Showing 27001 words to 30000 words out of 130248 words

Chapter 10 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5985

"Sannu Baba" yace "yawwa kiramin Faɗimatu" ajjiye zogalan tayi tare da shigewa cikin ɗakin su, a kwance ta samu Fannah tana sanye da wani farin lace mai kyau gashin kanta har wuyanta sai ƙamshi take ƙafafuwan ta har yanzu yana nan da jan lallen da baya barin fatarsu, idanunta a lumshe ta rungome pillow kunanta sanye da airpies tana sauraran tafsir wanda baya shigeta, kallo ɗaya Yana tayi mata ta ɗauke kai kafin tace "Kije Baba na kira" shiru Fannah tayi domin bata ta san me take cewa ba, cikin fushi Yana ta fisge wayar hannunta tace "Wlh kina wahalar da ganki a banza da wufi,wlh tallahi shima Mutumin nan bashi da aikin yi daya nace maki" Kallonta Fannah tayi kana ta ɗauke kanta wata light blue ɗin lafaya ta ɗauka kana ta ɗaura saman lace ɗin, cikin nutsuwa ta sanya flat shoe ta fito,a gaban iyayen nata ta zauna kamar ba zatai mgn ba sai kuma tace "Gani Baba" Kallonta Baba Baa'na yay yace "Sannu Faɗimatu, Allah yay maki albarka" kasa amsa masa tayi sai Mama kolo sa tace "Ameen" Baba Baa'na yace "maza jeki ana kiranki waje,biyayyar da kikai min kaɗai ta isa ki samu abinda kikeso a nan duniya da kuma lahira" tuni idanunta sun cika da hawaye domin harga Allah bata ƙaunar wannan mutumin ace mutum sa'an ubanta tsabar rashin tsoran Allah da kuma budurwar zuciyar da yake da ita yace zai auri ƴar cikinsa which can of selfish, bata iya ɗaga kai ta kalli mahaifin nata ba sbd zafi da raɗaɗin da zuciyarta take mata, runtsa idanunta tayi da ƙarfi ta shiga jan ajjiyar zuciya, sai da Mama kolo tace "kin bar Mutum a waje" gently ta miƙe tsaye tare dayin waje, a zaune ta samesa saman kujerar da aka kai masa, tsayawa tayi tare da ɗauke kai gefe guda, miƙewa tsaye yay yace "Haba Fatymerh babu ko gaisuwa??" Taɓe baki tayi tace "baka cancanci gaisuwar ba ai,kai fisabilillahi ko kunya bakajin ace ka auri ƴar cikinka" ta ƙare mgnar tana Jinjina kanta, kafin yay mgna wayarsa ya fara ringing, answering call ɗin yay,daga can ɓangaren Arjun yace "Abba ka dawo gida yanzu" da mmki Barrister yace "akan wane dalili mene ya faru Arjun" cikin damuwa Arjun yace "Abba! Sheikh missed bamu gansa ba" da ƙarfi Barrister yace "Sheikh!!" Calmly yay yace "kaga Arjun i knew you can handle it, ina abu very important so bazan iya dawowa ba" kasa mgn Arjun yay kawai ya kashe wayar, Fannah samun kanta tayi da kallon Barrister sbd sunan Sheikh da taji a ambata..
Arjun kasa komawa gida yay ga Granny harta fara kiransa a waya akan ina suka tsaya,ya gama zagaye amma ko alamar Sheikh bai gani ba,tashin hankalinsa guda Sheikh ba ƙafa ce dashi ba bare yace gida zai koma, rashin samun mafita yasa ya kira Abba, amma gashi yay burus da lamarin kamar bashi ne ya haifi ɗan a cikinsa ba, cikin ɓacin rai yaci gaba da driving motar... Sheikh na fita daga cikin ward ɗin kai tsaye can bayan Asibitin ya fara tafiya duk da cewa ba sanin kan Asibitin yay ba amma haka yaci gaba da tafiya sai da yace wajan mutuware inda yake da duhun jeji sosai sannan ya tsaya, lumshe idanunsa yay tare da fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakinsa, a hankali kuma ya ɗura kansa saman cinyarsa,sosai zuciyarsa take masa zafi,mai Arjun ya ɗauke sa? Bashi da hankali ko kuma bai son ciwon kansa ba ne? Abinda yay masa kyautatawa ne ko kuma cin zarafi? Da lafiyarsa da komai zai kawo shi ai masa wani medical check-up,ko dan yaga bashi da ƙafar da zai taka yabar masa Asibitin shiyasa ya zaɓi kawosa ba tare da yay shawara dashi ba? Yasan Arjun mai son sa da kuma kaunar sa ne,amma mene yasa yay masa haka? Ko da gaske gajiya yay dashi shine yasa yay masa wannan wulaƙancin,ji yay wani zazzafan zazzaɓi ya fara rufesa a hankali jikinsa ya ɗauki rawa tare da ɓari ya shiga haɗe fararan haƙoransa, iska mai sanyin yaji ta fara kaɗawa hakan yasa ya ƙara lumshe idanunsa yana jin zuciyarsa duk babu daɗi, dafa shoulders akai yanayin zafin hannunta yasa ya fahimci itace,kasa ɗagowa yay sbd jin kansa yake kamar zai rabe gida biyu, zagayawa tayi cikin nutsuwa kana ta durƙoshe dai-dai wajan ƙafafuwansa hannunta tasa ta ɗago kansa, wata sassanyar ajjiyar zuciya ya sauke da jajayen idanunsa ya shiga Kallonta idanunta ta janye sbd yanayin da tagansa ya ƙara tabbatar mata da cewa zuciyarsa sam babu daɗi,can ƙasa dai-dai kunnansa tace "Arjun..?" Kasa bata amsa yay sai jawota da yay kusa dashi ya ɗura kansa a saman wuyanta,shafa sumar kansa tayi tace "me yasa to?shi dole sai ya san abinda bashi da iko akai? Why Arjun yake maka haka?ina ɗaga masa ƙafa dalilinka amma baya fahimta, wlh idan akan ka ne zan iya yiwa kowa rashin kirki,babu wanda ya damu dakai sai dai kai ka damu da wani, what is this? Idan yana taƙamar yana taimaka ne ,sai ya basshi zan iya maka dukkan abinda yake maka" Girgiza mata kai yay tare da fashewa da kuka bakinsa har rawa yake ya shiga faɗin "No! Kada ki masa komai, Arjun he's my Best friend,Kada kiyi masa wani abu just let him go" ya ƙarasa mgnar yana rungome ta sosai a jikinsa ya shiga fesar da numfashi,abinda bai taɓa yi ba kenan a hankali ya ɗaga kansa tare da tallafo haɓarta slowly ya ɗura soft lips ɗinsa saman nata Muryarsa can ƙasa yace "Sorry!" Yana faɗin hakan ya datse bakinsa a cikin nata, lokacin da yay trying na kissing nata sai yaji kansa ya tsara da sauri ya zare bakinsa ya shiga faɗin dukkan addu'ar da yazo bakinsa, idanunsa na zubar da hawayen baƙin ciki yace "ki ɗauke ni, ki tafi dani Please Ai..rahh,go with me Airah hhh..






*SIRRIN MU na kuɗi ne, if you need my book just it's v #500 via👉🏾0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 ga ƴan Niger kuma sai suyi mgn ta wannan number 84506476*




NIMCYLUV✍🏾
20/10/2021, 20:44 - 🤔🤔: SUBSCRIBE MY YOUTUBE CHANNEL *Nimcyluv T.V*
https://youtube.com/channel/UClywbagpRx5qlVyOy0ZPPDA




########## 2️⃣3️⃣-2️⃣4️⃣ Ya ƙare maganar yana langwaɓar da kansa a saman wuyanta,ganin yadda duk ya shagwaɓe yasa ta saki murmushin jin daɗi domin farin ciki ƙarara ya bai yana a saman fuskarta.
Zame kansa tayi daga wuyanta tana faɗin "take it easy, nasan Arjun bai maka haka dan yaci zarafin ka ba right? Then kafi kowa sanin soyayyyar da Arjun yake maka all this ya nayi ne domin lafiyar ka" Lumshe idanunsa yay yana ɗan matsa hannunta, kasa ce mata komai yay duk da cewa ya fahimci so take yay mgn but he can't say anything sam baya jin daɗin zuciyarsa.
Zame hannunta tayi tace "da alama dai Sheikh ya manta harin da aka kawo masa last year a mosque ranar idin babbar sallah, da alama Rayuwata ya manta tuggun da aka haɗa masa na sace masa tayar mota, da alamar farin cikina ya manta maid ɗin data sanya masa poison a cikin abincin ka, gaba ɗaya wannan bai isa ka gane cewa Arjun domin lafiyarka yake wannan abun ba?".
Da Mmki yake sauraran dukkan abinda take faɗa masa,idanunsa a rufe amma bai hana ta gane cewa yana mmkin maganganun data faɗa masa ba, tayaya tasan wannan abubuwan da yake ɓoyewa? Yes! Yasan maid ta sanya masa poison a abinci amma ko Abbansa bai san da wannan mgnar ba daga shi sai Arjun suka sani kuma suka ɓoye mgnar,kawai yaywa Abbansa bayani akan yana son zuwa waje ya huta! shine shida Arjun suka bar ƙasar gaba ɗaya a can yay jinyar poison ɗin daya sha.
Numfashi ya sauke yana tuna abubuwan da suka faro a baya wanda suke dawo masa cikin kansa kamar yanzu komai ke faruwa.
Ganin yadda take ta surutu ko tsayawa ba tayi yasa shi saurin kama hannunta yace "Enough please okay!" Gira ta ɗaga masa tace "should I go with you or gida zaka?" Ɓata fuska yay yana ɗan taune bakinsa yace "just go with me...
Fannah dake tsaye kan Barrister kamar an dasa ta ko zama ta gagarayi sbd ɗacin da zuciyarta take mata, ji take inama tai ta zabga ihu ko hakan zai sanya iyayenta su fahimci halin da yake ciki,wlh da Auren wannan suger Dad ɗin ita kam gwamma mutuwar ta.
Miƙewa Barrister yay yana sakin lallausan murmushi yace "zan tafi amma zan dawo zuwa dare before na koma Abuja" banza tai masa ko ajikinsa bai wani damu ba saima wani kallo da yake binta da shi na zagi gane baki da wayo, hannu ya miƙa zai kama nata hannun da sauri ta juya tare da shigewa cikin gida,da Murmushi kawai ya bita kana ya juya zuwa inda yay parking motarsa slowly ya dinga tafiya kai kace wani saurayi ne wanda bazai huce shekara 30 ɗin nan ba, da haka ya shiga mota zuwa hotel ɗin da ya sauka. Fannah baƙin ciki da kuma takaicin tsayawa da Barrister yasa tun daga ƙofar shiga parlon nasu ta saki kuka bai taɓa zuciya bata taɓa tunanin auren sa'an ubanta zai zama ƙaddarar ta ba, sanin cewa idan tai kuka mai yawa kanta zai iya yi mata ciwo kuma iyayenta zasu fahimci bata aminci da zaɓin da sukai mata ba yasa ta share hawayen ta,banda sakin ajjiyar zuciya babu abinda take, a sanyaye kuma ta ɗaga labulan parlon bakinta ɗauke da sallama Murya kuma can ƙasa, Falta da Mama kolo mahaifiyarsu ne kawai zaune a parlon suna duba wasu new designer furniture a wayar Falta, kallo ɗaya Mama kolo taiwa Autar ta ta, Falta kam da ido ta bita har zuwa cikin uwar ɗaki, miƙewa tsaye tayi tace "Mama am coming" ko Kallonta Mama kolo ba tayi ba taci gaba da duba abinda take nema, kwance ta samu Fannah sai sakin ajjiyar zuciya take kana ganinta kasan bata cikin nutsuwarta dauriya kawai take, zama tayi gefen gadon tace.
"Aiye ye"
(Yadai) Shiru Fannah tai mata Murmushi kawai Falta tayi domin tasan halin ƙanwar tasu bata fiya son takura ba, ita kanta bata son wannan Auren,amma wanene ya san abinda gaba zata haifar? Allah kaɗai yasan abinda wannan auren yake nufi da kuma abinda yake ɓoye a cikinsa,banda haka tayaya wannan ƙaton mutumin zai kalli Fannah yace ita ya keso?? Bayan gasu duk a gidan babu auren koda yake ance komai lokaci ne, shi kuma aure kamar layin malkaɗe ne idan ka kai ko kana wajan ko baka wajan tabbas zai zo kanka, ajjiyar zuciya ta sauke tace.
"Chi'ne"
(Tashi). A sanyaye Fannah ta miƙe tana kallon yayar ta, Falta tace "Ayi wazo"
(Mene ya faru) girgiza mata kai kawai Fannah tayi idanunta na ƙara kawo ruwa sbd bata san mene za tace a yanzu ba,bata da ikon da zata buɗe baki tace bata son auren ko kuma tace Barrister bai mata ba,tunda ta riga ta aminci da magnar Baba Baa'na tun farko kawonta ma daya tambayeta ta tace masa ta amince so dan haka dole ta auro jarumta nutsuwa ta sanyawa zuciyarta.
Hannunta Falta ta kama tare da faɗin "look! dear kin san iyayenmu baza su taɓa zaɓa maki abinda zai Cutar dake da hankalinsu da komai ba ko?" Ɗaga kai kawai Fannah tayi tana jan numfashi "so You don't have to be worry about that, Aure ai ibada ce ko wanda ka aura kana so sai kiga kun samu saɓani dashi ya dinga nuna maki rashin daraja kala-kala, wanda kuma ka aura baka so ya wanci anfi samun kwanciyar hankali da su,so kiyi addu'a neman zaɓin Allah tare istikaara, nasan zaki samu sauƙi a ranki". A hankali Fannah tace "Nagode Yaa Falta" kanta ta shafa tace "it's my pleasure ƴar ƙanwata,keda kikaci sa'a kowa yana sonki a dangi ma,babu wanda zai bari aci uwarki yay shiru dan haka ki sake ki daina sanya damuwa a ranki domin bata magani just pray".
ɗaga kai Fannah tayi itama Ya Falta miƙewa tayi tana faɗin "kije kiyi wanka kici abinci zamu gidan Anty Yakura,daga nan zamu huce gidan kawo Modu" tana faɗin hakan ta fita a ɗakin itama Fannah ta miƙe tsaye tare da fara cire kayan ta, a gaban mirror ta tsaya tana kallon surar jikinta wai ace duk wannan baiwar da Ubangiji yay mata tsuhu ne zai mureta? Ita kam an gama da ita wlh, hawaye taji ya kawo idanunta da sauri ta share hawayen ta domin ta ɗauki niyyar auren kuma ko dawa yake tafe ba zata taɓa amincewa dashi ba....
Zaune yake a gefen wata ƙorama dake guda na, time to time ya kan lumshe idanunsa shi kansa bazai ce ga inda yake ba, waje ne kamar jeji amma bashi da duhu sosai ga wata daddaɗar iska dake kaɗa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa wanda ya bai yana sakamakon rigar jikinsa da Airah ta cire masa.
Gajiyayyun idanunsa wanda suke a ɗan lumshe ya sauke a kanta tana cikin ruwan tana wanka sai dry take masa tare da watsa masa ruwan, ya kanɗan murmusa bakinsa sbd sha'awar data bashi, sai ta ƙara zama ƙaramar yarinya a idanunsa, Ta ɗaure ƙirjinta da wani farin yadi haka ma waist ɗinta, ajjiyar zuciya ya sauke ya shiga shafa ƙirjinsa zuwa wajan red nipples ɗinsa wanda suke da ɗan tsini sakamakon brest ɗinsa da yake da girma, Murza Wheelchair ɗin ya fara har zuwa gaɓar ƙoramar cikin nutsuwa ya zura dugwaye fararen ƙafafuwan sa cikin ruwan, sanyi da kuma daɗin ruwan da yaji yasa ya ɗan saki wani sound mai daɗi, kallonsa Airah tayi tace "the you like it?" Juya idanu yay kamar bazai magana ba can ƙasa a taushashe yace "Yeah! Wajan very beautiful" "Olright get down" ta faɗa tana kama hannunsa tare da jawosa jikinta a hankali ta zamesa daga saman wheelchair zuwa ƙasa gefen ruwan gaba ɗaya ruwan ya kawo masa sama har wajan waist ɗinsa, haɗa ido sukai ya kwaɓe fuska yana ɗan lumshe idanunsa cikin ƙasa da murya yace "kayana" da ido tai masa mgna "meye samesu?" Shima da ido yay mata nuni da jiƙewar da wandon jikinsa yay, dry tai masa sbd ta lura yana da ƙyanƙyami bai son abu mai danshi, hannunsa ta kama ta ɗura a kanta ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fara zame masa wandon jikinsa, tana gamawa ta miƙe tare da nufar wajan data ajjiye nata kayan ta shanya masa su, ƙafafuwansa ya fara wasa dasu a ruwan yana jin wani farin ciki yana lulluɓe sa, gaba ɗaya damuwar dake zuciyarsa wacce Arjun ya sanya masa ta kau, wasai ya kejin zuciyarsa,yana ta zaune babu Airah hakan yasa ya juya yana kallon wajan da yaji kamar tafiyar abu, ƙatuwar mesa ya gani zabgegiyar gske sai juyi take a saman ciyayin wajan,ware idanunsa yay domin ya tabbatar da cewa Airah ce wannan mesar ganin yadda mesar ke juyi tana cikurkuɗewa waje guda yasa ya zare ƙafafuwansa daga cikin ruwan kamar yaro mai rarrafe haka ya dinga jan jikinsa zuwa wajan mesar, yana zuwa mesar tayo kansa tare da nan naɗesa ciff ta kwantar da kanta a saitin ƙirjinsa tai lamo sai fasa kai take, Sheikh samun kansa yay da Mutsa ba kinsa ya shiga yin addu'a cikin nutsuwa yana tofa mata a kanta zuwa jikinta, well yana shafa kanta da hannayensa, almost 5minutes suna haka kafin jikin mesar ya ɗauki rawa iska ta fara kaɗawa lumshe idanunsa Sheikh yay bayan iskar ta lafa ya ware manyan idanunsa yaga tuni mesar ta koma AIRAH tana kwance jikinsa sai rawar sanyi take, ga jikinta daya ɗauki zafi a rikice ya kalleta yana ɗago kanta daga jikinsa muryarsa bata fita sosai yace "Fairy..na! what..what wrong with you?" Girgiza masa kai tayi tace "babu komai kawai sanyi na keji" kanta ya shafa yace "okey! Just hug me nothing will happen in sha Allah!" Ya faɗa yana rufe ta da faffaɗan ƙirjinsa tare da ɗura kansa a saman wuyanta, riƙesa tayi sosai sbd wani sihirtaccen ƙamshi haɗi da ɗumi dake ratsa jikinta.
Ringing ɗin farko Arjun yay answering call ɗin da Granny take masa yana mannawa a saman kunnen sa tace "Haba Ranjun? Haka ake rayuwa fisabilillahi? To nidai babu ruwana ka daina ganin kai abokin sa ne ko ubansa bai isa ya taɓa Imamu na zuba masa ido sasakai yay abinda yaga dama ba, haƙƙi nama kaɗai ya isheka bare na yaron da baiji ba bai gani ba,ka ɗauke sa kuyita gantali a titi babu tsaro ba komai wannan lokaci na ƴan kidnama da ƴan dama,yaro ko furar da yake sha ta yamma bai shafa ba ina nan nai tsoru kamar dai wata nunafa,alhalin babu wanda naiwa munafurci,rabuna dashi tun ina yarinya".
Shiru Arjun yay yama rasa ta ina zai fara yiwa Granny bayani jin yay shiru yasa ta fara matsar ƙwalla tana share hanci tace "Nidai ka gayamin gsky kada kaji komai ai tsautsayi ne ko ba hk ba?". Sauke numfashi Arjun yay kafin ya share zufar dake karyo masa yace "No! Granny baki fahimta ba" cikin fusata tace "wlh kuma bazan fahimta ba, rabona da ganewa tun a makarantar allo, nidai kawai ka dawo min da jikana idan ba haka yasin polis zan kai ka". Daga can ɓangaren Arjun ya kalli wajan da yake yace "Look! Granny he's fine fa, muna tare da shi wajan Ummi but yanzu zamu dawo gida ai".
Tace "Ah to! Haka dai yafi daman na san ba inda zaka kai shi ai, to yaya Sadia?" Yana shafa kansa yace "tana lfy,tana ma gaisheki" yana faɗin hakan ya kashe wayar bai tsaya yaji mene za tace masa ba. Abun kamar wasa zazzaɓi mai zafi ya rufe AIRAH jikinta sai rawa yake Sheikh kam bai taɓa ganin ciwon aljanu ba sai yay ta Mmki daman Aljanu na cuta,gaba ɗaya ya manta shi malami ne bare ya samu amsar tambayarsa a cikin karatun da yake na yau da gobe, suna nan zaune saman ciyayi ta ƙanƙame sa shima gaba ɗaya yay covering ɗinta da ƙirjinsa bai san ta ina zai fara ba, bai san tayaya zai taimake ta, idanunsa da yake a lumshe ya buɗe yana ƙarewa ƙyakkyawar fuskarta kallo a hankali kuma ya sanya hannunsa ya shafi fuskarta idanunta ta buɗe da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login