Showing 60001 words to 63000 words out of 105295 words

Chapter 21 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6122

"Sannu Yar albarka, duk da nasan yanzu kin wuce zama dani, sai dai ina kara tuna miki kaf Deehar baki da wasu dangi sama da mu,.mune dolen ki, babu wanda ya wuce naka"
Haka suka zauna tana ta lallaba kyautah, har zuwa lokacin da Uwar bayi ta dawo.
Sannan ta tafi, bayan tafiyar ta ne Kyautah tace zata koma wurin Mama Uwa da zama,kallon baki da hankali Uwar bayi ta mata, sannan ta ce mata.
"Ki tafi ki nimo izini a wurin Abdullahi"
"Cab wancan kurman ne zai kula ni, kawai zan tafi"
"Wai ke Kyautah yaushe zaki yi hankali? Duk abin da yake faruwa dake Mama Uwa tana da hannu a cikin shi."
Idanunta ne ya cika da kwalla, ranta yana ɓaci ta ce mata.
"Tabbas masu iya magana sun yi gaskiya, da suka ce naka sai naka dadin zama sai bare, ba sai kin raba tsakanin mu ba" ta mike ta dauki yan tsumokararta, dariya ta bawa Uwar Bayi domin bata ga abu me zafi a maganar ta ba, asalima sai ganin wautar Kyautah da take, shi yasa bata yarda da Mama Uwa ba, domin makirar mata ce,.yanzu haka tazo ta ziga kyautah ce.
Ai kuwa Kyautah ta ficce ta koma can wurin su Mama Uwa,dake tunda Wabi ta zama ta Yarima Arshan shi kenan aka haramta mata zama cikin bayi. Haka ta nufe bangaren su Mama Uwa.
Suna zaune a tsakar gidan suna jiran zuwan.
"Uwa kina ganin zata zo kuwa?"
"Zata so"
Ai kuwa bata rufe baki, sai ga Kyautah a cikin gidan. Ajiyar zuciya suka sauke kusan a tare.
"Lalle maraba, shigo daga ciki mana" shiga tayi suka kaita har dakin da Wabi take, anan suka ga juna cikin farin ciki, nan suka baje aka yi ta hira. Har dare, tuwon dawa aka ajiye musu, nan suka shiga ci Mama Uwa ta basu yajin kalwa, suka fara ci kamar abin Arziki bayan sun gama, dakyar ta iya fitowa ya wanke hannunta, tana komawa ta zube tuni barci yayi gaba da ita.
"Taso muje, ai yau zaki rabu da wannan dan iskan cikin" haka suka nufi wurin bamaguje, dake dare yayi cewa yayi.
"Ku tafi sai asuba zaku zo ku zata dawo" tun kafin su zo suka cire kayan Kyautah ta saka, duk da kayan ya mata kadan, amma haka ta saka.
Cikin farin ciki suka dawo, ita kuma Kyautah tana ta barci, cikin farin ciki Mama Uwa ta kwanta, shi kuwa bamaguje tunda ya samu Wabi, haka yayi ya abu daya akanta, duk jarabar Arshan yau taga wanda tunda ya fara a farkon dare bai sauka ba, sai da sanyin asuba ta ratsa shi, sannan ya sauka ya sata tsuguno akan kasko. Haka kuwa gudan jini ya fado cikin tukunyar, ya saka wasu irin auduga ya goge mata gabanta, sannan ya ce mata.
"Ki koma kyautah zata amshi kome yadda ya dace"
Haka ta dawo a gajiye tana ganin yadda kowa yake fitowa ana kallonta, su a tunanin su Kyautah ce, haka ta wuce bangaren, tun da ta shiga ta kwanta bata juya ba. Sai a lokacin ta lura da Kyautah da take ta barci, tashi tayi ta cire kayan kyautah ta ajiye mata, sannan ta koma ta kwanta itama barci me nauyi ya dauke ta.
Sai da gari ya waye, ciwon ciki da mara ya tashi Kyautah, dungure take a dakin ga Uban jinin da yake zuba a jikinta. Wanda bata san na Meye bane. Haka tayi ta fama kafin kace me dakin an cika, dole aka kira Uwar Bayi, tunda tazo ta kasa fahimtar kome, tana rike da hannun Kyautah har zuwa lokacin da jinin ya tsaya, sai kaɗan da taimakon Mama Uwa aka mata wani, kallon ta Uwar Bayi taui fuska babu walwala ta ce mata.
"Yayi miki ko? Tunda ke baki jin magana"
"Uwar bayi ki barta anan zan kula da ita" wani irin banza kallo ta watsa mata.
"Ki kula da kanki, Uwa shi duniya kayi abin Arziki ma aka kare balle kayi ta banza." Daga haka ta fita, tana jin mutanen gidan suna yar karamin gulma irin ta bayi.
Tausayin Kyautah take ji, don haka ta nufi ɓangaren Abdullahi ta fada mishi abin da yake faruwa, tana zuwa ta samu da Ya Musa, don haka bata yi.kasa a gwiwa ba ta gaya musu abinda yake faruwa, abin yayi mugun aiki a ran Ya Musa, domin shima ya fara kokarin nuna mishi illar tarayya da Kyautah. Kawai bai fito ya gaya mishi bane.
Kallon Abid yayi.
"Zamu je mu duba ta, an jima"
"Tow"
Sannan tayi musu sallama, tana fita ya Musa ya ce.
"Yarinyar nan, abubuwa da yawa yana faruwa da ita, har aka Cigaba da zama da ita, gaskiya al'amarin da zai faru zai fi haka, kusan wata shida a garin nan kome sai ka samu ita ce a kan gaba, ban sani ba ko kana da wani dalili na rike ta amma tsarin bai yi ba kullum yarinya cikin rashin jin magana kamar a kanta aka fara marasa ji.
"Ya Musa!" Yadda ya kira sunan shi, yasa shi, nutsuwa.
"Ya Musa kenan, Baiwa ce fa kuma naga wasu masu iyayen sai abin da suke so suke yi ɓalle ita da bata da me tsawata Mata."
Shiru yayi yana nazarin kalaman Abid, tabbas magana ya gaya mishi. Ganin fuskar Abdullahi yayi yaga har zuwa lokacin babu wani canji, kuma yana son yaji me zai ce, amma sai yaki magana domin ya nunawa ya Musa bai damu ba.
"Ina son zuwa na dauko Raudah da mahaifiyarta"
"Tow Allah ya kai mu" ajiyar zuciya ya sauke domin kuwa bai yi zaton zai magana ba, halin Abdullahi sai shi ruwan sanyi dafa mod'a, bai fito ya ce mishi ya daina abin da yake yi ba, amma kuma ya zuba mishi na mujiya...
300₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
.......... Murmushi yayi yana kara jin dadi a ran shi, koda suka isa Abid bai ma tsaya ba tafiyar shi yayi, suna shiga ya wuce ta. Abinci ya gani ya kalle ta yadda take hadiye yawu ya ce mata.
"Garin kwadayi zaki mutu" tsam jikinta ya amshi maganar shi, amma bata kawo a ranta shi yayi magana ba ba, dan haka ta juya a hankali tana kallon gefe gefe da gefenta. Shima ya fuskanci bata gane shi yayi maganar ba, don haka ya share kawai, kamar me nazari abin ya fado mata juyawa tayi tana kara kallon wurin babu kowa daga ita sai shi.
"Hala Aljanun da na kira A fada ne suka fara bibiyata"
"Babu Aljani sai ke" ai kamar wacce kare ya zabureta, ta ficce da mugun gudu, domin wallahi bata kawo a ranta shi yake magana ba, karo tayi da Ya Musa. Haka kawai yake jin tsanar yarinyar tunda Galadima ya fara nuna mishi dacewar Raudah ta koma ɗakinta yasa shi fara jin tsanar Kyautah. Kuma yanzu yake kar gano rashin dacewar zaman Kyautah a cikin su, domin tun haduwar su da Abdullahi ya tattara abin da ya kawo shi ya ajiye a gefe, kamar bai da muradin kan shi, sai na bata kariya. In sha Allah yana kawo Raudah zai tunkare shi da maganar auren su.


"Ke dalla tafi can, kin zama kamar ballagaza mara kamun kai. Meye kike ihu kamar mahaukaciya!" Kura mishi Idanu tayi, tana jin zafin kalaman shi. Hawaye ne ya sauko mata tana nuna hanyar da ta fito, Abdullahi ne a tsaye hannun shi harde a kirjin shi.
"Magana nayi sai nake ganin kamar." Ta sunkuyar da kanta, shima Ya Musan kunya ce ta kama shi, musamman yadda Abdullahi yaƙe mishi wani irin kallo me cike da manufofi dayawa.
"Sai kike ganin kamar me?"
"Kamar nayi gamo!" Kakaro murmushi yayi ya ce mata.
"Tow gamo kuma?"
"Ih, magana aka min kuma daga ni sai shi" d'ago kai yayi da niyyar kallon Abdullahi yaga baya nan. Cikin jin haushi ya ce mata.
"Sakarya irinki ba dole tayi gamo ba, ai dole kiga abinda ya fi karfin ki, wawuya wuce ki bani wuri, babu abin da kika ji ko gani haukarki ce kawai ta baki haka."
Wuce ta yayi yana faɗin.
"Kafirar banza kafirar wofi" abin ya mata zafi dan haka ta nufi lambun da yake harabar bangaren ta zauna, tana kuka.
Lokacin da ya shiga cikin gidan, ya samu Abdullahi yana shan ruwa a hankali.
"Kayi mata magana ne? Naga ta rude sosai"
"Ih, a matsayinka na Uban da ya haifa Y'ace bai dace ka kausassha harshen ka akan wata ba. Domin da da dukiya ba kasan waye zaka mora ba." Ji yayi kamar an buga mishi guduma a tsakiyar kan shi, domin kunya ce ta kama shi hakikan, har jikin shi rawa yake.
"Kawai fada na mata ta kula"
"Hmm" ya fada mishi yana mamakin yadda yake shirin kare kansa, shiru suka yi kowa da abin da yake yawo a ran shi.
"Ranka shi dade, asuban gobe zan bar Deehar" Ya sani matsayin shi ne, a kira shi da haka amma tow, wani irin murmushi yayi sannan ya juya ga Ya Musa din ne, haka kawai yake ganin kamar bai da cikakken gaskiya, sai kaukauda kai yake, kawai sai yayi fuska kamar bai fahimci halin da yake ciki ba. Don haka ya dauke kai kamar bai damu ba.


Bayan son ya cire yarda da yayiwa Ya Musa ne, amma kuma dole haka ya faru, domin yana ji a jikin shi Ya Musa da ya sani ba shi bane a gaban shi, wasu na juya tunanin shi, tun a zantuttukar da suka yi da Fulani Babba ya fahimci akwai wata gaskiyar da yake binne a kasa, amma baya kaunar saka a haka a ran shi.
"Allah ya tsare. Ba zan hana ka ba, Ya Musa sai dai don mugun nufi ka ɗinkin lifidi ne." Kamar wanda aka watsa mishi ruwan zafi a jikin shi, zufa ne ya shiga karyo mishi, yadda Abdullahi yayi maganar kamar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, ganin shi yake kamar Ubanshi, hatta sajen shi da kasumbar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye.
Ji yayi kamar kafafun shi ba zasu dauke shi ba. Ya zube a kan gwiwar shi ya faɗin.
"Tuba nake ranka shi dade, wallahi babu wani manufa a raina, zan dauko Iyalina ne domin ina bukatar su a kan sa da ni. Amma ko zancen da kaji ana cewa na maida Raudah ɗakinta wallahi ban shirya hakan ba, asalima kawai shawararsu ce." Murmushin yayi sannan ya ce.
"Ina yafewa makiyi amma bana yafewa cin amana da butulci " daga haka ya mike ya bar shi nan a tsugune.
Tunda ya wuce can cikin gida ya nufi wurin hutawa ya zauna, dole ya kama Galadima yaci kaniyar shi, domin shi yake warware mishi aiki.


Tana zaune a lambu tana ta gurzan kuka, da ta gaji da kukan ta wuce bangaren Uwar bayi, tana zuwa ta shige dakinta ta kwanta a gadonta, sai kuka take kalaman Ya Musa yana kara kona mata rai. Haka Uwar Bayi tazo dakin ta same ta.
"Ke kuma da waye?"
"Babu" ta fada tana kara fashewa da kuka, domin kalmar yana kata ciwo kamar ta mutu, tun rana take dakin har dare bata futa ba, fuskar nan tayi jajjur kamar wacce aka mata shegen duka, tun daga bakin kofar shiga bangaren ta fahimci yana zuwa domin kuwa ana ta sanar musu, ga Yarima Abdullahi da Yarima Abid.
Lumshe idanun tayi ta juya ta cigaba da ƙwanciyar ta, duk wannan rigimar da ake akan idanun Uwar Bayi, wani irin farin ciki ne ya cika ranta ko babu kome Abdullahi ya nunawa sauran bayin cewa Kyautah tana da daraja, Mikewa tayi ta fito.
"Barkan ku, Yallabai Abid kune a daren nan, gashi tai barci."
Lumshe idanun shi yayi, sannan ya taka zuwa bakin kofar, ya d'aga labulen dakin, sai motsi take alamar idanunta biyu. Kasa kasa yayi da murya ya ce.
"Uwar bayi har dake a cikin masu ha'inci?" Sunkuyar da kai a matukar kad'e, tana girgiza kai ta ce mishi.
"Allah ya huci zuciyar ka. Naga tana bukatar hutu ne"
Shiga dakin yayi, ta kalli Abid.
"Dama yana magana?"
"Kwarai musamman akan kyautah magana yake sosai."
"Ya ilahi, Allah yasa kar ta zama raunin shi."
"Ba zata zama ba" Abid ya fada yana jiran shi.
"Nasan idanunki biyu" a matukar razane ta yaye mayafin ta juya, tana kallon shi a matukar razana.
"Tashi muje " ya kuma furta mata, ji tayi duniyar tana juya mata, a hankali ta tafi luuuuu, zubewa tayi ta suma. A hankali ya cincibeta ya fito da ita.
"Sai kace tsuma " ya furta a ranshi,
Domin bai ji kome ba, wannan shine karo na biyu da ya dauke ta, ganin shi dauke da ita yasa Abid ya bashi hanya.
"Lafiyarta kuwa?"
"Hm" ya fada, har suka bar bangaren suna shiga shsshinsa, ya kwantar da ita sannan ya juya ya barta a wurin.
"Me yasa me ta?"
"Razana tayi"
"Da me?" Abid ya tambaye shi yana zare idanu.
"Da magana ta" dariya ce ta kwacewa Abid.
"Yarinyar nan tana ji da kuruciya, ina ma zan samu irinta domin wallahi zata bawa mutum nishadi "
"Hmm!"
"Tun haduwar mu na fahimci, tana burge ka" inji Abid, tsuke fuskar shi yayi.
"Ba wani abu na fada ba, ita din zata iya zame maka wani abu na rayuwa. Idan har akwai bukatar hakan, amma ina tsoron kar makiya su mai da ita makamin yakarka."
"Adawa kake da ita?" Ya tambayi Abid.
"Wallahi ban tab'a adawa da abin da ake so ba, ni me bada rayuwata ce domin kai. Tsoron kar ta zama raunin ka ce"
Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Ba zata iya zama rauni na ba, sai dai zata iya karban haka a matsayin zalinci da zan mata"

"Kamar Ya?" Kallon Abid yayi yana Lumshe idanun shi," a gare ta zan zama mara adalci, ga al'umma zan zama rauninta, duk wanda ya kusanceta da mugun nufi, zan iya kawo ƙarshen shi a cikin su har da danginta." Kura mishi ido Abid yayi cikin girmamawa ya ce.
"Akwai yiwuwar kana da muradinta sama da soyayya a cikin gidan nan"
"Ka manta da batun ta ka nimo min sarkin Yaki Uzairu "
"An gama"
Ya mike zai fita ya ce mishi.
"Duk macen da zata yi kasadar bawa mutum irinka rayuwarta ba tare da ta sani ba, meye tukwaicin ta?" Abid ya tambaye shi, daura daya yayi a kan daya yana me kallon kofar dakin da take. Yana dan kad'a kafar shi irin wadda yake cikin nishadi.
"Tow ba sai ka fada ba. Malamin soyayya"
Ya juya ya bar zauren, shi kuwa Abdullahi yatsar shi ya kai kirjin shi daidai bugun numfashinsa.
"Nan ne wurin zamanta har abada"


Can tsakiyar dare Uzairu ya shigo, ya zube a kasa. Sannan ya ce.
"Ranka shi dade gani "
"A nima min amintaccen bawa ya bi sawun ya Musa har Numan, zan yafewa makiyi amma bana yafewa cin amana da butulci "
"Wannan haka yake, Ranka shi dade shekaru arba'in kafin haihuwar ka, Sarki Hayatudeen ya tab'a jagorantar wani yakin sukuru, da wasu gungun Yan fashi, shekaranjiya mun samu labarin yan fashin nan suna nan raye, kuma suna shirin kawo hari Deehar. Jiya na samu Alkali da su Chiroma da zancen wallahi sun ki magana, ranka ya dade yakin nan zai shafi talakawan da suke gefen Deehar ne, kuma sune manoman da suke kawo abinci mafi yawa Deehar, bayan araji da ake karba sama kima. Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ya kare bayin Allah nan ne domin cigaban Deehar yau bayin Allah nan suna bukatar wani me kare su, kuma sunki bamu damar fuskantar haka. Na gaya maka ne domin ko akwai abin da zaka iya"


Lumshe idanun shi yayi haka ya zame mishi al'ada, sannan ya bude idanun a hankali ya ce.
"A cigaba da shiri zan duba al'amarin"
"Allah ya baka iko dan Alfarman Annabi" gyada kai yayi, har Uzairu ya fita, yana zaune a wurin har asuba, sannan ya tafi masalaci. Bayan an isar da sallah, ya dawo gida tare da Abid. Lokacin ta fito daga dakin tana kallon su.
Sake dubawa tayi taga daga shi sai Abid, matsawa jikin Abid tayi ta ce mishi.
"Kasan jiya nayi mafarkin wai Basamude yana magana?" Kallon Abdullahi yayi da ya saka fuska, yana niman wurin zama.
"Ina sandar shi?"
"Ai dama yana gani lafiyar shi lau, kece baki sani ba." Luuuu ta tafi zata zube a jikin Abid ya daka mata tsawa.
"Kika sake kika fada jikinki sai na zane ki" kamar yar bori ta koma ta zube a kasa tana nishi sama sama.
"Abdullahi na gama zan fita "
"Akwai yiwar lokacin bayyana kan ka, a matsayin gwanin sarrafa takobi ya karato fa " ya fada yana lumshe idanun shi.
"Kai haba? Bari na kwashi labari "
"Ka tafi wurin Sarkin Yaki Uzairu zai baka sako ka kawo min, daga yau zamu fara sabunta horon yaki "
"An gama" zubur ta mike.
"Yallabai Abid na haukace ne?"
Kallon mamaki suka mata, kafin Abdullahi ya cigaba da bayanin shi.
"Wato nice Mahaukaciya a cikin gidan nan ko?" Ta fada da mugun karfi.
Wani uban harara ya maka mata, wanda yasa ta hadiye haukarta, ta shi yayi ya nufi inda take, tana ja da baya har suka dangana da bango.
"Idan kika kuma min ihu sai na yanke harshen ki" yadda yake maganar zaka dauka lallabata yake, rintsa idanunta tayi hawaye na zuba mata.
"Kar na kuma ganin kafarki a wajen masarautar nan idan ba haka ba" bude ido tayi, jikinta yana rawa.
"Kin ji ai"
"Abdullahi yarinya ce fa"
"Hmmm!" Juyawa yayi ya barta, ta zame a wurin. Kafin ta wuce dakin ta da rarrafe.
"Ka bita a hankali!"
"Ka amso sakon a wurin shi ina jiran ka"
Sannan ya mike ya fita, yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login