadda so da ƙaunar Zahraaansa suke ƙara ratsa zcyarsa, ganinta kawai kusa dashi yasa yaji ya nemi duk wani ciwo ya rasa.
Ware idanunsa yay ganin kayan da suke jikinta ba sune wanda tasa a Court ba.
Kenan kwana yay a asibitin ko mene? Agogon ya kala yana ɗan runtsa idanunsa yaga wajan biyar na Yamma.
Kallonsa ya mayar gareta yaga yadda ta riƙe masa hannu, lafiyayyiyan murmushi ya sauke ya miƙa hannu da shirin shafa kanta yaji an murɗa handle ɗin ƙofar, janye hannunsa yay yana mayar da idanunsa a hankali ya rufe.
Arjun ne da Ya Falta sai Moon a bayansu tana shigowa Deen ya shigo sai Oga Muhammad Jalal Kabeer bobo shida Jalilerh.
Zama suke A hankali Moon tace "Till now yana bacci sannu Sheikh, yanzu dai no more damuwa".
Arjun yace "Wlh idanunsa biyu haka yake ai" Bobo yace "Uhm Gulma yake da matarsa ƙilan" mintsininsa Jalilerh tayi ya riƙe hannunta yana bata kiss ba kunya.
Sheikh yana jinsu yana ta laluban kalmar da zai faɗa ne, jin Arjun na taɓa sa yasa ya buɗe ido yana ya mutsa fuska..
Gaba ɗaya suka haɗa wajan faɗin _"Congratulations from, RELESED FROM JAIL"_ kamar zai kuka sbd haushin da yaji na katse masa hanzari da sukai bai damu da Ya Falta dake wajan ba ya sassauta Muryarsa yace
"Barakallahu fiikuu, Shukkran, but kun shiga rayuwata".
Deen yace "Hhh naka wasa ne, idan zakai soyayyyar ka miye namu, tun kafin kayi mukai wanda zan ɗagawa ƙafa cewa ya fini iya soyayyya _ABU_MALEEK_ "
Bobo yay dry yace "Kai wannan ai makauniya ta gama dashi bashi da kunya sam" Murmushi Deen yay yace "Kasan garin da suka je ashe akwai wasu halittu kamar huro masu shan jini akai Sa'a ɗaya ya ciji makauniyar tasa, shi kuma Allah ya tsare sa shine daya koma masarauta ya killace ta ba tare da kowa ya sani ba yake bata jininsa take sha har taji sauƙi" Jalilerh ta zare ido tace "Mayya kawai ya aura wannan" Deen yace "Kaji ƴar iya ba kiji ance cizonta akai"
Jalal yace "Abin ya fara zuwa da raini kuma da babban likitan ƙashi kake mgn bada Lawyer ba"
Sheikh dai yana jinsu amma idanunsa na manne akan Fannah wacce ta fara mutsawa sbd surutun da ake, tashi tayi tana kwaɓe fuska idanunta ya sauka akan na Sheikh da sauri tai ƙasa da idanunta sbd kwarjininsa da yay mata ga wata kunyarsa daya kamata.
Moon tace "End of discussion abar dai Sheikh ya huta yaji ɗumin matarsa"
Murmushi Sheikh yay yace "Yawwa Queen, tattara su" Miƙewa sukai gaba ɗaya suna masa addu'a ya amsa da Ameen yaywa Moon gdy.
Fita sukai hadda Arjun da Ya Falta ganin hakan yasa Fannah ta miƙe yana ɗan motsa bakinta so take ta tambayesa jikinsa amma ta gagara ganin yana niyyar tashi yasa tai saurin yin bathroom.
Ba'a Sallami Sheikh a ranar ba sai washegari bai ƙara sanya Fannah idanunsa ba sbd kullum Granny da Ya Falta suna wajan Mama kolo da Yakura da Yagana sun koma.
Yana zaune a Parlonsa sanye da wani tattausan farin voyal mai manyan zane wannan karan ko singlet bai sanya ba, ana kallon ƙwantaccen gashin ƙirjinsa da tsinin brest ɗinsa, yana tunanin rayuwa tunanin Abbansa Barrister ya gama cika masa zcy bai taɓa tunanin haka al'amarin yake ba, wato ashe duk rashin kulawar da yake ƙin basa sbd yasan bashi ya haifesa ba, an kashe masa kakanni haka an nakasta rayuwarsa, daga ƙarshe an kashe masa Kawonsa Uncle Sham.
Ajjiyar zuciya ya sauke tunaninta ya faɗu masa miƙewa yay bayan ya gama shan lemon power horse energy, cikin nutsuwa yake taka ƙafafuwansa cike da kuzari a haka ya ƙara so babban Parlo yana zuwa tana tashi sosai kwana biyun nan take jin kunyarsa musamman idan ta tuna abinda tai masa a kwanakin baya, Granny tana ganin ta rangaɗa guɗa tace "Ga Imamu Ga Imamu,ma sha Allah Tubarkallah Ubanka sak babu abinda ya bambanta ka dashi"
Lumshe idanunsa yay yana kallon hanyar part ɗinta da tabi, sosa kai yay yace "Granny bari na tambayeta ko taga laptop ɗita" kallonsa tayi tace "Wa kuma zaka tambaya" ƙasa yay da idanunsa yana juyawa ba tare da yace komai ba, ƙasa Granny tai da muryarta tana faɗin. "Yau naga ɓatan nono a ƙirjin budurwa, wai wayo zai min, to Fisabilillahi zai hanashi keɓewa da matarsa ne? Ai sai Allah ya tsine min ko Amina?"
Anut Amina ta saki Murmushi tace "Haka ne kam, Allah dama ɗaukan ta yay zuwa wata ƙasar suka huta".
Mami tana jin Wayar tayi ƙara ta manna a kunne tace "Kayi min al'ƙawarin aiki me kyau amma tun ba'a je ko ina ba suna tare da junansu" bokan ya saka dry yana faɗin "Kinyi kuskure ai, tunda kika sanya maganin kuma ya tashi a banza baki kwanta da yaron ba, gashi kin bari wani ya ganku dan haka aiki ya lalace"
Dafe kai Mami tayi tace "Mene abunyi yanzu?" Bokan yace "To Salammiyya har yanzu ruɗun Duniyar bai gama sakinki ba ne?" Girgiza kai tayi tace "Kawai ka faɗa min sai wasa kake da hankali na" tsawa ya buga mata yace "Kaga wacce bata da rabon duniya bare na lahira daman can kuɗin ki nake ci, amma asiri bazai tasiri jikin Fannah bare Sheikh, kullum tana shan yawonsa bai ɗauke da tasbihi ga kariyar da suke samu daga wajan wasu daban, dan haka kiyi ta kanki nai nawa".
Yana faɗin hakan ya kashe wayar kuka Mami tasa tana haɗa ido da Bahaiyya ta zabga mata harara tana faɗin "Wlh Mami kin cuci ne Allah kuma zai saka min kin samar dani ta gurɓatacciyar hanya"
A hankali Sheikh ya murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗin Fannah, tana tsaye gaban mirror daga ita ƙaramin towel, frm head to toe ya fara Kallonta yana ganin yadda ta zama babbar mace ga cikinta yay girma yay mata kyau sosai fatar jikinta sai Shinny take, ko'ina na jikinta a murje gwanin sha'awa gashinta yana ɗigar da ruwa ya sauka har baya ya manne da fatar bayanta ga wani sihirtaccen ƙamshi na turaren AL'AJABU dake fita a jikinta, bai san yaya akai ba sai tsintar kansa da yay a bayanta ya zura hannayensa a cikin aljihun wando yana jefanta da wani irin kallo.
Ta cikin mirror'n ta hangosa gabanta ya