Showing 102001 words to 105000 words out of 130248 words

Chapter 35 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5980

part ɗinta, Barrister dai da Arjun suna zaune Anut Amina zuwa lokacin ajjiyar zuciya kawai take saukewa, idan ta rasa mijinta ina zata ita da ba'a nan garin take ba? Ina zata kai kanta a wajan wa zata zauna? Gaba ɗaya ta kasa kwantar da hankalinta, Granny sai fatar Majina take tace "Ta badai shkknan? Yaro da ko sauro bai taɓa kashewa ba shine za'a nema a rasa fisabilillahi? Duniya zaki damu ni Faɗimatu wanne kalar gantalallun mutane nake zaune dasu ne? Babu wanda ya damu da halin da muke ciki sai a samu gaba aita zare mana ido dan Allah, ungo number kira min jami'an tsaro yanzun nan" ta faɗa tana miƙawa Arjun wayarta tace "Maza Ranjun ni ba'a sallamawa dniya ni ba, idan ba hedikwata ne sai naje yanzun nan, ah to uban me ze saman tunda zcyta tsaf take ko ada sai dai a cucan ba dai na cuci wani ba, zamani ne dai ya sauya ni" kafin Arjun yay wani abu Sheikh ya ƙarasu wajan yana ɗan dai-dai ta fuskarsa, cikin son kawar da damuwar ransa yace "Anut Amina kije ki kwanta" kallonsa tayi da kumburarrun idanunta tace "Haba Sheikh tayaya kake tunanin zan iya runtsawa ban san halin da mijina yake ciki ba?" Gyara tsaiwa yay kana a hankali cikin ƙasa yace "Just pray, in sha bazan dawo gida ba sai dashi" kafin tai mgn wayar Sheikh ta sake ringing, kallo guda yaywa wayar yaji gabansa ya faɗi koda bai saved number Uncle Sham ba amma yana haddace da ita a qwaqwalwarsa, juyawa yay tare da nufar part ɗinsa yana kiran Arjun da hannu ganin haka yasa Arjun miƙewa yabi bayan Sheikh, daga can ɓangaren mai kiran ya sauke numfashi jin an ɗaga wayar yace "Assalamu alaikum fatan muna magana da Deedat Balarabe?" Shiru Sheikh yay yana maimaita sunan kamar yasan sunan kamar kuma mai sunan ya sani, samun kansa yay da faɗin "Wasalamu alaika Yes! I I'm" ya faɗa yana tsayawa gaban mirror Arjun kuma ya rufe ƙofar ya tsaya yana kallon Sheikh, Mutumin yace "Ma sha Allah! Kana magana da hukumar bincike ta fararan kaya na nan garin Barno" Gaban Sheikh ya faɗi kasa mgn yay sai "Uhm" kawai da yace Mutumin da yace "An samu Accident ne, wanda ɗaya daga cikin mutanan da suka rasa ransu a jikinsa muka samu layin da zamu kiraka fatan zaka halarci asibiti domin bincikar mamatan cikin gaggawa" .
Saurin Zama Sheikh yay wani gumi ya fara keto masa duk da sanyin a.c dake cikin ɗakin nasa, fuskarsa ya kifa saman tafin hannunsa ya shiga sauke ajjiyar zuciya da sauri², nan take kuma jijiyoyin kansa sukai raɗa raɗa saman goshinsa, kasa mutsawa yay sbd rawar da jikinsa yake shikenan sauran jigon nasa ya tafi a fili ya shiga faɗin _"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, La'ilaha illah anta Suhubanaka inni kuntuu minnal zaluminn"_ sai kuma ya saki wayar kasa tare da bin wayar suka zube saman carpet, Da sauri Arjun ya ƙarasu inda yake hankali tashe yace "Buddy Meke faruwa? Wane ya kira ka?" Kasa mgn Sheikh yay sbd abinda ya tsaya masa a maƙoshinsa ganin hakan yasa Arjun ya ruɗe tashin hankalinsa ya ƙara nunkuwa akan na da, "Dan Allah ka gayamin lafiya? Mene ya faru kai da waye? Wane kuma ya kiraka" Miƙewa Sheikh yay tare da shiga bathroom bai daɗe ba ya fito fuskarsa na zubda ruwa, kallon Arjun yay yace "Duba mana online ticket na zuwa Barno a cikin daran nan" da mmki Arjun yace "Amma tafiya cikin daran nan Meke faruwa ne? Ga tashin hankali nan duk ya bai yana a fuskar ka Sheikh" Sheikh na zura Light blue ɗin shaddar sa yace "I don't know how to explain you, Uncle Sham sunyi Accident" da ƙarfi Arjun yace "What Uncle Sham? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" da sauri ya kunna net akwai ticket amma sai na biyar ɗin asuba, Sheikh yace "kasai guda Uku" Sheikh yace ukun ne kawai amma shi kansa bai san waye cikon na ukun ba, Arjun waya yaywa Aliyah ya gaya mata basai dawo ba kana ya kira Umma, Sheikh kasa fita yay sbd Bai son haɗa ido da Anut Amina da Huda tausayinsu ya gama cika masa zcy, yasan shi abin tausayi ne then ba komai zai san cewa yafi shiga tashin hankali ba, har zuwa Asuba bai faɗawa Arjun Uncle Sham ya rasu ba, haka kuma kwana yay akan ladduma idanunsa har kumbura sukai.
Tun ƙarfe huɗu ya gama shiryawa haka Arjun Anut Amina take ƙyar ta bar Parlon ta nufi Part ɗin Granny, a hankali Sheikh ya tura ƙofar Library room ɗin bayan ya buɗe da key, tana kwance saman kujerar daya kwantar da ita, tsayawa yay a kanta yaga yadda take sauke numfashi da ƙyar sai ajjiyar zuciya take saukewa da alama taci kuka ta ƙoshi, slowly ya ɗago ta gaba ɗaya zuwa jikinsa, ya riƙe ta sosai, ba kowa a Parlon hakan yasa ya shige da ita zuwa part ɗinta, yana zuwa ya nufi bathroom da ita, ruwa mai zafi ya haɗa yana jin yadda take ƙara maƙale masa, a haka ya ware Laffayar tass ba tare daya cire sauran kayan ba ya sanyata cikin jucuzzi turo baki tana kwaɓe masa fuska sai kuma ta buɗe idanunta tana kallon Sheikh tai saurin ɗauke kanta dan bata ma son ta sake ganin mummunar fuskarsa, shima bai damu daya kalleta ba, da sauri ya juya sbd ƙirjinta guda ɗaya da yay tsalle ya fito yana zuwa bakin ƙofa yace "Ki shirya zamu Barno yanzu" da zuwa lokacin ya gama samun impormation cewa hadda su Baba Baa'na, jiri har wani diɓan sa yake, yana fita ya samu Arjun a Parlo sai kuma ga Barrister shima ya fito a shirya ashe shima yasai ticket ɗin tafiyar shida Fannah kowa fuskarsa babu annuri, Sheikh tasbihi kawai yake dan kansa ya kusa kuncewa, part ɗin Granny ya nufa yana zuwa tai saurin faɗin "Imamu akwai abinda kake ɓoyewa, nifa ba mutuniyar banza bace da zaku mai dani wata bi ta can" Kallonta kawai Sheikh yay kana ya kalli Anut Amina yace "Zamu Barno yanzu in sha Allah!" Da sauri ta kallesa tace "Me za kuyi a Barno Sheikh kuma at this hour? Dan Allah idan wani abu ya samu mijina ka faɗa min" Huda dake gefe tace "Ayyya Sheikh Daddy" wani tausayin yarinyar ya kama Sheikh ya sauke numfashi yace "akan Uncle Sham ne" jikin Anut Amina na rawa tace "Mene Uncle? Mene ya samesa kada ka gayamin wani mummunan abu a kansa" ya faɗa idanunta na kawo ruwa Miƙewa tsaye yay yace "Matsala suka samu da police amma Allahamdulillah komai ya daidaita In sha Allah, kici gaba dayi masa addu'a Allah ya kiyaye gaba yanzu addu'ar taki yafi buƙata" yana faɗin haka ya fita daga ɗakin baki Granny ta saki kafin saka salati tana tafa hannu "Muhammadur Rasulullah (S.A.W) shi Shansu meye haɗin sa da wasu Polis fisabilillahi?" Anut Amina sauke ajjiyar zcy tayi sam zcyarta bata yarda da mgnar Sheikh ba, bai taɓa yi mata ƙarya ba hakan yasa kawai ta amince da zan can dan bata son ƙarya ta Sheikh ɗin. Fannah a gaggauce ta shirya cikin wata lafiyayyiyar abaya mai kyau wacce ta kwanta a jikinta, tunda ta fito Sheikh yake Kallonta kana ya kalli Barrister yaga shima ita yake kallo haka nan ransa ya ɓaci, musamman da yaga yadda rigar ta kamata tai mata masifar kyau, ajjiyar zcy Barrister ya sauke kana ya haura upstairs domin ɗauko wayarsa, yana fita Sheikh ya miƙe ya makawa Fannah harara ita kuma ta murguɗa masa baki, bai damu da Arjun dake wajan ba ya shammace ta tare da ɗaga ta sama da sauri ta qanqamesa sbd tsoran da taji, Murmushi Arjun yay domin ya gama gane kishi ke damun Sheikh, tana shure² ya ƙarasa da ita ɗakin ta, tare da direta ya nufi wajan wrdrb ɗinta wani purple ɗin hijab ya ɗauko mata wanda zai sauka har ƙasan ta, fuskarsa ba walwala ya nufi inda take yana zuwa tace "Malam wai meye haɗi na dakai ne? Bazan saka hijab ɗin ba Bashi nai niyya ba" bai kulata ba ya jawota jikinsa tare da zame Vail ɗin kanta, lumshe idanunsa yay sbd ƙamshin sumar kanta daya daki hancinsa, a hankali ya tura hancinsa cikin sumar kanta yana jin yadda take mutsi zata gudu amma No way to run, sbd gama ɗaya ya riƙe ququnta da hannunsa, cikin nutsuwa ya fara fidda numfashi, yana shaƙar ƙamshin dake fita daga cikin gashin, kanta ya ɗaga fuskarsa daf da tata ya manna mata sumbata a jajayen laɓɓanta, da hancinta kana fatar wuyanta Murya can ƙasa a tsakiyar kunanta yace _"Sabahul khair Zahraaah! Mrng Jewel nah"_ ya faɗa yana jan fatar kunanta yana hura mata iska jikinta ne ya saki hakan yasa tai saurin rungomesa hijab ɗin ya saka mata, kana ya riƙe hannunta ya ɗura saman bakinsa yay kisses nasa, sai kuma ya maida hannun saitin zcyarsa yace "U belong to me Zahraaah, Only me kin gane ban taɓa nuna maki ɓacin rai na ba, wlh billahil Azim kika sake kika zauna kusa da Abba uhm" bai ƙarasa maganar ba yaja hannunta zuwa waje. Barrister ya kalli Arjun yace "A'a ina Son yay?" Arjun yace "Wai Anut Fatima yaje kira sbd part ɗinta ta koma tana kuka" kafin Barrister yay magana Sheikh ya ƙarasu Fannah na bayansa sai turo baki take gaba, Sallama sukaiwa su Granny kana suka ɗauki hanyar airport a cikin jirgi Barrister ya zauna kusa da Fannah da sauri ta miƙe taje kujerar dake farcing Sheikh ya zauna ganin haka ya rabu da ita, Sheikh yi yayi kamar bai san da ita a wajan ba. A haka suka ƙarasa Barno lokacin an gama shirya gawar su Uncle Sham a gidan su Fannah, domin tuni labari ya iske masu, tashin hankali ba'a saka masa rana Fannah kusan sumewa tayi lokacin da Tayi arba da gawar mahaifinta, cak Sheikh ya ɗauke ta daga wajan gaba ɗaya kana ya kira Yakura yayar Mama kolo wacce yaga ta fisu nutsuwa, yace ta kula da Fannah sbd Cikin dake jikinta, Yakura kallonsa kawai take sosai yay mata kama da wani ko wata amma ta kasa tunawa, yana tsaye akan Fannah da akaiwa allurar bacci tare da ɗaura mata ruwa wayar Yakura ta ɗauki ƙara tana dubawa ta ɗauka tace "Indoo kinji labarin abinda ya samemu ko? Yau munga jarrabawa ta Ubangiji sai addu'a kawai?" Bai tsaya jiran me za tace ba sbd bugun da zcyarsa take masa yay waje da sauri, yana zuwa ya samu har su Anut Amina sun ƙarasu domin ance a nan Za'ai jana'izar baki ɗaya, Anut Amina na ganin Sheikh ta nufesa da sauri ta riƙesa "Sheikh Mijina farin cikina, Duniya, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" sai kuma ta zube a jikinsa ba Numfashi, matan wajan suka riƙeta shi kuma ya ɗauki Huda ya bawa Ya Falta ita, wacce tunda yazo take mmkin ganinsa a wajan, gaba ɗaya unguwar ta cika da mutane, lokacin da Sheikh yaga gawar Uncle Sham kasa mutsawa yay abun mmki ko ɗigwan hawaye bai ba, a haka ya zauna ya dinga kwarara masa addu'a na samun rahamar Ubangiji. Lokacin da za'a saka Uncle Sham ya kabari rufe idanunsa yay da sauri kuma ya rungome Arjun dake kusa dashi yana sauke ajjiyar rungomesa Arjun yay yana shafa bayansa, dan yasan duk abinda Sheikh yake dauriya ce sai bayan abun zai zauna jinyar kansa da rashin kawon nasa. Wacce ake kira da Indoo duk yadda tasu ƙarasu a lokacin kasawa tayi sbd rashin lafiya. A nan kuma suka bar Fannah.


_40 days ago_
Bayan arba'in ɗin su Uncle Sham Fannah ta dawo gidan mijinta ba dan ranta yasu ba, Anut Amina itama tana gidan da zama gaba ɗaya rayuwar duk tai masu zafi. Sheikh na zaune bayan ya dawo daga Police station sbd binciken da ake akan motar Company sa, wacce ya tabbatar masu bashi da wata masaniyar komai, yana sanye da Armless sai 3 gauthier hannunsa riƙe da power horse yana sha, sai system da yake operating a hankali, rabin hankalinsa gaba ɗaya yana kan Fannah rabon daya ganta harya manta, ya azabto rashinta sosai. Ƙofar ɗakin aka buɗe tare da shigowa warin turarenta kawai yasan ita ce, dan haka ko ɗago kai bai ba cikin rangwaɗa ta ƙarasu tare da zama kusa dashi ta ajjiye masa wayarta, kallonsa yakai kan wayar yaga pictures ɗinsa shida Fannah suna rungome da junansu, harda vedio'n, ɗauke kai yay bai ce komai ba yaci gaba da abinda yake tace "Yau komai zai zo ƙarshe, ko dai ka amshi tayin da nai maka ko kuma na fallasa SIRRIN dake tsakaninka da matar Ubanka, daga ƙarshe ma cikin dake jikina zan ce naka ne" rufe system ɗin yay ya miƙe da sauri ta rungomesa cikin zafin nama yay cilli da ita tare da nuna ta da hannu yana faɗin "Ki shiga hankalinki, tayinki kuma akai kasuwa I'm not interested" dry tayi ta shiga zare cire hijab ɗin jikinta duguwar riga ce a jikinta ta yayyaga gaban rigar tasa hannu ta fito da ƙirjin ta ta baza gashin kanta, kwallon ta kawai yay yake kana ya kalli c.c tv Camera ya saki Murmushi, yace "zaki sanya kanki a halaka fa, don't kada ki aikata" kansa tayo gaba ɗaya sukai baya sbd bai tunanin hankan ba, wata gigitacciyyar ƙara Mami ta sanya tare da faɗin "Wayyoooo Barrister ka taimake ni wayyoooo Allah Sheikh ne" Barrister da Anut Amina da Granny da Fannah suka Miƙe da sauri sbd sosai sukaji Muryar Mami yadda take faɗin sunan Sheikh yasa gaba ɗaya suka ruga da gudu zuwa part ɗin Sheikh a tunaninsu wani abu ya samu Sheikh Imam hamdan Balarabe..










Ai weekend lfy🌚🌝


Contact to subscribe 08119237616




NIMCYLUV✍🏽
22/10/2021, 10:37 - 🤔🤔: About The Pregnancy
79-80






Da raguwar ƙarfinsa ya yi saurin zame jikinsa yana aikata mata da wani kallon tsana tare warning akan abinda tai masa, Su Granny suna zuwa suka tsaya cak domin abinda suka ganin yafi ƙarfin tunanin mai tunani duk wani mai cikakken hankali ba zai taɓa aminta da wannan Sabon yanayin ba, Musamman Anut da Granny domin Anut Amina juyawa tayi tana mmkin hali irin na Mami domin tun ba yau ba ta riga ta gama fahimtar matar da tsoran Allah sam, ƙaramin tunani da ƙwaƙwalwa gare ta,banda haka tayaya take ƙoƙarin tuzarta wanda duk duniya idan sun taro za'a samu fiye da rabi wanda zasu shaida halin Sheikh ba haka ba ne, Tayaya take ƙoƙarin cin zarafin wanda ya yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta? Shin ko dai akwai wata manufa ne wanda ya sanya tai masa? Ko kuma kawai kalar nata rashin ɗa'ar kenan, tsaki taja domin sai yanzu ne idanunta suke ƙara harshashu mata abinda ta gani. Harɗe hannu Barrister yay yana kallon ikon Allah wanda rabin kallonsa akan Sheikh ne yana son zcyarsa ta gasgata abinda idanuwansa suka gane masa a yanzu, domin bai damu da Mami ba he's knew exactly how is, Musamman ɓoyayyyun halayanta wanda suka bai yana ada ta hanyar binciken sirri da yayi. Granny haɓa ta riƙe tace "Na shiga uku Ni Faɗimatu meye wannan nake? Wacce kalar rashin daraja da ɗaya ce wannan? Saudala anya kina da hankali?" Kuka Mami tasa sakamakon jin Muryar Granny da tayi da sauri ta kalli Barrister suka haɗa ido tana ganin haka tai wajansa da sauri tana faɗin "Allahamdulillah! Allah Nagode maka, wlh Barrister Imam bashi da hankali, mai yasa tsoran Allan sa ya tsaya iya baki ba zcy ba, na shiga uku wai wacce kalar rana ce wannan nake gani,ace Ɗan mijina yana ƙoƙarin aikata zina dani, da naga wannan ranar gwamma naga ta mutuwa ta, Barrister dan Allah kayi hqr domin wannan ba shi ne karo na farko ba, ya cimma burinsa da buƙatarsa a baya, amma yanzu nayi ƙoƙarin kare kai na, daman Imam ya daɗe yana ƙwaɗayin jikina wlh ɗan iska..," ba ƙarasa faɗar haka ba Granny ta sauke mata wasu kyawawan maruka guda biyu a kuncinta tace "Ashe gantalewar taki harta huce tunanin duk wani gantalalle irinki? Tsabar giyar hauka na ɗibanki ki rasa wanda zaki laƙa bawa zam can banza da iska sai Imamu? Bin mata ki kaga yanayi ko menene? Wlh sai na kira maki police yanzun nan" Mami ko kallon Granny ba tayi ba ta riƙe Barrister tace "Believe me Barrister wlh yaronka bashi da gsky, ko ba'a kai na ba, Imam yana da good relationship between he and matarka Fannah, And cikin dake cikinta ma ina da tabbacin na Imam ne ba naka ba" wani jiri ne ya ɗebi Fannah zata faɗi Granny tai saurin riƙeta tana faɗin "Mugun nufinki da sharrin ki ya koma maki ka, Yarinyar dako kallo bata ishi Imamu shine kike jefansa da wannan gantalallan bakin naki" sai kuma ta fashe da kuka tana riƙe bakin zaninta, tare da face majina wayarta ta ɗauko ta fita waje tana faɗin "Wlh sai Allah ya saka mini, kaf zuri'a ta babu ɗan tasha dan haka kwanan siteshan ya wajaba a gareki shashasha, da ɗuwawo kamar dutse" Fannah kasa koda mutsi tayi idanunta akan Sheikh tana jin kanta na mugun sara mata, abin duniya yay mata zafi, shin da gske wannan cikin na Sheikh ne? Wata zyar tace mata "nasa ne mana, idan bashi ba waye ya taɓa kusantarki" jiri ne ya ɗebeta tayi baya zata faɗi Sheikh dake tsaye yana bin kowa da ido yay saurin riƙeta, Barrister kam ganin abun yake kamar a mafarki ya daɗe yana tunanin wasu abubuwa da yawa amma ya kasa fahimta, shin da gske ɗan cikinsa shike neman matansa? Ko Wannan dalilin ya sanya yaƙi yin Aure ne? Innalillahi wa'inna ilaihir, kallon Sheikh yay da yake riƙe da Fannah wacce gaba ɗaya tama rasa Meke faruwa da ita sbd ko ƙoƙarin zame jikinta ba tayi bata da wani kuzari sbd wani shork daya sameta, cikin jarumta da nutsuwa haɗi da kamewa Sheikh yaja Fannah zuwa saman bed ta zauna, lokacin ko iya buɗe idanunta ba ta son yi, bata ƙaunar Sheikh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login