Showing 39001 words to 42000 words out of 105295 words
Chapter 14 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
shi yayi sannan ya juya ga Easter.
"Lokaci yana zuwa!"
Daga haka ya saka kai zai fita.
"Ya Uzairu da gaske kake?"
"Ih mana, baki ji hujja ba."
"Naji" ta fada hawaye na zuba mata, sannan ta ce mishi.
"Na gode"
Fita yayi abin shi.
"Sarkin Yaki baka ce min kome ba, bayan tambayar da ka min"
"Na manta abin da zan gaya miki" ya saka kai ya fita,idanunta ne ya cika da kwalla.
"Babu me taimakona ya kenan?"
"Akwai mana ki jira lokaci" ya fada yana barin dakin.
Tashi tayi zata juya jiri ya kwashe ta, rike ta Uwar Bayi tai, sannan ta kalli yadda take kokarin suma.
Murmusa mata tayi,
Ƙasa kasa ta ce mata.
"Kin zata ke daya kike da ciwo a rayuwar ki, kowa yana da irin shi hakuri ake"
Daga haka ta lumshe idanun ta, kwantar da ita tayi, ta cigaba da aikinta.
---
Abinci yake ci yana, tuna yadda Raudah ta kai karar mahaifinta, saboda shi duk sai ya ji ya muzanta.
Dafa shi Abid yayi.
"Idan ka gama yangar kazo muje" murmushi yayi mishi.
Sannan ya ture abincin, yana son shakar iskar garin shi, dake yamma tayi likis tare suka fita, suna tafiya.
Daga nesa ta hango su,.tana dauke da kwando a kanta. Sai masifa take tana ganin shi ta tsaya cak.
"Basamude." Isa tayi inda suke.
Ta saka kwandon a gefenta kugunta kallon Abid tayi shima babu laifi kamar Basamude.
"Wai ku in tambaye ku mana?"
"Muna jinki"
"Amma a jinin samudawa kunne autocin su?"
Kura mata Idanu Abid yayi sannan ya ce mata.
"Yan mata me sunanki?"
"Kyautah, Easther!"
Kallonta yayi da kyau.
"Ke yar addinin Kirista ce?"
Gatsina fuska tayi tana karkace kai ta ce mishi.
"Kwarai ai ranar Easter aka haife ni, Lokacin da ake yakinin sako ya iso daga Orishilima, daga ruhi me tsarki"
Riko hannun Abdullahi yayi suka ci-gaba da tafiya, amadadin ta nufi masarautar a'a sai ta shiga bin su. Abid yana janta da hira.
"Amma me yasa baku bude fuskarku?"
"Saboda idan muka buɗe zamu razana ku. Kin san mu samudawa ne"
Fisge sandar Abdullahi tayi ta juya da gudu tana faɗin.
"Na rama abin da ya min, katoton wofi da bai iya kome"
Ta tafi da sandar, ran Abid ya ɓaci sosai.
Har zai bi bayanta, Abdullahi ya rike shi.
Ya rike hannun shi ya ce mishi.
"Yara ne ko?"
"A'a wata Yarinya ce fa wai ta rama abin da ka mata Dazun?"
Gyada kai yayi suka dawo gida, nan Abid yake ta masifa, har su Ya Musa suka same shi yana fada.
Murmushi Ya Musa yayi sannan ya ce mishi.
"Wai ta rama abin da ya mata ko?"
"Eh wallahi"
"Zata dawo da shi."
--
"Har yanzu bamu sami yarinyar ba, sai ma wata shaidaniya da ya samu yaki rabuwa da ita."
"Ih rashin wannan yarinyar zai janyo mana asara ku tabbatar an nimota, domin jinin Nahara yana tare da ita, zai kwana arba'in da ita, zaa kasheta ayi mishi wanka da jininta, shine zai bashi karfin gaske"
"Da wacce alama zamu gane ta?"
D'ago kai yayi yana faɗin.
"Babu wata alama da ya nuna domin nahira ya danne alamar"
---
Tunda suka kwanta take ta juyi, jikin ta kamar wacce ake zanewa haka take ji.
Kwalla ne ya zubo mata, Mikewa tayi ta nufi hanyar waje.
Babu wanda ya sani, ta nufi waje kamar wacce ake bude mata kofa haka tayi ta tafiya har zuwa inda ta yarda sandar. Dauka tayi tana juyawa ta hango mutum a bayan ta. A tsorace ta fadi tana me sake sandar.
Bacewa mutumin yayi ta dauki sandar ta rantama a guje, bata yarda ta nutsu ba, ta kwanta jikinta sai rawa yake. Dakyar tayi barci.
Washi gari da sassafe ta dauki sandar ta bar masarautar.
Kasuwa ta shiga tana kallon mutane.
"Sannu Baba shin ina niman wasu mutane ne zaka gansu kamar samudawa"
"Ayya bamu san su ba."
Haka tayi ta yawo a kasuwa, kafin ta hadu da Ya Haruna, dan ya lura ta gaji tun safe har rana tayi zafi.
"Kina niman yan autan samudawa ko?"
Idanunta ne ya cika da kwalla.
"Ih, ga sandar shi."
"Muje ki bashi da hannun ki" haka suka wuce har masaukin shi.
Tana zuwa ta ajiye sandar zata juya Abid ya ce mata.
"Waye kike tsammanin zai bashi." Murguda baki tayi tana faɗin.
"Tow kar ka bashi" zata juya taji kamar an rike kafarta kasa motsawa tayi, tashi Abid yayi ya bar dakin.
"Ayya haka zaka tafi ka bar mu" tana son fita.
Juyawa tayi taga ya fita can bata lura da Ya Musa ba, shima ya riko hannun shi ya sake ta fita.
"Kai ma fita zaka yi?"
Bai kula ta ba, durkusawa tayi ta dauki sandar ta d'ago zata mika mishi, idanun shi ya hango mata shi a kanta kamar yadda taga aljanin jiya, yin baya tayi Jikinta yana rawa.
Mika mishi sandar tayi ta shiga ja da baya. D'ago sandar yayi zai maka mata. Ta fasa wani irin kara, tana kare fuskarta.
Dafa kafadar shi aka yi, sannan abokin shi ya rike sandar.
Jin sandar bai sauka akan ta ba, yasa ta fita da mugun gudu.
Sai da ta ga ta tsira, sannan ta ce .
"Lallai wannan mutumin yana da hatsari idan na sake muka kara haduwa kashina ya bushe"
Iya tsorata ta tsorata, amma baki daya bata da wata kuzari.
Tana shiga bangaren su,.ta hadu da Uwar Bayi.
"Ina kika je?"
"Na'am!" Ta fara zare Idanu.
"Kin fara bin maza ne?" Ta tambaye ta kamar ba ita tayi tambayar ba.
"Iyye! Kai ina abin bauta ya min tsari"
Ta fada tana tura baki.
"Tow ina kika je?"
"Kawai na gaji ne na tafi bakin ruwa" ta fada a shagwab'e.
"Allah ya shirya ki"
"Tow"
Ta wuce tana murmushi ganin akushin abinci a rufe da sauri ta zauna ta fara ci.
Hannu baka hannu ƙwarya, hannu ƙwarya.
Tana gamawa tayi gyatsa ta mike zuwa wurin Uwar bayi, tana kallon yadda take kadi.
★‡★
"Samu yace min babu wata alama da zaa gane ta, ban san yadda zamu yi ba."
"Tow a shiga dauko su ana niman ta da karfin tsiya."
"Tow!"
-----
Tun daga wannan ranar aka shiga daukar yan matan ana kaiwa Arshan, amma babu wani sakamako me kyau, tunda aka fara haka kullum Easter sai ta gudu a masarautar.
Sai da aka lalata yan mata sama da saba'in a cikin ƙabilar Nahara, karshe da fitina tayi fitina. Da kan shi ya hana a kawo mishi watan domin bayan shi ciwo yaƙe, dakyar yake motsawa. Haka ya gayawa Namir ya fadawa Galadima shine da namijin Galadima.
A take aka fara hada mishi maganin karfin maza a ka tura mishi.
Sai da ya sha yana wanka da shi kafin yaji wani irin karfi ya zo mishi.
Kasancewar lokacin damina ya kutso kai haka idan aka kwashi yan matan za a dawo da wasu sun mutu wasu a watsar da su uwar bayi tayi ta jinyar su.
Ana haka wani dare aka zo suka hada da Easter.
*Kuyi hakuri ina busy ne amma Insha Allah zan kara muku na dare ko rabin shafi ne*
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
Kamar yadda ake kad'a shanu haka suka kad'a kan su. Gashi an fara ruwan sama. Haka suka isa bangaren, ana shiga da su ana fito da wasu yan matan.
Tsoron haka ya bayyana a fuskar ta karara. Kafin a fitar da Wadancan ta juya cikin su ta fita da gudu.
"Ku kama ta"
Amma ina ta ficce, shirayi yana kusa da kofar fada don haka kamar wacce ake ingizata waje, ta fita kafin a rufe kofar fada. Tuni ta fita dakaru kusan bakwai suka fita niman ta, ga Uban ruwan da ake da bakin kwarya wanda ya haifar da ambaliya a cikin gari. Za a iya cewa duk abin da ake a Deehar ba a taba wanda ya haifar da masifa irin keta alfarmar Yan matan nan ba.
Itama garin gudun ceton rayuwar ta.
Bata ganin gabanta, hawaye ne ke fita a idanunta, tare da cewa.
"Ubangiji gani gare ka, waye me ceto? Juyawa tayi daidai walkiya ya haska bayan ta, ta hango su suna biyo ta a guje, karar aradu tayi a firgice ta kuma juyawa kamar wacce aka hada da bango ta koma da baya ta zube keyarta ya bugu da wani abu, ba zata iya cewa ga abin da ya faru ba. Domin tajyo isowar su, wurin tare da sake wani irin aradu me mugun amo da sauti me karfin tsiya.
Kafin idanunta ya rufe ta kuma hango wasu mutane biyu a dab da ita. Daga nan ba zata kuma ce ga abin da ya faru ba.
Idanunta ya rufe.
Washi gari.
Sake lumewa cikin bargon tayi,.tana jin wani irin dumi me dadin tsiya, kamar mage haka ta sake shigewa. Gyaran murya taji, haske a yana gauraye dakin.
Bude idanunta tayi tana kallon Ya Musa sa yake gyara labulen, tashi tayi zaune kanta na sarawa. Ta koma ta kwanta.
"Wash Yesu Almasihu! Na gode da ka tsiratar da ni tun Wadancan aladun basu kama ni ba."
Fita ya Musa yayi ya barta da matan.
"Sannu kin tashi?" Matar ta ce mata,
"Ih"
Tashi tayi taga an sauya mata kayan jikinta, ta kalli matar cikin tsoro.
"Waye ya sauya min kayana?"
"Ni ce "
Matar ta faɗa, tana shirya dakin.
"Gaskiya na gode" dafe goshin ta tayi tana tambayar matar.
"Me ya faru?"
"Jiya su yallabai suka shigo dake, sun tsince ki a cikin ruwan da ake dake sun fita taimakawa mutanen gari."
"Tow" ta fada tana shafa keyarta, waje ta fito ta same su zaune suna karyawa, ga al'ummar garin Deehar da suka kawo musu abinci daga gida gida.
Juyawa Abid yayi ya kalle ta.
"Kyautah!" Ta kalle shi.
"Tawo nan" ta taka a hankali, tana rike rigar jikin ta, domin yayi mata yawa.
Zama tayi,.ya kalli Matar nan ya ce mata.
"Dauko mata mayafinta "
"Tow" ta juya a hankali, tana koma dakin,.sannan ta dauko mata.
Mika mata tayi, ita kuma ta amsa, kallon Abdullahi tayi tana mamakin shi.
Yadda yake cin abincin kamar ba zai ci ba.
A hankali aka fara watsewa a wurin, har ya rage daga ita sai shi.
Daukar yaji tayi ta zuba mishi akan abincin, ya dauka ya ci bai sani ba.
Haka bai mata ba, ta kuma zuba mishi gishiri da yake cikin yar tasar azurfa.
Salon mugunta iri iri take mishi, bai sani ba. Shi dai abin da ya wani sauyawan abincin, a ran shi ya raya shaidaniyar yarinyar nan ce, girgiza kai yayi ya mike abin shi bai kulata ba, ya bar wurin.
Sai da taga ya tashi abin ka da kwadayayya kawai ta fara kokarin cin abincin, abokin shi na Yaranta yayi ta zuba mata yaji kamar yadda ta mishi.
Sai da tayi nisa a cin abincin sannan ta fara cin me yaji. Kwalla take tana dakyar ta hadiye na bakinta, gashi ta hana shi ya bar mata itama.kuma bata san ya aka yi ba yaji a nata.
Madara ta sha ta mike tana kallon rigar jikinta, a hankali ta cire Mayafin kanta, ta yaga bakin Mayafin ta daure a saman cikinta bayan ta gyara zaman rigar jikinta, sai rigar ya zauna dai-dai. Sannan ta daura Mayafin ta fito a binta.
Tana fitowa waje, ta gan shi a zaune su Ya Musa suna raba kayan abinci. Ga talakawa.
Hango dakarun Deehar tayi da sauri ta koma bayan shi, tare da rike rigar shi.
"Me kuke yi anan? Baku san abin da ya faru bane an kashe dakarun Deehar har bakwai" sake k'amk'ame rigar shi tai.
"Ba kome ake ba, wadannan fataken ne suka sayi kayan abinci ake rabawa mutanen da ruwa ya musu barna"
"Hmm! Ayi a tashi"
Har zasu bar wurin dayan su ya ce.
"Muna nimam wata yarinya idan kun ganta a mika ta ga fada" rike rigar shi tayi da karfi, yana jin jikar ruwa a bayan shi.
Ajiyar zuciya ya sauke, d'ago kai tayi tana kallon jama'ar wurin.
Sake shi tayi ta juya zata nufi hanyar da dakarun suka bi, Abid ya ce mata.
"Kin san halin da masarautar yake ciki kuwa?"
A matukar sanyayye ta juya tana kallon shi.
"Koma me dole zan tafi" ta juya ta kama tafiya, zai kuma magana Ya Haruna ya rike hannun shi.
"Ta yarda da kanta ne, shi yasa zata tunkari masifar da take gabanta, idan da zata tsaya a gefen mu tabbas tafiyar zata bada abin da ake bukata." Ya fada da fulatanci kasancewar zaman su a Numan yasa sun koya sosai kuma sun iya.
--
Haka ta isa kofar masarautar ana ganin ta aka rufe ta, har fada aka kaita tare da gurfanar da ita a gaban mutanen fadar.
"Waye ya kashe dakarun da suka je kamo ki?"
"Ban sani ba" ta faɗa a hankali,
"Akwai mutanen da kika sani makiyan masarautar nan ne?"
"Ni fa ban san kome ba"
Duk abin da ake tunanin za aji a bakin ta,bata sani ba. Don haka suka sa aka fara zane ta.
Amma abu daya take fada bata sani ba.
---
"An samu Yarinyar nan fa, amma kuma bata san abin da ya faru ba, sai zane ta ake"
Mikewa yayi ya dauki alkyabar shi, ya fita daga shirayi ya nufi fada.
Yadda ake zane ta, zaka dauka ba zata rayu ba, tana kwance. Yana shiga ya lullube ta da alkyabar shi. Dole suka tsayar da dukan.
Tare da zubewa suna kwasar gaisuwa.
"Me tayi?"
"Akwai yiwuwar kawo hari masarautar nan ne,kuma wannan yarinyar ta san kome"
"Ta fadi abinda ta sanin?"
"A'a"
Daukar ta yayi har zai fita ya ce musu.
"Kar wani ya kuma tuhumar ta, bata san kome ba."
"Idan ba a bincike ta ba, yarinyar nan zata kawo masifa har cikin masarautar nan"
"Masifar da aka kawo shekaru ashirin da takwas ma yai ba a gama da ita ba, balle a kuma shigo da wani kar a kuma dukanta " ya sa kai ya fice da ita a kafadar shi.
Shirayi ya nufa da ita, yana zuwa ya kwantar da ita rub da ciki,
"Kai ka kira min Uwar Bayi "
"Tow ranka shi dade "
Ya fita Namir da yaji labarin abin da ya faru ya garzayo kusan a tare da da Uwar bayi.
"Kana Hauka ne? Taya zaka hana su binciken da ya dace?"
"Me yasa aka kawo min ita a jiya? Ita ba matar da zan sadaukar da ita bace, tun gani na da ita na ajiyewa Y'ay'ana. Don haka kowa ya yi kokarin dakatar dani sai naga karshen digon numfashinsa, Uwar Bayi a kula da ita"
Yana gama fadar haka, ya fita zuwa zauren shi yana jin kamar ya cire mata ciwon jikinta.
Yana zaune a wurin har uwar bayi ta gama gyara mata ciwon, sannan ta fito lokacin Fulani Babba ta shigo.
"Meye nufin ka Arshan? Baiwa ce kaskantaciya ka kare? Bayan kasan hukuncin cin amanar masarautar nan kisa ce "
"Fulani na yanke kuma na zarta duk wanda ya kuskura ya nuna mata yatsa sai na kashe shi, idan kuma aka mata kallon banza sai na nakasa mutum, dan haka zan iya kome domin na kare ta."
"Ka kore ta"
"Babu inda zata da ya wuce nan, kuma wallahi sai na sare duk wanda ya kalleta " ya furta a fusace yana kallon Fulani Babba.
"Ni kake gayawa magana?"
"Ba iya ke ba duk wanda ya shiga gaba na nake da shi."
Mikewa tayi ta fita ranta a jagule.
★‡★
Kallon gawar badakaren yayi ya wasu tsatsuba, kafin ya lumshe idanun shi.
Bude idanun shi yayi da sauri, saka hannun shi yai ya tab'a gefen wuyar badakaren, da sauri ya cire hannun.
"Kaico lokaci ya kure, tir da wannan yanayin mara dadi." Ya mike yana bin gawar badakaren da wasu abubuwan kafin can gawar ta shiga girgiza, kamar wacce aka hura mata wuta.
"Kaddarar da ta raba ta kuma haɗawa, ku bibiye masarautar Deehar akwai matsala"
Fita suka yi da sauri.
***
Kusan kwanaki uku kenan da ambaliyar ruwan sama, amma babu wani agaji daga masarautar deehar, sai daga Fataken nan dai guda hudu, abin da ya kara musu kaunar su kenan, musamman dan makahon cikin su. Sai dai abin da suka fahimta shi yake kamar bada duk wani abin da za ayi.
Don haka basu fasa bashi girma ba.
Haka kwanaki suka cigaba da tafiya har kusan wata guda, sai da aka fada matsanancin rashin abinci, yasa Ya Musa da Ya Haruna. Tafiya niman abinci domin wani irin fari ake, tafiyar sati Uku, suka yi sai gasu da kayan Abincin aka yi ta rabawa talakawan Deehar, wanda ya janyo suka daina biyan haraji. Duk wata ake amsa sai gashi kusan wata biyu ba a karb'a, wannan yasa mahukuntan fadar suka harzuka aka turo wakilai. Amma jama'a suka musu bore.
-
"Yarinyar nan bata kuma fitowa ba, da alamu sun kashe ta ne." Inji Abid yana me basu amsa.
"Anya ba zasu kashe ta ba, sai dai su zargi ko tana da masaniya akan abin da yake faruwa ba."
"Kamar Ya?"
"Kamar yadda tunaninsu zai basu. Dole muyi amfani da talakawansu, domin su juya musu baya, haka zai saka mu mika Abdullahi ga masarautar "
"Ya Musa Abdullahi baya ji baya gani me zai iya?" Ya Haruna ya tambaya.
"Zai iya mana, ku gwada bashi damar haka, ba Idanu ke gani ba zuciyar ce take gani. Dan haka a tunzura talakawa kuga yadda tafiyar zai bada armashi "
Gyada kai Ya Haruna yayi.
***
Duk yadda al'amarin yake kara daure mata kai, ya wuce tunaninta.
"Wai an kawo ni nan an daure ni ba a bar ni na fita bane?" Banza yayi da ita yana sosa kunnen shi, kallon marin kafarta tayi, tana faɗin.
"Zalinci a ko ina rayuwar ma an mai da kai kamar dabba, ban yafe ba."
"Kar Allah yasa ki yafe "
Ya tashi ya shige daya dakin da Abigail take zaune zaman jiran shi.
"Ban gane me Kyautah take a wurin ka ba?"
"Kina da matsala da haka ne?"
"Ko daya kawai zuciyata ce bata yarda da ita ba."
"Gara ta saba da yarda da ita domin ita din ta zo nan kenan, ita ba shara bace kamar ku, ku kuma kamar shara ne watsar da kazamta na nake akan ku duk lokacin da ya min "
Shiru tayi ta kasa magana, tana kallon kasa.
Janyota yayi jikin shi yana lasar wuyarta zuwa kirjinta.
***
Duk yadda aka yi ta niman, matsalar da zai tunkari masarautar ba a samu ba, sai dai wani banzan boren da talakawa suka fara na sun gaji da mulkin zalinci, yasa ran Galadima ya b'aci dan haka ya fita da kan shi. Yana fitowa ya samu al'umma dayawan gaske, wanda Abdullahi yaƙe musu jagorancin bore.
"Ku shafe duk wanda ya kusanci kofar masarautar Deehar "
Iskace me karfi ta taso, ta yafe gefen fuskar Abdullahi, arba yayi da fuskar da ya kusan....
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
.... Wani kallo ta mishi, tare da jin ina zata samu damar make shi. Amma tasan ko a duniyar mahaukata ba zata iya aikata haka ba, Yarima ne fa? Dan haka ta cewa Abid.
"Kuma zamu fita da shi da dadare kasan