Showing 108001 words to 111000 words out of 130248 words

Chapter 37 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5975

ba in sha Allah".
Lafewa Fannah ta sakeyi a jikin Anut Amina tana sakin ajjiyar zcy lokaci ɗaya wani zazzaɓi ya kawo mata ziyara hakan yasa Anut Amina ta kama hannunta zuwa part ɗinta.
Tea ta haɗa mata mai kauri ta bata, da ƙyar Fannah ta samu tasha rabi, jikinta na rawa ta kwanta Anut Amina ta ware mata A.c ɗakin kana taja mata kofa tai waje.
Barrister yana shiga part ɗinsa ya rufe tare da sanya dry tace "Na san me nake, da biyu nayi wannan, na jefi tsuntsun biyu da dutse ɗaya, you're lovely and smart hamdan, komai ya kusa zuwa ƙarshe komai zai dai-dai am going to be a richer old man hhhh!".
Wayarsa ya dailing number Alhj Kamal ringing ɗin farko ya ɗaga daga can ɓangaren Alhj Kamal yana zaune a office ɗinsa yana sauraran complain ɗin wanda yake son Alhj Kamal ya shige masa gaba a shari'ar da za'ai wanda ake tuhumarsa da yinwa wata yarinya fyaɗe, Numfashi ya sauke yace "Barrister kira da rana haka meke faruwa?" Barrister ya saki Murmushi yace "Aiki zakai min" Alhj Kamal ya kalli mutumin kusa dashi yace "Excuse me sir" kana ya baya mutumin baya yace "Uhm aiki akan menene? Kuma wanne irin aiki?" Barrister yace "Zan kai Sheikh court, ina son ka zama lawyer da zai kareni har na samu damar kai Sheikh gidan yari".
Wani shu'umin murmushi Alhj Kamal yay yace "Wannan ba damuwa ba ne ai, kawai ka shirya evidence masu ƙarfi wanda zamu haɗa mukai Sheikh ƙasa".
Jinjina kai Barrister yay yace "Sai Mgnar Saudat cikin jikinta ba nawa bane, shima ina zargin na Saudat ne".
Miƙewa Alhj Kamal yay tsaye kafin yace.
"Ba abin mmki bane, idan harya tabbata cikin Fannah nasa ne to babu shakka wannan ɗin ma nasa ne".
"Haka ne kam, ba za'a ɗauki lokacin zuwa Court ba, dan haka ka shirya" Barrister ya faɗa yana kallon files ɗin gabansa.
Alhj Kamal yace "Ko da gsky ko babu gsky irin wannan shirya ƙaryar mun saba ta, amma akwai abinda zakai min wanda shi ne zai zama gift ɗin shari'ar idan munyi nasara".
Barrister yace "kada ka samu zan maka komai" Alhj Kamal yace "Uhm kafa sanni Hamdan, nasan komai naka kada lokaci yazo kace ba haka ba" Barrister yace "Haba babu abinda zan iya ɓoye maka a yanzu ai, kai dai kawai kayi aikinka nima zanyi nawa".
Sallama sukai Alhj Kamal ya kalli mutumin gabansa yace "Yanzu kai da gske kai kayi fyaɗen ko bakai bane" kai tsaye mutumin yace "Da gske nine, amma babu abinda kuɗi ba yayi shiyasa ma nazo wajanka domin kayi hanyar da za'a kori shari'ar baki ɗayan ta" Alhj Kamal yace "Banda 4m Mgnar zata mutu" ba ɓata lokaci yay masa transfer kana yay waje abinsa hankali kwance.
Arjun kai tsaye gidansa ya nufa ya shaidawa Aliyah komai wacce cikinta ya tsufa, shiru tayi tana mmkin abin tace.
"Dear da gske kuma cikin na Buddy ne?".
Arjun fuskarsa ba walwala yace "Shine damuwar ai, da ace ba nasa ba ne abin da sauƙi, amma ya amsa yace nasa ne, nasan Sheikh tun ba yanzu ba baya ƙarya hakan baya give up akan abinda yake so, he love Fannah so he can do anything for her wlh".
Cikin damuwa Aliyah tace "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Meke shirin faruwa ne".
Cikin damuwa Arjun yace "Wlh baƙin ciki na rasa numbers da nayi a wayata yanzu wannan sim ɗin ba komai bane a ciki, ina da try number King Aliyou Eneye Ahuoyza taƙi shiga"
Aliyah tace "His wife is my friend, since muna school, munyi boarding school tare da ita Moon ɗin Dad ko?"
Cikin farin ciki Arjun yace "Yeah! Queen Maimunatou Sarauniyar Nufaz (Littafin Moon)".
Dry tai masa tace "Ga number mene gift ɗina?" Yace "Zan maki kiss guda ɗari yau, banda special abun, and zan siya maki littafin _ABU_MALEEK_ wanda kike ta naci nasan bazai fi ƙarfi na ba"
Rungome sa tayi tace "Wow thank you so much ko iya littafin Anut Na'ima ka siyamin wlh ka biya, zanji Abu Maleek da ƴar makauniyar sa, da kuma sauran matansa guda biyu"
Miƙewa tsaye yay yace "Naƙi wayon kiss ne dai sai nayi"
Yana faɗin hakan yay dailing number a wayar Aliyah yadda za tafi saurin ɗauka.
Lokacin da aka isa da Sheikh police station aka fara bincike ba taɓa lokacin Sheikh ya amsa yace da mai cikin da cikin nasa ne kuma duk mallakina ne, gaba ɗaya police ɗin suka tsaya suna kallon Sheikh yadda yake mgna a hankali kuma a nutse with confidence, nan take aka tura Mgnar court domin a yankewa Sheikh hukunci dai-dai da abinda ya aikata.
Miƙewa tsaye yay yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa yana tasbihi ga Allah, a yadda ya kejin sanyi a ransa yasan nothing will happen to him, no more separate with us in sha Allah!.
Ƴan sanda biyu ne riƙe dashi suna nufar ɗakin da zasu kaisa kafin gobe a zauna zaman Court, suna ƙoƙarin sanya Sheikh ciki sukaji ance.
"Tsinannu La'anannu, wlh kodai ko Haihuwar asara, shegu dakai kamar tankarar".
Da mmki Suka tsaya suna kallon tsuhuwar shi daman Sheikh tuni ya fahimci muyar Granny yana dai tsaye idanunsa a lumshe yana jiran yaji wanne kalar zagi zata ƙara.
Ɗaya daga cikinsu yace "Haba tsuhuwa wanne abune haka zaki dinga mana zagi a nan, kefa uwa ce, kin haifi kamar mu".
Bakin zani ta zare ta fara sharce hawaye tace "Muhammadur Rasulullah (S.A.W) wlh ban haifi gantalallu kamar ku ba, kaf zuri'a ta Babu ɗan ta'adda" police ɗin yace
"Haba Baba mu ce maki akai ƴan ta'adda ne? Aiki muke kuma samu akai komai mukai masa akan aikin mu ne, bawai dan ya cancanci ai masa ba, kuma banda abinki ai shi jikan naki ya amsa dukkan laifin da ake tuhumarsa akai, kawai kuje ko fara shirin zuwa Court"
Zare ido Granny tayi tace "Ko me? Koto ba, wlh billahi baku isa ba, sai dai na kwana a nan wajan"
Bai ƙara kulata ba ya tura Sheikh cikin ƙaramin ɗakin da ake sanya marasa Gsky, Kuka Granny tasa Anut Amina dai lamarin yafi kusa fin ƙarfinta Suda suka zo belin Sheikh sai kuma ai Mgnar court anya wannan abun babu zamba ciki? Tayaya mutum kamar Sheikh za'a akaisa Court Fisabilillahi! Da ƙyar taja Granny zuwa waje ta nemi wani D.S.P yace mata "Hajiya gobe misalin 10:30 za'a zauna a court kawai abinda zance maku ko nemi lawyer" yana faɗin haka yay cikin office ɗinsa.
Anut Amina lallaɓa Granny tayi har zuwa mota kana ta shiga itama taja motar zuwa gida.
Arjun ya saki ajjiyar zuciya jin an ɗaga kiran cikin Muryar girmamawa yace "Allah ya taimaki Fulanin Nufaz ya ƙara mata Lfy" daga can ɓangaren Jakadiya ta kalli Moon wacce take zaune tana duba wasu files tace "Allah ya ƙara girma da ɗaukaka ya kareki daga sharrin mutum da aljan, me Nufaz gaba ɗaya Giwa kike mai ban tsoro, kura mai kwarjini a idanun jama'a" murmushi Moon tayi tace "Meke tafe dake" kai tsaye Jakadiya tace "Kira ne daga Abokiyar ki, amma ba ita take mgn ba Mijinta ne"
Amsar wayar Moon tayi kana Jakadiya ta fice, tana kara wayar a kunanta King Aliyou na shigowa hannunsa riƙe dana babban ɗan sa wanda ya kusa kamashi a tsayi.
Gyaran murya Arjun yay yace "Assalamu alaiki Fulanin Nufaz Allah ya ƙara Lfy,Mijin Aliyah ke magana" amsawa tayi idanunta cikin na Deen kafin tai ƙasa da murya tace "Uhm ya akai?" Arjun yace "Muna buƙatar taimako ne akan wata Shari'a wacce za'a gabatar gobe" girgiza kai tayi kamar yana gabanta tace "Anya! Ba lokaci fa" kamar Arjun zai kuka yace "Taimakon Addinin Musulunci za kiyi, nasan idan kikaji wanda tsautsayin ya faɗa kansa zaki taimaka" handsfree tasa tace "waye?" Kai tsaye yace "Sheikh Imam hamdan Balarabe" da sauri King Aliyou ya kalleta tare da jinjina mata kansa tace "Ok akan mene?" Gyara zama yay shima yasa wayar handsfree ya shiga bata labarin komai na rayuwar Sheikh daga lokacin daya fara son Fannah har zuwa yanzu.
Deen ya amshi wayar yace "Goodness! Ku shirya Evedance we'll be there in sha Allah!" Daga nan sukai Sallama farin ciki ya cika zcyar Arjun, tashi yay ya shirya tare da yiwa matarsa Sallama.
Gajiyayyun idanunsa ta buɗe wanda sukai mata nauyin gaske tana jin kanta na sarawa kamar zai rabe gida biyu, cikin rashin kuzari ta ƙarasa buɗe idanunta tare dayin addu'a ta miƙe zaune, jikinta taja ta Jinjina da frame ɗin gadon Idanunta suka shiga tsiyayar da ƙwallar tausayin kansu Musamman Sheikh da abin yake shirin fin ƙarfinsa.
Hannunta ta ɗura saman cikinta wanda ya fara girma tana jin soyayyyar cikin na ratsa ko ina na jikinta dama zcyrta, da ace zata iya zubar da cikin da Tabbas zata zubar domin ta ƙaryata Barrister, amma ta fahimci Sheikh yafi son cikin fiye da komai, ta hangi zallar so da ƙauna a idanunsa, shafa cikin ta fara a hankali tace "Am so sorry sweetheart! A kanka ake wahalar da mahaifinka pls help me to find a solution" ta ƙare maganar tana fashewa da kuka tana faɗin "ya ruguza rayuwarsa because of me, Ya rabb ka kawo min ɗauki" turo ƙofar akai tare da rufewa aka shigo, ƙarasa shigowa Anut Amina tayi ta zauna kusa da ita, hannunta tasa ta ɗago kanta tace "Haba Fatima mene hakan? Ba dai kiyi believe kina son Sheikh ba?" Da sauri Fannah ta ɗaga kai, Anut Amina tace "Then why kike ta kura kanki, kin san mene zaki ki taimakawa Sheikh ai"
Baki buɗe Fannah take kallon Anut Amina kafin ta girgiza kai tace "i don't know what should I do, wlh ban sani ba kai na ya toshe Anut Amina dan Allah ki taimaki rayuwar mu nida Malamina kada ki bari a cutar da shi, bashi da kowa wanda zai taimakesa sai ke da Granny da kuma Arjun dan Allah ki taimaki Malamina, wlh zcyta sam ba zata ɗauka ba".
Kanta Anut Amina ta shafa tana maida hawayen idanunta tace "Kada ki damu ki dage da addu'a a wannan daren in sha Allah babu abinda zai samesa sai alkairi, amma kuskure Imam yayi tunda bashi da wata shaida ta kare kansa"
Girgiza Fannah tayi tace "Akwai shaida Anut Amina nice shaidarsa" Anut Amina kallon anya kina da hankali kowa tai mata tace "Wacce shaida kike da ita?" Miƙewa tsaye tayi tana ɗaukan duguwar riga ta sanya saman ƙananan kayanta tace "Nice Shaidarsa zance nina sanya yay tarayya dani, bada son ransa ba"
Miƙewa tsaye Anut Amina tace "Ke back to your right sense please, mgn ake wacce Hankali zai ɗauka, kowa yasan Sheikh Nigeria dama gefenta idan kice kikace ya kwanta dake shi kuma saiya kwanta? Bayan yasan illar hakan? Abinda kukai fa Babba ne matsayin matar mahaifinsa kike da ance wanine ma daban shine, daga jiya zuwa yau na fahimci maƙiyan Sheikh tun yana jariri kawai bani da hujjar kamasu ne, dan haka addu'a zamuyi kawai idan bashi da haƙƙin akan abin zai fita cikin ruwan sanyi"
Kuka Fannah ta ƙara sawa tana faɗawa jikin Anut Amina "Ba zan iya ba idan har akace za'a rufesa wlh sai dai a haɗa dani, domin nima mai laifi ce bawai ta ƙarfi yay min ba, dan Allah ki taimaki zuƙatan mu kada ki bari zuciyoyinmu suyi nisa da juna".
Rungometa Anut Amina tayi tace "In sha Allah I'll try my own Best, ki daina kukan idan kikai sanadiyyar cikin ya zube ko ya samu matsala fa? Kin san shi ne Abu mafi muni dazai ruguza zcyarsa shi ne zai iya rusa farin cikin sa, kiyi addu'a, muje kici abinci kiyi wanka zuwa safiya muga abinda hali zaiyi"
Hannunta taja sukai waje a Parlo suka samu Mami tana Shirin fita suna haɗa ido ta watsawa Fannah harara, ita kam ko inda take bata sake kalla ba, da ƙyar ta samu tasha tea ɗin da fatan dankali wanda yaji bushasshen kifi.
Mami na fita kai tsaye police station ta nufa bata sha wahalar ganin Sheikh ba, yana zaune ya tanƙwashe ƙafafuwansa idanunsa a rufe bakinsa na mutsawa a hankali yana Istigifari! Gabansa kuma wani bushasshen abinci ne da ruwan leda guda ɗaya, domin Barrister yace kada a bashi wani abinci mai kyau..
Hannu ta miƙa zata riƙe nasa hannu dake jikin ƙarfan ƙofar yay saurin zame hannunsa, murmushi tayi tace "Ok! Bazan taɓa ka ba idan baka so, nazo maka mafita ne, idan ka yarda ka amshi cikin jikina ni kuma nai al'ƙawarin Taimakon ka, domin idan ka bari kaje Court to tabbas za'a rufe ka ne baki ɗaya za'a haɗa maka da sharrin da baka san dashi ba"
Kamar yadda bai motsa ba haka bai buɗe bakinsa ba, shi sam bai damu ba ko hukuncin rataya za'ai masa abinda ya keso kawai Jewel tai farin ciki, ta haifa masa abinda yake cikinta yana da tabbacin zata kula dashi bayan ita ga Anut Amina ga Granny, duk zasu iya kulawa da jininsa.
Ɗan sanda take kanta yace "Hajia lokaci ya kusa fa" Mami tace "Look sweet Imam wlh zan fitar dakai domin koshi Barrister a yanzu idan nayi niyyar ɗaure sa zan ɗaure sa, shima yanayin komai a ƙarƙashi na ba tare daya sani ba, nasan cewa jikin Fannah naka ne sannan nasan cewa cikin jikina ba naka bane, haka kuma ko nakasar daka samu Mahaifinka shine sila, kuma shine silar rabaka da mahaifiyarka wanda har yanzu ba'a san inda take ba, akwai muhimmin abinda Barrister yake ɓoyewa a tare dakai wanda har yanzu nima ban sani ba, amma ka yarda ka karɓi cikina ka maidani matarka ta kwanciya a ɗaki, ina sonka Imam ina son komai naka, amma ni duk abinda zanyi babu wanda ya isa ya kamani, Mgna ta ƙarshe kuma mutuwar Uncle Sham ba tsautsayi bane ganganci ana tsane aka shirya hatsarin, kuma anyi amfani da motar Companynka, ko iya wannan zan iya amfani dashi wajan ganin an rufe ka amma bana buƙatar haka" Miƙewa tsaye tayi tace "kayi tunanin kafin mu haɗu a court gobe.
Duk inda Arjun da Anut Amina zasu samu evedance na kare Sheikh a Court sun nema sun rasa, time to time kuma suna communicating a waya Shida Moon, itama ta shiga damuwa domin wannan shine karo na farko da Shari'a zata kaita ƙasa, kuma ta ɗauki alwashin fidda Sheikh amma ba wata hujja da zata nuna haka sai tabi duk ta damu kanta, Murmushi kawai Deen ke mata yasan zatai winning na shari'ar kawai ta takura kanta sbd rigima.
Da daddare Fannah kasa bacci tayi, a daren kuma ta gayawa su Ya Falta komai dake faruwa hakan yasa sukace suma zaso zo goben.
Hankali ya tashi Gashi yanzu har ƙarfe 7 na safe ba hujja ba dalilinta, Barrister kam tunda ya fita cikin daren bai sake dawowa gidan ba, hakan yasa Anut Amina ƙara gasgata zargin da take masa.
Yana durƙoshe gaban wani baƙin Mutum wanda ya cika jikinsa da layoyi kala daban-daban yace "Duk yadda za'ai ayi Sheikh ya ziyarci gidan yari bana son ya fito sai na samu cikar muradin rai na"
Bokan yay dry yace "Kaga wanda ya yarda da duniya ya manta da lahirarsa, ai tun tuni kayi sake ɗan zaki ya girma kalli nan"
Jikin Barrister na rawa yace "Me zan gani waye wannan kamar Deedat? Bayan an tabbatar min ya mutu"
Dry bokan yay yace "Wannan shi ne babban kuskuren da kayi, ka manta da baya gabanka kawai kake hange"
Dafe kai Barrister yayi yana jin wani gumi na keto masa, kana ya kalli Bokan yace "Mene mafita?" Bokan yace "Kaga ciki mai manta kyautar gobe, kasan abinda muka saba ai idan kana son aikinka yayi".
Ba ɓata lokaci Barrister ya zame wandonsa ya juyawa bokan baya, just like yadda maza da maza suke abinsu, suna gamawa Barrister yay waje kai tsaye kuma ya nufi Federal Court of Appeal, domin Lokacin tara da wajan Ashirin, yana hanya Alhj Kamal ya kirasa yake shaida masa babbar lawyern da zata tsayawa Sheikh, tashin hankali ya bai yana akan fuskar Barrister sai kawai ya juya kan motar zuwa wani waje daban.
Court ta cika sosai da mutane domin harda wanda ba'ai tunani ba, Fannah na ganin Ya Falta da Yakura ta saki kuka tana riƙe su, rarrashinta sukai kana suka nemi waje suka zauna, Anut Amina na gefe Granny sai share hawaye take, Mami da Bahaiyya na can waje guda, Fareeq kam baka iya gane halin da yake ciki. 11 dai-dai Al'ƙali ya buga guduma Court ta zauna, kai tsaye ya buƙaci ganin wanda ake ƙara ƴan sanda suka nunawa Sheikh waje yaje ya tsaya, kana akace ana neman mai ƙarar kamar daga sama a kaga Barrister ya miƙe tsaye ya nufi wajan shima, Al'ƙali ya karantawa Sheikh laifinsa idanunsa cikin na Fannah ya amsa da "Uhm, da cikin da mai cikin duk nawa ne" Al'ƙalin yace "Ke nan kana nufin da gske kai ne kayi mata cikin" kafin yay mgn Fannah ta miƙe tsaye tace "Ba haka bane, ƙarya yake, nice wacce na tilasta masa kwanciya dani bashi da laifin komai, yana son ɗurawa kansa laifi ne kawai" Guduma Al'ƙalin ya buga tare da tsawatarwa Fannah yace "Is an order, Kada wani ya sake mgn ba tare da bashi dama ba" rubuce² Al'ƙalin yay kana ya buƙaci ko wanne lawyer ya gabatar da kansa, kai tsaye Alhj Kamal ya gabatar da kansa akan shike kare mai ƙara, nan fa tunani ya sauya Anut Amina ta fara duba wacce akace itace Lawyer Sheikh, babu ita babu labarin ta, A hankali Deen dake cikin Court ɗin ba tare da kowa ya lura dashi ba, nan Shima ya fara juya idanunsa yana son yaga ta inda matar tasa zata bayyana, jikin Al'ƙalin na faɗin "Malam Sheikh Imam hamdan Balarabe ko dai baka da lawyer ne?" Miƙewa Deen yay Yana ɗan covering jikinsa da Alƙyabbar jikinsa, kai tsaye waje yay dan bai son idanun jama'a su dawo kansa, Anut Amina ma miƙewa tayi ganin haka yasa Hankalin Fannah tashi zata miƙe Yakura ta riƙeta, shi kam Sheikh ko a jikinsa idanunsa a rufe bakinsa na motsa amma rabin tunaninsa yana kanta, da yana da hali babu abinda zai hanashi rungome ta ya rarrashe. Al'ƙali ya hana duk wasu ba yana da aka bashi daga ciki hadda vedio'n hannun Mami wanda Alhj Kamal ya bayar, gyaran murya yay bayan ya ƙara tambayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login