Showing 1 words to 3000 words out of 105295 words

Chapter 1 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6106

*......DASHEN ALLAH 🌳*


EXQUISITE WRITERS FORUM


Mai_Dambu...


*SADAUKARWA GA MUTANEN DA HAR KULLUM SUNA TARE DA MU*


BABI NA DAYA (1)


*(DEEHAR)*
*A karni na sha bakwai kafin zuwan Shehu Usmanu danfodiyo*


_Sun fara ba tare da sanin karshen ta ba, sun shafe tare da ruguza yarda da amincin juna! Kullaliyar al'amari ce da ta haÉ—a kusurwa uku! Duk yadda aka haÉ—a kusurwa uku toh dole a iya fuskantar sakamako mara dadi! Masu iya magana na cewa abokin mutum biyu munafikin mutum daya_


DEEHAR tana cikin lardin mafi kyau da tsarin Ubangiji, wuri ne da Allah ya shirya tankar dausayi domin cunkushe take da albarkatun kasa. Asalin mazauna yankin Deehar wasu kabilu ne da ake kira Noye, sun kasance manoma ne da kiwo basu da wani abun Azo a gani sai
Sun kasance masu imani da camfi sannan sun yarda da tsafi da bautar gumaka.


Ana haka wasu kabilu daga yankin kasar hausa suka ɓullo ta yammacin Afirka izuwa Deehar. Koda suka iso wurin sun samu yadda suke so, sai suka fahimci ai babu shugabannin a yankin, sannan su din su fito gudun hijira ne sakamakon yaki da fatara da mugun talauci dake addabar nahiyar su.


A cikin kabilar Noye akwai wanda suka yarda da shi sunan shi Rana, rana ya jima yana nazarin yadda zai bunkasa nahiyar su, amma sai aka samu rashin sa'a kabilar Noye basu yarda da tsarin shugabanci, kuma basu ra'ayin shi. Dan haka yaja bakin shi yayi shiru Rana boka ne mashahuri a yankin Deehar. Al'ummar Noye sun yi imani da Rana shi ne kawai mutumin da yake ganawa da Allah, shi yasa basu gardama da shi duk abin da ya ce musu.


A shekarar da Kabilar Hausa ta shigo garin Deehar sai da ya share kwanaki talatin da tara yana halwar tsafi, yana fitowa yace a kore su a garin.


An kuwa yi nasarar fatatakar su, daga cikin Deehar. Sai dai bayan wasu kwanaki. Sun kuma dawowa aka sulhunta da taimakon wani boka me suna Yauta, yauta shi ya fara bada shawarar ayi mulki, aka ki mau shi domin sun san cewa idan aka yi mulk ba mamaki akwai zalinci a cikin shi, su kuma sun gina jinin su da mutanen su domin a zauna lafiya babu wanda ya fi wani.


Sai da aka sulhunta, sannan Yauta da shi da wasu daga cikin Hausawa suka had'a gaggarumin biki da aka kafa garin tare da taimakon wasu kabilar Noye. Sun kuma amince da tsarin inda aka ware wani kogon dutse aka gina babban gida domin zaman lafiya hadin kan kabilu biyu. Wani abun da mutane basu gane ba akan Yauta shi lallai ala tilas so yake ya mulki al'ummar shi domin yayi bincike an tabbatar mishi za ayi dogon karni ana mulki a nahiyar.


Wannan yasa kafin kace me yabi wasu daga cikin manyan gidajen kabilar Noye ya kwadaita musu wannan al'amarin da alkawarin idan mulkin ya tabbata toh su zasu ji dadi da sauran su.


Sai da ya dauki tsawon shekaru goma yana lalab'a mutane kafin wasu daga cikin kabilar Noye suka fara bori a fara mulki da sauran su.
Boka Rana yaso ya nuna musu illar haka domin yasha bincike ya samu kabilar Noye zata iya shudewa a cikin al'amarin mulki za a iya mantawa da ita har duniya ta tashi. Ya gaya musu suka ki.


Yauta ya kasance me aiki da rauhanan Aljanu ya samu wani irin sirri na musamman dan haka ya samu kabilar Hausa suka bashi hadin kai. A cikin shakara na goma sha daya aka fara gina wata gagarumar Fada wacce ake gini babu dare babu rana. Sai da aka share shekaru goma sannan aka bude babbar Fadar da aka saka mata masarautar Deehar.


Ana bude masarautar Deehar wasu daya daga cikin kabilar Noye suka ce Basu san da zancen ba, kafin kace me sai ga jinin al'umma yana ambaliya a cikin garin Deehar da kewayar shi, an kashe manyan mutane da dattawan da suka bijire.


Daga cikin su har da boka Rana aka kashe shi, amma kafin a kashe shi sai da ya haÉ—a manyan mutanen da suka yi imani da tsofaffi da yara da mata suka kwana uku ana bunka tsafi me mugun hatsari kafin aka kashe shi basu gama aikin ba, sai dai sun tsinewa masarautar da jinin kabilar Noye ya zuba, kafin sati biyu an shiga gina gaggaruman ganuwa da ta kewaye garin baki daya, gari me albarka ta zama magunar ruwa, zalunci da mugunta, ta shige zukatan jama'a.
Sai da aka shafe shekaru ashirin da biyar ana gine ganuwar da mata da matasa, waÉ—anda suka kasance Kabilar Noye.


Bayan shekaru talatin da kafa mulkin kama karya da zalinci, aka wayi gari masarautar ta kuma fadawa wata irin sirrintacciyar al'amari da har yau aka gaza fahimtar me ya faru a cikin Masarautan Deehar.
Wannan shine takaitaccen tarihin kafuwar Deehar.
★★
*A Karni na sha tara bayan zuwan Shehu Usmanu danfodiyo*


A hankali ya kalli amintacce bawan shi ya kura mishi Idanu, kafin yayi kasa da idanun shi ya ce mishi.
"Kowa ya rena mai labari, in ka ga mai gudu shi ne." A hankali ya furta haka.
Tsugunawa bawan yayi kafin ya ce.
"Tabbas rayuwar tana dabaibaye cikin makauniyar makoma."
"Ba zan maka tilas ba Musa, sai dai don mugun nufi ka ‘dinkin lifidi ne, dama ce ka taya ni aikin da ban karasa ba. Idan har rana ta fad'i ta yamma toh kayi yadda ya dace, idan kuma rana ta fito ba tare da wata ta fad'i ba, ka nisanta tazarar sama da kowacce tazarar ba zaka dawo ka same ni ba, amma tabbas sakon ya iso gare ni, dan haka kayi nisan kiwo."


"An gama mai Martaba, Gaskiya ta fi dokin ‘karfe ‘karfi. idan da rabo in sha Allah tarihi zata maimaita kanta alkawarin Allah gaskiya ne, mun yi imani da Allah kuma haka duk wanda yayi imani da shi, Allah ya baka lafiya da nisan kwana sarki me duniya, me tausayin talakawan shi."


A wannan daren me cike da sanyin damina, Allah yayiwa Sarki Hayatudeen rasuwa bayan dawo daga rangadi na tsawon kwanaki dari da biyar (105) wato wata uku da wani abu.
Kafin kace kwabo labari rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya rasu. Shine Sarkin da ya kwashe shekaru saba'in da takwas yana mulki, ba a tab'a samun basaraken da ya kai wannan shekarun yana mulki ba,.domin yana da shekaru cas'in da tara ya rasu.
....


Kafin wani abu labarin rasuwar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya rasu, adalin sarki da ya haramta zalintar kabilar Noye, domin a tarihi shine ɗan ƙabilar noye da yayi nasarar mulki ba tare da an zubar da jinin kowa ba,.yayi mulki ba tare da zalinci ba.
Talakawa da attajirai na Deehar sun yi mutuwar adalin sarki, kafatan alummar Masarautar Noye sun yi kuka tare da fatan Allah ya basu adalin sarki irin shi.


A cikin Masarautan Deehar akwai tsohuwar bishiyar da ta kai kimanin shekaru dari biyar a masarautar domin koda aka gine masarautar ba a tab'ata ba, da aka zo za ayi sallah jana'izar shi sai da aka ga abin tashin hankali domin bishiyar ce take kuka da kururuwa. A tarihin rayuwar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye yana yawan zuwa wurin Bishiyar shan iska ana yawan ganin shi da yamma yana zama shan iska har da hira, a shekaru ashirin hawan shi mulkin ta fara zuwa tare da kafa rumfar shi. Daga baya sai aga idan yazo an kawo mishi kayan abinci da kayan lambu.


A hankali aka kewaye bishiyar tare da mata dashe dashe wanda yaja ake tsammanin Sarkin Hayatudeen Abdullahi Noye yana da kyakyawar alaka da mutanen boyen da suke wurin.


Haka aka yi ta jifar shi tare da miyagun asirai, amma bai same shi ba. Har zuwa rasuwar shi a daren jiya wanda aka samu wasu suna zargin kamar kashe shi aka yi ba mutuwa yayi ba.
Bayan anyi jana'izar shi aka kamo cikin gidan, sai dai kash duk cikin yaran sarki Hayatudeen Abdullahi Noye babu d'a namiji me lafiya da za a kira shi lafiyayyen.
Daga makafi sai guragu da kurame, wannan itace tsinuwar da suke fama da ita tun farkon kafa masarautar Deehar.


Sai dai wani abu daya da ya hana su cewa kome, musamman Waziri da galadima da Garkuwa, alkali, Tafida, sarkin Malamai, shiru suka yi suna sauraron bayanin da Sarkin gida yake tare da mikawa Maga takarda wata farar fatan barewa.
*Bayan gaisuwa da ban gajiyar dawowa daga rangadi. Ajiyar da ka bari yayi yad'o da ya banya idan har sako ya iso akan lokaci toh ina jiran sakon ka*
Kallon juna suka yi kafin wasu daga cikinsu ran su yayi mugun b'aci,
"Sakon daga wani masarautar aka turo? Sannan ina Ya Musa yake? Domin kuwa shi daya ya san kome" inji galadima da yake muzurai.
"An nime shi tun jiya ba a gan shi ba."
Shiru fadar yayi kafin suka mike suna faÉ—in.
"Sakon yana isar da cewa Hayatudeen ya ajiye wata mace da alamu har ciki ya shiga cikin alakar su! Wacce masarautan ya isa kafin dawowarsa?"


Shiru suka yi aka rasa wanda zai iya tuna masarautar da ya tsaya kafin ya iso Deehar.
"Indai haka ne toh tabbas babu abinda za a iya yi domin za a tsumayi nan da shekara daya a ga me aka samu. Idan mace ce shi kenan idan na miji ne sai ayi nazarin yadda za a rene shi a cikin masarautar." Alkali ya faÉ—a. Wannan hukumcin kamar hukuncin kisa wasu suka ji shi, domin Gara hukuncin kisa sau dubu da akan a jira matar da Sarki Hayatudeen ya ajiye dan haka wasu suka sha alwashin matukar suna numfashi babu wanda ya isa ya shigo musu da batun wani abin da sarki ya haifa.


Bayan an watse a fadar aka shiga cikin gidan tare da shaidawa Fulani Babba, itace uwar gidan Sarki Hayatudeen, da Magajiya, itace matar Sarki Hayatudeen ta biyu. Sai Kilishi itace matar Sarki Hayatudeen ta uku, sai Fulani karama itace Amaryan sarki Hayatudeen ta hudu, Akwai kwarkwarah da ya ajiye uku, Kwarkwarah Lanta, sai kwarkwarah Saro, sai kwarkwarah Zinaru.


Fulani Babba tana da yara biyar uku mata biyu maza, akwai Yusif, akwai Ado ana kiran shi me Kano, sai Bara'atu itace babba tana aure a masarautar Borno, sai Ummu Kulsum, tana aure a nan Deehar, sai Jamilah tana aure a masarautar kano.


Sai dakin Magajiya baki daya yaranta maza ne mace daya ce a cikin maza uku mace daya, akwai shamsudeen, akwai alkasim, akwai Muktari. Dakin Fulani Babba yaran ta maza Yusuf makaho ne, sai Ado kurma ne baya ji kamar yadda Yusif baya gani. Sai Magajiya Shamsudeen a nakashe yake baki daya baya dama a kwance yake. Alkasim kuwa bebe ne Baya iya magana. Muntari kuwa toh baki dayan shi dolo ne baya gane kome. Sai yarta mace Sailuba tana auren wani attajiri a cikin Deehar.


Dakin kilishi baki daya mata ne, bata da matsala domin an aurar da matan, Balarabiya, sai Ikilima, sai Shatu.
A dakin Fulani karama ne ba a magana domin baki daya yaranta biyar din nan kamar Magajiya take duk a na kashe suke, akwai Usman suna kiran shi Shehu, sai Kabiru, sai Ibrahim wanda ake kiran shi me rumfar bayi.
Haka kwarkwaran sa su kuma Allah bai basu haihuwa ba, sai dai ana kazamin kishi a cikin gidan sarkin Hayatudeen domin kowacce mace gani take kamar ita Sarki yafi so....
.......


*NAHMIFAK*
_Collections_


```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
Taku har kullum
#Mai_Dambu.
#Fri/November!/2022
https://chat.whatsapp.com/IaMvkv2GUO688AtLknlFqa
*......DASHEN ALLAH 🌳*


EXQUISITE WRITERS FORUM


Mai_Dambu...


BABI NA BIYU (2)


*Shashin Fulani Babba.*
Shashi ne me zaman kan shi wanda ya haÉ—a bayi maza da mata kusan guda sittin da bakwai saboda yawan hidimar Yaran ta maza biyu Yusif da Ado.


Duk inda Galadima Sule ya wuce zubewa ake a gaban shi sabida kwasar gaisuwa, har ya isa babban shashin Fulani Babba.
Can yayi ta keta manyan zaurirruka har uku, sannan ya isa babbar zauren ta da aka zuba manyan tumtum tare da jera su akan kyakyawar darduman, ya cire takalmin shi sannan ya shiga cikin zauren, ya hango.
"Assalamu alaikum!" Yayi sallama cikin dattijiyar muryan shi.
"Waalaakumun Salam, Abin mamaki batan kare da tsire tauraro me wutsiya sanin ka bala'i. Ganin ka masifa yau meke tafe da kai bayan ana can ana zaman makokin mai martaba?"


Kasake yayi kafin yayi kwafa ya ce.
" Hmm kowa yaki tsotsan yatsu bai ji zak'in miya bane waye ya gaya maka ganina yana da nasaba da iftila'i, ai gani na a gare ku shine mafi girma da alkhairi "


"Anya masu iya magana sunce a rashin kira karen bebe ya b'ata," fitowar Jakadiya ta zube a gaban shi tana faÉ—in.
"Tuba nake Galadima, Inda kaji mutum yana tsoron dare an daure shi ya gudu ne, Uwar É—akina tana marabtar ka"
Jinjina kai yayi sannan ya shiga cikin dakin tana kishingid'e kamar ba mutuwa aka mata ba, kanta sunkuye cikin tsananin isa da izza. Zubewa yayi duk da kasancewar shi Wanta babban Yayan su, amma yana bata wata irin girma me É—auke da ban mamaki.
"Ina mika sakon ta'aziyata" sai lokacin ta d'ago kai ta dube shi na wasu yan dakikai, kafin ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zaren yadin jikin ta na awalayo , murmusa mishi tayi sannan ta ce mishi.
"Domin rana daya ba a kin guziri ina jin ka" gyara zama yayi sannan ya kalli bakin kofar da jakadiya take tsaye. Itama kallon Jakadiyar tayi, dukar da kai tayi sannan ta fita daga dakin cikin girmamawa.
"Ko kin san makomar faffutukar da muke ina zata tsaya?" Ya fadi yana kasa da muryan shi.
Hura iskar bakin ta tayi wannan ta ce mishi.
"Duk saurin unguwar zoma ta jira a Haihu ko!"
Gyara zama yayi sannan ya kasa da murya ya ce mata.
"Bafa yadda kike tsammanin bane! Domin ranar tsafi bunsuru ke kud'i." Kallon tambaya ta mishi.
"Wato Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya samu wata sad'aka a tafiyar shi wanda ake hasashen tana dauke da cikin shi" firgit tayi ta kura mishi Idanu.
Idan bai yi karya ba, wallahi kwalla ya gani cikin idanun kanwar shi.
"Me haka yake nufi? Shirun ki sarewa ce a gare ni"
Hawaye ne suka zuba daga idanun ta, sannan ta lumshe idanun ta, mikewa yayi ya fita. Domin tunda tayi shiru nan ba zata kuma magana ba, Hakazalika ba zata ce mishi cikan ka ba, Fulani Babba mace ce, da ba a sanin gaskiyar gaban ta, shi yasa ba kowa take hulÉ—ar arziki da shi ba.
Haka ta cigaba da zama babu wanda zai ce ga abin da yake damunta.
*Shashin Magajiya.*
Ita din Y'ace ga Wazirin Deehar, kuma mafi soyuwa ga Wazirin Deehar, kallon ta yayi cikin nutsuwa ya ce mata.
"Hayatudeen ya gaya miki garin da ya tsaya bayan fitar shi rangadi?" D'ago kai tayi cikin ya tsina fuska ta ce mishi.
"Bai gaya min ba, domin ai ba a dakina ya sauka ba, a wurin Kilishi yq sauka."
"Lallai anyi sake Dan zaki ya girma domin kuwa ya ajiye sad'aka da har ake hasashen tana dauke da cikin shi. Dayawan sarakunan masarautar Deehar ba samamun Deehar bane haka zalika ba haifafun masarautar bane da girman su suke zuwa masarautar"
Kallon ina ruwa na tayi mishi sannan ta cigaba da sha'anin gabanta, ta ce mishi.
"Kasan bani da matsala da mulki domin ko na shiga maganar ba zai min dadi ba, ina fama da Shamsudeen da Muntari da bana son rigima ko na hana ba zai tab'a bawa Yarana daman mulki ba, tunda dai ba samun haka xan yi ba meye nawa da tashin hankali? Ana takai wake ta kaya"


Daga haka ta ja bakin ta tayi shiru, da ya auna maganar ta, sai ya fahimci ta fishi gaskiya dan haka ya mata sallama.
*Shashin Kilishi*
Kawunta shine Malamai ya shigo har cikin gidan, ya mata nasiha sannan ya tambaye ta ko ta san wani gari ya tsaya rangadin shi na ƙarshe?
Shiru tayi sannan ta dubi Yaranta mata kanana, kafin ta ce mishi.
"Ban sani ba, amma anan ya sauka bayan ya dawo daga rangadin."
Kura mata idanu yayi kafin ya ce mata.
"Nahira nasan halin ki, ba zaki fada bane kawai amma kin san inda Mai Martaba ya tsaya rangadin shi na ƙarshe "
"Wallahi ban sani ba Kawu" ta fada tana kallon kasa. Karkabe hannun shi yayi sannan ya fita tunda bata sani ba, babu amfanin dolanta mata, a bangaren Fulani Karama ita bata samu me tuhumar ta ba, domin kuwa ita din Bafulatana ce daga Masarautar Moddibo Adama wato yola.


Haka akayi ta binciken bayi da kunyangi da suka raka Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye rangadi amma ba a samu wanda zai ce ga inda suka tafi ba.


Shima wannan ba karamin tashin hankali bane, gashi Ya Musa an nime shi sama da kasa ba a gan shi ba.
Ranar da ya cika kwana uku, aka samu wata baiwa da aka yi tafiyar da ita.
Sai dai wani abin almara, koda ta zo babban zauren gidan ana sauraren ta, sai ta kasa magana, haka buga mata tsawa ta zabura tana zare idanu. Tana buÉ—e baki zata yi magana baki daya muryan ta, ya dishe. Tayi tayi ta fadi inda suka tsaya kafin sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya sallame su ta kasa fada.
"A zane ta, sai a korata karya take"
Dayawan manyan Fadar basu yarda karya take ba, masu idanu a duhu sun fahimci inda matsalar take ba zata tab'a fada ba, domin akwai mutanen boye masu bawa Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye kariya musamman abin da ya shafe shi.
Haka tana ji tana gani aka zane ta, sannan aka fitar da ita. Fitar da wani kundi aka yi Sarkin Gida ya mikawa magatakarda ya fara karantawa.
_"Ina farin cikin rubuta yar karamar labarina domin isa inda nake bukata! A raina da zuciya ta. Naji ina son nayi rangadi a cikin duniyar nan domin shan iska! Duk da akwai ciwo da kuma zafin da nake ji a tsawon shekarun saba'in da takwas da nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login