Showing 63001 words to 66000 words out of 105295 words
Chapter 22 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
jin shashekar kukan ta, har aka kawo abinciin, zoben arzufan shi ya jefa a cikin ruwan madaran, yasaka ludayi ya ciro, kafin ya goge sannan ya saka a cikin sauran abincin. Babu guba ya dauki abincin ya kai mata dakin, tana hade da kai da gwiwa tana ta kuka. Ajiye mata abincin yayi ya juya zai fita yasan halinta bude akushin dage-dagen yayi, sannan ya dauki madarar ya bar mata, munafika tana jin kamshin miyar dage-dagen ta d'ago kai ta gan shi tsaye, dauke kai tayi tana tura baki.
Komawa yayi zai dauke tiren ta ce.
"Kuma sai a hana mutum cin abincin?" Ta sauko ta fara diban dage-dagen da alkubus. Tana ci tana girgiza kai, mamakin halin ta yake bata da wuyar tsoro bata da wuyar sha'ani kamar me aljanu. Fita yayi sam ya manta yana da abubuwa dayawa a gaban shi, a zauren ya taras da Abid, yana kunshe dariyar shi, wani taune fuska yayi yana kurban madaran hannun shi. Sauke kofin yayi yana kallon Abid.
"Meye?"
"Wai naga har kun shirya"
"Uban waye yace muna fada?"
....500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
......... Wabi a tunanin ta yadda suke shiga jikin kyautah su cuce ta, haka take tunanin zata kuma shiga da sauki har ta samu Abdullahi. Haka suka gama wanki ta haɗa kayan suka nufi bangaren Uwar Bayi, tana bin Kyautah kamar wata jela, ita kan Uwar bayi sai da ta shinshino akwai wata a kasa, amma dake taga Kyautah kamar ta sake da ita yasa itama sai ta share amma tana kallon dukkan motsin su.
;;;;;;;;;;;;!;;;;;;;;
Tafiyar kwana uku ya kai su garin Firta, yadda garin yake yasa shi jin wani irin abu yana yawo a kan shi, garin kamar wata dausayi ne kome ka gani a garin Kore ne shar kasancewar garin yana gaɓɓar ruwa, ga albarkatun noma ta ko ina, gaskiya ba zai boye ba, garin ba na zaman mara mata bane, domin yana shiga garin yanayin shi ya sauya, yana jin wani irin shauki da bukatar mace, idan ya lumshe dara-daran idanun shi, kyautah yake gani tsaye a gaban shi. Haka yasa shi fara azumi, domin yanayin sanyin garin yana shirin kawo mishi tarnaki.
Abid ya lura da shi, sai ma abin yana bashi dariya.
"Idan nayi aure garin nan zan zo na barje amarcina da Amarya domin bana son yanayin garin ya wuce ban murza mace son raina ba" tsuke baki yayi tare da haɗe cinyar shi, yana zare idanu domin maganar Abid ya haifar mishi da jin kwarya-kwaryan damuwa. Kasancewar Sarkin Yaki ya turo musu inda zasu sauka, kuma al'amarin suna son yin shi kafin lokaci ya kure yasa kwanan su uku a garin suka shiga cikin dajin garin, sai da suka yi tafiyar kwana uku me kyau kafin suka isa wani kogon dutse.
Yadda suka ga hayaki yana tasowa daga can yasa su fahimtar yadda al'amarin yake, dama kuma an gaya musu yawan mutanen.
"Shigar Asuba zamu musu"
"Na zata shigar dare ne domin zai fi kyau"
"Shigar ragwayen maza ne, mu yi musu shigar asuba. Ta haka zamu iya yakar su, idan muka shiga da dadare zasu warwatsu har su cutar da wasu mutanen amma shigar asuba sun gama shashancin su, har sun gaji."
"Bani kyalena" bude wani karamin akwati yayi ya ciro wani bakin kyale, ya daura a saman fuakar shi, sannan ya haura bishiya ya kwanta, domin bayan isha suka isa wurin, shima Abid hawa bishiya yayi ya kwanta, yana wasa takobin shi da majajjawan shi har Abdullahi ya fara barci, murmushi yayi yana kallon yadda yake barci. Daukar mazubin kwarin shi yayi ya shiga faike bakin kwarin har zuwa lokacin da barci ya fara diban shi. Ƙwanciya yayi shima yana me ajiye kome.
Abin da ya faru da shi na Yaranta shi ne yake dawo mishi, a hankali ya bude idanun shi, ganin mutumin nan ne da yake bibiyar shi, amma sai yayi kamar bai gan shi ba, dan baya son mu'amala da mutanen boye, duk da daga dawowan shi sun zo tafi a kirga da alamun akwai abin da suke bukata daga gare shi ne.
"Kyautah tana cikin ƙwanciyar hankali" kamar bai ji ba, ys cigaba da gyara ƙwanciyar shi.
"Abdullahi kana jin mu fa, Mahaifiyar ka tana raye" bude idanun yayi ya zuba masa.
"A duniya wadannan sune abubuwan da suke raunin ka, ka nimo mata tana cikin gidan sarautar Deehar dan haka ba zance kome ba akwai gwanayen harbi suna nan kuma nasan zasu yi iya nasu ƙoƙarin, ka kula kar mata biyun nan su zama rauninka, da su makiya zasu zasu yi nasara a kanka, kayi hakuri na fadi haka ne domin ka saurare ni, mahaifiyar ka ta rasu tun a wannan bakar laraban"
"Me yasa zaka ce min tana raye? Bayan kasan bata raye?"
"Kayi hakuri, nayi kuskure ina son magana da kai ne" juyar da kai yayi yana hadiye wani abu a wuyar shi yayi bai kuma bin ta kan shi ba, wani irin kunci yake ji, a duk lokacin da ya tuna bai da ikon goge ranar, yana ganin yadda barde ya jifa mata mashi, har yau zuciyar shi tana ci da wuta, a duk lokacin da yayi ido biyu da Barde gani yake kamar kisar gilla bai dace da Barde ba, asalin kisar mummuke ya dace da shi wanda zai ta fatan ya mutu ya mutu amma yana raye.
Haka ya raba daren yana me raya shi da ibada dan saukowa yayi ya gabatar da Alola sannan ya yadda sallah, har goshin asuba, ya tashi Abid yayi Sallah shima, sannan suka fantsama bayan dutsen, wani irin mahaukacin sumame suka kai musu, wanda suka farmakin da basu zata ba.
Ihu da kururuwan maza ya cika daji,
Kafin wani lokaci wurin ya kacame da jini, yadda Abdullahi da Abid suke, wani irin juya majajjawan hannun shi yayi, ya wurgi wani da yake kokarin gudu, kawanya yan fashin suka mutu dauke da makamai masu tashin hankali. Hada bayan su suka yi.
"Kaico wadannan basu san inda suka fada ba ko?" Inji Abid.
"Ba mamaki lahira tayi baki, bari na ajiye tsohuwar dabi'a, bani gatarin da yake kugunka" inji Abdullahi,
"Cab ba zan iya baka gatarin nan ba, domin ina kaunarta kamar raina"
"Amma dai kai banza ne"
"Ga wata lauje can dauka mana"
"Taya zan dauki lauje bayan aladu suna zare min idanu "
"Kaii Ya ishe ku haka,"
Saka yarda biyu Abid yayi a bakin shi kamar me tunani ya ce.
"Kuma haka ne fa, dan haka bari mu sassanta kan mu." Kafin su an kara sun sake yin kan yan fashin da wani irin zafin nama, wurga mishi gatarin yayi, suka shiga dauki ba dadi. Kururuwan maza ya haifar da guje gujen namun daji, basu tsaya ba sai da suka karar da su baki daya, a cikin haka wani ya shammaci Abdullahi ya yanke shi, ai kuwa sai da ya cire mishi hannu tun daga kafad'ar shi, sun jike jagwab da jiki. Komawa saman gawarwarkin suka yi, suka zauna.
Saura mutum daya wanda shine ya yanki Abdullahi.
"Haka kawai ba zaku shigo wannan dajin ku yake mu ba, waye ya turo ku?" Zare rawanin kan su, suka yi Abdullahi ya ce.
"Abdullahi Hayatudeen Abdullahi Noye!"
"Abid Jafar Abid Noye!"
Tari mutumin ya fara, sannan ya tofar da jinin da yake bakin shi ya ce.
"Kamar yadda hayatudeen da Jafar wazirinsa suka zo wancan lokacin, haka kuka kara zuwa ai!"
Dariya ya saka tare da rike inda yake zubda jini.
"Masarautar Deehar cike take da mubafukai, masu amfani da kowacce irin dama, a haka sai da Sarki Hayatudeen da Waziri Jafar suka haifar da gaba a tsakanin su, domin gano wadanda suke kokarin ruguza mulkin shi, amma basu cimma matsaya ba, abin da na sani shi ne tabbas kuma ba kyale ku za ayi ba, domin kowa yana cike da ku. Aikin mu shi ne tadda tarzoma ne, dan haka ba zan iya baku labarin su waye suke shirin su. Gara ku kashe ni "
"Wannan bai da amfani" Inji Abdullahi.
Rike hannun shi Abid yayi sannan ya kalli dan fashin.
"Kyale shi, akwai wata gaskiyar da yake boye"
Ya fada cikin harshen fulatanci, sake shi yayi ya koma gefe.
"Waye yake turo muku makamai"
"Ta hannun Barde ake turo mana kome, iya shi ya san kome" yana gama fadar haka ya dauki wani takobi ya soke wuyar shi, Mikewa yayi yana kallon Abdullahi.
"Banza mara lissafi, Barde yake turo musu kome"
"Kyale su namun daji zasu cinye jikin su" daga haka juya.
Haka suka wuce gulbin da yake dajin, cire kayan shi yayi ya shiga cikin ruwan, kallon shi Abid yayi yana faɗin.
"Dan Iska yanzu kunzugu kake?" Wankan shi yayi domin bai da lokacin kula Abid.
Daga can Abid ya hango wani abu yana tawowa a cikin ruwan.
"Kai ga wani abu nan zuwa "
"Miko min wukar ka" cire wukar yayi ya cilla mishi, ya nutse cikin ruwan, yana kallon wani fusataccen kada, yaji karnin jini yasa shi biyo su. Ai kuwa ganin Abdullahi ya nutse shima ya nutsu, suka kama wani jahilin fada, sai juyi suke kamar zasu kashe kansu, wato kadan nan da yasan cewa zuciyar Abdullahi a fusace take da bai fara zuwa wurin shi ba, sai gashi kafin kace kwabo ruwan gulbin ta baci da jini, a hankali kadar ta dawo saman ruwa. Murmushi Abid yayi yana faɗin.
"Da kyau namijin duniya" fitowa yayi yana jan kadar, ya ajiye shi ya sauya kayan shi tare da saba kadar a kafad'ar shi suka bar daji, koda suka shiga cikin gari ganin su da kada yasa mutanen garin suka fara kokarin niman sanin a ina suka samo, su kuma suka ajiye musu suka bar kauyen. Tafiyar kwana uku ya kawo su gida, kafin su iso ma labari ya karade Deehar ga wasu mayakan fatake nan zuwa.
---
Bata kawo a ranta yau zai iya dawowa ba, dan haka Wabi ta dauke ta suka shiga cikin dajin da yake bayan masarautan.
"Abigail na gaji wannan tafiyar yaƙi karewa"
"Dalla can yanzu zamu isa, ina son magarya ne"
"Tow" ta fada tana kallon dajin yadda ya cika duhu, haka suka cigaba da ratsa dajin, sai da suka iso kasar wani bishiya, suka ga wasu mutane na saukowa a kasan Bishiyar, kallon Wabi mutumin yayi ya gyada mata kai.
"Wabi" Kyqutah ta kira sunanta a tsorace.
"Ke babu abin da zasu miki." Ta fada tana kallon mutumin ya tawo. Zai kai hannun shi jikin Kyautah ta ce.
"Kar ka fara yin abin da zaka yi danasani, Idan Yarima Abdullahi yasan cewa hannun ka ya tab'a jikina sunanka gawa" fisgota yayi ya haɗa da jikin shi.
"Yarima Maloho ko Yarima makaho, babu abinda za iya min, ke kuwa naji ance sun tafi yawo ki bari na miki abin da yake miki mana, babu zafi ai keda kike daukar maza biyu ga Abid ga Abdullahi, wai tukun waye jarumin ki a cikin su."
"Wabi kice ya bari" ta fada idanunta yana cika da kwalla,
" Ka bari mana, ina zuwa" tayi tafiyar ta.
"Wabi!" Ta Kwala mata kira,
"Kar ki bar ni a wurin su mana, na hadaki da Abin bautar mu kar ki tafi"
"Dalla can ba tafiya zan yi ba "
"Wabi!!" Ta Kwala mata kira banza tayi da ita, kuka Kyqutah ta fashe da shi, tana kokarin kwace kanta.
---
Sun samu nasarar shigowa Deehar bayan sub bude fuskokin su, kallon juna suka yi da Sarkin Yaki Uzairu, da idanun ya yi mishi magana, sannan ya wuce cikin Masarautan, lokacin da suka nufi fadar Uwar Bayi ta tare shi da bakar labari.
"Abdullahi Yar uwan Kyautah ta dauke ta, sun fita bayan masarautar nan, kuma akwai wasu daga cikin yan iskan bayin da suke tare yan mata idan suka shiga yin iccen girki." Sauka yayi akan dokin ya wuce wurin Sarkin dogarai, ya amshi bulalar hannun Sarkin dogarai ya juya kowa sai mamakin shi suke dama yana gani, labarin da ya karade Masarautar wasu basu yarda ba, sai da suka gan shi ua hau doki ya shiga kofar bai, Abid ya rufa mishi baya.
Haka suka nausa cikin dajin, da azzaben gudu. Tun daga nesa ya hangota daure a bishiyar sun mata tsirara. Wani irin jan linzami yayi ya kalli Abid idanun shi cike da kwalla.
"Duk wanda ya kalli tsiraicin matar da take gefena kome karfin amintar mu zan kashe shi Billahi azim!" Jin haka Abid ya juya da dokin shi, ya basu baya, wukar da yake kugun shi ya wurga, tsinke giyar tayi ta, kasa motsi tayi yana isa ya cire rigar shi ya lullube ta da shi.
Idanun shi cike da kwalla yana tsugune a kanta, ga bakinta da hancinta da suke zubda jini. Wani irin zafi yake ji a kirjin shi. A hankali ya mike.
"Laaa Ashe yana gani"
"Abid" ya Kwala mishi kira.
Tawowa yayi, ya kalle su.
"Kawai ka kashe su" ya bawa Abid Umarnin haka, daukar ta yayi ya bar. Shima dake ran shi ya ɓaci, ainun baya kaunar ganin bacin ran Abdullahi don haka ya wuce Haushin su ta hanyar musu wani irin kisan Wulakancin wanda tattara su ta daure gawarwarkin su a samar bishiya. Sannan ya bar su a wurin ..
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
.......... Gyara mata kwanciya yayi ya d'aga ta daga jikin shi, yana me Mikewa ya koma gefe, ya dauki akushin ruwa yayi alola. Wani irin sanyi ne ya gallabi wurin ya koma kusa da wutar ya haɗa wuta sosai, sannan ya fara sallah,bai tsaya ba sai da alfijir ya keto, sannan ya gabatar da sallah asuba ya zauna yana lazimi har gari yayi haske, bai ta she ta ba. Har gari ya waye tar hasken rana ne ma ya dame ta, ta farka tana kallon shi yadda yake ta haɗa wuta. Ganin sabin akushi yasa ta mikewa, ta nufi Abincin, daukar sanda yayi ya saka a tsakanin su da Abincin.
"Basamude"
"Kamata yayi ki wanke fuska da bakinki ko?" Sosai kai tayi tana faɗin.
"Hmm! Haka ne." Wucewa tayi ta dauki wani irin gora da ta gani a wurin da ruwa ta zaga cikin gidan su, ta kama ruwa ta wanke fuska da baki sannan ta dawo wurin shi. Ta zauna tana kallon shi.
"Basamude na fara ci, yunwa nake ji"
"Suna na Abdullahi Noye"
"Hmm! Ni nafi jin dadin Basamude" ta fada tana kai hannunta cikin tasar da take hango soyayyen kwai. Haka ta fara ci tana kallon shi.
"Kar ki cinye ki bar ni "
"Allah ya baka hakuri idan kace kar na ci sai na barka maka abin ka"
"Hmm" ya fada yana kallon ta domin duk wanda wannan bayanin bai hanata zuba loma ba, rike hannunta yayi ya kai lomar da ta dauka na kifi bakin shi.
"Basamude karka cinye min yatsu"
Bakin shi ya kai har yana lashe hannun shi. Janyota jikin shi yayi ya ce.
"Ciyar dani domin idan aka yi auren haka zaki ciyar dani "
"Tab Allah ya tsare gatari da saran shuka."
"Tow ai sai dai ki hakura da yancin ku"
"Tow meye ya kawo maganar jiya yau."
Sake janta yayi suna matukar kusanci da juna, "kin san idan muka koma yau gobe da safe zaki zama matata?" Janye idanunta tayi daga cikin na shi ta ce mishi.
"Haka ake auren babu sanyawan albarkan mutane "
"Daurawa za ayi a masallaci, bayan sallah asuba, idan kina son kuma muna komawa a daura"
"Tow Basamude dauke ni a jikinka, kunyar ka nake ji"
"Ai da gaske? Keda kika ganni babu kaya" ya fada yana kallon yadda ta rikice kamar a lokacin take ganin shi babu kaya. Matseta yayi yana magana kasa ƙasa.
"Gaya min kin gani ko baki gani ba?"
"Abdul" ta furta muryanta na rawa, har tsakiyar kan shi yaji sunan don haka ya zuba mata idanu.
"Matar Abdul!"
"Bar" hade bakin su yayi a karon farko a rayuwarsa da ya sumbaci mace, idanu ta zaro waje cikin tashin hankali da fargaba, yadda yake cinye mata bakinta, abinka da wacce bata saba ba, sai ta fashe da kuka ta shiga dukar kirjin shi tana ture shi, dakyar ya sake ta, ta koma can gefe zamanta akan cinyarsa ya haifar mishi da abubuwa dayawa kamar kar ya daina.
Kuka take tana komawa can gefe jikinta yana rawa kamar an saka mata wuta.
Kuka take tana ja da baya,
"Na fasa auren"
"Tow kin ga kuwa ai kun zauna a bayi, Arshan da Namir zasu cigaba da farautar ki da abin da kike takama da shi" ya fada idanun shi Jajjur.
Yadda ya cinye mata baki, sai shafa bakin take yana lura da ita ya share. Bayan ya gama tashi yayi ya shiga kokarin barin wurin ta mike itama tana bin bayan shi, wunin ranar sun yi shi ne a cikin Nahara, kafin suka juyo bakin ruwa, jirgin ruwa suka samu me kyau, ya tsaya ta shiga sannan shima ya shiga, yau taga ikon Allah domin jirgin da kan shi yake tafiya kuma da sauri. Sai da suka kusan shiga Deehar ta ce mishi.
"Na yarda da auren da gaske zamu samu yanci a cikin wata goma?"
"Ni na fasa"
"Abdul" ta furta tana rufe bakinta, domin kar ya kuma cinye mata bakinta, wannan mugun abun da me yayi kama?
"Kayi hakuri"
"Idan kina son daga yanzu zan kafa sharadi na"
"Naji!"
"Zan na zuwa dakin ki hira 1, Zan na tab'a ki a lokacin da yayi min 2, zan na niman ki idan zan yi wanka 3, dole ne kina zama kusa dani 4, kuma babu musu a zaman mu, kuma dole kina ado da rufe jikin musamman gashin ki 5, bana son ina ganin ki Idan Abid ya zo min 6, ban yarda na kuma ganin ki da Wabi ba 7, sune dokoki na"
"Yanzu babu ragi