Showing 96001 words to 99000 words out of 130248 words

Chapter 33 - Sirrin mu Complete by Nimcyluv.txt

25 Nov 2024

5982

Huda, bari dai nazo naji mgnar nan" ta faɗa tana nufar kitchen shiru Uncle Sham yay abin duniya duk yay masa zafi ga Sheikh har yanzu mai zo ba, wayarsa tai ƙara ya ɗauka ganin sunan Baba Baa'na yasa yay picking yana fidda murmushi Baba Baa'na ya kalli ɗan uwansa dake suma ya tabbatar yau jikin kawu Madu yau sai abinda hali yay yace "Shamsudeen! Jikin Kawo Madu ya tashi sai suma yake gashi yana ta kiran sunan ka" da sauri Uncle Sham ya miƙe tare da ɗaukan key ɗin wayarsa yana faɗin "Subuhanallah! Gani nan zanzo yanzu bari na siyi online ticket yanzu" Anut Amina tace "A'a Lfy dai?" Kasa ce mata komai yay sai rungome ta yay Murya can ƙasa yace "I love You! Ki kula da Huda" bai tsaya jiran me zata ce yay waje yana kiran driver. Sheikh tunda ya samu yaci Funkaso guda biyu wani bacci yay gaba dashi a saman sofa abinda bai taɓa yi ba kenan bacci da Zhur. Sai bayan asar ya tashe bayan sunyi Sallah suka nufi gidan Uncle Sham Anut Amina ta tabbatar masu Uncle Sham ya fita itama gata san inda ya nufa ba. Kai tsaye gida ya nufa yana zuwa ba kowa a Parlo kai tsaye part ɗinsa ya shige yana zuwa ya samu Mami zaune a saman kujera tana sharɓar tana ganinsa ta miƙe tsaye tare da faɗin "My Sweet Imam na shiga uku" ta faɗa tana faɗawa jikinsa.
22/10/2021, 10:36 - 🤔🤔: When All Is Gone
73-74


Da sauri Sheikh ya zare Mami daga jikinsa yana mata kallon baki da hankali, sai kuma ya sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya yana jiran yaji mene kuma zata faɗa masa nan gaba, Mami kuka ta saki tace "My Sweet Imam wlh mahaifinka baya tsoran Allah! Baya kulawa da haƙƙin Aure,Nima mutum ce kamar kowa amma bai damu da halin da nake ciki ba bai damuwa daya zauna dani ya kasance dani ba" sai kuma ta ƙara sanya kuka tana nufarsa ya ƙara ja baya still shanyayyun idanunsa na kanta, tace "Dan Allah My Sweet Imam ka taimaki rayuwata help me, ka taimaki mahaifiyar ji nake kamar zan bar duniyar" jajayen idanunsa ya juya mata wanda ya sanya Mami ta ƙara zaucewa tama rasa mene zatai, Yau Sheikh ya zama na Musamman ƙaunarsa ta musamman ce take yawo a jinin jikinta, musamman yanzu da yake yawo bisa ƙafafuwansa sai cikar halittar sa tafi fitowa tare da bayyana! Kasa mgn Sheikh yay sai Kallonta da yake da ido, Mami ta zube saman e ta riƙe ƙafafuwansa tace "Dan Allah My Sweet Imam ka taimaki Maminka, kai kawai nake dashi a yanzu kai ne kawai zaka iya bani abinda nake buƙata" da ƙyar ya samu ya fisgi Numfashinsa tare da buɗe daradaran idanunsa waje cikin nutsuwa da kamewa yace "Me kike so? Me Abba yay maki?" Ya faɗa yana lumshe idanunsa jine haka yasae Mami Miƙewa tsaye ta tsaya daf da Sheikh idanunta fess cikin nasa cike da soyayyarsa tace "Sweet Mahaifinka na daɗe rabon dana kasance dashi! Ina buƙatar Namiji yau ɗaya ka cikamin burina ka ɗauke min rashin mijina kuma mahaifinka,ka maye min gurbinsa pls Sheyykh" ta faɗa tana ƙara matsawa jikinsa, with much surprise Sheikh ya dinga kallon Mami yana son gasgata zan canta amma maganganun ta sun masa nauyi a kunne dama ƙwaƙwalwa, cikin rashin fahimta yace _"Pardon?"_ Murmushi ta saki tace "Haba sweet na! Kamar ba ɗan zamani ba kaga abinda nake nufi" ta faɗa tana ƙoƙarin rungomesa da sauri yaja baya yana zare idanunsa yace "kai! What? Ni kike tunanin zan aikata hakan God forbid!" Ya faɗa tana taune leɓansa, cikin dakiya tace "Eh! Nasan kaima kana buƙata shekarunka sukai kai tarayya da mace, na maka al'ƙawarin wannan zai zama *SIRRIN MU* our secret bazan taɓa bari kowa ya sani ba yau ɗaya" ta ƙare maganar taja shafa fuskarsa zuwa jajayen laɓɓansa, iska ya fesar kafin ya ɗan buɗe baki yace "Yasubuhanallah! Da matar uban nawa? Zina mafi muni? Da wannan ranar gwamma ba'a haifi Imam ba" soyayyarsa ta rufe mata ido tace "Wlh Sheikh saika kwanta dani, kasan how long dana kasance ina mafarkin samunka? Dan Allah kada kace a'a bazan iya hqr da kai" fiddo idanunsa waje yay yace "To fyaɗe zaki min kenan ko?" Da sauri tace "Wlh indai zaka tsaya" hannunsa ya harɗe yana ɗan sakin murmushi tace "ok go ahead" cikin sauri ta ƙarasu wajansa tana ƙoƙarin rungome yay saurin zare hannunsa ya zabga mata wani ƙyakƙyawan mari wanda ya kusa zata zauce tayi baya zata faɗi ya riƙeta yace "Nasan ne nake, koda ni ɗan iska ne na gwamma ce naje waje na nema da kuɗi dana kwana da matar Ubana, ki ɗauka na taɓa aikata hakan to wannan ƙaddara ce daga mai duka wanda babu wanda ya isa ya kaucewa ƙaddarar sa, dan haka ina jan kunanki tun ina kallonki da raguwar mutunci ki fice ki ban waje" kuka ta saki sbd masifar dake damunta duk abinda Sheikh yake faɗa ba abinda ta gane saima kunnuwanta da suke jiye mata wasu kalamai dana ban, cikin zafin nama ta tashi ta faɗa jikinsa tare da qanqamesa ta shiga ƙoƙarin zura hannunta a wani keɓantaccen shashe da sauri yay ball da ita tare dasa hannu ya jata zuwa bakin ƙofar Parlon sa yana fidda ta yasa key kana ya jingina da jikin ƙofar yana fesar da numfashi tare runtsa idanunsa wanda ya kejin sunyi masa nauyi ga wani zafi da suke masa. A hankali yaja jikinsa zuwa cikin bathroom yana jin wata kasala na shigarsa abubuwa da yawa sun masa yawa yama rasa wanne kalar tunani ya dace yayi, bayan ya watsa ruwa ya sanya Armless da 3gauther kana ya ɗauki ruwan zam², da gayan magarya ya buɗe ruwan tare da kafa bakinsa ciki ya shiga karanta sururin karya sihiri, sai da ya gama kana ya jijjiga tare da ajjiyewa gefe guda yana jiran ya jigo yaje har inda take ya ɗura mata idan taƙi sha. Fannah na kwance ta kasa cin komai sai rarraba idanu take ko mutsin kirki ba tayi ta zama kamar wata statue, wayar tace tayi ƙara sunan Ya Falta taga yana yawo da sauri ta ɗaga tare da mannawa a kunanta, daga can ɓangaren Ya Falta tace "Autar Mama kina lfy" kwaɓe fuska tayi tace "Ya Falta wlh duk a tsorace nake" Shiru Ya Falta tayi sai da Fannah tace "Lfy wai? Meke faruwa gaba ɗaya bni da nutsuwa dan Allah mene?" Kasa magana Ya Falta tayi sai kawai ta kashe wayar tare da riƙe Yana suka shiga rera kuka, baki da hanci Fannah ta saki ta shiga juyawa wayar ta kasa fahimtar komai bare da kirasu, saɓanin hakan ba sai kawai ta kashe wayar baki ɗaya. Uncle Sham na sauka a airport ya ɗauki mai taxci zuwa unguwar su Kawo Madu basu daɗe a hanya ba suka ƙarasa, bai ganin nawa ya bawa mai taxci ɗin ba ya nufi cikin gidan jikinsa na rawa duk da ƙoƙarin danne damuwarsa da yayi, yana shiga a tsakar gidan ya samu Baba Baa'na da Mama kolo sai matar Kawo Madu dake rusar kuka, dubansa yakai wajan Kawo Madu da yake ta faman suma an rasa mai yi masa komai, da damuwa a fuskar Uncle Sham yace "Yaya akai aka barshi a gida bayan yana cikin wannan halin?" Baba Baa'na yana share zufar yace "Wlh yaƙi bari ko taɓa shi ayi bare har akai sa wani asibiti, yace kai kawai yake son gani" Uncle Sham ya miƙe tsaye yace "Yanzu ganie shi kuma bai san inda kansa yake ba" Baba Baa'na yace "meye abinyi to?" Kai tsaye Uncle Sham yace "A samu mai taxci yanzu mu huce asibiti" Baba Baa'na ya miƙe kana ya kalli Mama kolo yace "Muje ina son mgn dake" Uncle Sham yay gyaran yace "Time is not our side, mu fara abinda yake gabanmu i think is better" Baba Baa'na yace "hkne bari naje muga" wayarsa Uncle Sham ya ɗauka ya shiga kiran Number Sheikh wacce Arjun ya tura masa amma baya ɗauka sai ringing take, tsaki Uncle ya sauke kana ya kira ta Arjun ya jita a kashe, Message ya shigayiwa Arjun da sauri kana ya tura yana gamawa ya cire sim ɗin ya sanya a cikin aljihun sa, wayar kuma ya ajjiye saman window.
Baba Baa'na yana fita ya nufi Babban titi ya daɗe tsaye kafin ya samu taxci ya shiga suka nufi unguwar da suke da zama, suna tafe amma tunani ne fal ransa, a wannan karan babu wacce take ransa kuma ta tsaya masa irin Mamansa _(FANNAH)_ tunaninta kullum yake damunsa, musamman da yake yawan mafarkinta tana cikin wani hali, dafe kansa yay ya shiga kiran sunan Allah yana jin kansa nayi masa nauyi a haka suka ƙarasa bakin ƙofar gidan, yana shiga suka kana Kawo Madu tare da sanyasa cikin mota, matarsa tace zata sukace a'a ta zauna, juyawa tayi sai kuma ta dawo da sauri tana riƙe hannun Kawo Madu ta saki kuka addu'ar da take son yi masa ta gagara faɗin komai.
Uncle Sham a gaba sai Kawo Madu da Baba Baa'na a baya a haka suka ɗauki hanyar zuwa babban prvt hospital.
A can cikin jejin Sambisa Tuɓe ne kwance cikin hali na rashin lafiya ko lafcecen hannunsa ya kasa ɗagawa sbd yadda ya kejin zafi da raɗaɗin ciwon na shigarsa, Tijama da jikinta ya fara janye wa ta kalli Tuɓe tace "Yakai jikana, ka sani cewa idan har haka tashi ba ka taimaki wannan ahlin ba, to kamar baka cikawa ƴar uwanka Airah burinta da muradin ranta ba, a yau komai zai iya lalacewa ba, wannan itace ranarka, wannan itace ranar! Ranar da zaka taimaki duban rayuwaka ranar da muke jiran zuwanta ka tashi kaje ka riskesu" ta faɗi mgnar ta riƙe masa hannu, numfashi Tuɓe ya fisga da ƙarfi idanunsa na tsiyayar da ƙwallar baƙin ciki da kuma damuwa da tarin tsanar kansa daya kasa cikawa ƙanwarsa muradinta wanda ta tashi dashi tun tana yarinya, kallon Tijama yay yace "Ya kaka ta! Ki sani a yanzu dani da gawa duk kusan abu ɗaya muke, babu abinda zan iya lokaci kawai nake jira, a yanzu wannan ahlin bamu suke buƙata ba addu'a da taimakon Allah suke nema"
Girgiza kai Tijama tayi a karon farko ta shiga zubda ƙwalla tace "Me kake nufi da haka Tuɓe? Kana nufin Mu zuba idanu akan wannan lukutar masifar? Kana nufin Mu zuba idanu a rama zuciyoyi biyun da suka mace a ƙaunar junansu? A yanzu bana damuwa da halin da Fatima take ciki, domin tana tare da Sheikh zai iya magance mata komai da izinin Allah, Amma Sheikh wa yake dashi? Kana tunanin zai iya shallake abubuwan da suke shirin samunsa, abubuwa mafi muni daga wajan wanda bai zato ba bai kuma yi tsammani ba? Haba akwai duba akan wannan lamarin" Murmushin ƙarfin hali Tuɓe yay yace "Haba Kakata, kada ki manta damu dasu duk Abu ɗaya yayi mu, Allah Ubangiji Subuhanahu wata'ala shi ya halarci mu, kuma nayi imanin duk zcyar da take da imani take kusanta kanta ga Allah ba zata taɓa tuzarta ba, al'ƙawari guda nayi maki wanda ko shine ƙarshen taimakon da zanyiwa Sheikh Imam hamdan Balarabe Tabbas zanyi masa"
Tijama ta kallesa tana sakin Murmushi tace "Tabbas wannan bawa na Allah bazai taɓa tuzarta ba, Sheikh Imam hamdan Balarabe zakai farin ciki farin ciki na har abada, gudan jinin ka zasu zama abin alfaharin ka, wata rana sai an samu Babban Malami kuma magajin mahaifinsa"
Sheikh na kwance yay rigingine idanunsa na saman bedroom ɗinsa, kana kallonsa zaka fahimci kamar tunani yake amma a zahiri ƙwaƙwalwarsa a toshe take ya samu wani irin shock wanda bai taɓa samun kansa a ciki ba, Miƙewa tsaye yay yana gyara zaman 3gauther ɗinsa yana tafiya cike da nutsuwa da kamala, gashi dai yau ranar farin ciki ce wacce ya kamata ace kowa yana farin ciki, sbd shan ruwa da akai _(ƙaramar Sallah)_ cikin nutsuwa da kamewa haɗi da cikar haibarsa ya ƙarasa bakin fridge kana ya durƙosa dai-dai tsayin fridge ɗin ya ɗauki bottle water mai sanyi tare da Apple guda ɗaya, yana gamawa ya nufi babban Parlo, tunda ya ƙara so wajan Fannah taji ranta ya fara ɓaci hakan yasa ta shiga sakin tsaki tare sauke nauyayyiyar ajjiyar zcy Granny dake zaune ta ɗura ƙafa ɗaya kan ɗaya ga plate ɗin farfesun kaza wanda yaji kayan ƙamshi sai tiriri yake akan cinyarta, kallon Fannah tayi tace "A'a Allah ya baki hqri, kyaci kanki yau naga jaraba, daman ance mace da ciki akwai iya neman mgn" Mami dake wajan ta saki wani shu'umin murmushi kana ta maida kallonta ga Sheikh wanda kwarjininsa ya cika mata ido "Yooo duk mai ji da masifar sa basai dai ta ƙare a kansa ba, fisabilillahi?" Ta faɗa tana kallon Bahaiyya da wacce take latsa wayarta da alama ita takewa tambayar, a hankali Sheikh ya ɓalle murfin bottle ɗin tare da kafawa a bakinsa ya fara sha yana lumshe gajiyayyun idanunsa Granny tace "Amina na nan zuwa ita da koɗaɗɗiyar ƴarta" Sheikh ya kalli Granny tana ɗan shafa ƙirjinsa yace "Uhm! Ba kyau fa" ya faɗa yana zama kujerar dake farcing Fannah kana ya maida hankalinsa kan Film ɗin da ake a telemundo na _When All Is Gone_ taɓe baki yay a ransa yana faɗin "Iskanci everywhere" kana ya sauya tashar zuwa CNN, ko inda fannah take bai kalla ba bare tasan cewa ya damu da ita, amma ƙasan zcyarsa wata iriyray azaba yake sha, sbd tafarfasar da take masa akan so da ƙaunar _Zahraaansa_ miƙewa Fannah tayi ta nufi kitchen tana tafe a hankali buɗaɗɗan hips ɗinta na yawo ta cikin Laffaya data sanya golden da ratsin ruwan huda, ƙafarta fara tass domin ta daɗe rabonta da lalle, daman niyyar ta idan taje gida Ya Falta ko Yana wasu suyi mata.
Kitchen ta shiga idanunta yay raurau kamare zatai kuka, jingina tayi sbd sarawar da kanta yake mata, mgnar cikin ta faɗo mata, cikin sanyin jiki ta sanya lallausan hannunta a saman cikin tana son gasgata mgnar cikin amma tunaninta da zcyarta sunƙi bata haɗin kai, ganin tana son zaucewa yasa ta shiga haɗa lemon juice domin shine abinda tafi so a yanzu sbd bata wani laulayi.
Granny ta kalli Sheikh tace "Shi Campanin zaka rufe? Bisa wanne dalili kenan?" Ta gefen idanunsa ya kalleta kana ya sauke Ɓoyayyiyar ajjiyar yana ɗan saita kansa idanunsa a hanyar kitchen ɗin yace "Kawai fa, ana samun kuɗi sosai amma bana ra'ayi?" Mami ta kalli Granny sai kuma ta sauya yanayi tace "na ɗauka shine Company da Barrister yake kula maka dashi?" Bai ce komai ba ya miƙe tsaye tare da nufar kitchen yana tafe yana faɗin "Granny bari na samu cup of coffee" yana faɗin haka ya shige cikin kitchen ɗin rufe ƙofar yay ganin bata juyawa ba yasa walking slowly ya nufi inda take tsaye, hucin numfashinsa mai fidda wani dadɗan ƙamshin ya fara dokanta idanunta ta runtse, tana jin ɓacin ranta na ƙara yawa, cikin nutsuwa Sheikh ya danya hanunsa a ququnta tare da manno bayansa da nata, a tare suka fidda wani numfashi, Fannah kam ta ɗauki al'ƙawarin ko kala ba zata ce dashi ba, kansa ya ɗura a bayanta yana jin nutsuwa na shigarsa a hankali ya fara ware Laffaya jikinta ya ƙyakƙyawan bayanta ya bai yana rigace half vest a jikinta, slowly ya fara ƙasa da hannunsa zuwa ramin cibiyar ta, bakinsa daf da kunanta yace _"Zahraaah"_ ya faɗa yana fesa mata Numfashinsa a kunne tare da sakar mata fitananniyar sumbata ƙasan kunanta, Wheel hannunsa na yawo bisa cibiyar ta. Arjun yana tsaye a kitchen shida Aliyah tana haɗa masa tea yaji wayarsa tayi ƙara alamar notification ya shigo, sassauta riƙon da yay mata yayi kana ya ɗauki wayarsa yana ƙoƙarin buɗe passward ɗin Aliyah ta saki ihu sbd ruwan zafin daya zubu mata a ƙafa a rikice ya saki wayar ta faɗa jikin jug ɗin shayin take ruwan shayin ya fara shiga cikin wayar.
Drip guda uku aka sanyawa Kawo Madu sai manyan injection da akai masa, anso bashi gado amma Kawo Madu yaƙi yarda, ana gama yi masa dukkan retirement ɗin daya dace ai masa aka samu ya farfaɗo yaji Kwari, Sannan suka nemi kai taxci wajan ƙarfe goma na dare suka ɗauki hanya, Kawo Madu ya kalli Uncle Sham kana ya riƙe hannunsa yace "Shamsudeen ka kira min Imam ina buƙatar ganinsa, babu da wani lokaci" jinjina kai Uncle Sham yay yace "In sha Allah ka kwantar da hankalinka" Kawo Madu ya kalli Baba Baa'na dake gaba shida driven taxci ɗin yace "Lokaci yayi da Imam zai san cewa...," Bai ƙarasa maganar ba sbd salatin da Baba Baa'na ya saki shida drive, Uncle Sham ya ɗaga kansa da sauri ya runtse idanunsa yana karatu sunayen Allah da kuma kalamar shahada, wata ƙatuwar tirela ce irinta babban Company tayo kan motar su Uncle Sham nan take kuma taxci ɗin tai ƙarƙashin tirelar, lokacin da taxci ɗin ta shige ƙasan motar ji kake wani ƙuuuuuuuuu tassss kawo nan su Uncle Sham suka fashe gaba ɗaya.






Sirrn mu isn't free book contact me to subscribe 08119237616








NIMCYLUV✍🏽
22/10/2021, 10:37 - 🤔🤔: Emotional
75-76






Not too long mutane suka zagaye titin inda accident ɗin ya faru, tashin Farko Baba Baa'na aka fara cirowa lokacin tuni rai yay halinsa, sbd cikinsa daya fashe ta hanyar tayar motar data taka cikinsa, daga Baba Baa'na sai Kawo Madu shi babu abinda ya same sa amma yana kwance samɓal kana Kallonsa kaga matacce, Uncle Sham ba kowa ya iya tsayawa yaga gawarsa sbd munin da jikinsa yay banda jini dake gudu babu abinda yake yawo, kansa fita yay cif.
Haka driven su Uncle Sham shima yaji rauni gaba ɗaya babu wanda ya tsira da ransa kafin kace wani abu an kashe titin gaba ɗaya ana jiran zuwan Ambulance, Ambulance na zuwa aka ɗauki gawar su Uncle Sham, securities kuma suka fara bincikar motar Company abun mmki babu driven babu dalilinsa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login