Showing 42001 words to 45000 words out of 105295 words
Chapter 15 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
dai ba zan iya daukar shi ba ko? Tow matukar ya fadi ba zan iya lamuntar daukar shi ba."
Fuskar shi cike da mamaki yake kallon ta, kafin ya ce mata.
"Ai kuwa ina ganin idan ya fadi kece zaki goya shi.."
"Na shiga uku! " Ta zaro Idanu waje, waɗanda har sun cika da kwalla. "Amma bayan bautar da kuke har kashe mutane kuke ko? Ban da rashin imani ina zan kai Basamuden nan? Na rantse da Yesu babu inda zan kai shi domin wannan ko dan tsako ya taka ba zai rayu ba balle ni, da kuguna yake had'e da baya."
Shi kuwa Abid dake irin mutanen nan ne,masu Shegen tsokana ya ce mata.
"Ai fa sai kiyi amma kece zaki goya Yarima Abdullahi zan nime miki zanin goyi" ya fada mata yana murmushi.
"Amma gawata kake buƙatar gani ko? Tow kwantar da hankalin ka daga nan shekara dubu" ta fada tana hararan shi kamar kwayar idanunta zasu fadi ƙasa.
----
Kallon Namir yayi yana faɗin.
"Ina son ka dauko min Yarinyar, ina son yarinyar."
Shiru Namir yayi har ya bude baki zai magana, Galadima da Fulani Babba suka shigo zauren. Mikewa suka yi sai da Fulani Babba ta zauna sannan Galadima da su, suka zauna.
"Barka da maraici, Fulani Babba."
Shiru tayi na wasu dakikai, kafin ta ce mishi.
"Daga yau ba za a kuma kawo maka mace ba, kayi kokarin niman hanyar da zaka samu soyayyar yarinyar da take tare da shi. Kar ka sake ka nimeta da ƙarfi, Namir ka gaya mishi ka kuma tuna mishi a duk lokacin da yaji wani abu kar ya sake ya far mata, ita muke bukata tsawon shekaru dan haka ya iya takun shi "
Tana gama fadar haka ta mike bata kara magana ba, domin ba zata kuma magana ba haka take abin da ta sani ta bada umarni bayan nan kuwa babu wani abin da zata kuma cewa. Lumshe idanunshi yayi kafin ya bude akan Namir yana me sake murmushi.
"Namamajo ka dai ji ko? Tow sai a bi kome a hankali."
----
Mulikah Hamid Garkuwa, ya ce ga garkuwar Deehar yar da tazo akan girma da shekarun iyayenta. Tana da yayu maza da mata, sai dai bata da Uwar domin uwar tana haihuwarta ta rasu. A hannun Garkuwa ta girma domin bai yarda da kowa ba sai kan shi. Kusan sa'ar Radiah ce.
Radiah 'Yace ga Galadima, bayan ita yana da wasu Yaran. Amma ita ya ajiye ta ne domin bukatar shi idan ya taso. Mahaifiyar Radiah kusan yan uwa ne ga Fulani Babba. Sai dai yadda Fulani ke nuna musu Yaran suna da daraja yasa Iyayen su,.hakura su bar mata su.
Kusan soyayyar da Fulani take musu ba wata azo a gani bane, kawai tana kallon Yaran akan wata rana zasu zame mata kibiya me linzami da zata cilla zuwa ga gadon bayan makiyanta. Kuma tayi kokarin kulla ƙawance tsakanin Radiah da Mulikah, wanda baka gane meye damuwar su.
Haka suka taso, a duniya babu yarinyar da Fulani Babba ta tsana kamar Aliyah bata kaunar yarinyar nan, musamman da Aliyah ta dauki yanayin Fulani karama, hatta maganar ta, haka yasa ake mata kallon kamar Fulani karama ce. Gata da hakuri kamar me shi yasa Fulani Babba take jin haushin ta. Kishin da suka yi da kakarta ya dawo kan yarinyar, sannan ta nunawa su Radiah su musguna mata.
***
Sallama yayi ta kwad'awa can ta fito tana kallon shi.
"Kazo?"
"Ih gani nan, ina yake?"
Nuna mishi dakin tayi da bakinta,
"Fito min da shi"
"Kayan wanki ne da zan fito da shi?"
Ta rike kugunta, tana kallon shi.
"Ih tow fito min da shi." Nufar dakin shi. Yana tsaye daga shi sai wata yar zani da ya daure kugun shi, daga kafa ta fara kokarin kallon shi har zuwa kugun shi. Gabanta ne yayi mugun faduwa ta zaro idanu waje.
"Wayyo na shiga uku!" Ta juya da gudu ta bar dakin, tare ta Abid yayi yana tambayar ta lafiya?
"Wayyo ni ban ga kome ba!" Kallon kofar dakin yayi, yana mamakin yadda ta rud'e.
Nufar dakin yayi ya same shi yana niman kayan shi, dariya ne ya kwace mishi, daukar rigar shi yayi ya mika mishi, yana dariya kai kyautah sai a hankali wato ganin shi tayi babu kaya shi ne ta rud'e.
A wurin saka wando ya juya bayan shi. A hankali ya saka wandon ya daure zariyar sannan ya juya. Kallon gefen yayi a ran shi ya ce.
"Ubangiji me halitta ko wace ce zata iya daukar wannan al'amarin?"
Hula ya saka a hankali ya daura rawani a kan shi, ba karamin kyau yayi ba. Rufe fuskar shi yayi yadda saura kwayar idanun shi. Suka fito daga dakin, Abid yana mishi jagora har.
Dauke kai tayi, cike da kunya Abid da yake janta da hira sai dariya yake a ran shi.
"Kyautah!"
"Na'am"
"Kin san yadda masarautar nan take? Zaki iya mana jagora mu dan wasa kafa?"
"Ba kome zan iya" ta fada tana satar kallon Abdullahi. Wani irin bugawa gabanta yayi tana me dafe kirjinta. Numfashin ta yana fita da sauri da sauri. Lumshe Idanu tayi tana faɗin.
"Wannan dan renin hankali dube shi kamar na make shi" haka ta wuce suna binta Abid yana janta da hira har zuwa kasuwar dare. Haka suka yi ta zaga kasuwar duk abin da ta gani ya bata sha'awa ta yaba tow Abid zai saya mata.
Kamar daga dama ta hango Arshan, bata san lokacin da ta rike alkyabar Abdullahi ba, a hankali ta koma bayan shi tare da boye fuskar ta a bayan shi. A hankali abin da ya faru ya dawo mishi, d'ago kai yayi yana shakar kamshin turaren da yake da yakinin yau yaji shi. Kamo hannun shi Abid yayi ya ce mishi.
"Yarima Arshan yana zuwa"
"Shi ne ta boya a bayanai?" Ya tambayi Abid,
Sai lokacin ya lura tana bayan Abdullahi.
"Hmm!"
Isowa yayi yana faɗin.
"Makaho da dan jagora, tare da allura cikin ruwa, barkan ku kanne na"
Lekawa bayan Abdullahi yayi yana murmushi.
"Kyautah idan da alƙawari da Amana ruwa ba zai ci dan kada ba. Fito mana" sake riƙe rigar Abdullahi tai tana jin Jikinta yana masifar rawa.
A hankali Abdullahi ya maida hannun shi ya dawo da ita gefen shi, sannan ya janyota jikin shi, mayafin shi ne ya warware ta kurawa fuskar shi kallo, idanunta cike da kwalla. Lashe bakin shi yayi yana me kara riko hannunta, suka ci gaba da tafiya. Haushi ne ya kama Arshan ya dauki wani ya d'aga da niyyar bugawa Abdullahi, ita kuma ta juya kenan, baki daya ta rud'e wani irin wawan runguma tayi mishi ta baya, daidai Arshan ya sake mata sandar a bayan ta. Tafiya sukayi kamar zasu fadi ya koma ya tsaya cak yana jin saukar numfashinta.
K'amk'ame shi tayi kafin ta sake shi zata fadi ya rike hannunta, janyota yayi jikin shi ta tafi baki ɗaya. A hannun shi ya kai keyarta yaji kamar ta mutu, kara saka hannun shi yayi a wuyar ta.
Jikin shi ne yayi mugun sanyi, ya shiga juye juye kamar yana niman wani a wurin.
"Me ka aikata? Kai da Fulani Babba ta ce ka nime soyayyarta shi ne zaka kashe ta. Subhanalillahi me zan gayawa Fulani?" Jan shi yayi daga cikin mutane.
"Ta mutu ko?" Ya tambaya Muryan shi yana rawa,
"Ina zan sani tunda ka mata irin wannan dukar bai zama dole ta rayu ba."
"Muje Namir" ya fada suna kara shiga cikin mutane, koda suka je wurin kamar babu kowa, sai yan kasuwan da suke nuna shi. Su kuwa Abdullahi ya dauke ta inda ya sakata a kafad'ar shi Abid yana mishi jagora.
"Itama kashe ta zasu ko?" Ya tambayi kanshi, haka suka kashe Innar shi, suka kashe Iyayen Abid. Wani irin tausayin yarinyar yake ji, tabbas wanda ya mata haka shi ya shigo dazun bayan fitar shi. Bangaren shi suka shiga ya kwantar da ita a dakin shi, kallon Abid yayi yana son magana amma babu baki cizon bakin shi yayi yana me d'aga kan shi sama, kafin ya sake murmushin takaici. Kamar wanda ake jiran abin ya faru sai ga Galadima har cikin gidan shi da Garkuwa.
Abid ne ya fito sakamakon sallamar da Sarkin gida yake rangad'a musu.
"Akwai baki a zaure" ya fada mishi bayan ya riko hannun shi. Gyada mishi kai yayi, Abid yana fita ya had'e hannun shi wuri guda.
"Me zan yi da zan kare lafiyarta da Rayuwarta?" Ya tambayi kan shi,
***
"Ina Abdullahi yaƙe?"
"Yana cikin turakar shi." Kallon juna suka yi garkuwa da Galadima.
"Amma kar ya manta shi fa Yarima ne, kuma Basarake bai dace yana hada inuwa da kaskantaciya baiwa ba"
"Ih tow, naga ai ba sabon abu bane akwai yan lele shafaffu da mai ai har kwanciya suke da kaskantanttun bayi" Ya Musa ya bada raddin abin da Galadima ya fada.
Shafa gemun shi yayi yana faɗin.
"Me abu da abin shi kura da kallabin kitse idan bai yi ba waye zai yi? Ko ance maka shi lusari ne yana da lafiya da haka zamu fahimci ko dari aka ajiye mishi zai zauna da kowacce."
"Baba Galadima ba a san maci tuwo ba, sai miya ya kare idan har aka ce jarumta ta ce tow kuwa ba mamaki kowa yana shirye ya gwada haka. Balle babu wanda yasan yadda inda rana zata fadi tayu ta fito ta gabar ta fadi ta arewa" inji Yarima Shehu,
Dariya Garkuwa yayi yana kallon Abdullahi da ya fito tare da tura sandar shi.
"Ba mamaki hasashen ku akan wancan nakasashen ne ko? Tow gamu dai ga garin Deehar bamu sani ba ko an fara sarakuna makafi ne hala"
Kallon yadda Galadima yayi maganar yasa jikin su yayi sanyi, Uwar Bayi da me maganin Masarautar suka shigo, murmushi Abid yayi ya ce mata.
"Tana wancan dakin" ya nuna mata dakin suka shiga, kin bin su yayi domin yana son yaji yadda suke gayawa kan su magana.
"Tunda jikin da sauki shi kenan"
"Sauki na Allah ne, kuma zai bata lafiya ban san me yasa ba a koyawa Yarima mu'amala da mutane ba, yake iya daukar doka a hannu baya tunanin haka ya zame masa kalubale ba ne?" Yarima Shehu ya faɗa, yana gyara zaman shi.
Shiru suka yi, sake murmushi yai ya ce.
"Ko da yake me Uwa a gindin murhu!"
Fuuuu suka bar gidan.
" A sauka lafiya!"
----
"Mama Uwa kinji labarin kyautah kuwa? Ance Yarimar da aka dawo da shi nan ya dauke ta tun daga kasuwar dare har cikin bangaren Yarima Shehu." Inji Wabi.
"Mtseeeeeew! Waye ya gaya miki Yarima Abdullahi zai yi wani abu? Yaron da ko a Masarautar bai da wani amfani, fatana kawai ki dauko cikin Yarima Arshan shine burina yadda zaki zauna a cikin masarautar yadda zaki iya goggaya da kowacce mace gaba ma kece uwar Sarkin Deehar " yadda Mama Uwa, suna wannan maganar ne a kunnen Ladi kuma yar dakin Uwar Bayi ce, domin basu zaci wani yana wurin ba.
"Mama idan kuma ya samu lafiya fa? Domin naji ana cewa yafi kamar da Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye sama da Arshan, sannan dabi'un shi tafi kamar da wanda yake jiran mulki Mama kiyi wani abu domin ban tab'a ganin shi ba, kuma na tambayi Easther kamanin shi bata ce min kome ba"
"Zan duba maganar ki kuma"
---
Sai kusan tsakiyar dare suka gama bata kulawa, suka fito har Uwar Bayi.
"Ki zauna da ita Uwar Bayi tana buƙatar mace a kusa da ita" inji Abid,
"Tow ranka shi dade" fuskar shi dauke da mamaki ya ce mata.
"Ranka shi dade ai sai Abdullahi "
"In sha Allah kai ne zaka zama mana Wazirin Deehar nan gaba dan haka, ka fara shirin amsar sunan ka daga yanzu "
"Ya Musa bai yi tsauri ba? Ka dai duba al'amarin da kyau....
(Kuyi hakuri nayi Bakuwa ce sai yanzu na samu kaina😂)
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
.....................................
Da gayya ta take mishi kafa, banza yayi kamar bai san abin da tayi ba, kawai jikin shi ua bashi ita din ce, shi yasa ya yi kamar bai ji ba. Sam ya kasa gane meye matsalar yarinyar tayi masifar rena shi.
Yana isa wurin tsohuwar bishiya nan kuwa, gud'a aka sake tare da buda algaita. Wannan yasa suka fahimci akwai rina a kaba, domin an kashe maciji ne ba a sare kan shi ba. Duk da an basu tsohon shashin su, fir ya Musa yaki amsa, ya ce a kai su ɓangaren Yarima Shehu. Kuma haka aka yi can aka kai su, ganin haka yasa Kyautah sulale kamar bata san kome ba, ta nufi ɓangaren su na bayi.
Tana shiga suka yi kicibis da Wabi.
Kura mata ido tayi, kafin ta sauke numfashi ta ce mata.
"Daga ina kika?"
"Waje" ta bata amsa, tana takawa kamar ba ita ba.
"Kyautah kin fara bin maza ne?" Cak ta tsaya kafin ta cigaba da tafiyar ta.
"Kice abin da yasa baki iya zama a cikin gidan nan kenan, kin san dadin su da yadda suke." Cikin fushi ta juya ga Wabi, rai a b'ace.
"Idan na fara hada shimfida da namiji, har abada ba zai kuma barci cikin kwanciyar hankali ba,.idan kuma soyayya na fara da shi, rayuwar shi zai bada domin kare tawa, dan haka ki iya da bakin ki."
"Idan ban iya ba fa? Ke har wani abu ne dake? Ke fa tsinanniya ce wacce alummar Nahara suka tsinewa. Wacce tabi namiji,.ta janyo mana masifa da bala'i a cikin garin mu." Ta fada da karfi, haka yasa mutane dayawa suka fara tofa albarkacin bakinsu. Kasa magana tayi idanun ta jajjur, taya zata wanke kanta? Waye zai yarda bata taɓa lalata kanta ba. Cikin bacin rai ta juya abinta bata kuma musu magana ba.
Tana shiga ta hadu da Uwar bayi, ranta ya gama b'aci.
"Ina kika boya?"
"Hmm!"
"Ina kika boya?" Ta daka mata tsawa,
Kasa magana tayi jikinta yana rawa.
"Durkusa" durkusawa tayi, ita kuwa ta fita can sai ga ta tare da dogarai hudu.
"Ku zane ta, sannan ku kaita wurin Yarima Arshan."
"Tow"
A can gidan Yarima Shehu, tun da aka kai su gidan, Fure da tare da Aliyah suka shiga aiki. Suna gamawa suka shirya ɓangaren.
"Fure ko a dauko kyautah ce tazo ta kama musu kula da gidan?"
"Ih, kuma kin kawo shawara."
Fitowa suka yi Fure tayi ta cewa Yarima Shehu.
"Allah ya baka nasara, ko zaka tura da a dawo da Kyautah domin ta cigaba da aiki."
"Tow Fure, Ya Musa muje da kai."
Haka kuwa suka fita tare har bangaren bayi, abin da yasa suka tafi da kansu saboda hukuncin Fulani Babba na hana kowa daukarta idan ba Yarima Arshan ba.
Suna isa suka samu ana zage ta, rike hannun Bafaden Ya Musa yayi yana faɗin.
"An yantatta daga yau ta koma bangaren Yarima Abdullahi da aiki.'
Fitowa Uwar Bayi tayi cikin girmamawa ta ce.
"Barka da hanya Yarima Shehu." Kura mata Idanu Ya Musa yayi, kafin ya dauke kai. Yana son tuna inda yasan muryan. Sam bata mishi kama da wacce ya sani ba. Sunkuyar da kai yayi.
"Mun zo a bamu Kyautah ce" ya fada yana kallon ta da take share kwalla.
"Kyautah bata jin magana, idan aka baku ita jan magana zata cigaba da yi karshe a korata"
"Idan kana cikin Deehar dole ka koyi jan rigima ta haka za a fahimci waye kai. A bata kayanta ta koma karshen Abdullahi" inji Yarima Shehu.
"Allah ya baka nasara, shi kenan ta shigo ta ɗauka."
Sake d'ago kai yayi ya bi bayanta da Idanu zuciyar shi tana rawa, anya ba ita ba ce? Muryan ce kawai.
Haka ta shiga cikin dakin su, ta dauki kayanta.
"Ki kula da shi