Showing 96001 words to 99000 words out of 105295 words
Chapter 33 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
mishi.
"Gwarzo na"
"Na'am" "Na gaji zaka dauke ni?" Murmushi yayi mata, sannan ya juya mata baya. "Na rantse da nahara, ba zan iya d'aga kafana ba" cak ya dauke ta, suka nufi tantin su. Ya kwantar da ita, rike shi tayi ya koma kanta yana murmushi. A haka suka kwana manne da juna, washi gari ta tashi da mugun gajiya, domin koda asuba sai da ya kuma murza kamar ba boye, haka suka kama hanya a gajiye, Uwar Bayi har ta fahimci yanayin ta baki daya a gajiye take kamar tayi kuka, idan suka tsaya Sallah, ita idan zata tafi fitsari dakyar take d'aga kafarta. Haka yasa Uwar Bayi bata kulawa duk tsayuwar da zasu yi sai ta haɗa wuta ta bata ruwan zafi, Aaliyah kuwa dariya take mata, tana faɗin
"Kyautah idan kika yi ciki kuma ban san yadda zaki koma ba." Haka yasa take tura baki kamar zata yi kuka, tafiyar sati biyu ya dace su yi, amma suka yi shi a kwana ashirin sabida Abdullahi yadda ya saka Kyautah a gaba, ai kuwa haka tayi ta kuka tana mishi rigima har suka isa Deehar, tsohon bangaren Sarki Hayatudeen aka bawa Abdullahi an gyara domin su Uzairu da Ya Haruna suka gyara, masarautar an sake fasalin shi, Fulani Babba tana nan bata da lafiya gefenta guda ya shanye, fada kuwa an kwashe kome na cikin shi an gyara tare da zuba wasu kayan, bayan an farfasa wasu wuraren aka cire binne binne.
Bangaren Waziri yana kusa da na Abdullahi, dan haka kome nasu kusan guda ne, sai da aka yi kwana uku ana saukar qur'ani, sannan aka yi nadin sarautar su, sai ranar Mama Uwa da Wabi da Raudah suka ga Kyautah, a gefen shi kamar suyi Hauka, sannan Abdullahi ya hana su ganin Kyautah duk abin da za ayi kar a tab'a barin su, su ga Kyautah itama tunda suka dawo ta lura baya son ganin su sai bata fara niman su ba, amma kullum cikin damuwa take.
Bayan sati biyu da dawowan su ne, dakyar Mama uwa suka samu ganin ta, Abin da ya basu mamaki yadda Kyautah ta koma kamar ba ita ba, ga Bayi ta ko ina an zagaye ta. Zama suka yi aka kawo musu abinci.
"Kin manta da alkawarin nahara ne?"
"Ban manta da alkawarin nahara ba, sai dai ina bukatar rayuwa, mutanen nahara kuma nayi imani da abin bauta zasu koma nahara, sai dai ina bukatar rayuwa, ina bukatar ganin Mahaifiyata, ina son Mijina."
"Mama uwa kin ji dadi miji"
"Ih, dadi miji, ba ta hanyar banza na san shi ba, na san shi ta hanyar ibada ne, ya kare rayuwata domin na rayu akan me ni zan kare rayuwata akan mutanen da basu cancanci zama da ni ba, kun san gaskiya ban tab'a mu'amala da wani da namiji ba, sai Abdullahi. Kuma Nahira ya sani wannan ita ce garkuwar soyayyar da nake tare da shi, sai dai anyi kuskure domin ranar da na fara ganin shi ranar ya zame min mahadin rayuwata, gashi ki je idan akwai wanda xai iya bada rayuwar shi domin nahara ba laifi amma ina bukatar mutane biyu a rayuwata Abdullahi da Mahaifiyata, kuma zan tsaya muku amma ba zan baku rayuwata ba "
Yadda take maganar ba karamin basu tsoro tayi ba, dan haka babu shiri suka bar zauren, a kofar fita suka hadu da Uwar bayi. "Ba koda yaushe mutane, irin ku suke samun yadda kuke so ba, yanzu dai ta san ciwon kanta sannan ta san darajar kanta ta kuma san akan me ake rayuwa kuma ta san banbancin rayuwa dan haka na bar ku ne, ku shigo dan na lura tayi kewar ku, idan kuka saka zuwa abin da Abdullahi zai yi da kan shi ba san iya cewa ga shi ba. Miyagun mutane masu dabi'ar dabbobi." Tas Uwar bayi tai musu sannan suka tafi, cikin bakin ciki da b'acin rai an bata musu rai sabida kyautah. Kuma sai su dauki mataki me mugun ciwo, sai sun sakata kuka.
Lokacin da suka shigo shima yana cikin gidan, amma a ɓangaren shi koda ya gama abin da yake ya nufi wurinta yaji maganar da take gaya musu sai yaji ta kara kwanta mishi a rai. A hankali ya shiga tana zaune tana share kwalla, zama yayi a gabanta yana share kwalla.
"Kina kewar Umminki ko?" Gyada kai tayi, murmushi ya mata sannan ya ce mata.
"Shi kenan, amma me yasa kika gaya musu haka?" Rike hannun shi tayi sannan ta ce.
"Ina bukatar rayuwa domin kai da Ummina, kuma su suna bukatar tawa rayuwar ne domin kansu idan na tafi a haka waye zai kula min da Ummina?" Jan kumatunta yayi ya ce.
"Gaya min gaskiya ina sona ko?" Hada goshinta tayi da nashi " ban san yawan son ba, amma ina sonka dayawa dayawa, ko na mutu." Bakin shi ka kai saman nata ya rufe yana kara matseta a kirjin shi. Sun jima a haka kafin ya janye yana kallonta.
"Ina sarki guda an bar ni babu abinci " mikewar tayi da sauri ta nufi dakin girki sai gata da kayan abinci, Uwar bayi na biye da ita da Ladi, haka suka shirya mishi, ta zuba mishi yana ci yana kallon ta.
"Kin ci kuwa?"
"Ih, naci sosai."
"Zoki taya ni ci"
"Na koshi fa"
"Dauke abincin na koshi " zama tayi ta wanke hannunta ta fara ci tana bashi, yana bata hannun su yana gogan juna, burin daya Kyautah ta amshi Musulunci, duk abinda ake bukata ta cika, dan haka zai zuba mata ido, haka suka gama sannan ya dauke ta zuwa d'akin shi, daga nan labarin ya juya irin nasu, wanda yasa shi baki daya ya manta da duniyar da yake da ita kanta suka yi nisa. Uwar bayi da Ladi suka kwashe kayan. Sai bayan da kome ya kammala sannan ta narke mishi da kukan jikinta yana ciwo, shi kan zuwa yanzu ya saba da rigimar kyautah, ta bashi hadin kai ya dawo tana ganin laifin shi gashi ta yi wani irin sabo da shi, idan bai leka fada ba, suna manne da juna, da dare mana suna like da juna, ko motsi bata iyawa domin ya zame mata kamar kaska ne, haka suka gina rayuwar su, lokaci zuwa lokaci tana fita yawon shan iska, a wani yammaci ne aka kawo mata labarin Wabi tasha guba. Shiryawa tayi ta fita ita kanta ranar bata wani jin dadin jikinta, amma jin labarin yasa ta shiryawa ta nufi wurin su. Duk inda ta wuce sai an gaishe ta ake tana nufar dakin ta same ta tana barci. "Akan me ta sha guba?" "Sai kin tambaya ne? Bayan cin amanar da kika mata? Kin san dai dole ki sadaukar da kanka ga al'umma Nahara"
"Idan naso ba? Idan naso ba!! Nayi iya karfina, Nahara ko gobe idan dattawan Deehar suka bada damar barin ku masarautar zaku bari amma ku sani Ni din ina da tawa Rayuwar, Abdullahi Hayatudeen Abdullahi Noye shi ne rayuwata shi din rayuwata ne, dan haka ba zan baku rayuwata ku yi yadda ya muku ba, idan ta cigaba da haka ba zan hana kowa ba, amma matukar kuka ce zaku yi amfani da kusanci ku cutar da ni, har abada baku ba nahara. Nasan ba guba kika sha ba wani haukar ki ce na rantse da nahara wannan ya zama karshe" tana gama fadar haka ta fita, dayawan bayin da suke gidan sai jikin su yayi sanyi.
"Yanci kuke nima? Amma kuke abu kamar munafukai? An gaya muku ban san abin da nake ba ne, duk wanda ya fasa gulma da yayyata ni ya rena kan shi, kuna cewa tasha guba dan kawai naki sadaukar da kaina saboda na auri sarki na rantse sai na saka an sare kan mutum, idan haka shi zai baku yanci tow ba laifi ga fili ga doki...
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
......... Tsoron abin da zai biyo baya, yasa baki daya suka tsorata da kyautah ai sun san ba haka take ba, ita ma da ta koma bangarensu kuka tayi ta yi tana ganin kamar duk wani abu da yake faruwa laifinta ne, tana zaune har Abdullahi ya shigo gidan, sam baya son ganin kwalla a saman fuskarta. D'ago ta yayi yana faɗin.
"Waye ya saka min Kyautah kuka?" "Yaushe al'umma ta zasu samu yanci?" Shafa gefen fuskar ta yayi yana murmushi ya ce mata.
"Sai ranar da kika bukaci su koma da kankie" daura kanta tayi a kirjin shi tana murmushi har ta manta da tana kuka ne wannan yarinyar da ganganci take. Yanzu zata yi kuka yanzu zata kama dariya, kamar ba ita ba. Haka ta ja hannun shi suka shiga bangaren shi ta taya shi rage kayan shi.
"Mai Martaba!" Bai tab'a jin ta kira shi da haka ba, domin kuwa Jan gwarzo ne ko Basamude, amma yau ta kira shi da Mai Martaba. Zuba mata ido yayi yana jira daga gare ta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce mishi.
"Tunda muka dawo ban ga sauran." Hannun shi ya saka a gefen fuskar shi yasa kallon yadda take rau-rau da idanunta.
"Suna gidan Iyayen su" ya fada yana me cire babban rigar shi da ya gaggareta cirewa.
"Ina ga ai su basu da laifi" ta fada tana rike rigar shi.
"Ih, amma ba zan iya zama da su a matsayin mata ba, idan ke kin gaji da hidima na zan iya aure ko na tara kwarkwarah amma bazan mai da gidana sansanonin yaqin juna da kishi ba, zaman lafiya nake nima ba tashin hankali ba."
"Allah ya huci zuciyar ka, ba da wata manufa nayi magana ba." Ta janye hannunta daga jikin shi yasan za a rina dama, amma sai ya ce mata.
"Idan kina son a dawo da su, ba matsala sai na dawo da Raudah!"
"Cab na rantse da nahara, sai na kashe ta yarinyar da tace bata sonka ai ba zata tab'a sonka ba"
Shafa cikinta yayi yana kallon cikin idanunta, ya ce.
"Anya ban yi ajiya a nan ba?" Buge hannun shi tayi tana faɗin.
"Ko da wasa babu ajiyar da kayi a nan na.gaya maka" bakin shi ya kai kunnenta.
"Ni nasan nayi, tun kwanakin da muke Rano, domin naji yadda yarinya take kara k'amk'ame ni tana min kukan"
"Ka fara bani tsoro, ayi mutum bai san abin da yake fitowa bakin shi ba, kaga bari na shiga na hada maka ruwan wanka"
Dariya yayi sannan ya zauna tana gama haɗawa ta fito, tana kallon shi ta hanyar d'aga mishi gira ɗaya, ta ce.
"Muje kayi na maka wanka"
"Yarinya Kice kina son gani na a tube shi ne zaki ce, zaki min wanka." Ajiye numfashi tayi sannan ta ce mishi.
"Kaga babu lokaci, zoka wuce kayi wanka tow!" Murmushi yayi sannan ya ce mata.
"Tow da sauki" ya na zuwa bata fahimci me yake nufi ba ya ɗauke ta sai ban dakin, kiri kiri ya ya watsa mata ruwa ya jika adon jikinta, sannan suka shiga duniyar su, Dakyar suka fito ta saka kayan shi, ta nufi daki ta shirya, sai da ta gyara jikinta ta fito ta bashi abinci, tun a wurin cikin abincin, ya azazzaleta dakyar ya ci wani abu suka fada sha'anin rayuwar su.
Sai bayan sun nutsu tana kwance a jikin shi ya ce mata.
"Kyautah ko zaki musulunta ne?" D'ago kai tayi ta kura mishi ido, kafin ta mayar kirjin shi, tana sauke ajiyar zuciya.
"Zan duba!"
"Shi kenan"
Ya cigaba da shafa bayanta, haka tayi ta tunani har na wani lokaci, kafin suka kuma shiga wanka, bayan sun fito ne ya dauke ta suka fita zuwa gidan Abid. Anan suka zauna sai dare ya dawo da ita.
***
Bayan wata guda, yanayin ta ya dan sauya kaɗan. Musamman yadda take kara jin kwadayin abin da idanunta bai gani ba, fita tayi domin tana kewar Wabi, ta nufi wurin su. Tana shiga ta samu sunyi kunun tsamiya, kamar ta kwace, amma ta hakura ta zubawa Mama Uwa idanu kafin ta fara magana.
"Nazo gaida ku ne" kallon ta Mama Uwa tayi tsaf ta hango cikin da yake tare da ita, dan haka ta ce mata.
"Zaki sha ne?"
"Ih" zuba mata tayi, tasha ta koshi. Sannan suka shiga hira kamar basu ba, itama Wabi ganin haka suka shiga hira kamar yadda suke sai can ta mike zata tafi.
"Idan kina so kina zuwa karba, tunda kin san ba za a bari mu shiga cikin gidan ba."
"Tow ba damuwa" haka kuwa suka rakata zuciyarta daya, bata kawo cewa zasu iya cutar da ita ba, haka Mama Uwa tayi ta shirya mata makirci, tare da Ya Musa da yake nan kamar babu shi, bayan wasu kwanaki. Wabi ta ke gaya mata zata musulunta, har cikin ranta taji dadi, da dare suna kwance ta ce mishi.
"Wabi zata musulunta!"
"Tow yayi kyau, ki dai bi a hankali ina sane da kika zuwa wurin su, ba zan raba ku deG. Amma idan suka cutar dake zan basu mamaki"
"Kai haba babu abin da zasu min, ka kwantar da hankalin ka" gyad'a mata kai yayi yana da fatar kar son yan uwa irin ta yasa wani abu ya sami cikin da shi da Uwar bayi suka san da shi, domin baki daya tunanin ta bai. Bata mutanen nan iya zama haka, shi kuma yasan da walakin goro a miya.
Haka suka kasance, har wani ranar Laraba, bai da zaman fada yana kwance tare da ita, ta nufi wurin su wabi. Ta amso kunun tsamiyar a hanya suka hadu da Raudah. Bata kulata ba domin bata son magana kunun kawai take hari ta je ta sha, amma Raudah sai da ta bangajeta. Har wasu dogarai sun tasowa Raudah.
Murfin akushin kunun ne ya fadi, ta durkusa zata dauka Raudah ta dauka.
"Ku kyaleta" saka akushin tayi a cikin mayafinta.
"Yanzu nasan domin wannan kika fito? Idan na zubda fa"
"Na hadaki da Abin bautar ku, kar ki zubda min shi, ina jin shi kamar rayuwata ce"
"Idan naki fa?" Idanunta ne cike da kwalla, ta ce mata.
"Idan kika sake ya zube, na rantse babu me dakatar dani, sakawa a azazzabrta dake." Mika mata akushin tayi tana juyawa.
"A sha lafiya, uwar magajin deehar" ta fada tana dariya, bata kulata ba ta bar wurin tana shiga suka hadu da Abdullahi tsareta yayi da idanu, alamar tambaya.
"Abu na amso wurin Mama Uwa, bata nan ma Wabi ta min shi." Bai ce kome ba ya nufi dakin shi ya zauna ta fara nazarin yadda zai rabata da su, ita kuwa tana bude akushin babu kome a ranta ta fara shan kunun tass, sannan ta wanke bakinta, ta nufi dakin shi ta zauna a gefen shi.
"Yarinyar nan ta dame ni" ta fada tana kallon shi.
"Wacce?"
"Tsohuwar matar ka" ta fada a shagwab'e, tana kwantar da kanta a kirjin shi.
"Me take miki" lumshe idanunta tayi tana shakar kamshin turaren shi, ta ce mishi."kyaleta ya wuce" a hankali ya mirginata cinyar shi, sumbatar bakinta yayi suka cigaba da tafiya da junan su, kamar zasu cinye junan su. Sai da suka gurje juna, tana kwance a saman shi, maranta ya kulle. Tsaki tayi ta tashi a hankali ta nufi ban daki, tsugunawa tayi, da zummar fitsari, sai jin saukar abu tayi kamar an bude mata ruwa a maranta, tare da ciwon mara da baya.
"Gwarzo" ta kira sunan shi, dira yayi a gadon ya shigo domin yadda yaji ta kira sunan shi ba lafiya. Bude kofar yayi yaga yadda jini yake bin ko ina tana durkushe akan gwiwar ta.
"Me ya faru?"
"Jini kawai...." Iya abin da ta iya faɗa kenan, ta koma zata zube, ya rungume ta, ya rikice ya rasa me zai mata kawai fita yayi daga dakin ya dauko kwarjallen shi,.ya nad'e mata shi a kugunta, ya saka mata dogon rigar shi ya futa da ita.
"Uwar bayi?" Ya kwala mata kira.
Fitowa tayi, idanun shi cike da kwalla.
"Ina ga shi ne bari ko?"
"Muje gidan Amaza" ita ce unguwar zoman masarautar, abin tausayi idanun shi sun yi jajjur, a hanya suka hadu da Abid.
"Lafiya"
"Bari tayi" Uwar bayi ta bashi amsa, haka suka isa gidan, aka shiga bata kulawa amma ina cikin ya fita, d'an tayi wata hudu zuwa biyar, wanda yayi daidai da ranar da suka fara haduwa a Rano, shafa fuskar ta yayi yana kallon d'an tayin, da yake kunshe cikin auduga da aka lullube shi da yadi ruwan gwal, irin ta masarautar deehar, komawa gefe yayi ya rufe fuskar shi hawaye na zuba mishi.