Showing 123001 words to 126000 words out of 130248 words
jikinta na rawa alamar saƙonsa yana kai mata Kafin ya zame kansa ya durƙosa dai-dai cikinta ganin zai ɗaga rigar yasa tai saurin shafa kansa Kallonta bisa dole ta ɗauke idanunta ya ɗaga rigar a hankali ya manna bakinsa dai-dai cibiyar ta ya hura kaɗan kafin fara karato addu'ar daya saba, ya shafa a cikin sannan ya fara mata wasa da cibiya da sauri ta zame ta faɗa jikinsa ya rungome ta yana faɗin "Sabahul khair Zahraaah na" idanunta a rufe tace "how was your night?"
Kallonta yay yace
"Kike tambaya the night was good sbd ke na daɗe banyi bacci mai daɗi irin na jiya ba"
Pls Kurratul aini Kada ki rabu dani kinji ya fara yana ɗura kansa a shoulder ɗinta kamar ƙaramin yaro dry tai masa tace
"Da Zahraaah da abinda yake cikinta duk Mallakin ka ne"
ta ƙare tana dry sarai yasan tsokanarsa take kawai ya share tare da miƙar da ita ya nufi bed tace
"Bari na bawa Unborn child ɗina abinci" zamewa ta farayi tace "Haba dan Allah" Wayarsa ta ɗauki ƙara ganin sunan Arjun yasa yay picking a hankali tare da sata a handsfree cikin murna Arjun yace
"Buddy My Aliyah ta haifa min ƙyakƙyawan yaro mai kama dakai and kasan menene nama bashi sunan his name is Imam Mohd"
farin ciki ya faɗaɗa a fuskar Sheikh yace
"Ma sha Allah, congratulations Buddy, thank you Sai nazo ganin little Imam"
ya faɗa yana ƙara sakin Murmushi kafin ya miƙe ya fasa abinda yay niyya yace
"Ki shirya muje"
sosai tai farin ciki daman ta daɗe rabonta da fita sai zuwa asibiti. daman a shirye take perfume ta fesa ta sanya hijab ɗinta a Parlo ta samesa sanye da wata haɗaɗɗiyar shadda wagambari da huma jaddara, yay kyau sai walwali yake kamar ango.
Yana ganinta yace
"Sai mun dawo" Granny tace
"Allah dai ya tsine idon maƙiya"
Anut Amina tace "Ya tsone dai ko Granny" Granny tace "To meye ne bambancin? Ba gwamma ya tsine ba daya tsone ida ya tsone idan ya tashi daga aiki ba, ai kinga addu'a ta tazo da sauƙi ko dan Allah?"
Anut Amina tace "haka ne kam"
Tashin hankali ya bayyana a fuskar Mami idanunta akan Lubna wacce take halin mutuwa babu bakin magana, tace "Na shiga uku dan Allah Lubna tashi ki faɗa masu inda dukiyata take, kada ki mutu ki barni babu ko sisi"
Wacce take ɗakin tace "Ai sai dai kiyi hqr domin ko sisi Babu a nan duk kuɗin da suke hannunta mun ƙarar wajan yi mata magani"
Mami ta ɗura hannu akai ta fasa ihu tana faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wai Meke damunta haka ne na shiga uku ni Saudat dan Allah ki rufamin asiri, ko rabi daga cikin dukiyata ne ki ban"
Matar mai suna Sailuba tace "Ta kamo da ciwon ɓarin jiki, bayan dawowarta daga wani gari Nima ban san shi ba, mgnar kuɗi kuma ko biyar wannan ba zaki samu ba da zaki taimaka mana ma so muke"
Mami bata tsaya jin wani abu ta fita tana faɗin "kin cuceni Lubna, Allah ya isa ban yafe ba, da nabi shawarar Fariha da babu abinda ya sameni, babu miji babu sweet Imam babu dukiyata innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Tana tafe tana faɗa bata san Lokacin da tazo titi ba sai ƙarar mota da taji kafin tai wani yunƙuri motar tai gaba da ita.
Sheikh yabi jaririn da kallo cike da so da ƙauna, yana fatan shima yaga nasa haka, sun daɗe sosai kafin suyiwa su Arjun sallama Fannah ji tayi kamar ta ɗauke jaririn musamman da taji ance sunan mijinta aka saka, daga nan suka huce ganin Dr ya tabbatar da lafiyar Babyn a nan kuma yaga Twins sai kawai yaja bakinsa yay Shiru yaga abinda hali zaiyi zuwa Lokacin haihuwarta.
Yana driving yana jifa mata Murmushi suna shira sama², hannunta riƙe cikin nasa tace "Yanzu idan na haifi Namiji wanne suna zaka sanya?"
Wani lafiyayyan murmushi yay sbd daɗin da yaji yace "Ina fatan ace baby girl ce" kwaɓe fuska tayi tace "Ni aboki nake so na samawa Mijina mai tayaka aiki" Kallonta yay sosai yace "Ke baki son Taimakon ne?" Girgiza kai tayi tace "Ina so mana, amma nafi buƙatar naka" shafa sumar kansa yayi kafin yace "Uhm, da mace da namiji duk ɗaya, duk wanda Allah ya bani ina so, idan namiji na samu in sha zai samu sunan SHAMSUDEEN sunan Uncle Sham"
Fannah tace "Wow Anut Amina zatai farin ciki sosai wlh, idan macace fa?" Jimm Yay kafin yace "Ayshatul-humaira" idanu ta buɗe sosai tace "Wow i like the name, Allah ya kawota cikin Aminci"
Yana tsayawa a danja yace "Na sakar maki Ameen" Malt ta gani mai sanyi ana tallah ta kallesa sosai ya gane amma yay masa maza tace "Nurul hayat" buɗe ido yay yace "Baza ki sha ba, abun kan titi" marai-raice fuska tayi tace "pls mana" ta faɗa tana zura hannunta a aljihunsa yace "Ko biyar ba zaki gani ba, rabon da naga kuɗi da idona na manta" da sauri ta buɗe hand-bag ɗinta tunawa da kuɗi ciki ta zaro ɗari biyar ta baya mai Malt ɗin ya bata ɗaya" dai-dai nan danja ta masu hannu.
Ganin yadda take juya abun yasa "Gulma ta me ciki" dry tayi tace "Allah kuma naji ban son sha fa" wayarsa na ƙara yace "Na You sabi" yana ɗaga kiran yaji Muryar Bahaiyya na kuka tana faɗin "Ya Sheikh Mami" shiru yay kafin yace "what wrong with her" shiru yay sai kuma yace "Ok shiru to"
Juyawa motar yay ya nufi hospital Fannah da ido kawai take kallonsa har suka shiga hospital ɗin, hannunta riƙe cikin nasa suka isa emergency, da sauri Fareeq da Bahaiyya suka faɗa jikin Sheikh suna kuka, bai ya mgni sai jijjagasu kawai sa yay, kafin ya zare jikinsa ya nufi room ɗin da take yana shiga ya rufe idanunsa sbd ganin Mami kwance a saman bed a naɗe mata gaba ɗaya kanta da fuskarta, ga hannunta ɗaya a gutsire an naɗe da bandeji, saurin juya yay faɗin "Subuhanallah!"
Fannah zata shiga yay saurin riƙe ta suka nufi office Dr yace "Gsky ta samu matsala a ƙwaƙwalwarta wanda ya shafi tunaninta, sannan hannunta ya fita sakamakon accident data samu, wanda hakan yake shirin taɓa lafiyar cikinta"
Ajjiyar zuciya Sheikh ya sauke yace "Allah ya bata lfy kayi komai ka nema mata nurse mai kula da ita"
Yana faɗin haka ya miƙe Buhaiyya tace zata zauna wajan Mami, uwa uwace dan haka Sheikh ya rabo da ita.
Lokacin da labari ya samu su Granny hannu ta shiga tafawa kafin ta fara shassheƙar kuka tana sharce majina tace "Allah sarki Saudala Allah ya jiƙanki yay maki rahama"
Da mmki Sheikh ya kalleta baice komai ba Anut Amina tace "bafa mutuwa tayi ba" Granny tace "A'a wlh ba ruwana, meye bambanci hannufa ya fita fittt babu na danna kumfuta"
Da daddare Sheikh ya gama shirin kwanciya wayarsa tayi ƙara ganin baƙuwar number kawai ya share, ƙara kira akai Fannah dake tsaye ta ɗauka tare da manna masa a kunne, daga can ɓangaren aka sauke ajjiyar zcy kafin ace "Assalamu alaika, Ya Sheikh Aslam ke mgn" Shiru Sheikh yay yana son tuna inda yasan sunan can kuma yace "Ohh Ykk?" Aslam yana kallon Ammi wacce tai shiru tana kallonsa yace "Allahamdulillah, fatan kaima Lfy kake" Sheikh ysa hannu ya jawo Fannah jikinsa yana zare rigar jikinta tare da tura hannunsa cikin ƙirjinta, yace "In sha Allah" Aslam yace "Alfarma nake nema dan Allah" Sheikh yace "Uhm" jin hakan yasa Aslam cewa "Ammina keson gaisawa dakai, ta damu sosai kullum cikin mgnarka take"
Miƙewa yay zaune yace "Ok to" da sauri Ammi ta amshi wayar idanunta na kawo ƙwalla bakinta har rawa yake wajan faɗin "Farin ciki na!"
Da saurin Sheikh ya runtsa idanunsa yana jin kansa na sarawa shiru sukai kowa na jin sautin fitar numfashin ɗan uwansa, kafin cikin ƙasa da murya yace "Am...Am..Ammi" da sauri Ammi tana kallon Aditya tace "Na'am Farin t na, kullum ina jin wa'azin ka wanda yake samun farin ciki da nutsuwa ,dalilin hakan yasa nake ce maka farin ciki na"
Kallon Fannah yay wacce bacci ya fara ɗauke ta sbd abinda yake mata yace "Ngd Sosai Ammi Allah ya saka da alkairi" cike da farin ciki tace "A kullum addu'a nake maka kamar ɗan dana Haifa aciki na, Allah ya tsarekae ya kiyaye ka daga sharrin mutum da aljan ya ɗura ka bisa maƙiyan ka, ya kiyaye ka da kiyayewarsa" wani farin ciki da nutsuwa ya kama Sheikh wanda bai taɓa samun irinsa ba, sun daɗe suna magana hadda su Aditya da Anushka.
Suna gama wayar ya ajjiye sai soyayyar Amminsa ta dawo masa sabuwa yay rashinta sosai, juyar da Fannah yay yace "Wake Up Madam, tashi kiyi aikin lada"
Kwanci tashi ranar suna yazo aka sawa sunan ɗan Arjun Imam, akwatina wajan biyar Sheikh yay tare da abin yaka Saniyya da rago, Fannah ma ba'a barta a baya ba ta haɗawa Aliyah irin turarensu na kanuri.
After 2mnt
Cikin Fannah ya tsofa sosai, Sheikh ya dainae dadewa wajan aiki, har kuma lokacin Mami bata farka daga duguwar suman da tayi ba, itama cikinta ya shiga watan haihuwa sbd kusan wata guda ne dana Fannah.
Fannah na zaune ta miƙar da ƙafarta wacce ta kumbura sosai, Sheikh na matsa mata duk ta Marai-raice masa sai kuke kuke take ita cikin ya dameta, Kallonta yay yace "Mai ciki gani nan tafe" pillow ta ɗauka ta cilla masa yay saurin cafewa kuka ta saki tana faɗin "Allah daga wannan bazan sake ba"
Dry yay sosai tsayawa tayi tana ganin yadda yay mata kyau zati da cikar haibarsa sun ƙara fitowa sosai ya zama babban mutum, musamman yanzu daya ƙara zama Sheikh ɗin gaske, ƙasumbarsa ta ƙara yawa sai sheƙi take.
Yace "Da ganki za kizo inda nake kina faɗin pls Nurul hayat, just like Yadda kikai baya pls Malamina ka soni kamar yadda nake sonka" kunya ta kamata ta rasa yadda zatai sai kawai ta fasa ihu tare dasa hannu ta hau dukansa, sai da tayiwa dan kanta Sannan ya lafe jikinsa tana sakin kukan shagwaɓa, rungome ta yay yana faɗin "It's Maman twins" ware ido tayi tace "Twins?" Ya ɗaga mata kira yace "haka nake ji a jikina, kin san mijin naki kwarzo ne da kin sauke zaki daɗa ɗauka" wayarta ta ɗauki ƙara sunan Ya Falta ya bayyana ta ɗauka Ya Falta ta saki kuka tana faɗin "Fannah Mama babu Lfy dan Allah kizo kada ta mutu" da sauri Fannah ta kashe kiran tana sakin kuka, nan da nan Sheikh ya siya masu online ticket ƙarfe ɗaya na rana jirginsu ya ɗaga zuwa Barno.
Suna zuwa suka samu Mama kolo tana bacci ansa mata ruwa sai Yakura wacce bata daɗe da zuwa ba, Sheikh na tsaye bayan sun gaisa da jama'ar wajan, kamar daga sama su kaga mace ta shigo a firgice sai twins na biye da ita, Yakura ta miƙe tsaye tana faɗin "Indoo" da sauri wacce aka kira da Indoo ta faɗa jikin Yakura tana faɗin "Yakura i want my child, na shiga uku Yakura i want my child to come back to me" ta faɗa tana sakin kuka...
NIMCYLUV ✍🏾
22/10/2021, 10:39 - 🤔🤔: Second To The Last Page
93-94
Hankali tashe Yakura ta shiga faɗin "Ke Indoo mene haka, mene ya faru daza ki shigo kamar an kuroki?" Kuka wacce aka kira da Indoo ta saki tana ƙara riƙe Yakura tana faɗin "Yakura an cuceni, an cuci rayuwar ɗana data Mijina, an sanya min tsanar abinda na haifa daga ƙarshe an mantar dani cewa ina da wani ɗa a duniya bayan su Aditya, me suke nema dani ne? What i have done to them?" Murmushi kawai Yakura tayi tana kallon Sheikh wanda idanunsa ke ƙasa yana duba system ɗinsa, Fannah idanunta akan Indoo kana ta juya ta kalli Mijinta sbd zallar kamar da taga sun yi, Su Ya Falta da Yagana su kawai suke kallo.
Sheikh a jikinsa yaji ana kallon sa jin hakan yasa ya kashe wayarsa a ɗan sanyaye ya kalli Fannah ba tare daya kalli saitin matar da take kuka ba, bakinsa yake ta juyawa yana son yace wani abu amma ya gagara, sai kawai ya fara ɗaga ƙafafuwansa ya suma tafiya zuwa waje, Fannah ce ta Miƙe tana satar kallon jama'ar ɗakin taga babu wanda yake Kallonta sai kawai tabi bayansa tana ɗaga ƙafa da ƙyar sbd tsofan da cikinta yay, yana tafiya a hankali yaji ana binsa yanayin tafiyarta kawai yaji yasan ita ce, juyawa yana sauke kallonsa a kanta kafin ya juyawa gaba ɗaya gareta hannunsa saman shoulder ɗinta yace "Ke ba kiji nauyin jikinki ne?"
Turo baki tayi tana marai-raice fuska tace "To ina zaka kuma?" Cikin idanunta ya kalla kafin yaja numfashi yace "To na mamajo ne da zan zauna cikin mata?" Girgiza kai tayi tace "Amma Nurul hayat naga kuna kama sosai da wannan matar fa"
Juya fararan idanunsa yay sosai a kanta kamar bazai mgn ba sai kuma yace "Wa?" Tace "Wacce ta shigo yanzu mana, Allah Nurul kamar ko har tsoro ta ban" yana sakin Murmushi tare da matsa shoulder ɗinta yace "kada ki firgita min twins dake shirin zuwa duniya Madam" hannu tasa ta shafa farar fuskarsa tare da jan hancinsa tace "Uhm to ina zaka" bakinsa ya ɗura anata hancin ya ciza kaɗan tana lumshe idanunta yace
"Waje mana"
maƙalesa tayi tace "Nima zani"
"uhm" kawai yace yana sukutar ta cak yana mata dry har bakin ƙofar shiga parlon nasu ya direta yana bata side hug yana sumbatar forehead ɗinta yace
"I'll be back Kurratul aini" Yana faɗin hakan ya juya cike da nutsuwa da Kamala yana tafe yana ɗan buɗawa a haka yay waje.
Fannah hawayen shagwaɓa na zubu mata tai cikin Parlon da turtsetsen cikinta, tana shiga ta nemi waje ta zauna tana ƙara satar kallon wacce aka kira da Indoo domin suma tunda suka tasu basu taɓa ganinta ba.
Yakura tace
"Yanzu Indoo kuma sai kizo duk a firgice kamar wacce aka kuro, yaushe rabon da mugana da juna kuma da kika tashi zuwa fisabilillahi sai kiyi mana haka, komai nutsuwa yake so"
tana share hawaye tace "Haba Yakura, idan banyi kuka ba yaya zanyi? Na yarda da ɗan dana Haifa tun yana zanin goyo, ban san cinsa shansa ba, balle tarbiyyar sa ba, kina tunanin haƙƙin Allah bazai kamani ba da wufintar da kyautar da yaymin ba, ƴar ƴar amanace a garemu dole Allah zai tambaye mu su ranar lahira, yaya muka kula da tarbiyyar su?"
Jinjina kai Yakura tayi tace
"haka ne kina da gsky, amma ki fara nutsuwa nai mki bayani ƙilan nasan abinda baki sani ba"
shiru tayi sai a lokacin ta ɗaga idanu ta kalli su Ya Falta da Yagana kana ta juyo da Kallonta zuwa ga Fannah, ƙuri tai mata da ido kana ta maida kallonta zuwa ga cikinta, a hankali ta sakar mata tattausan Murmushi, Fannah ta saukar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta tace.
"Nda wattu (Ina kwana)"
Kallonta ta ƙarayi still idanunta na kan cikin Fannah tace
"K3lewa silai (lafiya lou)"
Fannah bata ƙara magana ba sbd kunyar matar data keji, amma a ƙasan zcyarta tambayoyi ne masu yawa, me yasa take kama da Sheikh ɗinta? Wanne yaro take iƙirarin ta tafi ta bari har haka? Then ita ɗin Wacece daga ina take, da sauri ta ware idanunta musamman da ƙwaƙwalwarta ta shiga tariyo mata wasu bayanai da akai lokacin zaman Court Sheikh, kallon matar tayi idan harta haɗa da zan can Court ta haɗa da na wannan matar yanzu waje guda hakan na tabbatar mata cewa wannan Mahaifiyar Nurul hayat ɗinta ce, wani farin ciki mara misaltuwa ya gama Fannah, kullum tana kula da yanayin Sheikh yana da damuwa kawai dannewa yake sbd bai son nuna mata damuwarsa kuma bata huce rashin Iyayensa, Al-hakkamu kenan, gagara misali sai gashi Ubangiji ya dawo masa da Iyayensa a lokacin da basuyi zato ba kuma ba suyi tsammani ba.
Shiru tayi kawai tana ƙara satar kallon kamar kafin Yakura tace
"Nda amfatoye?(Ya mutanan gida)" murmushin ƙarfin hali Indoo tayi tana kallon su Anushka da suka lafe a jikinta sbd babu wanda suka sani tace
"Aslam da Ur Excellence suna waje"
haɓa Yakura ta riƙe tace "To maza shigo dasu" kafin ta kalli Fannah tace "Kira min Imam yanzu" dai-dai nan Mama kolo ta fito da bedroom tana ware idanun ganin Indoo wacce ba tayi tunanin gani ba.
Sosai sukai farin cikin ganin juna kafin su zauna suna hira ta yaushe gamo Indoo yi kawai take amma hankalinta gaba ɗaya yana kan Fannah su take tace Wacece amma ta gagara tambaya.
Sheikh a hankali yake tafiya bawai haka kawai ya fito ba, tunda matar ta shigo ya kasa samun nutsuwa zcyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi yana jin kunanta har ƙasan zucyarsa, hasali ma ji yake kamar yasan muryarta amma at where shine abinda bai sani ba, a daddafe ya isa waje inda ya ajjiye mota wacce ya samu lokacin da suka iso Barno.
Aslam dake cikin mota a gaba kamar ance ya ɗaga kai idanunsa ya sauka akan Sheikh dake fitowa yana dafe da kansa..
Da sauri ya ɓalle murfin motar ya fito fuskarsa cike da farin ciki ya nufi inda Sheikh yake tsaye yace
"Ya Sheikh kai ne da gaske? Gsky Am happy to see you, banyi tunanin ƙara ganinta soon ba"
Murmushin dole Sheikh ya ƙaƙaro yana kallon Sheikh, Governor Deedat Balarabe yana kishin giɗe a bayan motar hannunsa riƙe da jaridar darly trust ta yau yana dubawa yaji Wayarsa tai ƙara ganin sunan Maman twins yasa ya ɗaga kiran yana sakin lallausan murmushi daga can ɓangaren muryarta a ɗan maƙale tace
"Ur Excellence ka shigo" Jinjina kai yay yace
"To rigimammiyya ta"
dry tai kaɗan kana ta kashe kiran, daga yafiyar tasa ta sirri ce yasa ko securities babu iya suke nan.
Yana fitowa idanunsa ya sauka kan Sheikh dake kallon Aslam yana ɗan faɗaɗa fuskarsa, jin idanu a jikinsa yasa ya ɗaga kansa sukai idanu huɗu da Deedat wanda yake tsaye kamar an dasa shi, kallon kallo aka shigayi kowa yana hango kamar kowannen su a fuskar ɗan uwansa, Aslam yace
"Papi, My lovely Dad kenan"
Deedat Balarabe shine ya