Showing 18001 words to 21000 words out of 105295 words
Chapter 7 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
iyalin shi, y fitar da wasu daga cikin iyalin shi. Musamman karamar matar shi da tsohon ciki, tare da babban da babban amintaccen bawan shi da dukiyar da zasu rike, dama Allah bai bashi haihuwa da yawa ba, yaran shi uku ne kuma duk mata ne, sai wannan Amaryan da ya aura bayan rasuwar Hayatudeen, tana da Yaro kamar Abdullahi, duk da Waziri yaso ya hada su, sai Kilishi itama bata da kishin kai sai yadda aka yi. Sai wacce take bin kilishi tana aure a masarautar Karaye na kasar kano, sai daya tana aure a masarautar Bauchi.
Iya su ya haifa, sai Amaryan da yayi aura ita tana da d'a namiji dan itama bata haihuwa a kai a kai.
Koda suka masarautar, anyi nasarar kamata amma Amintaccen bawan Waziri ya samu guduwa da Abid, domin lokacin da aka kawo musu farmakin ita tace su tafi kawai Abid ya tsira. Ita zata koma wurin mijin ta.
Koda aka kawo ta, dare yayi dan haka Waziri bai sani ba, yana can wurin su Abdullahi domin yana da labarin abin da zai faru a cikin wannan daren.
"Ya Musa ka ɗauke su, ku bar Masarautan Deehar, don Allah ka kula min da su, kar ka dawo sai lokacin da ya bukaci sanin asalin shi."
Fita suka yi ta kofar baya, sannan suka fara gudu,.a lokacin an kawo hari gidan, waziri suka samu dan haka suka tasa kewayar shi zuwa fada.
Anan yaga iyalin shi baki daya, bakin cikin da takaici ya cika ran shi.
"Meye na iyalina a cikin wannan al'amarin?"
" Ina Abdullahi da Kubrah suke?"
Galadima ya tambaye shi.
"Ban sani ba" ya basu amsa.
"Toh ba damuwa haka ma Arziki ne, ku musu yankan rago har itama me cikin can!"
Tare matar shi yayi yana faɗin.
"Zaku kunco yakin da zai kare nan kusa ba. Kar ku fara"
"Garkuwa ji wai kar mu fara, uban waye ya ce maka ba zamu iya tare yakin ba? Ai sai mun shafe ƙabilar noye hankalin mu zai kwanta, dan haka ku shiga gida gida, duk inda kuka san yan ƙabilar noye suke a fitar da su, kashe su."
"Mai gida! Ka gaya musu inda suke don Allah kar a taba wanda bai ji ba bai gani ba."
"Ko na gaya musu ce miki aka yi zasu bar su ne? Ai ba zasu bar su ba. Domin zuciyar su cike take da zalinci babu abin da zan gaya musu "
Haka suka tasa keyar su har waje, kafin tsakiyar dare, an tara kabilar Noye baki daya, sai da aka kwashe majiya karfin sannan aka daure su wuri guda, aka watsa musu mai da ya yi. Suka kunna musu wuta.
Matan su kuwa a wurin akai ta keta alfarman su,.ana kashe su.
"Ku kamo min matar waziri itama mu d'anna irin nata."
Tsayawa yayi a gaban matar shi da ta gama tsorata.
"Ba zan iya kallon kuci zarafin al'ummar Noye da mata na ba, zai fi kyau idan kuka kashe ni sai ku baza zalincin ku."
D'aga hannu Galadima yayi daga can nesa aka wurgo wata irin mashi, ta huda kirjin Waziri sannan suka nufi matar shi, tsoro da tashin hankali ya sakar mata da jini kamar an yanka dabba, ganin halin da take ciki yasa Garkuwa yana zuwa ya sare kan ta.
Zalinci me suna zalinci aka yi shi a wannan daren, sannan suka saka nimo musu Abdullahi, domin sun san basu bar cikin masarautar ba.
Dan haka suka nufi cikin masarautar, haka suka yi ta niman su,.kafin suka hango wata barauniyar hanyar da ba a cika bin ta ba, dan ta shekara kusan dari, sannan ita kanta hanyar tana cikin dajin kwankwamai ne, dan haka suka bi wannan hanyar.
Dajin kwankwamai wata irin daji ne da take dauke da wasu miyagun Aljanu da dabbobi, duk da an rufe kofar ne tun kafin hawan sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, lokacin mulkin Abdullahi Shehu Noye, aka rufe hanyar tare da niman tsarin Allah ya kare masarautar da miyagun dabbobin da Aljanun.
Sai akayi kofar karfe aka rufe hanyar, sannan aka manta da wannan barauniyar hanyar, tsawon karni guda.
Sai yau Waxiri ya samu mukulin kofar ya bawa Ya Musa. Dakyar kofar ta bude, lokacin da ta bude wani irin busashen iska ne suka shaka mara dadi da ni'ima, wadda ya haifar musu da jin ƙishirwa me tsannani.
Rufe kofar suka yi, sannan suka nufi cikin dajin tare da dawakan su, a guje.
Duk da dare yayi, Abdullahi yana tare da Ya Musa.
Kubrah tana ita ɗaya, haka suka yi tayi ta gudu,. Sai da suka yi tafiya me tsananin a cikin duhun dare da duhun dajin. Kafin suka fahimci ana biyo su.
Harbin su aka shiga yi tare da niman kashe su, amma basu samu nasara ba, sai akan Dokin Kubrah, wurgi yayi sa ita, dole Ya musu ya ja linzami, ya tsaya cak sannan sauka tare da riko hannunta, yana goye da Abdullahi.
"Ya Musa ka tafi da shi kawai,.don Allah ya tsira domin ya wanke dattin da yake Deehar"
Sake Harbin aka yi ta kwala ihu, tana me zubewa kasa.
"Ka tafi nace" ta fada cikin azabar da take ji da gudu ya nufi dajin, harbin shi suka yi da baka, sai da ya sake wata irin kara, sannan suka cigaba da gudu, yana jin ihun ta da kakarin ta. Bai tsaya ba. Amma yana jin dumin jikin Abdullahi da ruwan da yake sauka a kafadar shi.
Duk da baya gani amma jikin shi ya bashi,.wani abu ya same Innar shi. Haka suka cigaba da gudu, dake yana rungume a kirjin ya musu bai san halin da yake ciki ba.
Sun yi gudu sosai wanda yasa har asuba suka isa saman kan dutsen kogin kwankwamai. Domin har asuba tayi.
Isowa suka yi da wuta a hannun su.
"Ya Musa ka bamu wancan kurma, beben, makahon zamu rabu da rayuwar ka shi muje bukata "
"Ba zan baku shi ba, sai dai ku kashe ni"
"Haka ka zab'a?"
"Fiye da haka ma" ya basu amsar yana nazarin idan suka fada tabbas bai zama dole su rayu ba, sannan idan ya basu Abdullahi bai zama dole su bar su a raye ba. Wannan shine ake kiran gaba kura baya siyaki. Dan haka ya juya bayan shi. Jifan shi suka yi da gatari, ba tare da ya shirya ba, suka fada cikin ruwan me ɗauke da mugayen abubuwan tashin hankali.
......
*A Hausa historical ancient*
500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number +2347035133148 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
+234 803 879 6871 zuku iya tuntubar Number nan.....
#Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
Mai_Dambu...
BABI NA SHA DAYA (11)
The book isn't free
Bayan son daukar abin da Nahira ya gaya mishi, amma tsoro da fargaba ya cika mishi zuciyar shi.
"Ko ba yau ba, wata rana shi din zai zamewa al'umma haske a cikin duhu."
Komawa wurin Abdullahi yayi ya dauke shi, suka bar garin Nahara, lokacin da suka isa masarautan ana kiraye-kirayen sallah asuba. Dan haka ya wuce da shi ba tare da kowa yasan da fitar su ba.
Washi gari da safe aka tashi da wani babban al'amari.
Domin baki daya Abdullahi bayiia ji baya gani. Idanun shi tar kamar madara amma kuma an wayi gari baya ji baya gani, sake farantin hannun ta Kubrah tayi ta fashe da kuka, tana me jijjiga shi amma ina baya ganinta.
Hannun shi ta kai fuskar ta, yaji danshin hawaye, kamar yana ganin ta, haka shima hawaye ya shiga sauka mishi.
A hankali labarin abin da ya same shi ya fara yawo a cikin masarautar, musamman gidan sarautar da maganar munafuncin bai kaɗan bai yawa.
Sosai aka yi ta yayyata al'amari ta kai baya fita ko nan da can, waziri da kan shi ya kawo mishi wata sandar da kakan Abdullahi ya tab'a amfani da shi, yazo har gidan ya lallube hannun shi ya danka mishi. Yana shafa kan shi.
Samun sandar da take kamar ta tarihin masarautar yasa shi fara fitowa waje yana shan iska.
A haka ma bai tsira ba, Dan Yarima Arshan yana dibo abokan shi, su zo su kwace sandar suna mishi dariya, sannan wani abin takaici idan suka kwace sandar suka yi, wannan ya dake shi wannan ya mare shi, karshe sai sun kai shi kasa hankalin su yake kwanta.
W
ani lokaci haka Ya Musa zai zo ya dauke shi, amma baya tab'a kuskure ya nuna gajiyarwa shi a abin da ake mishi.
---
Duk wani bangare hankalin mutanen da suke son haka maraba da halin da yake cikin.
Dake akwai sauran Yaran marigayi Hayatudeen Abdullahi Noye, wanda basu yi aure ba.
Dan haka aka shirya gaggarumin biki, duk wani shigar da za ayi, an tura mishi shima a matsayin dan gidan, dan haka bayan an daura aure, Ya Musa ya mishi jagora har cikin gidan inda za ayi kome a harabar Fulani Babba.
Lokacin da suka isa wurin ya cika, dan haka suna isa aka fara sanarwan gashi ya iso.
Wurin da zai zauna aka bashi, aka fara hidima duk da bai san me ake yi ba, haka aka kawowa kowa abinci har da shi, Allah da ya tashi taimakawa bai ci kome ba, kuma ko tab'a kome bai yi ba..
Fulani Babba tana hakimce ta ce a kai mata shi.
Haka suka rike sandar shi har inda take, wucewar shi Yarima Shehu yaji ya sake Boyayyen ajiyar zuciya.
"Waye ya wuce!"
Ya tambayi Matar shi da take kusa da shi.
"Yarima Abdullah!"
"Allah sarki!" Ya furta a hankali, har wurin da Fulani take aka kai shi wurin ta.
Riko hannun shi tayi tana faɗin.
"Ya Musa kace anan kayi aure ka tare?"
Murmushi yayi cikin girmamawa ya ce mata.
"Ko daya ai da kai da kaya duk mallakar wuya ce."
Murmushin da bai kai fatar baki ba, yayi sannan ta kalli Ya Musa.
"Ance baya ji baya gani?"
"Eh haka Allah ya ƙaddara, sai dai ni na fi tunanin lokaci ne zai gabatar da haka imma yana gani ko baya gani"
Kallon masu zuba abinci tayi sannan ta gyad'a musu kai, a hankali suka kawo abinciin, aka saka a gaban shi.
Daukar abincin tayi ta mika mishi, tare da tallafar hannun shi ya fara ci.
A hankali ya fara cin abincin, wanda yake gauraye da kasa, da yaji da gishiri.
A hankali yake ciki yana lumshe idanun shi, wanda kana gani zaka fahimci a rikice yake, amma tsabar juriya da kuma yadda Ya Musa ya mishi alama da hannu akan duk abin da xa ayi ko da zaa bashi kar ya tab'a tsorata ko ya shiga damuwa.
"Ya Musa kace Abdullahi akwai jarumta?" Ta tambayi ya Musa.
"Shi jarumta ba koyar da shi ake ba, haihuwar mutum ake da shi ranki shi dade."
Mika mishi ruwa tayi ya masa ya saka a bakin shi, lumshe idanun shi yayi saboda azabar zafin ruwan, a hankali ya ajiye mata, jikin ta ne yayi sanyi ta kalli abincin cikin borin kunya ta ce.
"Ba da fatan ka koshi" ta dauki abincin ta kai bakin ta, furzawa tayi tare da kiran me raba abincin.
Yana zuwa ta saka aka kama shi.
"A kan me zaka kawo gurbataccen abinci ga Yarima Abdullah"
"Tuba ranki shi dade, afwa." Haka suka gama hayaniyar su, a wurin tashi ya koma wurin zaman shi, Arshan ya saka mishi kafa, ya fadi suna kallon abin amma babu wanda ya yi magana, sai d'ago shi Ya Musa ya yi. Murmushi ya yi sannan suka koma wurin zaman su.
Haka aka tashi taron, sai da suka koma hanyar gida ne, ya saka hannun shi a bakin shi ya yi ta kakaro amai, Allah da ikon shi sai da ya amayar da abin da ya ci, sai wanda ba a rasa ba.
Koda suka isa ya gaji, kwanciya ya yi, kallon Ya Musa tayi sannan ta ce.
"Wani abun ya ci?"
"I, amma ya yi aman sa." Ya bata amsa, idanunta cika da kwalla, ta cigaba cewa.
"Ina son mu bar Deehar wallahi zuciyata bata da nutsuwa a nan."
"Ina me baki hakuri, amma tabbas barin ku Deehar akwai matukar wahala."
Sauka kwallar suka yi masu matukar zafi da ciwo, ba yau ta fara kuka ba amma a tsakanin wadannan lokutan tsoro ne me tattare da firgitarwa, bata da garkuwa sai Allah. Sadauki yayi kankanta da fadawa masifa irin wannan.
"Babu wata hanya ce? Gaskiya ina son barin Deehar"
"Ranki shi dade, barin garin nan daidai yake da rasa rayuwar kowannen mu, dama mu rayuwar mu domin ku muke yin shi, na ginu domin nayi biyayya dan haka duk inda zaku rayuwar mu fansa ce a gare ku."
"Na gode sosai" ta fada,
Haka suka yi ta niman hanyar da zasu fita daga masarautar amma abin mamaki babu wata hanya, haka kawai aka kara tsaurarra tsaron da babu irin shi a masarautar, karewa sai da ta kai sashin su, an zuba wasu irin dakarun kota kwana.
Wannan abin ya kara firgita Kubrah dan ita da danta basu cikin kariya, domin an wayi gari fitar da Abdullah yake an hana shi, baya fita ko ina, amma a haka suka nimo mishi malami da yake koya kishi karatu.
Domin rufe bakin Waziri da yake kalubalantar su, haka ya taso cikin kangin rayuwa, ita kanta Kubra niman raba su ake, amma Ya Musa da Waziri suka tsaya akan su, duk yadda ka nime izinin ganin su, sai a ce a tafi Fada a nime izinin.
A cikin wannan yanayin, Mahaifin Kubrah ya zo.
Fir aka hana shi, ganin su. Sai da ya kwashe kwanaki kamar biyar. Kafin aka nimo Ya Musa ya shiga da shi cikin gidan.
Koda ya ga kubrah da Abdullahi sai da ya yi kuka, tare da niman izinin tafiya da ita, amma suka hana shi dan haka ya ce musu.
"Zan tafi masarautar Rano, domin su shiga alamarin ba zan iya jurar ganin jika na da Y'ata cikin mugun yanayi ba. Wallahi Gara ganin mutuwata da na gan su, cikin tashin hankali da damuwa ba."
Babu wanda ya tanka mishi, haka ya gama hayaniyar shi yayi tafiyar shi.
Tabbas yace gara yaga mutuwar shi da yaga halin da Kubrah take ciki, sun cika mishi kudirin shi. Domin sai da aka bishi a baya har zuwa iyakar kasar kano da Deehar, sannan suka kashe shi aka daura gawar shi akan dokin shi, ya kai shi masarautar Rano.
Wannan tashin hankalin tab'a, Innoh sosai ta dimauce ta shiga damuwa babu diyarta babu mijin ta da jikan ta.
Wannan abin ya tab'a kimar Masarautar kano dan haka, aka tura dan sako har Masarautar Deehar, sai ga manyan dattawan Masarautar sun zo ta'aziya, tare da wanke kan su abun ya tab'a zukatan al'umman masarautar Rano, dan haka Sarkin Kano da na rano, suka bukaci a kawo musu, Abdullahi da Kubrah, sun amsa da Toh, domin bayan komawan su, an kawo su amma sai dai zuwan su na tsawon kwanaki uku ne, domin kuwa a tare suke da dakarun, sannan suka tura sakon cewa ana bibiyar rayuwar Abdullahi ne yasa aka tsannanta masu kula da shi, duk da haka Sarkin Rano yayi bakin kokarin shi wurin nunawa
*A Hausa historical ancient*
500₦
#Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*
Mai_Dambu...
BABI NA SHA UKKU (13)
Lekawa suka yi domin tabbatar da cewa sun nutse a cikin ruwan, sannan suka juya daga saman dutsen, dan su tabbatar da sun cika aikin su. Daukar gawar Kubrah suka yi zuwa cikin cikin masarautar, aka hada da nasu Waziri da Matar shi.
Ba a tab'a gashi tashin hankali kamar wayewar garin Laraba ba, domin sun ga abin da ya basu tsoro ya kuma gigita su a duniyar su, sun shiga mawuyacin hali a ranar, wanda ya kama muguwar tsoro da tashin hankalin a cikin masarautar. Har ta kai babu me iya tari ba tare da an zubar da jinin shi ba. A hankali suka kame sauran kabilar Noye suka yi ta bautar da su, sannan suna fad'ada masarautar da karfin tsiya. Sai da ta kai ta kawo masarautar babu wani me iya ja da su. Hatta sauran masarautun ƙasar hausa domin karfin zaranta mazan da Deehar take ta ita, sannan bayan haka suna da wani irin karfin tsiya da idan suka tunkari gaba nahiya sai sun rusata.
Gashi Allah ya azurta su da dimbin arzikin albarkatun kasa, domin ana tono zinari, wacce da ita aka kara gyara manyan manyan hasumiyar masarautar, yadda daga nesa ka hango su zaka fahimci cewa akwai arzikin ban sha'awa da ban mamaki.
Allah ya kara musu Ni'imar arzikin noma, domin suna noma na fitar hankali, har ta kai ana fita da shi kasuwancin sauran makotan masarautar.
Haka shekaru suka yi ta tafiya, suna kamo kananun yankuna da basu da addinin musulunci, suna mai dasu bayin su.
A gefe guda suna da burin shiga garin Nahara, domin sun ji labarin cewa a can a ka kai Abdullahi Noye jinya. Kuma an tabbatar musu hakan.
Shi yasa suka yi ta kokari shiga Nahara, amma abin ya ci tura.
Sannan duk abin da ake ana yin shi ne yadda Arshan zai yi mulki shi yasa Allah ya dauke mishi tausayi da imani, bashi da imani da tausayi. Tun yana dan shekara goma sha biyar yake kallon Mata ba a bakin kome ba.
Domin haka zai saka a shigo mishi da su dasu suna rawa tsirara gaban shi, wadda haka yake masifar burge shi yaga mace a tsaye da diri tana rawa a gaban shi,.yafi kome kwantar mishi da hankali.
Sannan abin da yake kara mishi farin ciki, yaga ya kusanci mace an