Showing 3001 words to 6000 words out of 105295 words
Chapter 2 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
ina mulki. Sai dai na kasa fahimtar A ina matsalar nakasar da Ahalin sarauta suke samu? Nayi bincike ga aljanu da mutane sai dai al'amarin da daure kai! Amma na kuma fita ko zan samu maganin ciwon Ahalin Noye da suke rab'e a cikin Masarautan Deehar _
Daga nan ya kuma buɗe shafi da aka yi rubutu da tawada a kai sannan ya cigaba da cewa.
_Tabbas a iya shekarun da suka rage min zan yi kokarin kawo karshen rikicin da yaki ci yaƙi cinyewa na matsalar nakasar Ahalin masarautar Deehar. Sai dai bani da tabbacin hakan me yiwuwa ce domin na fahimci akwai musababbin da mafarin haka! Zan yi kokarin ganin nayi koyi ga Magabata na! Ko Allah zai saka a samu wanda zai hana haka? Sai dai nasan baki daya zuri'a ta, nakasassu ne! Da wannan nake muku fatan Alkhairi _
*HAYATUDEEN ABDULLAH NOYE*
Kallon juna suka yi ba tare da sunce kala ba, domin ya tabbata dai ya boye wata kusurwa.
Haka Alkali yayi gyaran murya sannan ya ce musu.
"Marigayi Hayatudeen yayi tafiya ga manyan masarautun ƙasar Hausa, dan haka zamu fara bincike ta can za a tura jakadun mu, ko ina idan yaso idan aka samu ya ajiye sad'aka a tawo da ita domin ta haifi abin da take dauke da shi, domin samun damar yin adalci ga kowa dan haka babu rabon da za ayi dole sai an samu inda ya ajiye sad'akar shi sai a san abin yi"
"Allah ya hutacce da mutane wahala."
Haka aka wakilta amintattun dakarun Masarautar aka raba su tare da tabbatar da an basu nan da kwanaki arba'in su kawo duk matar da aka tabbatar da ita din sad'akar sarki ce.
Abin da ya dagula musu lissafi ba kome bane sai b'atar dabbon da Ya Musa yayi domin dai babu shi babu labarin shi. Dan haka
A kowanne bangaren kokari suke ace an samu nasarar samun matar sai dai abin mamaki tsawon kwanakin da suka dauka da yawon da suke na bin masarautun yankin baki daya babu labarin haka. Sannan an yi matukar bincike masu bin bokaye da yan bori suna yi, masu bin kome ana yi amma babu labarin kaf hankalin su ya tashi.
★
A gaban wani kasungurmin boka suke zaune wanda ya raba kasa da sama yana zaune akan iska ya kyalkyale da dariya sannan ya ce musu.
"Ku gama wahalar ku, tabbas haka zai faru kuma ma nace ya samu, sai dai zamu yi kokarin tura wakilan mu a duk inda suke su kawar mana da su, amma kusani mulkin nan da kome zai iya zama a hannun ku. Amma bai zama dole ku samu yadda kuke so ba.
Ba mamaki hakkin jinin shi ya saka ya bibiye bakar inuwa, wacce zata haifar da masifa da bala'i, idan kuka yi imani da haka zaku cika dukkan muradin shi zai iya zama kariya a gare ku"
"Ya shugaban mu, mu masu biyayya ne ga duk abin da ka saka mu akai koda kuwa haka zai kai ga bada rayuwar mu ne, so muke Deehar ta zama gaggarabadau ga tsararrakinta, tafi kowacce masarautar mulki yadda za aji shakkar tunkarar mu."
"Anyi muku lamani"
★
Yau kwanaki hamsin da rasuwar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, a hankali mahaya dawakan suka isa cikin masarautar, suka shiga cikin sassarfa sannan suka nufi bargan dawakai suka ajiye dawakan. Suka nufi kofar fada.
Suna shiga suka zube tare da kwasar gaisuwa.
Kallon Juna suka yi sannan suka ce.
"A bisa binciken da aka tura mu, toh zamu iya cewa Alhamdulillahi sannan gefe guda wasu Wuraren babu nasara, sai a wani ƙaramin gari ne da muke tsaya kafin mu isa masarautan kwantagora. Mun samu labarin Marigayi Sarki Hayatudeen ya tsaya a garin inda ya sayi wata baiwa suka wuce. Sannan muka shiga ga masarautar kwantagora inda muka samu wannan baiwa me suna Deli.
Sai dai mun so dawowa da ita amma Sarkin kwantagora ya hana mu dawowa da ita inda ya ce mana.
Ba zai bada ita ba, domin sai ta haihu ko kuma a turo wasu manyan da zasu tafi da ita gudun kar a halaka da abin ita da cikin ta"
Shiru fadar ya dauka wato duk yadda aka so hana dauko wannan al'amarin sai da aka samu waɗanda suka binciko ta. Dayawan ransu yayi mugun B'aci dan haka suka boye domin kar su fitar ya zama matsala...
*NAHMIFAK*
_Collections_
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
*Ba a san maci tuwo ba sai miya ya kare*
Taku har kullum
#Mai_Dambu
Saturday/November/2023
*Hausa Historical Ancient*
*......DASHEN ALLAH 🌳*
EXQUISITE WRITERS FORUM
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
Mai_Dambu...
BABI NA UKU (3)
Ransu ya yi matukar b'aci amma sanin a kwai zagon kasa yasa baki daya babu wanda ya ce kala, sannan a ka shirya manyan dattawan Fadan Galadima da wasu mayaka kimanin dari biyu, suka nufi masarautar Kwantagora. Da yawan waɗanda suka nufi can kwantagora wasu zuciyar su biyu, domin sun tafi ne domin wata manufa nasu na kan su.
Tafiya ce ta kwanaki da ba zasu wuce arba'in ba, ya kai su masarautar kwantagora. Cikin girmamawa a ka mashi jakadar Deehar kafin Mai Martaba ya musu iso akan bukatar su. Sun yi farin cikin jin haka. Sai da suka kwashe kwanaki kamar uku sannan a ka basu Zulai itace sad'akar sarki Hayatudeen. Suka nufi Deehar da ita.
Lokacin da suka isa dare yayi dan haka suka yada zango a cikin harabar filin da yake cikin Masarautar tare da bai wa Zulai kariya na musamman.
Cikin tsakiyar dare me ɗauke da al'amarin ban mamaki, wasu irin surutai marasa tushe da kan gado suka shiga tashi.
Sosai aka fara samun iska me tafe da guguwa wanda sun san cewa aika ce daga wasun su, kuma duk wannan abin ana yin shi ne domin kar cikin Zulai ya kai labari, don haka aka shiga aiko da miyagun jifa.
Irin wannan yana faruwa amma ba kasafai ba, sai idan an kusan Haihuwar Ɗa namiji a cikin masarautar don haka Galadima da Wanbai suka yi tsaye tare da kare Zulai wasu dakarun suna masu mamaye ilahirin masaukinta.
Artabu ake har gari ya waye, sai da alfijir ya keto sannan waɗannan ababe suka sarara bayan sun fasa wata ƙara me ƙarfin gaske. Sannan suka tafi, ita kan Zulai tsoro yasa ta takurewa wuri guda. Har gari ya waye, sannan suka mata magana ta fito fuskar ta a kumbure domin bata rintsa idanunta ba daren jiya ba.
Jagora suka mata har zuwa cikin fadar masarautar, aka gabatar da ita.
"Ku kaita shashin gabar, a bata duk wani abin da take bukata" inji Waziri yana kallon ta.
Kafin ya mai da hankalin shi kan sauran mutanen Fadar ya ce.
"A saka idanu a kanta ita da abin cikin, domin bai zama dole su tsalleke yanayin gidan nan ba."
Shigowar Sarkin gida da wasu abubuwan ya zube su a gaban jama'a,
"Sarkin gida lafiya?"
"Wannan sakon ya iske shi a turakar Marigayi Mai Martaba."
Daukar takardan saman ya yi, ya mik'awa Maga takarda.
Buɗe takardan ya yi cikin kulawa yaga tambarin masarautar Rano.
Cike da mamaki yake kallon mutanen fadar, kenan mai Martaba kafin ya rasu yasan da za a nemi wannan sakon.
_ASSALAMUN ALAIKUM_
*BAYAN DUBUN GAISUWA DA BAN GAJIYAR RANGADIN DA KAYI, ALHAMDULLAHI AJIYAR KA TAYI YAD'O DA YABAN YA ALLAH YASA KA ISO LAFIYA*
SAKO
DAGA
SARKIN RANO
Ajiyar zuciya kowa ya sauke suna kara jin wani irin tsana akan Marigayi Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye.
"Ai sai a tafi Ranon ko a taho da ita, domin bata cikakken tsaro." Inji Chiroma.
Kura musu idanun sarkin yaki ya yi, sannan ya ce musu.
"Wannan matar itace Ya Musa yake tare da ita. Domin kuwa idan ba ita ba, toh akwai wani abu a ƙasa. Don haka ayi kokarin ganin a kawo ta, har da Ya Musan domin akwai wani abu."
A hankali Zuciyoyin wasu ya kasu gida-gida domin kuwa basu zaci haka ba, dan haka aka shirya dakarun na musamman karkashin jagorancin Wazirin Deehar da Shamaki, suka nufi masarautan Rano.
**
Tafiya kwanaki goma ya isar da su Rano, tare da samun tarb'a na musamman.
Bayan sun huta, Waziri ya shigo da zancen rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Tabbas Sarki Abbas ya girgiza domin abokin shi ne tun Yarinta, dan haka ya yi kasa da kai sannan ya ce.
"A kwai Yarinyar da ya gani anan tun zuwan shi kafin ya wuce rangadi, sunanta Kubra, Mahaifinta bayi ne da Sarkin Borno ya bamu su, lokacin auren mata ta Hadizah. Sune suka haifi Kubra suka mata takwara da mata ta. Yar ya gani ya amsa a matsayin sad'akar shi. Kuma ya yi wannan rangadin da ita."
Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya sauke ajiyar zuciya. Ya labarta mishi abin da yake faruwa.
Shiru Sarki Abbas na Rano ya yi sannan ya ce.
"Ya turo Ya Musa ko?"
"Eh Ya Musa yana tare da su, sai dai nayi alƙawarin kare rayuwar ta da abin cikin "
Jikin Waziri ne ya yi sanyi ya kalle Sarki Abbas.
"Idan alkawari ne nayi maka rantsuwa da Allah zan bada rayuwata domin kare uwar da ɗan!"
Sanin girman rantsuwa da Allah tare da girman Waziri ya mike tare da mishi iso cikin gidan, domin shi daya ya samu ganin Mai Martaba sarkin Rano. Shima din saboda a kwai kyakyawar alaka ce me karfi a tare da su.
Lokacin da suka isa cikin gidan, ya saka a ka kira Fulani Hadizah, tana zuwa ta samu wuri ta zauna, sannan ta miks gaisuwa ga Wazirin Deehar. Kafin ya tattara nutsuwar ta ga Mijinta.
Sai da ya yi shiru kafin ya ce mata.
"Takwaran ki ce za a mai da ita Deehar" dake kirjinta tayi tana girgiza kai ta ce musu.
"Deehar?"
"Kwarai da gaske!"
"Kubra tai kankanta da masarautar Deehar." Ta fada hawaye na zuba mata.
Shi kan shi Sarki Abbas wallahi jikin shi ya mutu balle ita.
"Kuyi hakuri, In sha Allah babu abin da zai faru da ita sai alkhairi"
Zuwa yanzu waziri ya tsorata shi ma da son daukar Kubra.
"Ba mu san me a ran ka ba, sannan ba zamu hanaka daukar ta ba. Sai dai a nimo Ya Musa."
Haka kuwa aka tura Jakadiya, kiran shi.
Yana shigowa ya zube akan gwiwar shi ya gaishe da Wazirin Deehar .
"Ka kyauta ko! Ashe da wannan yanayin ka zab'i shiru ka sulale ka tafi, me yasa baka gaya min ba?" Waziri yake tuhumar Ya Musa.
Idanun Ya Musa na zubda hawaye ya ce.
"Ka gafarce ni, amma Amana daya ce ita ya bani akan Kwarkwarah Kubra. Taya zan rushe amanar da ya bani?" Ya fada yana share kwalla.
Jikin waziri ya kara sanyi.
Maganganun Magajiya ya dawo kan shi, ya kurawa Ya Musa idanu sannan ya ce mishi.
"Amana daya ce! Kuma ya baka nima kuma na kara baka, sai dai dole a kaita su ganta sauran kuma ka yarda da Allah ka yarda da ni ba zan zalince ka ba. Itama kuma ba zan zalince ba" domin ya fahimci matukar ya saka zalamar son mulki jikokin shi ba zasu yi ba, Hakazalika idan ya juya ya ce sai yaga bayan abin da a haifa sai dai ya rasa ran shi.
"Mai Martaba sarki Abbas, ina niman Alfarman saka baki su dawo Deehar babu abin da zai faru sai ikon Allah"
Sun tsayar da maganar tafiya washi gari. Don haka Ya Musa ya musu iso har cikin gidan wurin iyayen Kubra, tabbas yaga mace inda ake kira mace dole Sarki Hayatudeen ya rud'e, duk da lullube take da babban mayafi, bai hana shi hango tsagwaran kyau da Allah ya zuba mata.
Ya gaya musu rasuwar Mai Martaba sarki Hayatudeen, a firgice ta zuba mishi ido kafin ta sunkuyar da kai tana me fashewa da kuka, tabbas tayi rashi ita aka yiwa mutuwa, kuka take sosai me shiga jiki, shi kansa sai da ya fahimci irin kaunar da take yiwa Sarki Hayatudeen, ai dole taso shi kuma dole ta yi kukan mutuwar shi domin yasan kan mace, ya kuma san yadda zai bi da mace kome kankantarta ta fada kaunar shi mara iyaka.
Haka ta kwana tana kuka, har kunya iyayen ta suke ji domin basu tab'a ganin haka daga gare ta ba, tana da kunya sosai domin ko cikin jikinta bata so su sani ba, sai dai rashin lafiya da walwla yasa dole suka d'ago ta, tare da kiran unguwar zoman masarautar ta duba ta.
Washi gari
Suka dauki hanyar Deehar, haka ba karamin al'amari ba ne a gare su, sannan an bata bayi goma mata masu kula da ita. Har suka isa masarautan, wanda suka mishi shigar almuru. Tun kafin su isa wurin Bishiyar kukan da Sarki Hayatudeen yake zama aka aji an fara bushe bushe da algaita da k'ak'aki, haka ya tabbatar da ilahirin masarautan sun fahimci wadancan mutanen boyen sun yi na'am da macen da aka kawo kenan. Dan haka suka wuce cikin Masarautan Deehar, babu b'ata lokaci aka nufi shashin Magajiya da ita, domin wannan tafiyar Waziri ce. Da kan shi ya mika ta da Yar shi.
"Ga Kubra nan, nasan yadda zuciyar ki bata da tsatsa zaki kula da ita" wani kallo ta mishi sannan ta ce mishi.
"Wallahi ba zan rike matar da Hayatudeen ya rab'e ta ba, domin kuwa ba zan iya cigaba da kallon idanun ta a matsayin matar da mijina ya kwanta da ita ba."
"Ni..."
"Baba ka tafi da ita kawai" haka ya fito da ita jikin shi a mace, ya nufi wurin Kilishi, wacce sai yanzu aka fahimci tana dauke da karamin ciki bayan rasuwar Sarki Hayatudeen.
"Waziri ka tafi min da ita ba zan amshe ta ba, domin kuwa rab'ar mijina tayi, sannan abin da take dauke da shi, shi nima nake dauke da shi."
Jinjina kai ya yi, sannan ya fice wurin Fulani Karama ya shiga da sama.
"Kamar Muryar Waziri yaushe ka dawo daga Rano?" Wani matashin saurayi makaho ya tambaye shi yana rike da sandar shi.
"Na ji kamshin Ya Musa"
"Yarima Usmanu gani nan." Ya nufe shi yana kukan farin ciki. Juyawa yayi sannan ya ce mishi.
"Ku uku ne?" Domin Allah ya mishi baiwar fahimtar mutane a wuri musamman suka haura biyu zuwa uku....
*NAHMIFAK*
_Collections_
*Hausa Historical Ancient*
#Mai_Dambu
#wed/Nov/2022
*......DASHEN ALLAH 🌳*
Mai_Dambu...
*NAHMIFAK*
_Collections_
```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```
BABI NA HUƊU (4)
"Tabbas haka ne, mu uku ne tare da Sad'akar Mai Martaba " Waziri ya fadi haka,
Shiru yayi yana kallon can gefe guda, sannan ya ce musu.
"Me yasa kuka dawo da ita? Me yasa baku bar shi a can ya rayu lafiya lafiya ba? Kun manta inda muke ne? Bai zama dole ya kai labari ba. Dan haka Ya Musa hakki ne a kan na kare rayuwar shi."
Kamar wadda aka watsa musu ruwa, suka yi shiru suna kallon shi. Fitowar Fulani Karama ta kalli Kubra da take tsaye. Sannan ta juya ga Waziri.
"Baba Waziri lafiya?"
"Ita ce sad'akar Marigayi shi ne nayi tunanin kawo ta kafin a gyara wancan wurin."
Sake kallon Kubra tayi, yarinya ce karama ba babba ba, dan haka ta kalli Yarima Shehu. Kamar yasan tana kallon shi ya ce mata.
"Ki daina kallona Ammah, ki kalli abin da yake gaban ki." Lumshe idanunta, ta yi sannan ta kwalawa baiwarta kira ta ce mata.
"Shiga da ita d'akin da yake gefen turakata."
"Toh uwar ɗakina" sannan tayiwa Kubra Jagora har dakin da yake shirye.
"Allah ya saka da alkhairi, Kubra da abin cikinta, amana ce a gare mu don Allah."
Mikewa tayi tana faɗin.
"Abin kasuwa na mai ciniki ne, idan ta iya ta tsira. Idan ta fadi a rasa kowa ya huta."
Jinjina kai Waziri ya yi sannan ya ce mata.
"Na gode Fulani, fata na gari lamiri." Sannan suka fita, cak ta tsaya a bakin kofar shiga cikin bangaren ta.
"Ammah lokaci ne yayi da zaki cika wasu mafarkan, domin masu iya magana sun ce ba ni in ba ka, shi ne tanka."
Juyawa tayi ta zuba mishi idanu.
"Mafarkina akan ku yake!" Ta fada a fusace.
"Bikin Magaji bai hana na Magajiya, wannan fa so min tab'i ne." Ya fada yana me tafiya da sander shi har bangaren shi.
Bin shi tayi tana kallon shi, tabbas akwai boyayyen al'amari a cikin kan d'an nata, sai dai kuma al'amarin yana bata tsoro. Ranar da Mai Martaba zai rasu da tafiyar shi da abin da ya faru sai da ya labarta mata. Tare da bata shawaran boye wasu abubuwan a ranta. Har ya kusan fita ya ce mata.
"Kin zata haka kawai na ce miki ki amshi kiran da zai zo daga gare su Ammah? A ranar da Abba ya dawo naji ba na jin al'amarin d da yake fita a jikin shi idan ya kusanto ni. "
Murmusa mata ya yi, sannan ya juya yana kallon inda take tsaye duk da baya gani kuwa.
"Koda aka ce ya rasu naje dakin ni da sauran Yan uwana, amma ban ji haka daga gare su ba. Matar da suka gabatar a fada ban ji tana da