Showing 48001 words to 51000 words out of 105295 words

Chapter 17 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6101

ta ce mishi.
"Ina son zuwa gidan"
"Ki jira na shirya" ya janyota jikin shi, jiya Uwar bayi bata saka mata maganin wanke mara ba, dan haka suka durje juna kamar ba gobe sannan suka yi wanka tare suka fito. Kallon shi take tana faɗin.
"Yau kafi ko yaushe kyau"
"Na gode" ya shirya, suka fita daga cikin gidan. Ya rasa me zai kai mata sai ya nufi bangaren Fulani Babba ya samu tana tare da Galadima da Chiroma, gaishe su yayi sannan ya ce mata.
"Fulani ina son naje na gaida yarinyar nan ne"
"Tow shi kenan" ganin ya yi shiru tattaro nutsuwar ta yayi kafin ta ce mishi.
"Kana son wani abu ne?" Kasa yayi da kai sannan ya ce mata.
"Ih, ban san me zan kai mata ba ne"
"Shi kenan, jeka bari na saka a hada maka y'ay'an itacce"
"Tow Allah ya kara girma" ya fada yana komawa gefe, kiran Jakadiya tayi , ta fada mata abin da zata yi ita kuma ta gaya mata ai tare da Wabi yake. Murmushin yake tayi sannan ta ce mata.
"Ba damuwa" haka Jakadiya ta nufi dakin ajiya ta fito da sakon a kwando. Ta kai ta nuna mata, sannan ta nufi waje ta bawa Wabi. Yayi godiya suka fito.
"Fulani kina ganin haka alkhairi ne barin wancan nakasashen a raye?"
"Hmm!" Ta fada tana murmushi.
---
Sun isa gidan suka same ta zaune dasu Abid, an tura mata abincin. Tsakura take tana kallon naman. Tana so amma kuma da kunya ta cinye namar a gaban idanun Abid.
"Na takura miki ko? Bari naje na dawo." Yana fita suka hadu da Arshan da Wabi, kallo daya Abid yayi mishi ya dauke kai, dan wani irin tsanar shi yake ji.
Yana fita kuwa, ta sunkuci namar kazar ta fara mata cin yunwa kamar wacce ta shekara bata ci kome ba, turo kai Wabi tayi ta ganta cikin jin wadaka da nama, ta cika bakinta sai fama take. Abdullahi yana zaune fuskar shi nad'e da rawani.
Sake namar tayi ta rarrafa har wurin Abdullahi ta rike kafar shi tana me jingina kanta a gwiwar shi.
Murmushi Arshan yayi idanun shi yana kanta.
"Ya jikin naki" kallon fuskar Abdullahi tayi taga babu wani sabon abu, sannan ta ce mishi.
"Sauki"
"Easter!" Ajiyar zuciya ta sauke ganin har da yar Uwarta, mikewa tayi a hankali, ta nufi wabi duk da a duke take tafiyar, dake tana da juriya ne yasa ta mike dan ta nuna tana da lafiyar, ko ace ta samu sauki.


"Kyautah garin yaya haka ya faru?" Ta tambaye, kallon inda Arshan yake tayi sannan ta riko hannunta suka nufi dakin da yake nata, suka zauna.
"Ya Mama Uwa?"
"Tana lafiya kin san ba za'a barta tazo nan ba."
"Ki gaida min ita " ta fada tana kallon kasa .
"Kyautah da alamu akwai wani abu a tsakanin ku da Abdullahi?"
"Na rantse miki babu kome" murmushi tayi sannan ta ce mata.
"Baya bude fuskar shi ne?"
"Yana budewa mana amma yafi son zama haka, domin yana jin dadin haka"
"Ga Kyautah can Arshan ya kawo miki, idan kin ga wani abu da bai miki ba, ki fada da wuri domin haka bai da ce ba, zaman ki da shi babu wani a kusa." Gyada kai tayi tana mamakin Wabi wato ita zata yiwa hudubar akan zamanta da Abdullahi.
Gyada kai tayi tana faɗin.
"Tow" haka suka fito, Arshan ya ce mata.
"Kiyi hakuri da abin da ya faru" ya fada yana kallonta.
"Ya wuce" haka ya suka bar gidan, suna fita ya koma kan abincinta, tana ci tana gama ci Abid yana shigowa, kallonta yayi ya kalli kwandon kayan marmarin da Arshan ya kawo.
"Me za ayi da wannan?"
"Babu"
"Ki fitar da shi a rabawa mutanen, idan Uwar Bayi tazo ta tafi da shi"
"Tow" ta ce.
Can wurin azhar aka turo bayi suka kwashe kayan Abdullahi suka koma sashin su na da can, an gyara wurin sosai.
Yafi na Arshan girma domin sashin dan iyalan Sarki aka ware su, sai gashi ya samu a matsayin na shi, kusan daidai yake da bangaren Fulani Babba, dan haka wannan karon aka turo bayi babu iyaka, sai dai Uwar bayi ce aka bata damar tantance su.
Haka yanayin ya ci-gaba da tafiya, domin ita dai ba za a hanata kwadayi ba, Allah ya taimaka shi ba me yawan ciye-ciye bane, matsalar da aka fara samu a gidan shi ne, yau da suka cika sati daya da dawowa gidan.
Abincin ta buɗe tana hadiye yawun,
"Yau kan kun shiga uku a hannuna" ta fara cin abincin, kamar wacce ta shekara bata ci abinci ba. Haka take ci ita burinta kar Abdullahi yazo yaci. Sai dai kuma bata gama cin abincin ba, taji kamar ana tsinke mata hanjin cikin ta. Yunkurin hadiye Abincin bakinta take son yi amma ta kasa, gudan jini ne ya fara fita ta bakinta tare da abincin sai hancinta da kunnenta. A wurin ta zube tana shure-shure. Shi kuma sun fita da Abid haka kawai jikin shi ya bashi babu lafiya, kamar ya yi tsuntsu ya isa gidan. Suna isa Abid yayi tursu dan babu kowa a gidan sai ita. Abincin ma an dauke tana wurin a kwance cikin jini. Rike hannun shi Abid yayi yana faɗin.
"Sun saka mata guba" ya fada mishi kamar yadda suke mishi bayani, wurgi yayi da sandar shi ya fara nimanta da kafar shi.
Isa wurin Abid yayi ya ɗauke ta, sannan ya mika mishi ita.
"Rayuwar ta yana cikin hatsari ka ajiye abin da kake boyewa domin kare rayuwarta, kana ji kana gani babu amfanin boye mata waye kai. Duk fadin Masarautar nan ita ɗaya ce take fadawa kasada domin kai, wannan shi ne karo na biyu kar ayi na uku domin bai zama dole ta rayu ba."
Haka suka nufi bangaren Uwar bayi da ita. Ita tace su nufi wurin masu magani, sukayi ta fama da ita har gidan me maganin.
★‡★
NUMAN.
Tun bayan tafiyar Abdullahi, ta fahimci mahaifiyarta fushi take da ita.
"Ayya innah kiyi hakuri" ta fada tana matsar kwalla.
"Hmm! " Kawai ta ce mata domin ba wai ta tsani Raudah bane amma da ciwo abin da ta aikata.
Tun bayan tafiyar su take yawan shiga dakin shi, tana gyarawa wai tana yin haka ne dan kawai Innar ta yarda tayi nadama.
Amma ba nadamar bace, kawai tana son ta hanyar da zasu shirya da Mamanta.
Yau ma kamar kullum tana cikin dakin shi tana gyarawa, idanunta ya sauka akan wata tsohuwar adaka , janyo shi tayi ta saka wata kamar dutse ta fasa, sannan ta bude murfin adakar, ta hango wani alkyaba ta gani da tambarin masarautan sak zanen tambarin irin ta wuyar Abdullahi, a hankali ta shiga Ciro kome na cikin adakar gumi ne ya karyo mata ta gogewa, daukar kayan tayi ta fito waje.
"Innah daman Abdullahi daga masarautar yake?"
"Sai yanzu kika hango abin da Babanki ya hango Miki? Sakarya shashasha ai kin rasa shi kenan, kuma da kike tsammanin nakasashe babu abin da ya same shi, wacce zata iya zama da shi da gwagwarmayar rayuwa yake nima. Ba wacce zata so shi dan abin hannun shi da duniyar shi ba. Dan haka sai ki kara himma akwai masu gani da lafiya. Dan haka sai ki zauna zasu zo auren ki amma Abdullahi kan ya tafi kenan"
Kasa magana tayi tana kallon Innah tayi kafin ya juya dakin rai ba dadi.
Insha Allah ko zata tafi babu me goyan bayanta sai ta dawo da Abdullahinta domin da ita ya dace.
(Yarinya Deehar tana jiranki)
★‡★
Deehar.
Dafa shi Ya Musa yayi yana faɗin.
"Lokaci yayi fa boye halin da kake ciki ya kare idan ba haka ba, zasu kashe ta ne tunda ita bata san kome ba. Kome ta gani yi take abinta"
Janye hannun Ya Musa yayi yana Lumshe idanun shi.
Har yanzu mamakin yadda suke son kashe ta yake yaga dai shi bai nuna yana bukatar mulkin su ba, amma yadda suke kokarin ganin bayanta ne ya bashi mamaki. Shigowar Fulani Babba yasa duk suka juya ban da shi babu al'amar yasan da shigowar ta.
"Ya yarinyar da jiki?"
Ta tambaye Ya Musa tana nuna alhininta.
"Da sauki "
"Ya kamata a kama wanda ta saka guban domin ta haka za a magance matsalar masarautar "
"Hmm! Ina ga a bar shi kawai Allah zai tona asirin masu yi" Inji Abid yana kallon Abdullahi.
Murmushi tayi tana me cewa.
"Tow ba damuwa idan kuma zaku iya aikin sai ku yi"
"Ko daya ba zamu iya aikin ba, amma Allah zai mana kome ai ita bata san abin da ya faru ba, duk wanda yake kokarin cutar da ita tow yana son ta fusata Abdullahi ne, duk da muna kan Nima mishi magani,ba zamu sake barin a cutar da shi ko ita ba."
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
"Ya Musa idan ana sara ana duba bakin Gatari."
"Haka ne ranki shi dade, hasken fitila bata hana zakara gane asuba tayi. Dan haka muna aika sako ga masu da cewa shi me ramin keta ya gina shi dan kaɗan ba kato ba, gudun kar ta fada da shi."
Ranta yayi mugun b'aci dan haka ta sake murmushi ta ce mishi.
"Ya Musa, bi ba yar aikarka ba ce. Sannan wannan shine zancen iska ga mutanen banza. Idan har Yusif da Ado sun samu lafiya ba makawa zai samu lafiya."
"Kuma haka ne fa, tow amma ai su haihuwar su aka yi da nasaka shi kuma tsintar ta yayi daga sama ta ka, kenan shi zai iya warkewa su kuma..."
"Ya Musa!" Ta kira sunan shi da ƙarfi
"Fulani Babba!" Shima ya daka mata tsawa.
"Kar ka tono ramin da zai binne ka kai da Yaron da ka gama wahalar da kanka kan shi."
"Fulani Babba! Kar ki damu da wannan, ai dan zaki ya girma ko yau na mutu sadaukarwa ce a gare ni shi din kuwa mashi ne me linzami"
Takowa tayi tana kallon shi.
"Kar ka manta kana da baya fa" murmushi tayi,
Sannan ta fita iya kalaman shi sun isa su tarwatsa mata zuciyar shi.
"Idan wani abu ya faru ea su ba sabo bane. Sai dai ki sani Kubrah ba kwarkwarah bace ni dake mun san gurbin ki ta maye....


500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu


*A Hausa historical ancient
.......Cak Fulani babba ta tsaya a bakin kofar fita, juyawa tayi tana murmushi ta ce mishi.
" Ya Musa, ka manta cewa abin majinyaci na mai magani ne? Kar manta ana sara ana duba bakin gatarin ka yafi sari ka bani, me abin faɗa shi yake gudun abin kunya "
Shiru yayi domin idan ya kuma magana zai iya fusata Fulani Babba ainun, kuma baya son dalilin haka a kuma tab'a Abdullahi domin al'amarin zai mishi yawa. Fita tayi tana jin b'acin ranta yana kara nunkuwa. Ga kuma batun nimawa Abdullahi magani da Ya Musa ya fada tabbas idan Yaron nan ya samu lafiya a yadda take hango kwayar idanun shi, akwai bala'i mara iyaka.
Tana shiga bangarenta, ta saka aka kira mata Galadima wanda shima sai da ya gama ja mata rai kamin yazo, tana ganin shi ta sauke ajiyar zuciya.
"Nakasar da take cikin Deehar tabbatacciya ce ko akwai makarin sa."


A rikice ya d'ago kai yana kallonta, kafin ya girgiza mata kai yana faɗin.
"Tun iyaye da kakanni an tabbatar da cewa bai da makari"
Mikewa tayi zubur tana zaga dakin.
"Taya za a ce babu makarin shi? Bayan gashi nan sun fara shirin nimawa Abdullahi magani. Ga Yarana biyu a nakashe? Yaya ya zanyi?" Ta fada cikin matsanancin damuwa da matukar ciwo.


Kura mata Idanu yayi sannan ya ce mata.
"Ban san ya zanyi ba, amma zan nime ya wadda zai mana hidimar haka domin kin san ba karamin al'amari ba ne" sannan yayi shiru kafin ya kara da cewa.
"Ki daina damun kan ki akan wancan Yaron."
"Tsaya kai ne ka bada umarnin a saka musu guba?" Da mugun sauri ya kalle ta.
"Kamar Ya? Ko kadan ai bana kome da ka sai da umarnin ki waye ya kai ne ni balle yaga jimawa na?"
Ya fada yana zare Idanu, gyada kai tayi tana faɗin.
"Kowa ya rena me labari an kama shi ya subuce ne, tabbas bayan wannan sawun akwai masu aiwatar da nasu aikin bayan mu." Kura mata idanu yayi sannan ya ce mata.
"Kai haba?"
"Kwarai da gaske domin kuwa an sakawa Abdullahi guba."
"Ya mutu ne?" Ya tambaye ta idanun shi a waje.
"Kamar ta wanka mishi mari haka ta kalle shi, kafin ta ce mishi.
"Kai dalla can, yana nan a raye baiwar shi ta ci, Yarinyar da nake son Arshan ya kasance ta da soyayya."


Mikewa yayi jikin shi yana rawa, ya ce mata.
"Tow wallahi ba iya mu ke niman hanyar kashe shi ba, hatta wasu suna nan suna farautar rayuwar shi dan haka me kika gani?"
"Ai sabo da kaza bai hana a yankata, don haka muna kan shirin mu yana nan. Don haka kada mage ba yanka bane, koma waye yana gaya mana mu cigaba da shirin yana bin bayan mu"


"Amma da mamaki fa, ace an samu wanda yake bibiyar al'amarin mu haka, kuma shima da nashi nufin kamar mu. Tow amma ai"
"Shiiii!" Ta saka hannu a bakinta tana girgiza mishi kai, sannan ta ce mishi.
"Kana danne harshen ka, ba koda yaushe ake fadan shirin gaba ba"
Gyada kai yayi yana kallon ta, sannan ta sallame shi tana me nuna mishi hanyar waje.


-----
"Kin tabbatar ba ita bace ta bada gubar asaka mishi?" Gyada kai Halime tayi tana faɗin.
"Ba ita bace, domin da ita ce ba zata tab'a shiga damuwa ba. "
"Shi kenan Halime jeki kawai zan kuma niman ki"


Fita tayi tana sauri kamar ba ita ba, shiru uwar bayi tayi, sannan ta juya tana nazarin abin da Halime ta gaya mata. Tow idan ba Fulani Babba ba waye? Shigowa Ladi tayi kamar zata ajiye abu ta ce.
"Ina ga kamar matar Ubanta ba zata gaza aikata haka ba, amma a tsaurarra bincike." Daga haka ta fita, lumshe idanun ta, tayi na tsawon lokaci kafin ta bude shi akan Wabi da take ta murna bayan ta shigo da kaya niki-niki.
"Kai zai miki kyau, Yarima Arshan ne ya baki?" Wani juya idanu tayi tana faɗin.
"Ih, sa'a ta ce samun bazata."
Murmushi Uwar bayi tayi tana me juya kanta, domin wallahi idan ta kula abin Wabi zata iya cin Uban su daga ita har Uwarta. Sai dai kuma taya Uwa zata sakawa Abdullahi guba? Na farko jin shi take bata tab'a ganin shi ba, sannan kuma bata da yakinin akwai abin da ta sani akan shi, damuwar ta yarta ta samu shiga ne a cikin fadar kuma ta samu sai me ya rage? Kai ina ba zata aikata ba.
Idan kuma tayi haka dan a cutar da Kyautah fa? Ai dama ba sonta take ba? Wannan shine ayar tambayar da ya shiga kanta.


---
Kusan kwanaki goma tana kwance tayi fayau, sai cikar da tayi na alamar makerin budurci ya fara bayyana halittar jikinta, don dama Kyautah tana da fasali me kyau, bata da yawan kiba amma doguwar mace ce, irin angarma matan nan ne, fara ce domin kuwa yanayin Uwarta ce. Tana dakyau me sanyi da shiga rai, tana da wata irin baiwa na duk lokacin da zaka kalle ta dauka zaka yi masifaffiya ce, nan kuwa bata da fada sai dai bata yarda da reni ba. A duniya raunin kyautah su ne, Mama Uwa da Yarta domin ko wuta suka ce ta shiga zata shiga babu ja. Su kuma ganin bata da kowa sai su yasa suke cutar da ita.


Jan numfashi tayi tare da tari, Abid ya mike zai shiga dakin, sandar hannun shi ya saka a hanyar. Yana me kallon kofar shiga zauren,
"Na zata zaka cigaba da zama haka ne" tsuke fuskar shi yayi ya cigaba da zaman shi, kishingid'a yayi shi bai nuna alamar zai je ba, kuma bai bawa Abid damar zuwa ba, dan haka suka cigaba da zama. Can kuwa ta fito tana kallon su, ta rame kamar ba ita ba. Sumar kanta har gadon bayan ta. "Na zata na mutu ne" girgiza kai Abid yai yana mamakin yadda ko a ina take bakin ta baya mutuwa.
"A'a kina raye, matukar ba ki daina cin abin da baki sani ba, mutuwa zaki yi" Abid ya bata amsa, wani kallo tayi mishi,
"Da alamu bakin cikin namar da nake ci ake son yi ko?"
"Ko ɗaya, Allah ya baki sa'a " Abid ya bata amsa, domin ya lura ko kura albarka, me maganin Masarautar ne ya shigo, ya kalleta sannan ya tab'a wuyarta ya ce.
"Sannun kin ji, kin ketare rijiya da baya. Allah ya kiyaye" ya fada cikin kulawa sannan ya musu sallama. Wannan laluran ya bata damar kame harshen ta, daga kwadayi domin sau uku ana kawo abincin Abdullahi amma tana dauke kanta, sai ya fara ci take ci. Shi kuma da gayya sai ya cinye namar baki daya yake tura mata abincin.
Ai kuwa duk lokacin da ya cinye abincin yana shan harara, da kanin magana, sannan ita a matsayin ta na baiwa hawai tana yarda a cutar da ita ba ne, kawai gani take idan tayi shiru zai ci da rabonta ne, yasa bata iya hakuri da abin da idanunta ya gani, sai ta magantu.


---
"Samu babu abinda za a iya yi ne kuma? Ya kamata a dakatar da su." Ya fada bayan ya zuba uban tagumi, yana kallon bokan.
"Me kake so ayi? Ita yarinyar ya dace ku bawa Yaron can aurenta, idan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login