Showing 51001 words to 54000 words out of 105295 words
Chapter 18 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
haka ba tow babu abin da zamu iya yi."
"Ana cin wata, wata tana kunce zani. Tow bari muga abin da zamu iya" ya fada yana barin bukkar, domin wannan shi ne tashin hankali wanda ba a saka mishi rana.
Bayan tafiyar shi da sa'a guda, wani badakare ya shigo tare da zuba jakar tsaba ya ce.
"Mai nama shi ke da niman wuta. A daura daga inda aka tsaya."
Dariya Samu yayi sannan ya ce mishi.
"Tilas a gyarawa Amarya ɗakinta, ko a san inda dare yayi"
Juyawa badakaren yayi yana faɗin.
"Ka dai san kan aikin ka, ganin mabaraci ma biya ne, dan haka kar ka manta da aiki me kyau, karramawa ce "
;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;
Mulikah Hamid Garkuwa
Shirin da suke ba wani a zo a gani ba ne, amma kuma tana jin daukin da son ganin Yarima Abdullahi, duk tana son gayawa Radiah amma tana tsoron, kar ta ce ta munafunce ta.
Shirin da suka yi ita da kunyanganta Laraba.
"Ya shugabata,kin yi kyau kamar dare dan goma sha huɗu, kin zama tauraruwa a cikin taurari." Murmushi tayi sannan ta ce mata.
"Na baki sarkan azurfan can" ta nuna mata tana murmushin farin ciki.
Mulikah tana masifar kaunar ace tayi kyau, duk da babu karya tayi kyau kuma tana da kyau, sai dai bata kaunar a yabi wata a gabanta idan ba Radiah ba. Saka alkyaba tayi a kan tudun gashin kanta, sannan suka fito tana share goshinta. Zauren mahaifinta ta nufa domin shi yasa ta, ta shirya ta je ganin Abdullahi. Yana sa buri da wata manufa kafin Fulani ta bada umarnin haka yake ga Gara ya idda na shi nufin domin ba zai jira umarnin Fulani ba, ai kowa yana da na shi damar dan haka ba zai kuma jiran haka daga gare ta ba.
Murmushi ya sake mata yana faɗin.
"Mulikatuh kin yi kyau, Uwata dan haka idan kin ji ga wancan kyautar ki kai mishi, daga gare ki "
"Na gode sosai Abbana"
Har ta mike tare da ɗaukar kyautar ya ce mata.
"Kar ki bi wurin Radiah "
Gyada kai tayi tana cewa.
"Tow"
Haka ta fita, sam sai take jin babu dad'i sun saba abin su, su biyu
Ko fita ne su biyu suke fita, sam sai take jin babu dad'i sun saba abin su, amma yau Abbanta ya bata Umarnin tayi kome ita ɗayan ta.....
*Ku danyi hakuri ina busy ne wallahi*
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
Tunda ta shigo zauren suke kallon kallo da Kyautah, matsa mata tayi tana me wucewa dakinta. Shi da Abid suna zaune,
"Sannun ku" ta fada tana murmushi, kallonta Abid yayi yana mai da mata murmushin.
"Sannun ki." Ya riko hannun Abdullahi yana mishi bayanin da cewa ga Mulikah Hamid yar garkuwa, tazo wurin shi. Wani irin tsuke fuskar shi yayi yana faɗin.
"Ta tafi ina da abin yi"
"A'a ba za ayi haka ba, munafiki amma da nace zan shiga wurin Kyautah hanani kayi dan iska"
Kyaf-kyafta idanu yayi kamar me gani, sannan ya gyara zama.
"Idan da na barka haka zaka shiga kanta? Ita fa a karkashin kulawata take kai kuma dake dan iska ne shi ne zaka shiga?"
"Me haka yake nufi? Akwai wani abu ne a tsakanin ku da ban sani ba" Abid ya tambayan shi. Ganin bashi da niyyar bashi amsa, yasa shi dole yayi shiru har Mulikah ta gama tsarguwa, domin yasan dai baya ji baya gani, sai dai a duk lokacin da a kalli fuskar shi tsoro yake bata, don haka jimawa kad'an ta ce zata tafi domin ta gaji da zaman shirun da take yi, ba dadi ajiye mishi kyautar tayi, Abid ya mata rakiya.
"Baya magana ko?" Ta tambayi Abid,
"Ih, baya magana sai dai an yi mishi bayanin da hannu"
"Ayya amma kana ganin bai da wata matsala bayan wannan." Murmushi yayi mata, sannan ya ce mata.
"Bai da wata matsala" hango Aliyah yayi tana zuwa ita, fuskar ta a sake tana isowa ta ce mishi.
"Baffa ina wuni?" Cikin kunya,
"Lafiya lau, Aaliyah ya su Babanki?" Ya tambaye ta,
"Suna lafiya, Baffa Abdullahi suna cikin gidan?"
"Ih, yana ciki"
Ya bata amsa, ganin Mulikah bata fuskar magana ba yasa,ta wuce abin ta.
"Na gode " ta fada tana me wucewa, bin bayanta yayi da kallo, yarinyar tana da mugun nutsuwa da hankali,
"Ta maka ne?" Mulikah ta tambaye shi.
"Tana da sanin ya kamata ne." Shiru tayi tana jin idanunta yana cika da kwalla, amma bata yarda tayi yadda zai gane ba, domin bata son ya gane bata ji dadin yabon Aaliyah da yayi ba. Yana rakata inda ya da ce ya juya abin shi.
Aaliyah kan suna haduwa da Kyautah, suka baje a zauren suka shiga hira har da shewa don ma Abdullahi ya bar zauren, hayaniyar su ta ishe shi, koda ya shiga dakin shi ganin kome yayi a gyare kamar ba a dakin ta yi kwanaki tana jin ya ba.
_Yarinyar nan ta tsallake rijiya da baya, sannan Allah ya kare ta yadda bamu zata ba, sai dai gubar ya ci jikinta yadda bamu gane haka ba, iya kokarina a matsayin me magani nayi amma ban gane kome ba, sai dai akwai tsarin da ya kare jikinta, ku saka idanu akan ta domin zai ta damunta lokaci zuwa lokaci wanda zai iya kashe ta_
Maganar da me maganin Masarautar ya gayawa musu, idanun shi cike da damuwa, yayi shiru tow itama ta zama abin harin su kenan.
Shigowa Abid yayi dakin ya zauna,
"Makahon karya" bai kula shi ba, dole ya zama makaho domin gano su waye akan shi.
Shiru yayi bai ce kome ba, ya kuma ce mishi.
"Dan kurma ba magana ne?" Lumshe idanun shi yayi,.sannan mike yana cire alkyabar shi, yana gama cirewa ya haɗa har da rigar shi,Mikewa Abid yayi yana faɗin.
"Banza dai bai yi ba, gashi zaka yi tsirara a gabana, irin abin da kayi a gaban Kyautah kenan"
Nan ma bai ce mishi ci kanka ba. Haka ya fita, damuwar da take dankare a kan shi yafi karfin shi, dan haka ya gama ya rufe tagar dakin ya rage hasken dakin sannan ya shiga bandakin, bai fito ba sai can. Wani lokacin yana da wata munafukar al'ada shine fitowa babu sutura a jikin shi, musamman idan bai shiga da mayani ba.
Ai kuwa yau ma haka ya fito, ruwa na gudu a jikin shi. Ita kuma niman dankunnen ya shigo da ita dakin niman dankunnen, sai bincike yake bai kawo ita zata shigo dakin ba, dan haka ya fito gaba gadi, abin shi Mikewa tayi ya bude tagar zata juya idanun ta ya sauka akan shi yana tsaye ruwan da yake sumar shi yana sauka a jikin shi da mugun gudu,
"Humm!" Ta ce, ta ja da baya kaɗan, yadda take kyaf-kyafta idanu tana kallon kirjin shi me cike da gar gasa. Yasa ta rudewa baki daya, shakuwa ta fara kamar wacce ta damki dankalin hausa.
"Kwaf-kwaf-kwaf" kuma ta kasa motsi, domin bata tab'a ganin da namiji tunbur ba sai yau, duk maguzancin su, suna da kamun kai ba bala'in da tsare kimar su.
A hankali ta fara ja da baya daga yadda ta tsaya, kuma dan tsiya tana kallon shi, idanunta na kaiwa kugun shi zuwa maran shi, da tafasa wani irin ihu, ta juya da mugun gudu, sai dai kash faduwa tayi ta kuma juyawa suka yi ido biyu da da shi, har lokacin bai motsa ba, da rarrafe ta fice a dakin jikinta yana mugun rawa, fadawa jikin Aaliyah tayi ta fashe da kuka me ban tausayi.
"Wallahi ban ga kome ba, na rantse da abin bauta ban ga kome ba." Ta fada tana rike wuyarta.
Tashi Abid yayi ya shiga dakin, shima hango shi yayi zaune a saman gadon shi, babu kaya a jikin shi.
"Amma dai ka cika babban dan iska. Meye haka don Allah? Wallahi duk ta firgice kamar taga dodo." Dauko mishi kaya yayi yana me ajiye mishi.
D'ago manyan idanun shi yayi ya kura mishi sanan ya dauke kai kamar bashi ba, haka ya shirya suka fito a tare, tana ganin shi ta koma bayan Aaliyah.
"Baffa zan tafi"
"Ki gaida Baffanki" ta juya ta fita, itama Kyautah shigewa daki tayi suka bar gidan.
Duk da tasan baya gani, amma haka bai hanata takatsantsan da shi ba, gashi dai iya kugun shi da ramin Cibiyar shi ta gani wallahi abin yaki barin kanta, ita bata ga kome ba iya wannan wurin ta gani, amma ji take kamar ta bindige kanta.
Tana zaune wuraren la'asar, tana zaune ita ɗaya. So take tafi amma tana tsoron kar ta fita ya nime ta. Can kuma ta ce.
"Dan bai da kunya, sai ya nime ni bayan tulin abin kunyar da yayi"
Ta tashi ta fita abinta, nufar wurin Mama Uwa.
Lokacin da ta isa, babu kowa a zauren girkin. Suna ta hira murmushi tayi ta gaishe da sabuwa, sannan ta gaida Mama Uwa.
Kallonta Mama Uwa tayi tana cewa.
"Kyautah ko kina laulayi ne? Irin wannan kyan da kika yi kamar me shigar ciki "
"A'a, Mama bani da lafiya ne amma naji sauki" Mama Uwa ta samu labarin rashin lafiyar ta, amma dake tana son mai da maganar wani fuska na daban ta ce mata.
"Ban ga alama ba, ga shi nan kirjin ki ya kuma cika. Har zuwa kataranki cinyoyin ki sun kara cika,gaya min gaskiya Yarima Abdullahi yana saka miki wani abu a gabanki ne "
"A'a ban ga kome ba, na rantse da Abin bautar mu nahara ban ga kome ba, asalima sau biyu na tab'a ganin shi babu kaya" kallon juna suka Mama Uwa da Sabuwa,
"Kwanta nagani idan har kin yi zamu gani, idan baki yi ba zamu gane fa." Da sauri ya d'ago fatarinta, sannan suka janye dan kamfen gabanta, cike da takaici take kallon gaban Kyautah.
"Hmm!" Sabuwa ta ce.
"Bari na kara tabbatar da haka, sai na gwada ki" ta mike ta dauki wani sanda. Zata tura mata gabanta.
"Yarima Abdullahi zai shigo dakin girki " yarda sandar tayi ta saka Kyautah Mikewa.
Jikinta na rawa, shigowa suka yi shi da Abid, sunkuyar da kai Mama Uwa da Sabuwa,
"Wuce muje" Abid ya daka mata tsawa, hawaye na zuba a idanunta
" Ku kiyayye" Abid ya gaya musu, bayan fitar su ne, suka fara jajjanta al'amarin da cewa ai Kyautah ciki ne da ita, kafin kace me labarin ya bazu har wurin Fulani Babba.
Abin ya bata mamaki dan haka da kanta, ta tura aka kira Uwar Bayi.
Zama tayi cikin girmamawa,
"Naji an ce baiwar da take kula da Abdullahi cike ne da ita? Kuma kin san al'adar masarautar nan"
"Wallahi Fulani Babba ban san kome a kai ba, nasan dai Yarinyar tayi rashin lafiya, amma Insha Allah zamu bincika"
"Tow yana da kyau. Sanan a dawo da ita bangaren nan, domin Yarima Arshan zata aura bana son kananun magana su yawaita akan ta" da wani irin sauri Uwar Bayi take kallon Fulani Babba, kafin tayi kasa da kanta, sannan ta ce mata.
"An gama" sannan ta mike tana faɗin.
"Ki huta lafiya" idan hankalin Uwar Bayi yayi dubu sai da ya tashi, domin wallahi bata ganin dacewar Arshan da Kyautah, haka ta nufi gidan Abdullahi ta samu Abid sai fada yake mata.
"Waziri da kayi hakuri, ta haɗa kayanta ta koma wurin Fulani Babba, domin ita ce aka zab'awa Yarima Arshan"
"Kamar Ya?" Ya tambaye ta, rike sandar shi yayi.
"Ih, tow dai Fulani Babba ta ce wai ana zargin Kyautah da ciki" taune lebben shi yayi, idanun shi Jajjur.
"Taso muje"
Tashi tayi ya nufi dakin ta, ta dauki kayanta ta fito hawaye na zuba mata. Haka suka fita, har bangaren bayi aka kai ta, aka duba lafiyarta sannan suka wuce shashin Fulani Babba.
Abin mamaki, ta murna da Kyakyawar tarba aka amshe, sannan aka nuna mata dakin da zata zauna.
Duk sai ta zama bakuwa a cikin bangaren, domin bata saba ba. Haka suka yi ta zama har dare, da farko ita da wasu bayi biyu suka kwanta, barci me nayi yayi gaba da ita. Can sai taji kamar ana shafa kafad'ar ta zuwa cikinta, bude idanu tayi tana kallon Yarima Arshan.
"Gimbiyata" zubur ta mike, tana kallon dakin kamar ya juya mata, ita a tunanin ta a bangaren Fulani take, wani abu ya dauko ya nufe ta, kafin ta dira ya watsa mata a fuskarta, komawa tayi ta kwanta. Tana jin shi yayi ta wurgi da ita tsakiyar gadon, dakyar take jan numfashin ta, bata taɓa ganin tashin hankali ba sai yau, tana ganin yadda ya kashe hasken fitilar dakin, sannan ya shiga wasu irin surutai, yana yi yana nufota tare da wani katon maciji a wuyar shi .
Daga nan bata kuma sanin kome ba, sai dai kafin kome ya dauke mata taji wani irin ƙara, tare da wasu kalamai.
"Idan na daura abu a matsayin nawa bana buƙatar abokin tarayya" daga nan kuma bata sanin me ya faru ba.
---
Buɗe ido tayi zata gyara ƙwanciyar ta, ta shaki kamshin turaren Abdullahi, lumshe idanun tayi, kafin ta kuma budewa dakin shi ne, hasken rana yana shigowa dakin, tashi tayi zaune tana kallon dakin, kanta ya juya yaushe tazo gidan? Yaushe ta fado gidan.
Abin da ta sani bayan dare yayi Fulani Babba tasa an shirya mata ruwan zafi tayi wanka, tasa aka bata wani rigar alfarmar da turare ta shafe jikinta, sannan ta kwanta. Lumshe idanunta tayi tuno abin da ya faru shigowar Arshan kamar mafarki, kayan dake jikinta ba nata bane na Abdullahi ne.
Dirowa tayi a gadon, tana zare idanu jan rigar tayi sama, ta fito zauren suna karyawa.
"Mafarki nake ne? Jiya na bar nan yau kuma na ganni a nan, anya banyi hauka ba?"
Ta fito tana zare idanu kamar mayya,
"Muje ki sauya kayan ki, ai gobara ce ta kama bangaren Yarima Arshan......
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
..... Koƙarin take taga fuskar shi, amma asalima yau rawani ya bankawa kan shi, sam yaki yarda su hada idanu balle a kai ga zancen sun ga juna, ai dama akwai sakon da a fuska kana iya karantar shi, tow yau bata ga kome ba, sai ma b'acin rai da ta hango a cikin idanun shi. Kasa magana tayi tana jin babu dad'i. Kallon Uwar Bayi tai kamar zata yi kuka ta ce mata.
"Wani abu ya faru ne?" Ta tambaye ta, idanunta waje, girgiza mata kai tayi sannan ta ce mata,
"Yarima Abdullahi ya ce kar a kuma barin ki, fita idan ba tare da shi ba."
"Kamar Ya? Ni haka kawai za a mai da ni kamar wata takalmin kowa, sai shure ni kowa yake yana yadda ya so da ni, kawai ban ba zai yiwu ba"
"Zai yiwu mana tunda gashi nan kina bangaren shi," Uwar Bayi ta fada.
"Wai ni fa ba zan yarda ba"
Shegen gardaman tsiya ne da ita yasa Uwar bayi ta buga mata tsawa, dole ta nutsu, ai kuwa yau akan Basamude zata sauke. Jidalinta don haka bayan Uwar bayi ta fita ne, ta fito babu kowa, yana zaune kuma abin takaici babu riga a jikin shi, dan haka ta wuce abin ta, ganin bayan shi tayi a kone kamar abu ya zuba mishi me zafi.
"Madalla, haka kawai akan ka sai ukuba ake daurawa mutum" ta harare shi, ta wuce abin ta. Lumshe idanu yayi yana jin rigimar da ba zai kare ba. Shigowar Abid da Aaliyah da kayan abinci, suka fita lekewa tayi ta ga abinci ga shi yana tiriri, takowa tayi ta zauna ta dauke akushin dage-dagen, kawai ta fara cinye namar, bata bar kome ba sai tarin kashi ta tura mishi tana gyatsa, sannan ta janyo gishiri ta zuba a cikin abincin tana hararan shi. Kafin ta bar wurin tana yi tana b'ata rai.
Kwashe gishirin yayi ya ci Abincin ba zata tab'a sauyawa ba.
---
Kwance yake ana ta zuba mishi danyen madara, sakamakon wutar da ta kama shirayin shi, ta kone murus. Shima dakyar ya fita, sannan wani abin mamaki basu bi ta kan Kyautah ba tana raye ko tana mace oho. Daga waziri har Fulani Babba babu me nutsuwa.
"Ya jikin na shi?"
"Da sauki zamu ce, amma kuma an nime yarinyar an rasa bata tare da shi."
"Kamar Ya? Kana nufin wutar nan ta cinye babu ita a cikin Shirayi?"
"Ih, ranki shi dade." Taya haka zai faru bayan ita da kanta, ta bashi umarnin a ya tafi da ita, ace bata cikin dakin.
_Haduwar su da Abdullahi zai iya haifar da matsala, domin Nahira bata zalinci sai dai tayi taimako idan kuma aka gurbata jikin yarinyar da kazamta dole hasken nahara ya barta ya koma wani irin haka zai bamu damar daukar hasken domin mu daura a kan Arshan wannan macijiyar zata taimaka mishi matuka wurin kusantar Yarinyar ita ce zata janye hasken Nahara_
Ga koshi ga kwanan Yunwa wannan ai masifa ce, yanzu fisabilillahi dan damar da suke nima ne suka rasa, shi kan Arshan ba a ta batun shi, domin da alamu yasha duka a kafin wuta ta kona shi.
"Hmm! Fulani ya kamata a dauki mataki domin tunda Yarinyar nan Kyautah ta shigo mugun bala'i yake sauka a masarautar nan, sannan kun dage sai wata alaƙa ya shiga tsakanin su da Arshan ba fa