Showing 9001 words to 12000 words out of 130248 words
darajar fata ba kace a shafa maka wani losha,meye ma wani losha fisabilillahi" Shidai bai ce komai ba domin a karo na farko kenan yaji bai ji daɗin yadda Granny ke shafa masa mai ba,ji yay gaba ɗaya yana da bambanci da wanda Airah ta shafa masa da Asuba, comp ta ɗauka ta taje masa sumar kansa ta kwanta sosai har saman goshinsa,kana tai hanyar wardrobe tana faɗin "Uhm kai kaji wani zance Imamu" idanunsu akan madubi yana kallon yadda jikinsa ya ƙara buɗewa sosai kamar wanda yake yin risilin, jin yay shiru bai magana ba yasa Granny ta ce "Idan bakai miskilanci ba ai sai Allah ya ka maka wlh, domin Ubanka Did...," Sai kuma tai shiru ta cikin madubin ya kalleta ya ce "Speak up Granny,meye Did...?" Girgiza kai tayi tace "A'a babu ruwana da gulma haramun ne wlh,daman wani zance nake som tsegun ta maka da naji Barista ya faɗa" gaba ɗaya attention ɗinsa ya bata yana faɗin "Uhm" wani tissue ɗin yadi mai masifar kyau ta ɗauko masa mai manyan zane gashi shara shara domin komai na jikinsa ana iya gani,wajansa ta ƙarasa tare da sunkuyawa ta bashi boxer ya saka sbd daga shi sai pad,tun yana yaro haka ya tasu kakarsa ke masa komai, shiyasa ba yajin akwai abinda zai iya ɓoye mata a jikinsa sai dai tsaraicinsa, farar singlet ta bashi ya zura a jikinsa bakinsa ɗauke da addu'ar sanya kaya,sai kuma wandon yadin shima yasa rigar mai ɗinkin Jamper ta bashi ya saka, sannan ta miƙa masa babbar rigar kayan, girgiza mata kai yay ya ce "No! Granny ban so" Juyawa babbar rigar tayi tace "Wallahi baka isa ba,ba zan wahalar banza ba ka ga yadda kai kyau kamar dai ɗan firazdat ko ɗan sarki? Kai ma sha Allah" Murmushi yay mata yana ɗaga hanunsa saboda parfume ɗin da take saka masa, lokacin ɗaya ƙamshin Arabian Ohud ya cika cikin bedroom ɗin nasa, harami ta ɗauko masa ya ce "bari sai Friday bani jar darata" wata hula ta bashi mai kyau tana ɗauke da gashi,a saman sumar kansa ya ɗura kana ya sanya farin bluetooth da farin glass ɗinsa yay wani kyau he look like king of Saudi Arabia, baƙin covert shoe ta saka masa a farar ƙafarsa, sai da ta gama masa komai sannan ya kalleta ya ce "Jazakillah bilkhair Granny" zama tayi ta ce "Ni dai amana zan gaya maka wlh,idan kaci kai da Allah babu ruwana da shiga hurumin Ubangiji" lumshe idanunsa yay ya ce "Uhm feel free what's is the matter?" Tagumi tai sai kuma ta ce "Barista ya kitsa abu babu shawara fa, wai Gwamna ya nemi a baka auran ƴarsa,kullum tana jin zantukan ƙaryar da kuke a redio,sai ta kamu da sonka hankalinta duk ya tashi hakan yasa Gwamna ya ce ta gaya masa tace ai Sheikh Imam hamdan take so, to ashe ma ya san Ubanka Barista shine fa ya ce da Barista yana neman sa a govmat house,to Ubanka dai ya yarda ni da waccan ɓarauniyar kuma bamu amince ba" Kallonta kawai Sheikh yake sam bai mamaki ba domin Arjun ya faɗa masa cewa ana yawan kiransa ace Imam ake nema kuma macace,wani lokacin messages harta email ɗin Arjun,to babu mamaki yarinyar ce, Granny tace "banda gantalewa ta yaran zamani yaushe mace take cewa tana son Namiji? To wlh zamanin mu sai an kaika ɗakin mijin kake sanin wa kake aura,kaga ina da shekara 9 akai min aure hatta nono wannan a ɗakin Mijin na samesa" wani ƙawataccen Murmushi Sheikh yay yace "Am hungry" Granny tace "Me kace?" Idanunsa ya mayar bakin ƙofa ya ce "yanzu 12 past 23 yunwa fa" miƙewa tayi bayan ta gama gyara wajan kana ta tura Wheelchair ɗin zuwa tsakiyar haɗaɗɗan parlour'n gidan, har gaban dinning ta ajjiyesa kana ta shiga zuba masa abin breakfast ɗin, Arish ne da meat shawarma sai tea da yaji kayan ƙamshi da na'a na'a tai tashin ƙamshi yake, bisimillah yay yasa yatsun hanunsa guda huɗu ya fara cin meat shawarma bayan ya gama cin abincinsa Granny ta kawo karamin bowl ya wanke hanunsa ya goge da tissue kana yay hamada.
Bayan Sheikh yana mutane sallar zuhur Arjun ya koma cikin gidan su ya ɗauko ɗaya daga cikin sabbin motocin Sheik wata ƙarama mai ash color sabuwa dal, Arjun na mazaunin driver Sheikh na ɗaya side ɗin idanunsa akan littafin Zajid zaujain, sosai Arjun ke gudu da motar sbd yasan Sheikh bai son tafiya a hankali "Buddy wallahi aure nake sonyi na gaji a matse nake,Am tried pls daga nan mu huce gida ka tayani roƙan Ummi ta barni nai auran tunda ina so" lumshe idanunsa Sheikh yay lokacin ɗaya yaji tunanin Airah ya faɗo masa, Where is she? Shine tambayar da yaywa kansa, one day kenan yaya kenan idan ya kasance da ita na adadin sati guda kamar yadda ta ce? A haka suka shiga cikin gidan redio'n Arjun yay parking kana ya fita daga inda yake zaune,a back side ya ɗauko wheelchair ɗin Sheikh kana ya taimaka masa ya zauna, har cikin reception ɗin gidan redio'n suka shiga,kowa ya ga Sheikh sai ya tsuguna ya gaishesa,hatta ga wanda suka girmi Sheikh babu a abin da ya siya masa mutunci face Iliminsa sa hqrinsa haɗi da taimako da kyautatawa talakawa, da sauri ya fara gabatar da program ɗinsa na LAFIYAR MU, Mutane da yawa sun buƙaci ya buɗe masu wata ƙungiya ko kuma gruop wanda zai iya yi masu wani bayanin idan yana free,wasu kuma sukace ya basu number wayarsa, Shi dai murmushi yay kawai domin yasan a redio kawai suke jin zazzaƙar muryarsa,amma shi gaba ɗaya bai san yadda zai iya using da wata waya ba,ya wake dashi? Bashi da wanda zai nemasa a waya,a haka suka gama program ɗin shida Arjun kana suka ɗauki hanyar gidansu Arjun. Ummi ta ce "Haba Imam i don't think is nacessary,idan Arjun yay aure bazai samu lokacin kula da komai naka ba" wani abu mai ɗaci Sheikh ya haɗiye idanunsa akan Ummi mahaifiyar Arjun yace "No! Ummi i trust Arjun zai iya komai nawa,yin aurensa bashi ke nuna zai ƙi kula dani ba" Murmushi kawai Ummi tayi tace "Imam ka manta da shirman Arjun fa,and think yourself mana,kalli condition ɗinka,babu wanda ya dace da yay Aure sama dakai,yana da kyau ace kafin wani yay maka wannan mgnar kayiwa kanka" idanunsa ya lumshe kafin ya sauke numfashi yace "Try to understand us Ummi, the way mutum yace zai aure to let him do" Arjun yace "please Ummi i lover so much i need her i want marry her wlh ina sonta" harara Ummi ta watsa masa tace "kai dai Arjun anyi mara kunya,akan na hanaka shi ne ka ɗauko bawan Allah yana cikin hutawarsa,wlh baka da kunya ka kiyaye ni Arjun" Murmushi kawai Sheikh keyi,shi ina ma yana da uwar da zata hanashi abu aida yaji daɗi,he need mother new mother yana son yaji ɗumin uwa mahaifiya,yana son yaji uwa ta rungomesa inda zai samu yayta kukan saman ƙafaɗarta,baya da wannan ƴan cin bashi da uwar daza taji damuwarsa bare harta bashi shawara mai kyau,babu uwar da zata kwantar dashi zaman ƙafaɗarta tasa yay kuka mai yawa ko yaji sauƙin zuciyarsa, tagwayen ajjiyar zuciya ya sauke kallon Ummi yay inda take faɗin "Shikenan yaje yay aure Allah ya sanya albarka,Amma Imam kai ka nemu matar Aure" zoben hanunsa ya kalla ya ɗan murza kaɗan yace "bana da interested Ummi" ganin yanayinsa ya sauya yasa ta rabu dashi, farin ciki sosai Arjun ya shiga rungome Ummi yay yana faɗin "thank you so much Ummi" murmushi tai tana shafa kansa tace "kuje daining ga lunch na jera maku" girgiza kai Sheikh yay idanunsa a ƙasa yace "Am full Ummi" Ummi ta ce "daman koda yaushe you're full" dariya Arjun yay ya ce "Rabu dashi Ummi,ko a gida yake baya cin abinci iyanzu sai dakakkiyar fura" miƙewa Ummi tayi tace "ta kwana gidan sauƙi ai,ina da fura wlh" kwaɓe fuska Sheikh yay bai ce komai ba "Ummi ko kin dama bai zai sha ba indai ba Granny tayi ba" yana faɗin hakan ya nufi hanyar fita daga parlour'n yana tura Sheikh dake zaune saman kujera "To ai shikenan Allah ya baka lafiya Imam Ubangiji ya kawo ƙarshen wahalar" da Ameen ya amsa har suka fice daga parlour'n Ummi na zabga masa addu'a.
Da daddare Barrister ne zaune shida Mami da Granny wacce take yankawa Sheikh apple a plate, Sheikh na zaune yana farcing mahaifin nasa yana kallon yadda suke cin abincin su hankali kwance,idanunsa ya mayar kan Granny wacce tace "Fisabilillahi ace ƴar ƴan itatuwa sune abinci? Gsky wannan ba halin zama ba ne Babana" Mami ce ta ajiye spoon ɗin hannunta ta ce "Granny ai wannan sun fi sanya jiki lafiya" "au haba? To Allah ya taimaka nikam wannan sakalcin ba dani ba" shiru sukai mata harta gama surutun da jan plate ɗin Sheikh yay tare da sanya fork ya caki apple,amma ya kasa kaiwa cikin bakinsa sai juya Apple ɗin yake, Barrister ne yace "Yadai son?" Kallon Mahaifin nasa yay ba tare da yay magana ba ya ɗauke kansa a hankali kuma ya tura Apple ɗin cikin bakinsa,duk son sa da Apple yau jiyaye batai masa daɗi ba, he's lost his appetite gefe guda kuma tunanin Airah ne fal a zuciyarsa tun safe rabonsa da ita he's worried, bisa dole ya ci gaba da shan Apple ɗin dan bai son kwana da yunwa yasha rabi ya ture plate ɗin gefe yana hamdala, kallonsa kawai Mami take can kuma ta ce "Sorry my soul kana fushi dani ko? Kasan yanayin aikin nawa" bai ce komai ba ya danna wani abu a gefen Wheelchair ɗin a hankali ta fara tafiya sai da yaje parlour sannan ya tsaya, BBC news yakai ya fara kallon labarai, gaba ɗaya suma suka dawo parlour'n Barrister yace "My son" ko kallansa Sheikh bai ba idanunsa akan cenema ya ce "Uhm" Barrister ya ce "be ready you getting marry soon" ba Sheikh har Mami sai da ta kalli Barrister kasa daurewa tayi ta ce "what wrong with you Barrister? Yaya kake magana ɗaya tun safe? Wanne irin Aure wai ana zaune lfya gaba ɗaya Imam nawa yake ne?" Bai kulata ba yace "kana ji na ai?" Jinjina kai Sheikh yay still idanunsa na kan cenema, Barrister ya ce "Governor da kansa yake neman alfarma gareni akan haɗin Auren daya keso muyi,ƴarsa Nana tana sonka sosai" nan ma shiru Sheikh yay sai murza zoben hanunsa yake yana jin zuciyarsa nayi masa zafi, miƙewa Barrister yay ya ce "ka shirya Nidai na amince" kai tsaye Sheikh ya ce "Ni kuma ban so" da sauri Barrister ya ce "meye baka so ɗin?" Kwallon Granny Imam yay ya ce "Granny bacci zanyi" miƙewa tayi tana faɗin "to Babana yau Ubanka ina ga ƙaryarsa zai gwada a kanka" tana faɗin haka ta tura Wheelchair ɗin zuwa flat ɗin Sheikh,wani Murmushi Mami tayi ta ce "Ina raye Imam yay aure?.over my died body" tana faɗin hakan itama ta nufi flat ɗinta,a tsaye ta samu Barrister ya gama shirin bacci hucesa tayi ta nufi bathroom tai wanka ta shirya cikin kayan bacci, a parlour ta samu Barrister ta ce "Gud night" da mmki ya kalleta ya ce "what the you mean by that? Kisan ke nake jira wai meke damunki ne? Rabuna dake yau wajan sati biyu kenan ko an gaya maki dutse ne ni?" Kallonsa tayi tace "kayi hqr Barrister ban jin zan ƙara baka jikina babu abinda kake tsinana min ko 30mins da ƙyar kakeyi a jikina no test gaba ɗaya salam kake i can't waist my time akan wanann" tana faɗin hakan ta nufi bedroom ɗin ta, Juyi kawai Imam yake ya kasa runtsawa shi kasansa bai san dalili ba a karo na farko ya kejin wani a zababban fellings a tare da shi mararsa har wani kumbura tayi tana ɗagawa, jin bai taɓa jin abu makamancin haka ba yasa ya tashi zaune tare da dafe kansa ya shiga fesar da numfashi,ji yay an dafa shi da sauri ya ɗaga kansa idanunsa ne ya sauka akan Airah wacce take tsaye tana masa Murmushi, fuska ya kwaɓe mata ganin haka yasa ta zaune kusa dashi tana faɗin "Am sorry my life na barka da kewata ko?" Kasa mata magana yay sai hanunsa daya sanya ya jawota jikinsa ya rungome ƙamƙam kamar wani zai kwance masa ita...
20/10/2021, 20:41 - 🤔🤔: *SIRRIN MU*
*BY*
_✍🏾 NIMCYLUV_
_It's #500 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 ga ƴan Niger suyi mgn a nan 84506476_
🆓P
EPISODE1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣
Idanunsa ne suka kaɗa tare da yin jaa,bai san ya ya ake samun farin ciki a wajan mace ba, haka nan bai san yaya ake jin son wata ɗiya mace a duniya ba, hasali ma duk matanan duniya kallon mugwaye yake masu,ba tare daya san dalilin da yake masu wannan kallo ba.
Sai gashi yanzu a karan farko yaji yana son kasan cewa da mace,yana son jin ɗumin jikin mace wanda ya rabonsa dashi tun sanda mahaifiyarsa ta kawosa duniya, bai san daɗin zama da uwa ba, Uban ma bai san daɗin zama dashi ba, Granny ya sani sai kuma Arjun ɗinsa wanda ya zame masa komai.
Yau shi Imam yake jin kewa mace na damunsa kewar ma ta ALJANA,daga jiya zuwa yau yaji komai ya sauya masa lokaci kaɗan ne wanda zai zo ya huce wanda zaiji bai yi tunaninta,ko kuma bai murza zoben dake maƙale a hanunsa ba.
Kallonsa Airah tayi ta ce "Bakai bacci ba?" Kai ya ɗaga mata kamar ƙaramin yaro kafin kuma ta ce "Ka san me?" Nan ma ya girgiza mata kasance yay alamar a'a, ta ce "I want to sleep with you, ina son yin bacci a shoulder ka, i want make you happy zan baka farin cikin duk daka rasa a rayuwarka" idanunsa a lumshe yake ya ce "sure?" Da sauri ta ce "Of cos my life" zareta yay a jikinsa yana fesar da numfashi ya ce "Tell me something Air..aah!!" Yadda yay pronouncing sunanta a ɗan rarrabe yasa ta lumshe idanunta, ta ce "Ina jinka" kallonta yay ido cikin ido da sauri ta ɗauke nata idanun domin bata iya jure kallonsa, ajjiyar zuciya ya sauke kafin yace "Da gaske Uwa na barin ɗan ta riƙo a hannun ex-husband ɗinta? What i mean duk Uwar da take da tausayi da kuma jin ƙai,bai dace ace dan sun samu Matsala da mijinta ta ce zata ajjiye ɗan da gaba ɗaya ko 1week bai cika da haihu ba,hakan shi zai sanya mijinta ya dawo da ita ko kuma ya fahimci cewa abinda yake ba dai-dai ba ne? She leave me ta rabu dani tun ina cikin zanin goyo ban san daɗin nonon uwa ba,ban san daɗin jikin Uwa ba,ban san farin cikin da ake samu idan ana tare da Uwa ba,mene laifi na? Me yasa zata ɗauki laifin mahaifina ta ɗura min, bata san cewa ɗan ta na buƙatar ta bane? Bata san cewa am nothing without her ba? Ba ta san cewa ta haifi nakashasshe wanda bashi da gata bashi da mai kula da shi ba, i want to my Mother ina buƙatar ta, i missed her a lot".
Airah tsayawa tai tana kallonsa kafin ta ce "No at all, baka san dalilin rabuwa kai da tayi ba,baka san irin zafin da taji a lokacin da zata rabu da kai ba, sannan baka san damuwar da take shiga idan ta tuna ka ba,zata iya yiwuwa duk abinda ta aikata she's not her fault, koda tana sani babu wanda baya kuskure a rayuwarsa, nasan one day she most come back to her son definitely, so you don't have to worry about that My life".
Ajiyar zuciya ya shiga saukewa yana rungome pillow hannunsa a ƙirjinsa da gaske yana buƙatar kulawar Uwa,yana son Uwa ta rungome sa,yana son yaji mahaiyarsa na lallashinsa, yana son ya faɗa mata yadda yay missed nata da kuma abinda yake damunsa, amma bashi da wannan freedom ɗin dole ya samawa kansa salama ya amshi rayuwa a yadda tazo masa.
Zare pillow dake ƙirjinsa tayi tace "Why are you hurting your self like this? Come on! Hug your wife not pillow,hug me you'll feel better".
A karo na biyu kenan a iya kacin rayuwarsa daya rungome mace, koda yake bazai iya sanya Airah matsayin mutum ba,amma yadda take tsaye gabansa babu wanda zai ce mata ta haɗa jinsi da Aljanu bare kuma kayi tunanin Aljanar ce.. Rungome ta yay sosai yana sakin ajjiyar zuciya, a yadda ya rungome ta kaɗai zai tabbatar bai taɓa riƙe hannun mace ba bare ya rungome ta,ya nayin komai a ɗan tsorace amma tsoransa iya kan mace ya tsaya da dukkan alamu mata sunyi masa tabo a zuciya.
Kallonsa tayi taga ya rufe idanunsa kamar mai bacci, jajayen laɓɓansa ta shafa tana jin wani difference feelings na ratsa jikinta tana son Sheikh fiye da sosai,domin a kansa ta karya al'adar su ta shiga jikin Bil'adam bare har su tare a inda suke,amma yaya zatai? Sonsa ya ja mata komai ba iya sonsa ba tana son kasancewa da shi ne domin bashi kariya tana son lokacin da Tijama ta ɗauka ya cika a ranar Sheikh zai san komai game dashi.
Gashin dake ƙwance saman ƙirjinsa ta shafa tace "Ina son zame maka Uwa, ina son zame maka Aboki,ƙawa Sannan ina ka amince dani matsayin matarka, ba zan taɓa cutarka ba, zan baka dukkan farin cikin daka rasa ka yarda dani Please"
Ƙara lumshe idanunsa yay still kuma yana riƙe da ita a jikinsa yace "Your request accepted my fairy".
Miƙewa tayi ta kashe all light ɗin dake ɗakin ta window'n baya ta leƙa taga yadda garin yay duhu ga wata iska mai daɗi da take kaɗawa,sai walƙiya da ake da alama a koda yaushe ruwa na iya sauka "Uhm what are you looking for?" Kai tsaye tace "the weather,garin yay daɗi musamman sky abin sha'awa" bai ƙara magana ba yaja ba kinsa ya rufe,wajansa ta ƙarasu tace "ko kana son fita ne?" Ware manyan idanunsa yay yace "kai No!!" Kusa dashi ta kwanta tare da ɗura kanta