Showing 24001 words to 27000 words out of 105295 words

Chapter 9 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6095

naga duniya tow ce maka aka yi zan kula ka ne"
"Ai kuwa da kin kula shi da kin ci uwaki"
Juyawa tai tana kallon yarinyar da bata wuce tsarar su Abigail ba.
Murmushi tayi mata sannan ta ce mata.
"Wai ke da ni kike?" Ta tambaye ta,
"Sai ka karci kan uwarki zaki fahimci da wacce nake."
Juyawa Easter tayi tana kallon gefe da gefe, kafin ta ce mata.
"Eh tow Kya karci ta uwatai" sannan tayi gaba abin ta, haka take bata san tsoro ba, ba ta san fargaba ba. Abu daya ta sani matukar tana da gaskiya wallahi babu me tab'a lafiyarta.


Shan gabanta yarinyar tayi tana faɗin.
"Dan Ubanki kafirin nan, da ya butulcewa abin bauta, kar na kuma ganin ki."
"Tauuu" ta dauke ta da mari, rike kuncinta tayi tana kallon Easter da ko a jikin ta.
"Yo da nasan wancan abin yana kula ki, dan kan Ubanki ai da bai ishe ni kallo ba, wawuya me abin faɗa" da matukar kunya a samu mace a cikin garin Nahara tana fada akan Namiji, sabida girmama Jaruma Nahara, suna da wani irin alfahari akan kasancewar su mata, babu namijin da ya isa su yi fada da shi, koda kuwa kwace maka shi aka yi wannan jijji da kai da alfaharin Jaruma Nahara yana jinin su.
Tun da ta tsinka mata mari tayi tafiyar ta, shima Matashin tafiya yayi ya barta cikin kunya da tashin hankali.
A hanya kuwa daukar kara tayi tana tafiya,
"Lati kar ka min kome, kasan matukar ka d'aga min fatarina tsinuwa da masifa zata auku na hada ka da Jaruma Nahara kar ka min kome" ware idanu tayi tana kallon wurin bishiyar tsamiyar da yayi duhuwa, tana kuma jin muryan Abigail.
"Ba wani abu xan yi ba, gogawa zan yi ke kamar baki waye ba. Ai idan muka fita wajen Nahara ba karamin dadi muje ji ba mata da kan su suke zuwa mana"
A hankali take takawa tana jin muryan Lati, a hankali ya leka hasken farin wata ya haska ko ina amma ban dasu.
"Su waye ne a wurin?"
"Na shiga uku! Mayyar nan ta gan mu" inji Abigail ta ture shi tana daura fatarin ta, da kuma matarin Kirjinta.
Fitowa suka yi, ta saka hannu a baki tana mamakin su.
"Me za a goga? Kuma a iya za a goga?" Ganin bata fahimci kome ba yasa suka mai da ita shashasha na gaske.
"Ai babu kome kawai jin ciwo tayi nake son goga mata ganyen tsamiya" tab'e baki tayi, daga haka ta wuce abin ta. Janyo Abigail yayi jikin shi yana cewa.
"Ki san yadda zaki yi amma ba wani abu bane, duk fada ake da camfi"
Juyawa tayi ta ga yadda suke manne da juna.
"Na shiga uku! Me kuke yi ne haka?"
Sake ta yayi yana me cewa.
"Ina duba ciwon ne" bata iyawa da takaicin su, dan haka ta nufi gida abinta.
--
A daren Magaji yana kwance a bayan Mama Uwar, har barci ya fara daukar shi ta ce mishi.
"Ban fahimci makomar Wabi da Lati ba, shin ba za a yanta su bane?"
Dan ita a tunanin ta, ai auren Lati da Wabi shine abin da zai hana Kyauta zama wani abu.
Bude idanun shi yayi sannan ya ce mata.
"Ki yiwa yarki fada kar ta zama wutar da zata tadda mana fitinar da bamu da ruwan kashe shi"
"Ban gane ba Magaji?"
"Eh haka na faɗa." Ya juya abin shi bai kuma tanka mata ba, haka ta kwana cikin ranta a kudire da mugun niyya.
Asubar farko, ta nika garinta sai gidan Nahira.


Yana zaune a dakin shi na aiki ta same shi,
"Nahira meye kace akan yar kishiyata?"
Ta tambaye shi,
Lumshe idanun shi yayi yana motsa bakin shi.
Kafin ya bude idanun shi.
"Ban san me zai faru ba, sai dai goben su tana hannun abin Bauta. Bai zama dole sai na duba yanayin su ba. Sai dai ita Yar kishiyar ki zata iya zama farin ciki ga al'ummar Nahara"
"Y'a ta fa?"
"Ban san kome akan ta ba, sai dai ta kiyayye abin da take yi ita da Lati!"
"Karya kake Nahira! Ita sai ta zama fitilar farin ciki ga Al'ummar Nahara. Idan kuma kana ganin zaka iya tow ga fili ga me doki"
"Bakin cikin mutum shi yake kashe shi" daga haka ya nuna mata hanya.
Fita tai tana jin kamar ta kona gidan Nahira ta huta, tunda ya sake maganar ya shiga kunnen Magaji tayi imani cewa ba zai bar yar shi haka ba.
Dan haka koda ta isa gida, ta samu yaran suna ta diban ruwan amfanin gida.
Kallon Easter tayi bakin ciki da hassada ya cika ranta, yarinyar wata irin boyayyen halitta ce da ita, idan har nan da shekaru uku zuwa hudu, ta zama cikakkiyar mace, tabbas Yarta lokacin ta tashi aiki.


Shi yasa duk rintsi ba zata, tab'a barin ta tayi aure ba sai Wabi tayi taga inda Wabi tayi, kafin tayi nata wannan shine alwashin ta.
A can rafi wurin diban ruwa, Lati ne yazo yana jiran Abigail wato wabi.
Tana zuwa dake tasan da zuwan shi ta cewa Easter.
"Kin ga ki tafi ki dawo, kafin nan nayi wanka sai ki zo min da wasu kayan sawan"
"Hmm" ta bata amsa,
Haka ta dauki tulun ta nufi hanyar gida, ita kuma Abigail ta bi inda Lati yake mata magana.
Tana isa wurin shi ya amshi tulun.
Ya ajiye mata.
"Ina Kyauta?"
"Ta tafi, kafin ta dawo ai zaka gama" ta fada tana kallon shi.
"Eh amma ai kinsan ba zata dawo da wuri ba ko?"
"Eh ba zata dawo ba."
"Tow" ya janyota jikin shi, sannan ya shiga tab'a ta, ta ko ina.
A tsorace ta ce mishi.
"Kace min camfi ne babu wani abin da zai faru ko?"
"Ke babu abin da zai faru duk karya ce"
Ya zare fatarinta, ya shiga bin tsakanin cinyoyinta, wani irin kuka ta saka da ƙara.
Toshe mata baki yayi, shi ba yau ya fara ta'adin shi ba, amma ita ce mace ta farko da ya samu a matsayin cikakkiyar mace.
Ganin zai hallakata yasa ta fara kokarin kwacewa daga jikin shi.
Ai kuwa ya saka mata karfi baki daya, ta koma ta mike mishi.


Lokaci guda garin Nahara ya koma wani irin duhu da yanayi me ban tsoro, tashi yayi bayan ya gama biyan buƙatar shi ya shiga tattab'a. Amma iya bata motsi, ganin duhun har tafin hannun shi baya gani yasa shi, tashi a guje ya bar wurin duk da ba haka yaso ba.
-
Bude idanun shi yayi yana kallon garin.
Kafin ya hango Easther da take tafiya a tsorace.
_Nan da wasu yan kananan Lokuta kaddran yaranka zata sauya. Ita wannan babban al'amari yana bibiyarta Yar Uwarta kuma ban san me zance ba! Amma tabbas akwai abubuwan da ba kowa zai sani ba_
Bin ta yayi da ido kamar zai kirata, kafin yayi tunanin haka tayi nisa,
A bangaren Nahira fitowa yayi yana kallon yadda garin yayi duhu.
"Sun karya mana tsari da kariyar mu! Bamu da hanyar tsira." Ya faɗa.,


A hankali garin ya fara washewa, ya koma kamar da.
Ganin garin yayi haske yasa ta, nufar rafin anan tayi ta niman Wabi bata ganta ba. Sai a can ta hango kafarta.
Da sauri ta isa wurinta, turus tayi a tsorace ta sake ƙara zata juya Abigail ta riko kafar ta.
"Na hada ki da abin bautar Baban mu, ki rufa min asiri, kar ki fadawa kowa ki min alkawarin haka" cikin tsoro ta ce mata.
"Nayi me yasa miki?" Ta tambaye ta tana matsawa jikinta.
"Ya cuce ni yayi min dadin baki, yar uwata Easther ki min alkawarin ba zaki tab'a tona min asiri ba."
"Nayi miki babu wanda zai tab'a sanin haka"
Ruwan tulun ta dauka ta wanke Jikinta, suka nufi rafin tayi wanka suka koma gida, lokacin da suka isa gida, nan take bawa Mama Uwa labarin karya wai faduwa tayi a rafi bata ganin gabanta har ta fada akan wani kututture ya suke mata gabanta.
"Nice na taimaka mata ma"
Gyada kai Mama uwa tai, amma bata yarda ba.
"Kyauta ki boye maganar nan kar ki yarda ki gayawa kowa kin ji"
Gyada kai tayi tana tausayin Yar Uwarta.
Haka Mama Uwa suka yi ta kula da Abigail babu wanda ya sani.


Zuwa yamma likis, ta warware kamar babu abin da ya faru da ita,
Suna zaune a dakin su ita da Easther aka shigo gidan aka fada musu sakon me gari da Nahira.
"Ana kira ga Iyaye da Yan mata matukar sun san akwai abin da yarsu tayi toh maza su turata gidan Nahira a kashe ta. Domin tare abin da zai faru a gaba."
Riko hannun Mama Uwa tayi cikin tsoro.
"Mama Uwa!"
Girgiza kai tayi.
Zuciyar su baki daya a rabe yake, suna shiga cikin dakin su. Ta kalli Easter. Zubewa Mama Uwa tayi a gabanta tare da hada hannunta dukka biyu.
"Easter ki taimaka mana kar na rasa Wabi! Nasan boye min gaskiya ku ka yi...
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
+


234 803 879 6871 zuku iya tuntubar Number nan.....


*A Hausa historical Ancient*
24/Nov/2022
#Mai_Dambu








Wacece Easter?
500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu


*A Hausa historical ancient
#Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*
START YOUR GOLDEN HOURS NOW.... 08130269641 HURRY UP DON'T MISS IT...


Mai_Dambu...
BABI NA SHA BAKWAI (17)


Baki daya idanunta da ƙwaƙwalwarta ya tsaya cak da aiki, tana zaune ne amma idanun ta da tunanin ta abu daya suke ta maimaita mata. Wato kashe Baban su da Nahira tare da dan Gidan Nalado. Maza uku da suka nime kare ta, domin kar a kashe ta a kan idanunta aka kashe su.
Duk gaggara da rashin jinta, sai da ta kai tana tsanar kanta.
Fisgo kafarta badakaren yayi da karfin tsaya ya fara kokarin zare mazargin wandon shi. Tare da jan ta gefen da babu hayaniya, ita kuwa sai bin shi take, yana kai ta wurin ya ture ta ta fadi ƙasa kanta ya bugu da wani dutse, "dumm!" Kan ya mata tana jin yadda yake ratsa cinyoyinta da abin da bata san meye shi ba idanunta a rufe suke rub. Sai dai jin karar da taji da zubar ruwa me dumi yasa ta bude idanunta.
Tana kallon gawar badakaren wanda ya zube a jikinta matacce. Ajiyar zuciya ta ja daga nan bata kuma sanin me yake faruwa ba, sai da rana ya kwala sosai. Ta bude idanunta tana kallon inda suke a katon jirgin ruwa suke.
A hankali ta tashi zaune tana jin Jikinta kamar an daureta, ga kayan da bata san irin shi ba, an daura mata.
Kallon matan garin Nahara yasa ta rarrafawa zata nufi wurin su.
"Tsinanniya mara albarka karki zo inda muke kar mu ma rashin albarkanki ta shafe mu."
Inji Mama Uwa,
Cak ta tsaya tana kallon su, koma tayi ta kwanta tana haki, tare da rungumar kafarta tana kuka.
Sautin kukanta ne yasa Sarkin Yaki takowa har inda take, ya durkusa ya mika mata wani gurasa.
D'ago kai tayi tana girgiza kanta.
"Amsa kici" ya fada yana mika mata, tashin hankali da damuwar da take ciki ya ishe ta, ko yunwar bata ji.
Amsa tayi ta ajiye a gefenta.
Tana ganin yadda aka bi sauran matan da b'antaren gurasan,
"Waɗannan matan baki dayan su, mallakar Deehar ce kar wani yayi gigin tab'a koda hannun su ne, domin suna karkashin kulawar Masarautar Deehar ce. Kamar yadda ya faru da Fairoz haka zai faru da duk wanda ya kusanci daya daga cikin su, wannan sakon Galadima ne da Fulani Babba."
"Mun ji, mun amince." Suka fada baki dayan su.
Mika mata goron ruwa yayi ta shige abin shi, domin bata wuce sa'ar Yar shi Rayyanah ba. Ruwan tasha ta wanke fuskar ta.
Sannan ta kalli yadda suke cin gurasar hannu baka hannu ƙwarya, sannan ta fahimci ita yar gata ce domin ba a daure ta ba, kamar su yadda aka saka musu igiya aka daura su.
Rarrafawa tayi ta turawa Abigail gurasarta. Sannan ta koma ta kwanta. Kafin ta mike tana tafiya a hankali, har ta isa bayan jirgin. Tana kuka kamar ranta zai fita, tare da dukar kirjinta. Tana kallon yadda suka bar garin Nahara wuta naci da alamu an shafe ko ina babu wannan Albarkan da ake da yakinin suna da shi.
Jin shashekar kukan ta yasa shi lekata.
Yana ganin yadda ta rike kirjinta tana kuka.
Yasa shi fitowa har inda take.
"Yarinya me yasa ki kuka?"
"Garin Nahara" ta fada tana kallon shi.
"Me yasa kuka mana haka? Meye muka muku da zafi haka? Bamu tab'a cutar da kowa ba, hatta dabbobi suna da ikon tafiyar da rayuwar su yadda suke so me yasa?"
"Shekaru ashirin da takwas, an kawo wani mara lafiya garin ku, tun daga lokacin ake son sanin ta ina za a karya garin ku, domin laifin su na amsar mara lafiya"
Jiri ne ya kwashe ta kamar zata fadi.
Ta koma ta zauna a ƙasa, sai hawaye shar da yake zuba mata.
"Laifin mu kawai taimakon da Nahira yayi?" Ta tambaye shi tana kallon shi.
"Ba shi ne laifin ba, akwai wata gaskiyar da ya boye akan Yaron, dan haka ake niman shi a lokacin ruwa a jallo, ba a samu shiga Nahara ba. Karshen Yaron mara lafiya ya mutu."
Wani irin razana tayi tare da ja baya.
"Shima ya mutu?"
"Eh Deehar bata daukar reni, sannan bata daukar ganganci. Tana aiki ne bisa fasalin da ta zama Yarinya ta kar ki kara tambaya ta"
"Kun kashe min Babana! Kun kashe Nahira min, sannan kun kashe shi a daidai lokacin da ya bada rayuwar shi domin ceto na! Idan har na shiga ina kace toh Shegiya aka haife ni " kafin ya fahimci abin da take nufi, ta fada ruwa tsundum.
"Ina kuke!" Da gudu dakarun suna iso, dan haka suka fada ruwa, domin ceto ranta.
Koda suka fada tasha ruwa sosai, cikinta yayi tirtsitsi, tana fitowa yasa aka kunce wasu mata biyu, suka matse cikinta, sai ga ruwa ta hanci da baki.
Sai da tayi ta aman shi, sannan barci yayi gaba da ita. Lokacin da ta farka sun isa garin Deehar, a bakin ruwa suka tsaya, shi yasa aka tashe ta.
Ganin wata duniya, da bata tab'a ganin shi ba. Yasa ta koma zata lumshe idanu, Abigail ta ce mata.
"Wasan kwaikwayon ya isa haka." Sake bude idanun tayi, taga suna mikewa, sai lokacin ta lura itama daure take da igiya hannu da wuyar ta, suna shiga kofar garin aka fara rangad'a gud'a, ana jifar su da tumatur, ana musu bakar magana.
Kafin su bar cikin talakawan Deehar, an wulakanta su, haka suka wuce har zuwa lokacin masarautar Deehar.
Rike hannun Abigail Mama Uwa tayi tana faɗin.
"Na gaya miki, kina da farar ƙaddara, shi yasa muka samu kan mu da shigowa cikin Deehar, idan har muka yi biyayya toh wata rana sai kin haifa mana jinin gidan nan."
Tana jin su bata yi mamaki ba, domin tun a jirgin ruwa ta fahimci bata da kowa sai ita ɗayan ta.


Ai kuwa suna isa cikin Masarautar, aka fara nuna musu hanyar da zasu nufa.
Yan mata aka raba su da iyayen su, tare da nuna musu wani hanya.
Su kuma iyaye mata aka nuna musu hanya.
"Mama!" Abigail ta fada da ƙarfi, tana niman isa wurinta.
Janta aka yi tare da labta mata bulala, ihu ta tsalla, wani bafade mara imani da tausayi ya daka mata tsawa.
Hadiye kukan ta.
Easter ta riko hannunta, suka nufi hanyar da ake nuna musu.
"Kyautah Mama Uwar!"
"Kar ki samu za a dawo mana da ita." Ta fada tana share mata hawaye.
Haka suka nufi wani babban gida me ɗauke da wata ƙatuwar zaure.
Sannan aka watsu kamar dabobbi.
Kaya aka kawo aka bisu da shi ana basu, kafin aka ce musu.
"Ku tashi, kowacce ta ajiye kayan ta, sannan akwai zanin wanka a can dakin ku yi tafiyar jerin gwano, zaku kowacce ta dauka ta dawo wurin kayanta"
"Toh"
Haka suka yi ta shiga dakin, suna daukar zanin wankar me kyau da kauri.
Sannan suka dawo wurin kayan su.
Suna tsaye aka nuna musu wata ta kofa.
"Zaku shiga wancan dakin, za a duba yan matancin ku!" Kallon juna suka yi, Abigail ta rike hannun Easter hankalinta a tashe.
"Kyautah"
"Meye?" Ta tambaye ta,
"Zasu bude gaban mu ne su duba,"
"Toh ba shi kenan."
"Kyautah ki taimaka min, kar su gane ni"
"Wannan Alƙawarina ne!"
Haka yan matan suka yi ta shiga, sai da aka zo kan Abigail,.tana shiga da Easter ta fasa wata irin kara, ta zube a wurin tana hauka da bori. Dole ba a duba Abigila ba, aka turota masu dubawan suka leko.
"Wacece yar Uwarta."
"Nice" Abigail ta fada Jikinta yana rawa.
Ta kama Easter ta kaita gefe, ganin murmushi akan Abigail yasa ta, fahimtar ba a duba ta ba. Dan haka ta ware ta koma layin karshe.
A hankali yazo kanta.
Tana shiga suka sakata ta cire kayan jikinta.
Sannan suka bude kafarta, tare da saka wata karfe me kama da halittar da namiji, a tsorace.
Sakamakon azabtar da ta ji.
Haska wurin suka yi, suka samu kofar a rufe take da angurya yayi kaca-kaca a wurin.
"Tashi ki daura zanin wankar ki"
Tashi tayi a hankali.
"Kande ita zamu sakata a cikin sunayen masu zuwa bangaren waye kenan?"
Kallon Easter tayi sannan ta ce mata.
" A kaita shashin Yarima Shehu, dama suna niman me yiwa Fulani Aliyah hidima! Sauran da daya ta dazun a kaita bangaren Fulani Babba, yan mata uku a kaisu bangaren Kilishi. Guda uku akai bangaren Magajiya. Sai biyu a kai su ɓangaren kwarkwarah Biyu Zinaru da Zuwairah. Sauran a duba kosassun cikin su a kai su ɓangaren Yarima Arshan a can zasu yi ta mishi hidima."


Duk da an raba basu, amma sai da aka banbanta su daga kayan sakawan su.
Abigail an basu koriyar doguwar riga. Sai wasu jajjayen riga, Easter an bata kalar zinari domin kalar ita ɗaya ce da shi.
Sannan aka tara su a wuri guda.
"Zaku fara aiki daga gobe! Sannan dokokin masarautar Deehar, ta haramta Sata, idan kayi sata za a yanke maka hannu. Idan kabi namiji matukar ba wanda aka zab'a maka ba, sai an maka bulala, idan aka kama ka da laifin cin amanar masarauta za a kashe ka. Idan aka same ka da ɗaukar zancen wani bangare a kai a kai wani bangaren toh a kai ka gidan Yari, sannan kowacce ta zauna inda aka kaita ban da yawon duba inda aka kai yar uwarki, ban da Gulma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login