Showing 21001 words to 24000 words out of 105295 words

Chapter 8 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6115

daure mata kafa da hannu yana yadda yake so. Domin tun daga lokacin da idanun shi ya fara budewa ya zama mara kunya na fitar hankali. Baya jin maganar kowa sai na Fulani Babba domin son shi take kamar tayi yayya. Hatta Uwar shi Zulai sai da aka rabata da shi, tana ji tana gani a ka kore ta a masarautar tare da mata gargadin kar a kuma ganinta.
★‡★
Bayan shekaru ashirin da takwas.
Kauyen Nahara.
Gidan Mijinyawa.
Shigowar shi gidan kenan da wata tumemiyar littafi, ya zubawa yar budurwar da ba zata wuce shekaru sha uku idanu.
"Baban mu ka dawo daga aikin Allah?" Ta fada tana washe bakin ta,
"I, na dawo Easther." Ya fadi haka yana kallon ta ganin yadda kayan Jikinta suka b'aci da datti.
"Easther"
"Baban mu, muje ka huta ai kawai yau na tsokano zuma ce, garin gudu na faɗa a gulbi" ta amshi littafin shi, ta wuce bukkar shi.
Raba idanu take domin tasan Mama Uwa sai ta zane ta, tunda ta tsokano zuma ya harbi wabi, wato Abigail kuma ko a gaban Ubansu ne sai ta dake ta. Balle kuma a gaban Mijinyawa kakan su.
"Sannun ku da gida?"
Bur Mama Uwa ta fito, da bulalar ta. Kallo daya yayi mata ya dauke kan shi, tunda yasan bai da ikon hanata dukar Easther din.
Ai kuwa ritsa ta tayi a dakin Baban su.
Dama gata katuwa, dan haka ta tare kofar bukkar.
"Wani ɗan banten uban ne yace ki tsokano zuma?"
"Na rantse miki da Yesu Almasihu Abigail ce."


"Zaki ci kundugurun ubanki yau kuwa!" Ta fada tana nufar ta zata dake ta. Aikuwa Easther ta taki sa'a ta bangajeta suka zube s kofar dakin. Ta haura kanta, ta fice daga gidan baki ɗaya.
Gidan Nahira ta nufa, ta zauna a kofar gidan shi tana share kwalla.
A hankali ya fito da sandar shi da yake dogarawa, ya zuba mata ido.
"Kyakyawa!" Juyawa tayi tana kallon shi da dara-daran idanunta.
"Idan kika samu dama, ki nima mana yanci kin ji."
"Kaka kenan! Wani yanci bayan nima ba yancin nake da shi ba a gidan Ubana ba" zama yayi yana kallon ta, sannan ya ce mata.
"Ke ce yar matar Magaji da ta koma garin su?"
Washe baki tayi tana kallon shi, sannan ta gyad'a kanta.
"Je ki kira min Baban ki" ya fada mata.
"Toh" ta fada cike da tsoro.
"Ina zuman da kika ciro bayan kin kore su?"
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
"Na bawa Jatau, dan yau bai da abinci ni kuma na samu kanzo na ci dazun!"
"Kin kyauta"


Da gudu ta juya, tana tafiya tana tsalle, ta tuma can ta tuna nan. Har ta isa gidan su.
Zata shiga gidan, ta hango Lati. Dan gidan Me garin Nahara.
Kallon juna suka yi, sannan ta wuce cikin gidan. Ita ya ce yana so amma haka Abigail suka kwace mata shi, a soron gidan ta hadu da Babanta, yana yiwa wasu matasa uku da suka zo amsar addinin Kiristanci wa'azi da nuna musu irin arzikin da rabo da yake cikin addinin, murmushi tayi domin ba karamin kaunar Addininsu da mahaifin ta take ba.
Hannu ta saka a bakinta sannan ta kai goshinta, da kafadar ta hagu da dama.


Sai da ya sallame su, sannan ya kalle ta yana zaune bisa kan kututture.
"Kyauta me yasa baki jin magana? Kin fi son kullum ayi ta dukan ki ne?"
"A'a Baban mu, inji Nahira wai kaje"
Kura mata idanu ya yi, zuciyar shi tana tsoron kar wani abu ta kuma tsokanowa ba.
"Me kika kuma tsokanowa?"
"Na rantse da Yesu Almasihu ban yi kome ba" ta fada tana zare idanu.
"Toh muje"
Haka ya sakata a gaba, suka tafi har gidan Nahira.
Murmushi ya yi.
"Me yasa kake tunanin zata aikata wani abu? Akwai batuttuwar da ya da ce ka sani amma dole kayi hakuri. Ita din kai ka haife ta amma kaddaran ta ba irin na kowa ba ne, yadda take kyauta a zuciyarka haka take kyauta wata rana a gare mu, sai dai na hango hayaki da wuta yana ci a garin Nahara. Amma ban kawo akwai tsaftaciyyar ruwan da zai kashe shi ba, sai shekaru biyar da suka wuce lokacin da ka kawota bata da lafiya"
Shiru Nahira yayi sannan ya cigaba da ce mishi.
"Ka bar maganar masu magana, amma ita zata zama farin wata sha kallo"
"Na gode sosai Nahira." Daga haka ya koma ya riko hannunta suka bar wurin.
--
Da daddare suna zaune dake ya zo bukkar Mahaifin shi ne, dan haka ya shiga bashi labarin abin da Nahira ya fad'a, matar Baban shi ta goma sha biyu, me suna Zunkud'i ta saka kunne tass ta kwashe kome, ta sulale kamar zata ta fi gona bahaya, ta tsallake ta nufi sashin shi Mama Uwa.
"Ke Mama Uwa kina ina Nahira ya buga kasa a kan yar kishiyar ki, da alamu zata shahara a duniya "
Dukar kirjinta tayi.
"Ke Zunkud'i kar ki kashe ni, maza su ki kai ni kushewata. Kyautar ce zata zama wata a duniya?"
"Kina mamaki ne? Toh bari ba gaya miki abin da ya kai Magaji sashin mu kenan, dan haka sai kin tashi tsaye kamar yadda kika raba zaman lafiya tsakanin Uban da Uwar dole kiyi haka."
"Na gode da wannan labarin" ta fada tana kwafa.
"Haba ina sai kin bani mad'i domin ba zan kawo labari irin wannan na tashi da godiya ba. Miko min mad'i domin gobe nazo da wata labari me zafi "
Tashi yayi ta nufi inda goron kori take ta zuba mata madi me yawa a wata karamar akushi. Ta bata tana faɗin.
"Duk abin da kuka yi da Mijinyawa ki gaya min "
"An gama"
Haka ta fita tana farin ciki, sannan ta nufi sashin su.
--
Abigail da Easther suna dandali, inda ake gad'a, idanun ta yana kan yan mata da samari.
"Sannu kyakyawar Nahara" juyawa tayi ta kalle shi, sannan ta mai da kanta wurin wutar da aka kunna s filin.
Duk mazan wurin sanye suke da fatar namun daji, haka dabi'ar su take, maza suna rufe alauran su da fatar ne kamar fatari, kirjin su kuwa saka fatar suke kamar Mayafi, mata kuma kuma suna rufe dukiyar fulanin sune da fatar, a daureta ta baya har zuwa cibiyar su, sai fatari da suke sakawa a kugun su har zuwa gwiwar su.
Suna Kwalliya sosai, domin mazan har wani abu suke sakawa kamar hula, ko fatan kan kura ko ta zaki. Wanda yafi jarumta dai shi yake shigar Alfarma.
Su kuma Yan matan, zasu gyara gashin kansu da wurri, musamman ake musu kananun kitso kamar ta kabilar fulani, sannan ta jera a gashin su.
Suna da wata al'ada, duk da kasancewar su maguzawa, basu hakewa mata sai an Nahira ya saka musu albarka.
Sannan duk macen da tayi sake wani abu ya tab'a budurcinta, toh ba makawa, sai masifa ta fadawa alummar garin Nahara, da wannan suka yi imani domin asalin garin Nahara sunce an kafata ne da wata budurwa wacce take da sunan Nahara, a da can baya garin baya rabuwa da hari da kuma ambaliya da annoba, da manyan manyan bokaye suka yi bincike sai suka tabbatar idan garin zai samu kariya dole a sadaukar da mace budurwa wacce bata tab'a soyayya ba.
Haka yasa suka amince aka sadaukar da Nahara da cewa duk wacce ta bada kanta ba a yantatta ba toh tabbas zata janyo musu fitina da masifa, sun rike wannan al'adar kuma ana kan ta tun zamanin iyaye da kakanni.
Kallonta yayi yana murmushi.
"Me yasa baki magana?"
"Ba a tsaga min baki dan na zama magananiyya ba!"
"Tow yayi kyau, kin san irin kyan da kike da shi kuwa? Ba mamaki masana ilimin tarihi basu gaya miki kina kama da Jaruma Nahara ba"
"Na shiga uku! Inji barawon zuma ni a suwa? Karere bikin kawar kawa."
```Haseer collection dealer ce kayanmu suna da sauqi sosai price dinmu price din sari ne zaki samu kayan mu cikin sauqi alhmdllh ga kadan daga ciki ina Matan iyayen giji! Yau ga sabon labari mun zo muku da shi kawo kunnen ku kuji labari.
1: royal jelly 2500 me 60pc babba 19k me 365pcs
2: sugar wanita 2500
3: extreme maca 4000
4: vitamin c 2200/2500
5: vitamin e 2000
6: gluta white 2500
7: khusus 3500
8: pesona 2500```
+


234 803 879 6871 zuku iya tuntubar Number nan.....


*A Hausa historical Ancient*
24/Nov/2022
#Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*
Mai_Dambu...


BABI NA SHA BIYAR (15)


Mijinyawa
Bamaguje da yake cikin kauyen Nahara, babban mutum ne da yake noma da kiwo, uwa Uba shi din baduku ne da yake sarrafa fata da jimar su zuwa wasu sassa domin fatauci.
Mijinyawa yana da mata goma sha daya, kuma a cikin matar shi nan babu wacce ta haifa mishi ɗa sai dangana, matar shi ta sha daya. Lokacin da ta haifi Magaji sai ta mutu, ko ganin dan bata yi ba.
Magaji ya taso cikin kulawar matan Ubanshi goma russ din nan, domin sun fahimci idan kana son shiga toh dole ka kaunaci magaji.
Sai ya zama Magaji shi ne abin kishin matan gidan, domin kuwa kowacce tana kyautatta mishi ne domin kaunar Uban shi.
Duk da ba wani kishi aka yi a zaman su ba, sai gashi Magaji ya zama ɗan da ake kishi akan shi kowacce so take lallai ta rike shi dan Mijinyawa ya so ta.
Asalin sunan Mijin yawa, Danladi ne amma saboda yawan aure aure yasa aka saka mishi mijin yawwa.
Saboda zumunci da jin dadin yadda suke kyautattawa dan shi yasa shi ma yayi musu ixinin su dauko yaran Yan uwan su.
Kafin Magaji ya cika shekara goma gidan ya cika da yara, kuma Mijinyawa shi ya basu damar rike Yaran kamar Magaji.
Saboda gata irin wadda Magaji ya samu yana da shekaru goma sha biyar aka mishi Aure da Uwa, sai dai Uwa ta kasance mace me yawan wabi.
Tana haihuwa dan baya wuce shekara daya ya koma.


A lokacin karfin Mijinyawa ya fara ja baya, sai ya fara fita da Magaji zuwa fatauci da sana'ar shi, idan suka tafi suna wata biyar wata shida.
Haka ya cigaba da tafiya da shi har Magaji ya cika shekara ashirin lokacin duk wadda ya ganshi ya ga cikakken namiji, ga kyau ga kuruciya.
Haka yasa duk inda ya shiga sai ya samu masu bashi mata, domin shi mutum ne me yawan fara'a da kamun kai.
A lokacin da ya cika shekaru talatin a duniya ya zama me daukar duk wani nauyi da gidan su baki daya.
A lokacin da ya kara zama shahararren attajiri a cikin garin Nahara, domin yana da jakuna na shi na kanshi, sannan yana da doki daya.
Domin fa a lokacin me arzikin sayan doki ba karamin attajiri bane, dan haka da yawan mutane sune mishi kallon me kashin kudi alfadari.
Ana haka Magaji ya tafi fatauci can gabashin nahiyar bakaken fata, inda ya sauka a kasar Habasha a lokacin.


Kwanan shi biyu, ya shiga kasuwa da kayan da yazo da shi, kasancewar basu samu irin kayan shi, sai suka fara saya kamar hauka. Kuma Allah ya taimaka yazo da jakuna kusan guda goma sha biyar da kayan, haka kayan suka yi ta karewa.


Magaji yana da baiwar fahimtar Yaren duk ƙasar da ya shiga,.kuma wannan dabi'ar Fatake ce. A cikin sati biyu ya iya Yaren su ta Amhara. Sosai a cikin satin na uku ya fara karya musu harshe, lokacin da ya cika wata guda zuwa biyu nan, suka hadu da Jessica, ita din yar ƙabilar Amhara ce da take cikin kasar babanta Babban malamin majami'ar catholic ne a wancan zamanin.
Duk da kuwa suna riko da addinin Kirista bai hana su bawa Yaran su abin da suke so ba, dan haka lokacin da suka ji labarin soyayyar ta da shi, sun kira shi suka mishi tambayoyi ya bada amsa yadda ya dace sai dai ya gaya musu shi bai san wata addini bayan maguzanci ba, basu yi mamaki ba, dan haka suka tallata mishi addinin su, wanda ya amsa hannu bibbiyu. Uwa Uba bai boye musu yana da iyali ba, basu ki ba.
Domin suna son duk abinda Jessica tace tana so.
Ba ayi bikin ba, sai bayan ya dawo ya gayawa Mahaifin shi da matar shi, ai kuwa tayi tsalle ta diro ba zata zauna da kishiya ba.
Shi kuwa ya ce mata ba zai fasa ba, idan da ya bi na mutane toh tuntuni ya dace ya yanta wasu mata a gaban Nahira.
Jin haka yasa ta hakura, ta shiga faffutukar niman maganin da abin da zata haifa ba zai mutu ba.


Watan shi biyu ya koma aka yi auren shi da Jessica, suka bude rayuwa me albarka da kaunar juna.
A lokacin ya maida hankali sosai wurin kasuwanci da niman Ilimin addinin Kirista.


A haka suka shekara bakwai lokacin Ta haifi yarta Mace wacce a take ya saka mata suna da Kyauta, dan bai kawo zata haihu kusa ba.
Ta haifi yarinyar ranar Easter san haka aka saka mata suna Easter. Tare da saka mata Albarkan iyaye da kakanni. Da mata Kyakyawar fatan zama mace me daraja, domin sun yi imani duk macen da aka haifa ranar Easter zata kasance mace me darajar da babu irin ta a cikin alumma.


Lokacin da Easter ta cika shekaru biyar zuwa bakwai a lokacin Magaji wanda ya koma Jacob, ya dauki Jessica zuwa garin su, da tarin dukiya me yawan gaske. Domin iyayen ta attajirai ne.
Lokacin da suka isa garin Nahara, Easter ta fara wani irin zazzaɓi har da suma.
Aka suka mata yan dabaru kafin su isa gida, amma ina dole kafin su isa gida sai sun tsaya a gidan Nahira, domin shine akan hanya.
Amma wani abin mamaki shine suna isa kofar shi suka same shi a kofar gidan yana tsaye, da kan sa ya amshi yarinyar.
"Haba Nahara! Kishin ne ya motsa akan kyauta? A kyale ta mana, ai itama tana da irin hasken ki sai dai nata daban da naki! Idan har Nahara ruhinta me tsarki ne toh tabbas da kanta zata albarkaci kyauta"


Ya dauki lokaci yana magana kafin, Easter taja numfashi. Ya mikawa Magaji yana faɗin.
"A kula da ita, domin daraja ce da ita ba kamar sauran Yaran mu ba."
Da farko Jessica bata yi imani da abin da ya fada ba. Amma kuma lokacin da suka isa gidansu Magaji sai ta fara gasgata abin da Nahira ya gaya musu.


Jessica tasha mugun wahala a hannun Mama Uwa da sauran Matan Mijinyawa, domin macen da namiji yake so baya iya boyewa haka ya kasance domin Magaji ya kasa boye kaunar shi me girma akanta.
A lokacin Wabi wacce suna zuwa ya sauya mata suna zuwa Abigail, tana sa shekara goma. Yayin da Easter take da shekara bakwai. Tsana da tsangwama yasa baki daya basu sakewa a gidan sai Magaji yana nan, a hankali lokaci ya tafi. Ga damuwar gidan su Magaji yasa Jessica rokon shi alfarmar ya mai da ita gida, ta gaji ba zata iya zama a cikin gidan ba.
Fir yaki toh yana sonta, dan haka ta nemi taimakon Nahira, shi kuma ya roketa da ta bar musu Kyauta.


Ganin girman shi da abin da yake mata, akan matsalar Yarta yasa ta hakura ta bar kyauta, da saka idanun shi. A cikin yaran Magaji yasa mutane biyu suka rakata har garin su. Bayan wata uku suka dawo bayan an basu sakon Kyauta.
Haka yarinyar nan ta girma cikin wahala da azaba, idan Yaran gidan suka yi abu ita ake daurawa, ita kan ma ta saba abu na faruwa koda bata nan, ana fara magana zata ce ita ce.


Wabi idan tayi abu, karshe ita ce zata amsa akan ita ce, koda kuwa kashe Easter za ayi ita babu ruwanta, ita kuma Easter tana amsar laifin Wabi ne ba dan kome ba sai bata da kowa sai Wabi. Amma ita tana ganin ai dole Easter ta amshi duk abin da tayi domin ita ce karama.


Haka suka taso, kome ya faru zata ce Easter ce.
A dawo labari.
----
Jikinta yana rawa, taja da baya tana girgiza kai.
"Yanzu kin fi son ki ga an kashe yar uwarki? Haba Kyauta meye a cikin wannan duniyar da ban miki ba? Tun da Mamanki ta watsar dake na rike ki kamar nice na haife ki ashe ba zaki iya bada rayuwar ki domin Yar uwarki ba? Shi kenan ta je a kashe ta, Abigail wuce ki tafi a kashe ki, son kai da son zuciya yana tare da masu son dawwama a gidan duniya"
"Mama Uwa!" Abigail ya kira sunanta cikin kuka.
"Ki je bakome wadda ya miki haka Nahara ba zata bar shi ba, yara goma na haifa kece kawai naga girman ki, wayyo nayi asara na boni na lalace"
Riko hannun Abigail tayi, tana girgiza mata kai.
"Idan har na barki kika tafi waye zai kula da Mama Uwa kamar ki? Na amshi haka ba kome bane kake da saka ran samun shi. Na roke ki da ki kai Mama na wurin da aka binne ni" sannan ta share hawayen ta, ta juya ta fita daga dakin, ta wuce dakin Baban su. Ta zube a gaban shi tana kallon shi.
"Ban yi riko da Addinin mu ba, na fada hallaka na ci amanar Nahara, tsinuwa ya tabbata a kaina, zan tafi na isar musu da cewa nice na aikata zunubi mara iyaka, ka yafe min"
Daga haka ta juya ta fita daga cikin gidan, ajiyar Zuciya Mama Uwa ta sauke.
"Idan har ta mutu yau, tabbas zaki bar Nahara izuwa Deehar a can akwai rayuwa me albarka, zaki tafi can ki rayu koda a baiwa ce domin cika min mafarki na na haihuwar Kyakyawar Y'a irin ki"


"Mama ina ne Deehar?"
"Masarauta ce da take tsallaken ruwan Nahara, ki tafi can ki rayu domin ki nunawa Nahira cewa bai isa yayi kome ba. Alwashin sa akan Easter karya ne. Ke zaki rayu a cikin farin ciki da daula me yawan gaske!"


"Idan har haka ne toh ba makawa sai mun share tunanin me cewa ba zamu kai labari ba...
500₦
Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*




Mai_Dambu...


BABI NA SHA HUƊU (14)


Matsowa ya yi kusa ita, tayi baya tana kallon shi bakin ta a sake. Lashe bakin ta tayi tana zare idanu.
"Waye kai?"
"Nalado" ware idanu tayi sosai cikin tsoro ta ce mishi.
"Na gidan rumbun hatsi?" Lumshe idanun shi yayi yana budewa a hankali akan ta fess.
"Kin amince na kai maganar mu gaban Nahira?"
"A'a" ta mike jikin ta yana rawa,
Cike da mamaki yake kallon ta.
"Me ya sa?" Ya tambaye ta,
"Ai zaren ba irin yadin ba ce."
Ta fada tana mikewa, shima mikewa yayi.
"Jima mana"ya ce mata.
"Wai kai lafiyar ka? Yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login