Showing 3001 words to 6000 words out of 130248 words
kariya akan kariyar da Ubangiji yake baka, ba lallai kasan abubuwan da suke ɓoye ba amma ni nasan komai naka, dan Allah accept, kada ka juyan baya, kamar yadda Mamana da Abbana sukai min,Tijama da Juɓe sune kaɗai suke supporting nawa" ta ƙare maganar tana saka masa kuka tamkar ba Aljanna ba, sosai zuciyarta da kuma hurinta haɗi da gangar jikinta suke ƙaunar Sheik Imam,tun tana zanin goyo wata rana ta ji Iyayen ta na magana akan haƙurinsa da kuma jarumtar sa da taimakon da ya kewa talakawa , tun a sannan ta kamu da soyayyarsa mai wahalar gaske, bata da magana sai ta Sheik, wata rana tayi suffa irinta Bil'adam ta shiga cikin gari, tashin farko gidansa ta nufa tai rashin sa'a lokacin ya je sauke farali a ƙasa mai tsarki, bata tsaya ɓata lokaci ta nufi makkah a nan tai arba da shi a cikin harami gaban ka'aba yana sanye da fararen kaya masu ɗaukar ido, surar jikinsa a bayyana ga six packs ɗinsa abin birgewa, fari ne jajirr kamar ka taɓa shi jini yay tsartuwa haka yake, ko ina na jikinsa gargasa ce kwance sai sheƙi take gwanin sha'awa, is too young domin bazai wuce 23 zuwa 25 ba,t a ɗauka babba ne sosai, amma yanayin hutu da kuma cima mai kyau yasa ya zama cikakken Namiji mai jini a jika da kuma lafiya, yana da faɗin ƙirji wanda duk rabin ƙirjin sa gashi ne kwance lub-lub, kana ganinsa kasan yana gyming yana da wasu kalar fresh pich lips wanda suke very soft and shinny he's behaving like king of Saudi Arabia, eye lashes sunyi zara-zara har saman girarsa, babu abinda ya bawa Airah mamaki sai ganin sa da tayi saman wheelchair da alama yana da nakasa bashi da ƙafa, tun a lokacin taji tausayinsa ya kamata sosai, gashi dai babban mutum yana da komai na rayuwa kuɗi, ilimi both boko da Arabic yama fi ƙarfi ga Arabic domin a nan Saudi'a yay karatunsa, maganar kuɗi kam ba'a magana, bai rasa komai na rayuwarsa ba, babu abinda ya nema ya rasa, amma ya rasa farin cikin sa uwa uba babu ƙafar taka wa, a nan ta gama kallonsa ta koma cikin dajin da suke da zama, tun daga ranar ta ɗaura lalurar duniya a kansa sonsa take sosai, taɓa ta da yayi yasa ta sauke ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske, kafin ta ɗaga jajayen idanunta ta kalle shi, saurin ɗauke kanta tayi saboda ba zata jure kallon cikin idanunsa ba, maganarsa ta dawo da ita hayyacinta inda yake faɗin "Ashe baki da tausayi ke mai son kanki ce ban sani ba? tayaya zan iya soyayya da Aljana what kind of rubbish ?" Cikin hasala itama tace "You can Sheikh Imam Hamdan ,sau nawa kana tarayya dani a Matsayin mata" da sauri ya kalleta Murmushi tayi tace "Yeah! I'm pregnant with your unborn child Sheikh, bana da niyyar cutar da kai ko kuma cin zarafin ka, bana son na haifa maka ɗan Haram domin dani da kai duk Halartattun ƴa ƴa ne, sai da aka yi Aure aka haife mu, mai yasa ni kuma zan zaɓi haifar ɗan zina? Ko kayi accepted ɗina as your wife ko kar kayi kasan ina da ƙarfin ikon da zan zauna da kai na saka kayi tarayya dani, ask me why banyi haka ba? kasan dalili shi ne ina sonka Imam, so mai ƙarfi da kuma girman gaske, tunda na bar iyaye na ai ya kamata ka karɓe ni, ka zame min gurbin dana rasa, nima na baka farin cikin daka rasa na shekara da shekaru, ina sonka saboda Allah! Burina bai huce na kula da lafiyarka ba, zuwa yanzu kasan baka da kowa sama dani saboda nice matarka!" Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya, murmushi kawai ya saki kafin yace "Na ji mai dani gida" kuka ta saka masa tare da zubewa ƙasa ta riƙe ƙafafuwansa tace "dan Allah dan girma ALLAH! Ka so ni kwatankwacin yadda nake sonka, wallahi zan iya mutuwa idan baka amince dani ba, kuma ɗanka dake ciki na ba" wani bala'in tausayinta ne ya kama shi, ace wai Aljana ita take sonsa har tayi tarayya dashi ya sanya mata ƙwansa a cikin ta, yaya zai yi da rayuwarsa yanzu shi?ta yaya zai iya rayuwa da ita a cikin gidan su? Yadda take masa kuka sosai da kuma yadda take begen nasa akan ya so ta yasa bai san lokacin da yace "Okey! Imam hamdan accepted you as his wife" cikin farin ciki da Murna Airah ta ƙwala wani uban ihu tace "Didn't i told you Tijama, bana gaya maki cewa my Imam has a good heart ba" kallan yadda take tsalle da murna haɗi da ihun yasa cikin ƙasa da Murya yace "Don't scared your Husband" tsayawa tayi da rawar tana jin wani farin ciki na ratsa jikinta, cikin tsananin farin ciki tace "Thank you so much Sheik, thanks once again i can't stop loving you you're my everything" lumshe idanunsa yana jin abinda ya aikata kamar ba dai-dai ba ne,amma yaya zai yi da ita? Ba zata taɓa barinsa ba indai ba amincewa yayi ba, shi yasan bazai taɓa yin tarayya da ita ba, shiru yay kawai yana sauraren bugun zuciyarsa, ganin tai masa shiru yasa ya buɗe idanunsa da sauri ta ɗauke idanunta wanda tun ɗazo ta ɗaura su a kansa, kamar zai kuka yace "gida Please" wajansa ta ƙarasa tare da durƙusawa a dai-dai ƙafafuwansa ,kana ta saka hannunta ta ɗura saman laps ɗinsa tace "Why are you so worried ?" Shiru Imam yayi mata yana tsareta da fararen idanunsa, Murmushi tayi tace "don't worry, yanzu za'ai mana bikin" ware idanunsa yay sai kuma yay calming yace "Owk" miƙewa tayi kana ta haɗe hannayenta waje guda ta shiga tafa hannayenta, cikin ƙaramin lokaci Tijama da Tuɓe suka bai yana, dariya Tijama tayi tace "Congratulations Airah, congratulations Sheikh Imam Hamdan " bai ce komai ba sai hannunsa daya miƙawa Airah kamar yadda ta buƙata,wani ƙaramin ring wanda yayi dai-dai da yatsansa, kana ganin zoben kasan cewa an kashe kuɗi wajan yin sa, banda haske da ƙyalli babu abinda yake, a saman Ring ɗin a rubuta I&A, fuskarta cike da farin ciki ta sanya masa zoben, kallonsa tayi tace "Now is your turn" jikinsa ya shiga lalubawa yaji babu komai sai wani sirin sarƙar gold, cirota yay a jikinsa kana ya nuna mata sirin sarƙar,wajan sa ta ƙarasa tare da durƙosawa dai-dai ƙafafuwansa tai masa nuni da wuyanta, A hankali ya sanya mata sarƙar, tafi Tijama da Tuɓe su kai tare da faɗin "Congratulations Airah and Imam Masha Allah!" Haka nan dai yaji ya samu kansa cikin farin ciki shima, kallon Airah yayi suka haɗa ido ganin yadda idanunta ya cika da hawaye yasa a hankali ya ware mata hannayensa da sauri ta zo wajansa tare da faɗawa jikinsa , a tare suka sauke ajjiyar zuciya, shiru Sheikh yayi yana duban agogon hannunsa yasan yanzu Subhi ya kusa yana buƙatar komawa gida, ƙasa yayi da murya dai-dai fuskarta yace "Can i go?" Fuska ta marairaice tace "babu wani gift?am your wife Sheikh" taɓe baki yay yace "me zan maki?" Dariya tai tace "ok lemme give you a special kiss Rayuwata" zaro ido waje yayu tace "Yes! Sabon sunanka ke nan a gareni RAYUWATA" lumshe idanunsa yayi kafin ya saki jishi tare da faɗin "Uhm" Sumar kansa Airah ta shafa a hankali kuma ta sanya bakinta cikin nasa da niyyar bashi hot kiss.....
20/10/2021, 20:38 - 🤔🤔: *SIRRIN MU*
*BY*
_✍🏾 NIMCYLUV_
_This book is for sale it's #500 via 0116886423 Sulaiman Naima s union bank, evidence of payment 08119237616, ga mutan NIGER sai suyi mgn a wannan number 84506476_
EPISODE5️⃣-6️⃣
Da sauri Sheikh Imam Hamdan ya zare bakinsa, bai son abin da take shirin yi masa,kuma bai son ya ɓata mata rai saboda ya tabbatar da ingancin son da Airah take masa,shima garesa yana son ya kwatanta yi mata nasa kalar halaccin ko da ba zan so ta ba,ta guji iyayenta a kansa to namiji yay haka ai yana tare da fushin Allah bare kuma ace mace,dan dai bai son kalar nasu abun ba, tunda suɗin ba wai kamarsa suke ba, Shiru Airah tayi tana jin babu daɗi a cikin ranta kuma bata son takura masa saboda ta ga kamar bai gama yarda da ita ba,ita kuma burinta bai huce ya yarda da ita su saba su zama tamkar Aminan ƙwarai wanda dukkan abin da ya samu ɗaya sai ɗayan ya ji a jikinsa,ganin yadda duk ta sauya fuska kamar dai za tai kuka yasa ya tallafo haɓarta yana lumshe idanunsa kamar bai shirin yin bacci a wajan,cikin ƙasa da Murya wannan karan da larabci ya ce "Ma'aa sa bakiii?" Girgiza masa kai ta yi tana Murmushi ta ce "it's time to go home" taɓe bakinsa yay tare da fesar da numfashi cikin nutsuwa da fitllatanci ya ce "You look so worry" Idanunta a saman fuskarsa tana kallan ƙwantaccen beard ɗinsa da ke Shinny gwanin sha'awa, hannunta ta miƙa ta shafa sajen nasa ta ce "Yeah!am worry" ba tare daya kalleta ba ya ce "Why?" Sosai Airah ta matsu kusa dashi tare da ɗura kanta a saman cinyarsa ta fara kuka kamar ƙaramar yarinya,sai da ta gaji dan kanta Sannan ta tsaya da kukan tana sakin ajjiyar zuciya kafin a hankali ta ce "I Missed you Soo much i missed a lot Rayuwata,kasan lokacin da na ɗauka ina fama da iyaye na akan ka,na rabu da su yanzu saboda ina tunanin zan samu farin ciki a wajan ka,ashe nayi kuskure su Aljanu ba halittar Ubangiji ba ne? Bama da Zuciyar daza mu so dukkan abin da mu kaji muna sonsa ashe? Na daɗe ban yi bacci mai daɗi ba kasan mene yasa? Ba na son taku raka kona matsa maka,a kullum baka da lokacin kanka sai na Mutanan gari dana wa'azi a matsallatai da ba wa mutane darasi,baka samun nutsuwa cikin dare idan kuma nace a wannan daran zanzo inda kake bazan barka kayi bacci ba,zakai ta mafarkai kala daban-daban ƙarshe ka tashi da ciwon kai,ni kuma bana Fatan hakan ya kasance da kai,shiyasa na zaɓi nai nisa dakai ina buƙatar ka Imam,ina sonka kai ne Rayuwata kai ne farin ciki na dan Allah don't ever betray me,kada ka samu wata a jinsin ku kace zaka manta dani" hannunsa ta kama ta ɗura saman cikinsa tace "I'm pregnant with your unborn child Rayuwata me and your unborn child need you please don't ever trying to betray me" kasa magana Sheikh yayi saboda wani tausayinta daya ratsa zuciyarsa ware mata hannayensa yay da sauri ta shige jikinsa tana sakin wani sabon kukan covering yay mata da faffaɗan ƙirjinsa "it's okay AIRAH!!" Turo bakinta tayi gaba tare da dukan ƙirjinsa tace "stop calling my name Rayuwata just give me a beautiful and special name" wani lafiyayyan murmushi yay mata ya ce "just look at you, you're crying like a baby" kanta ta ɗaga lokacin na farko kenan data sanya idanunta cikin nasa, slowly ta dinga nufar bakinta zuwa ga nasa, copping face ɗinsu tayi waje guda Sannan ta buɗe masa bakinsa da hannunta da sauri kuma ta sanya bakinta saman nasa zatai kissing nasa.
A firgice Sheikh Imam hamdan ya farka daga nauyayyan baccin daya ɗauke sa mai cike da tarin mafarkai na abun mamaki, ba tare daya buɗe idanunsa ba ya shiga karato addu'ar da addini ya kuya mana idan mun shiga cikin irin Wannan bad dream ɗin kamar haka:
_اعوذ بكلمات الله التامات من غضبه وقابه،وشرعباده ومن همزات الشياطين وأن يحضرون._
_(Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa,da uƙubarsa,da sharrin bayinsa,da kuma wasuwasin shaiɗanu,da kuma kada su zo mini (acikin Al'amurana)._
Bayan ya kammala addu'ar ya ware manyan idanunsa sannu a hankali kuma komai na mafarkin ya fara dawowa cikin brain ɗinsa,murza hanunsa yay yaji wani sabon ring wanda bai san dashi a hanunsa ba, kallonsa yakai zuwa ga zararan yatsun hannunsa wanda suke dugwaye masu kyau, wani farin zobe ya gani wanda akai masa rubutu da I&A shafa zoben yay ya shiga fesar da iska daga cikin bakinsa, idanunsa yaja ya rufe a hankali sosai yake son tuna sunanta amma ya kasa, Yun ƙura wa yay daga kwancan da yake ya jingina bayansa da jikin fuskar gadon,a godon da yake manne jikin bangon ƙawataccen bedroom ɗin nasa ya duba,juya idanunsa yay ya ga lokaci har ya fara jaa domin tuni akai kiran fari, yana ta zaune shiru babu abin da yay kuma babu wanda ya shigo cikin flat ɗin nasa,ga lokaci yana ta tafiya, hankali yaga iska na kaɗa labulan dake maƙala jikin window, With much surprise ya fara bin window'n da kallo,domin ya tabbatar bai kwanta bacci ba sai da Granny ta gyara masa komai ta rufe ko ina,amma ya ya akai window'n ya buɗe shi ɗaya? Ganin bashi da amsa babu kuma wanda zai tambaya yasa ya ja bakinsa yay shiru ya bi window'n da kallo,ganin iskar tai tawa yasa ya lumshe idanunsa yana jin sanyi da wata nutsuwa na ratsa jikinsa, seriously Imam he's more handsome guy he's innocent and smart,jin ana shafa sumar kansa yasa ya buɗe ido ganin Granny tsaye a kansa ya sanya ya sakar mata tattausan Murmushi "Sorry sweetheart I'll keep you waiting am sorry for that,na makara ne" jinjina kai yay ya ce "Uhm" Wheelchair Granny ta jawo tare da buɗe ta,sai da tazo daf dashi sannan tace "Get down sweetheart" jan jikinsa yay sosai zuwa gefen gadon da taimakon Granny ya samu ya zauna a saman Wheelchair ɗin cikin nutsuwa ta turasa zuwa cikin Bathroom ɗin sa,Wow wow! Very beautiful komai na cikin bedroom ɗin white color ne, shower, Sink, mirror, Jakuzzie, towels, Bathrobe anything is white color, hatta bathroom slippers ɗinsa fari ne tass, tana kaisa bathroom ɗin ta taimaka masa ya sauya kujera daga wacce yake kai zuwa wacce take gaban shower wacce always a cikin bathroom ɗin take sbd wanka, fita Granny tayi tare Wheelchair ɗin kana taja masa ƙofa, kasancewar farar Singlet ce jikinsa yasa bai sha wahalar zare ta ba,haka nan three gaiter na jikinsa zuwa pad ɗinsa gaba ɗaya yay naked, sexcy eyes ɗinsa ya sauke saman laps ɗinsa wacce take fara tass sai Shinny take ga wasu gashi da yay kwance saman cinyoyinsa abin birgewa,ikon Allah! Kenan duk ƙyansa da da iliminsa both sides arabi da boko uwa uba dukiya ta abin mamaki amma hakan bai hana Ubangiji ya tausyesa da wata lalurar ba,sai Allah ya saka yana ɗaya daga cikin jerin guragun duniya,lallai kuɗi zasu iya yi maka maganin komai amma banda lalura,abu biyu zuwa uku ne kuɗi ba zai iya sama baka so ba, na farko Lafiya,na biyu Soyayya,na uku kwanciyar hankali tabbas kuɗi ba zasu taɓa sama maka ɗaya daga cikin waɗan nan ukun ba,duk isarka ko mulkinka ko tarin Dukiyar ka kuɗi baza su taɓa sama maka soyayyar mace ba,haka kuɗin ka bazai taɓa sama maka Lafiya ba,yau ina shugaban mu Umar Musa ƴar addu'a? Da kuɗi na bada lafiya da tuni yana raye yana yawo ko ina cike da kuzari da kuma ishasshiyar lafiyarsa, haka nan duk mai kuɗi bashi da kwanciyar hankali kullum cikin tunani haɗi da zullumin rayuwa yake, Ajjiyar zuciya Sheikh ya sauke bayan ya gama tunani a ransa,ganin ba wani kashi yake ji ba yasa yana daga inda yake tsaye ya kama Manhoon ɗinsa zuwa cikin toilet ɗin yay fitsari kana ya wanke sama da ƙasa zuwa tsakanin cinyoyinsa na Monhoon ɗin, Wheelchair ɗin yaja zuwa wajan shower ya sakarwa kansa ruwa lumshe idanunsa yay yana jin yadda ruwan yake dukan saman fatarsa, yana kammala wankan yay brush kana yay alwala, hannunsa ya miƙa ya ɗauki long towel ya ɗaura saman waist ɗinsa,ya zamana iya faffaɗan ƙirjinsa ne a waje wanda yake ɗauke da kwantaccen gashi da kuma manyan brest, duguwar ƙafarsa yasa ya bubbuga ƙofar bathroom ɗin,babu jimawa Granny ta shigo fuskarta ɗauke da Murmushi tace "ka kusa yin late a Masque ɗin Rayuwata" saurin kallanta yay saboda jin sunan data faɗa and he try to remembered inda ya taɓa jin sunan Rayuwata, Murmushi kawai yay ba tare da yay magana ba,domin yawan surutu baya cikin tsarinsa,idan kaga yay magana to Granny ce ko kuma best friend ɗinsa Arjun, sauya masa Wheelchair ɗin tayi kana ta jingine ta cikin bathroom ɗin ba gefe guda, a gurguje ta shafa masa wani lotion mai ƙamshi da kuma kama jiki sbd yau taga an tashi da sauyin weather, wata farar Jallabiya mai ƙyan gaske ta bashi ya saka bayan ya saka pad ɗinsa da boxer sai kuma singlet,ta san bai son kayan nauyi yana iya cirewa a ko ina, hiraminsa ta ɗauko ta saka masa a saman sumar kansa kana ta ɗura masa ta wani baƙin igiya na saman hiramin ta ɗauki casbawa ta bashi,wani simple slippers ta bashi mai kyau da tsada,kana ta fesa masa parfumes Difference, dry tai masa tace "Kai Sweetheart kayi kyau kamar a sata a gudu" a karo na farko ya saki Murmushi cikin ƙasa da murya yace "Jazakillah bilkhair Granny" "no need dear it's my pleasure" ana haka Alhaji Hamdan ya shigo shima cikin maroon ɗin jallabiya ya ce "shira bata tashi kullum sai za'a Mosque" Murmushi kawai Granny tayi ta ce "Sai kun dawo ka kula da shi" Barrister ya ce "Ohh Wow! Ni ba'a ta tawa ko?" Harara tai masa ta ce "wa yake batun babba ga ƙaramin yaro" dry shima yay ya ce "wane yaron Mother? Kullum ke kike maida Imam ƙarami,shiyasa baya ɓoye taɓararsa a gaban kowa" Granny tace "Yau na ga abin da ya dameni ni Faɗimatu,to banda Allah ya baka ɗa mai hankali da nutsuwa da tarin hankali uwa uba ilimi banda haka Imam ɗin guda nawa yake? Duudu bai huce 23 zuwa 25years ba fa" ganin sunata surutu yasa Imam yin gyaran murya ya ce "we getting late Abba" Barrister ya ce "Sorry my son da sauran time ai" yana faɗin hakan ya tura Wheelchair a hankali suka nufi Mosque ɗin dake wajan gidan Barrister Hamdan Balarabe,Granny na ganin fitarsu tai Murmushi