Showing 45001 words to 48000 words out of 105295 words
Chapter 16 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
sosai, yana bukatar kulawa sosai."
"Tow" ta fada tana jin haushin Uwar Bayi.
Haka ta fito suka nufi bangaren Yarima Shehu, sannan aka wuce da ita bangaren Yarima Abdullahi, tana shiga Abid ya ce mata.
"Ga daki can, ki kai kayan ki, idan ya gama abin da yake zai fito yana nan dakin sai ki kula da abincin shi kafin ya fito. Ai kin fahimci irin aikin ki"
"Ih" ta fada tana nufar dakin da ya nuna mata, babban burin ta ba kome ba ne tana fitowa ta gutsire cinyar kazar can. Ai ba gani yake ba dan haka tana kaiwa dakin ta fito wani irin yawu ne ya cika bakinta, ita kan ba zata cuci kanta ba. Wallahi cin kazar zata yi.
Tana fitowa ta zauna ta fara cin kazar, tana jin takun shi amma bata damu ba, ai ba gani yake ba. Allah ne ya kwace ta aka kawota wurin shi babu abin da zai iya mata bata inda maza suke mata kallon danyen nama, bata inda Arshan kullum yake ji kamar ya cinye ta danye ba.
A hankali yake lallube har ya zauna, lokacin ta cika bakinta da nama. Kallon shi tayi tana faɗin.
"Humm-mahumm baka ji baka gani baka magana. Tow sannu shugaba ai kuwa nayi kiba har da teb'a" kai hannun shi yayi zai fara cin abincin, dan yana bin kamshin girkin ne, ta janye tiren, tana wurga mishi kallon banza tare da gatsina fuskarta.
Sai ya hakura ya koma yana kallon ko ina, haka kawai sai ya bata tausayi ta tura mishi tiren har yana tab'a kafar shi. A hankali ya fara kokarin cin abincin tana hararan shi, duk inda ya saka hannun shi ta jagwagwala. Haka ya hakura ya ci, madaran ma shanyewa tayi ta bar mishi rabi.
Haka ya tab'a abincin ya bar sauran,.ta dauka ta shiga durawa kamar jaka tana gama cinyewa tayi katon gyatsa. Ta mike tare da kwashe kayan ta kai wani daki,.ganin ruwa yasa ta wanke tana goge bakin ta.
Can wurin la'asar ta fito tana kallon shi, yana zaune akan buxu da alamu ibadar shi yake. nufar wata kofa tayi ta bude tsakar gida ne babba, ga dan karamin gulbi. A hankali ta nufi gulbin ta fara cire kayanta kamar ba kowa, kwabe kayanta tayi ta fada wanka. Saidai tayi ta gaji gashi tana mugun son ruwa rashin dama ce shi yasa bata dama ba.
Tsakanin ta da Abdullahi kuwa kusan shi akan kawo kula da ita, a lokacin da ya cika kwanaki goma sha biyar, ya fahimci cewa ita ke cinye abincin kafin ya fito dan haka ya saka Ya Musa akan ya fada a kara mishi yawan abincin da ake kawowa, sannan wani abin da ya kara mishi hakurin zama da ita ba kome bane, tana da tsafta kamar hauka, dake akan kawo mishi kaya sabi daga Yarima Shehu, ita ke zab'a mishi kafin ya fito wanka, bayan ta ajiye a inda yake dauka. Sai ta fita, yana fita a dakin zata koma ta gyara, tana gamawa zata mishi jagora har wurin su ya Musa, su kuma su nufi Fada.
Da wannan yasa shi jin ba laifi zai iya zama da ita. A can kuwa Yarima Arshan kamar zai yi hauka, lokacin da yaji labarin kyautah ta koma bangaren Abdullahi dan haka yau ya kasance juma'a, sai da ya baza mutane akan Abdullahi yana barin gidan a zo a gaya masa.
Aikuwa haka ce ta faru, Abdullahi yana barin gidan, ya nufi gidan.
Ana ganin shi aka bude mishi, dake kifi ce tana can tana wanka, daga ita sai wani mayani da ta daure kirjinta zuwa kasa. Murmushi yayi ua cire kayan shi, ya nufi cikin ruwan yadda ta nutse cikin ruwan haka ya shiga tana d'agawa suka yi Idanu biyu da shi.
"Wayyo" ta furta tana kare kirjinta,
A hankali ya tako har gaban ta, ya fisgota yana dariya. Jan mayanin yayi ta rike hannun shi, ya fisge da karfin tsiya ya tura ta, kare kirjinta tayi tana fashewa da kuka, saka mata kafa yayi , ta fada cikin ruwan ya bita tare da jan mayanin kasa, yana sauke wani irin ajiyar zuciya. Kamota yayi ta zame tare da fita da gudu, fitowa yayi ya bi bayan ta. Karo tayi da Abdullahi.
Wani irin kuka ne ya kwace mata, cire alkyabar shi yayi, ya lullube ta. Kamar yasan babu kaya a jikinta, haka ya wuce da ita d'akin shi, ya sake ta sannan ya wuce wurin kayan shi, jin babu motsin Arshan yasa ta fitowa ta nufi ɗakinta.
Tana shiga taji an shake ta.
"Ba ki isa ki hada ni da wani ba, karya kike wani ya mallake ki." Tari take idanunta a waje, sannan ya fisge alkyabar. Ji yayi kamar an zuba mishi tsimagiya, babu shiri ya sake ta ya fita da gudu.
Da rarrafe ta dauki kayanta, ta saka tana kuka kamar ranta zai fita. Wannan wacce irin masifa ce, a yau tayi alawadai da rashin ganin Abdullahi domin tasan da yana gani babu mamaki da ya taimaka mata. Haka ta zauna a dakin tana jin shi ya fita daga cikin gidan.
Koda aka kawo abincin yaga bata ci ba, don haka ya kara fahimtar akwai abinda ya faru da baya nan, domin dawowar shi yasa shi fahimtar haka tun shigowar shi. Tsigar jikin shi ne ya mike da mugun gudu, tare da jin kamar kunama ta harbe shi. Yaso Raudah amma zuciyar shi bata tab'a harbawa haka ba sai yau, me haka yake nufi? Lumshe idanun shi yayi yana son yaji tana lafiya, dan haka ya dauki abincin da lallube ya nime ɗakinta. Yana shiga yaji shiru amma bai fasa ba, ya ajiye mata abincin yana bubuga sandar hannun shi. Haia yasa ta bude idanun ta.
Kwalla ne ya zuba mata, ta goge da bayan hannun ta, sannan ta nufi wurin abincin ta dauka tare da riko sandar shi suka fito zauren shi. Zama yayi yana kallon inda take duk da ya fahimci haka ne sanadin rike sandar shi. Zama yayi domin ya gane cewa yana saman shimfidar shi ce, itama zama tayi ta tura mishi abincin tayi.
Baki daya yau bata da nutsuwa amma ba zata iya wuce Namar da ta gani saman abincin ba, dan haka ta fara ɗauke kazar ta yageta yadda zai mata. Lallubar kazar yayi yaji wayam. A ranshi ya sake murmushin mamaki babu ruwanta matukar nama ce tow anan zata nuna maka ita kura ce. Dan haka tana ci tana girgiza kai baki daya ta manta da abin da ya faru, kadan ya tab'a ya bar mata kafin wani lokaci ta cinye baki daya ta tashi ta nufi dakin girki ta wanke su.
Tana fitowa ta hango Abid zaune da alamu magana suke.
"Kyautah basamuden ki yana son zuwa yawo cikin masarautar!"
"Tow amma har da kai ko?"
"Ih amma ba fitar rana bace da daddare zamu fita."
A ranta ta ce kuma dai! Ban da kinibibi irinta makaho me zai iya gani a dare kai da rana ma, sai an maka jagora salon yaje yaci tuntube ya bar mutane da aiki....
300₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
.......
A wani irin razane yayi baya, yana zare idanun shi. A hankali Mayafin ya zame har gefen wuyar shi, taswirar dake jikin tutar deehar wacce take gefen wuyar Hayatudeen Abdullahi Noye ya bayyana a kafad'ar Abdullahi Noye.
Kamar zai fado daga bisa dokin da yake kai, ya gigice iya gigita dan haka yayi baya yana jin zufa na karyo mishi.
"Kun ga wani mutum da mayafi a fuskar shi?"
"A'a babu kowa nan" kamar Ance ya d'ago kai ya hango Ya Musa da Abdullahi suna tafiya, kafin ya kad'a linzamin dokin shi zuwa cikin jama'a sun b'ace. Juyawa yayi ya dawo kofar Deehar da gudu.
Shiga cikin masarautar yayi kai tsaye ba tare da wani tunani ba.
"An yanka ta tashi." Ya fada jikin shi yana rawa.
"Me kake nufi?" Sarkin Malamai ya tambaye shi.
"Ya Musa da Abdullahi basu mutu ba." Zubur suka mike.
"Alhamdulillahi, toh ai shi kenan a dawo da su cikin masarautar ba"
Jin Chiroma da Tafida.
"Kamar ya?"
"Kamar yadda aka yi tsammanin sun mutu sai a dawo da su."
"Me zamu cewa talakawan mu?"
"Yanzu ma me kace musu? Bayan kasan sarai bori suke."
"Ni ban gane ba, ya zamu yi da batun talakawan?"
Mikewa Alkali yayi shi da Garkuwa suka ce.
"Ina ga a fita a nime jin ra'ayin sun,idan aka ji sai a mai da hankali akan Abdullahi."
"Gaskiya ba zai yiwu ba, sannan idan aka ce Abdullahi zai dawo cikin masarautar nan akwai tashin hankali mara iyaka."
"Kasan me kace? Idan ba iya bakin ka ba zai kai ka ya baro ka "
A hankali aka fara watsewa, ambaton sunan Abdullahi da Ya Musa yasa hantar cikin wasu ya kad'a,.kuma abin takaici shi ne basu nuna akan idanun su ba.
Sai dai Galadima ya bayyana kiyayyar shi da dawowan Abdullahi Noye.
Daga Fada wurin Fulani ya nufa ya zauna a gabanta, yana sauke numfashi shi.
"Fulani!"
D'ago kai tayi ta kalle shi, sannan ta cigaba da cin tufar da yake hannunta.
"Ashe Abdullahi bai mutum ba" ya fada Muryan shi yana rawa.
"Toh sai me? A dawo da shi cikin fada mana"
Ta fada fuskarta cike da murmushi.
"Tunda ya dawo akwai"
"Babu kome d'ana ya dawo gare ni, a dawo da shi cikin gidan su."
"Arshan fa?"
"Kul na kuma jin ka ambaci Arshan" zare idanu yayi yana faɗin.
"Fulani Arshan ɗin"
"Ka fada a fada a dawo da Abdullahi cikin gidan"
Kamar zai yi kuka ya mike, sannan ya fita daga dakin.
Fuskarta dauke da murmushi, ita tasan abin da take nufi.
---
Magajiya tana zaune, Amintacciyar baiwar ta, ta shigo ya gaya mata.
"Idan ya shigo masarautan ki fara gaya min" ta fada tana murmushi itama.
"Hmm" ta kuma sake murmushin farin ciki.
Tana kurban ruwan zafin hannunta, tana lumshe idanun ta, wannan shi ne tana kasa tana dabo, ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
---
A lokacin da labarin ya isa wurin Kilishi, cikin farin ciki ta cewa matar.
"Ga wannan tagulan tun na aure na ne, amsa ki tashi kin kawo min labari me dadi"
"Godiya nake ranki shi dade" ta amsa tana godiya sannan ta bar dakin.
---
Lokacin da Zinaru da Zuwairah suka samu labarin ganin Abdullahi, ko a jikin shi domin kishin gidan Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ai ba akan shi kawai ake ba. Don haka wannan bai shafe su ba.
***
"Galadima ya gan mu, sannan a dakatar da borin gobe zasu bukaci ganin talakawa da shi Abdullahi" Ya Musa ya faɗa, yana kallon su.
Shiru Ya Haruna yayi sannan ya ce musu.
"Shirun mutanen nan fada, babu alkhairi ina ji a jikina suna shiri ne"
"Ih, nima haka ai ba yau aka fara ba, don haka duk abin da zai faru sai ya faru Abdullahi da Abid zasu shiga fada da yardan Allah."
Haka suka yi sallah suka ci abinci, can wurin dare ya fara rabawa, gashi garin Yayi duhu, kamar yadda suka tsammani haka kuwa aka kawo musu harin bazata. Sai dai dama sun bar gidan tun kafin haka ya faru, asalima shiri ne suka yi tare da kare kansu.
Da ikon Allah suka ga bayan dakarun, a daren mutanen unguwar suka fito, ganin dakarun Deehar da manyan makamai yasa suka fara kokarin boya duk da an kashe su .
"Ya Musa wai meke faruwa ne?"
"Babu sun turo a kashe Yarima Abdullahi Noye ne"
"Laa dama shine Yarima Abdullahi Noye? D'an Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye?"
Wannan ma shima salon siyasa ce, bayan sun kyautatta musu, sannan suka saka su bore. Kafin aka bayyana musu shi a matsayin Yarimar Deehar, kenan talakawa sun san waye shugaban su me taimakawa ne a gare su, domin yana cin abincin su, yana shan kome irin nasu sab'anin Arshan da ya taso, Iskanci ya sani.
"Mun bi Allah da Manzonsa,.muna masu muba'aya ga Yarima Abdullah."
---
Daukar tulun giyar yayi ya sha sosai, kafin yayi wurgi da shi.
"Waye shi? Yaushe ya rayu?"
Ja baya taii, tana kokarin kunce hannunta.
"Ke! A fadin Deehar kin ga namijin da ya fi ni?"
A hankali surar Basamude ya dawo kanta. Ga dai idanun shi dara-dara masu lafiya da firgita maza, amma sam basu da amfani.
Zubewa yayi a jikinta, ya fara kokarin kwara mata amai, ta ture shi.
Yana gama aman, makulin marin yana fadowa.
Dauka tayi ta bude kanta, a hankali ta shaki iska me dad'i, sannan ta nufi hanyar waje. Idan ta nufi cikin Masarautar sake daukota zai yi, amma idan ta bar masarautar zuwa wurin Basamude fa? Ita yanzu ta fi gane Basamude yo baya gani fa.
Haka ta saka kai ta fita kamar mara gaskiya.
Kasancewar dare yayi babu wanda ya lura da fitarta.
Haka ta nufi can wajen gidan su, a lokacin suna tare da jama'ar unguwar da suka fito, a hankali tayi ratsa su har ta isa cikin inda yake zaune.
Kallon shi tayi sannan ta cewa Ya Musa.
"Baba me ya faru?"
"Kawo hari aka yi, ina kika boya?"
"Sun same shi ne?"
"A'a babu abin da ya faru"
"Hmm, tunda na koma Yarima Arshan yasa aka saka min mari sai yanzu na fito idan na cigaba da zaman fadar ba zai bar ni ba"
"Tow kin ga mu ma."
"Korata kuke?"
"A'a Kyautah akwai hatsari a tattare damu" Ya Haruna ya gaya mata.
"Shi kenan amma dai, kun san ba zai yiwu na koma a daren nan ba ko?"
Ta fada tana kallon Basamude, wanda shi kan bai san tana yi ba.
A gefe guda, Ya Musa yana jin ina ma da Raudah ce, Kyautah yadda take kokarin shiga jikin Abdullahi ba tare da sanin ta ba, murmushi yayi.
"Tow muje"
Rike hannun shi Abid yayi ya gaya mishi tazo, dauke kai yayi yana mamakin yadda ta dauki kwanaki bata zo ba sai yau, yau din ma cikin tashin hankali.
Dakin da ta tab'a kwana nan ta kwanta.
--
"Har yanzu babu wani labari?"
"Babu"
"Ku bincike sosai, kar a bada wata kofar da za a gane" inji Galadima da yake tsaye jiran dakarun da ya tura su kashe Abdullahi. Domin matukar yana raye Abdullahi ba zai tab'a zama sarkin Deehar ba har alfijir ya keto babu labarin dakarun da ya tura. Dole tasa ya koma masarautar.
---
Washi gari
A malaken shanu aka kawo dakarun Deehar har kofar masarautar aka zuba musu, sannan suka juya abin su.
Bayan an zuba su ne, talakawa suka sake fitowa domin tir.
Tare da bada goyon bayan su ga Abdullahi.
A lokacin Garkuwa da Alkali, Tafida da Sarkin Yaki Uzairu suka nufi wajen masarautar.
"Mun san an yi laifi, muna bada hakuri da rashin isowar mu akan lokaci."
"Mu Abdullahi muke so"
Shiru ne ya ziyarci zuciyar su, kafin Tafida ya ce musu.
"Muma shi muke so, ina Ya Musa yake?"
Matsa mishi a kayi ya fito yana takewa Abdullahi da yake gaba baya."
Duk da akwai mayafi a fuskar su, aka bai hana su gane su ba, musamman Abid da shima kana ganin shi kaga Waziri.
Ga Ya Haruna.
"Mun gode a nuna girmamawa kuka yiwa Yarima Abdullahi Noye, shima kuma ya nuna cewa shi uban kasa ne domin rungumi matsalar al'ummar shi, in sha Allah zamu bashi damar zama daya daga cikin mutanen fadar mu."
Duk da maganar ba wai tana musu dadin fada bane, amma kuma tana musu yajin fadar shi.
A kwai gaskiyar da dole sai an fadeta koda ba ason ta. Don haka lokaci ne da zasu fadi gaskiya koda kuwa zasu mutu, lumshe idanun Ya Musa yayi sannan ya cire mayafin shi ya ce musu.
"Zamu shigo da Yarima Abdullahi amma gidan Yarima Shehu zamu sauka."
Shiru suka kuma yi kafin suka ce.
"Tow ai wannan ba kome bane. Muna mara da ku."
Duk da ba a san meye a zukatan su ba, sai dai Ya Musa da Ya Haruna sunyiwa talakawa alkawarin tsaya musu a koda yaushe. Kafin suka shiga cikin gidan sarautar a karo na biyu. Kyautah tana biye da bayan su, cike da mamaki dama Basamude dan masarautar Deehar ne? Yo ita Idanun shi kawai ta gani..
0142529598 Ramlat abdulrahman Manga Union bank
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
#Mai_Dambu
....... Kaiwa da komowa Arshan yake kamar zai tadda dakin baki daya, kallon Namir yayi sannan ya ce mishi.
"Ka ji labarin halin da take ciki?" Shigowa dakin Galadima yayi bai yi wata-wata ba, ya kifawa Arshan mari a fuskar shi.
"Sakarai dakiki mara lissafi, idan yarinyar ta mutu ba iya kai ba hatta mu ba zamu tsira daga farmakin da zamu fuskanta ba, jahili wanda bai aiki da ƙwaƙwalwar shi." Daga haka ya fita a gidan.
--- Kallon ta Uwar bayi tayi tana ta barci.
"Allah ya baki lafiya!"
Ta furta, a zauren kuwa Yarima Shehu da Ya Musa sun bar gidan, Abid da Abdullahi suna zaune a zauren , ƙarshe a nan suka kwana.
Koda suka tafi sallah asuba sun hadu da Arshan amma babu wanda ya kula wani. Bayan sun fito aka turo kiran Arshan daga ɓangaren Fulani Babba.
Lokacin da ya isa taba barci, sai da ya zauna har kusan hatsi ta farka. Abin karyawa tasa aka kawo musu tare, suna ci tana tana jan shi da hira.
"Da nace kar ka taba lafiyarta shi ne ka dake ta?"
Girgiza kai yayi yana faɗin.
"Ba ita nayi niyyar duka ba."
"Tow kar ka kuma ka daure, nasan kana sonta." D'ago kai yayi yana kallon Fulani Babba, murmushi tayi mishi sannan ta ce mishi.
"Na sani sosai, shi yasa nace ka nime soyayyarta."
"In sha Allah "
"Ka bar kome a karkashin mu, kar ka kara tab'a lafiyarta dan zan hukunta ka."
"Ba zan kuma ba"
"Zaka iya tafiya."
"Ki huta lafiya"
"Allah ya sa" ya fito yana sauke ajiyar zuciya, gidan shi ya nufa ya samu Wabi tana kwance tana kallon shi.
"Me yasa me ka Yarima na?"
"Kyautah ce ba lafiya tana gidan Abdullahi." Duk da tana kishin Yar Uwarta amma bai hana ta firgita ainun ba.
"Me ya same ta?"
"Abu ne ya fado mata a baya" gyada kai tayi sannan