Showing 30001 words to 33000 words out of 105295 words
Chapter 11 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
kewaye shi da kara, kafin ya samu sauƙin da afuwan rayuwa. A haka yake noma na rani da damina, mutane ma tausayin Abdullahi yasa ake kaunar su, musamman da suka gane cewa shi din bawa ne ga Abdullahi, yasa Jauro Ummaru ya bawa Ya Musa auren yar shi Zainabu wacce suke kiran da Jabu. Da farko taso kin ya Musa sai dai abin a ƙabilar Noye ce, mazan su jarumai ne a cikin turakar su.
Haka yasa ta damke shi da hannu bibbiyu.
Abdullahi yana da shekaru ashirin cif a duniya Allah ya basu cikin Raudah, koda aka haife ta. Sun daura soyayyar ta a saman na kowa, haka shima Abdullahi.
A lokacin Allah ya haɗa Ya Musa da Ya Haruna, a wani cin kasuwa da yazo yi cikin kasuwar Numan.
Ai kuwa ba karamin al'amari bane, bayan gaishe gaishe da suka yi, nan yake tambyar shi.
"A ina kasamo d'a?"
"Abid ne dan ga Wazirin Noye"
"Don Allah"
"Wallahi kuwa! Shine ɗan da muka baro gida amma Mahaifiyar shi ta koma, daga baya naji labarin an kashe su ita da mahaifin shi, amma naki gaya masa."
Shiru suka yi sannan Ya Musa ya ce mishi.
"Da ka gaya mishi, nima Abdullahi yana tare da ni. Amma shi yasan Mahaifiyar shi ta rasu"
"Ayya gashi dama burin Waziri ne had'a su abota kaga kenan ba zan kuma tafiye-tafiyen da nake da shi ba, zan bar shi a wurin ka nima sai na nemi wuri na zauna."
"Shi kenan" haka ajiye maganar, sannan suka cigaba da cin kasuwa ana tashi a kasuwa suka wuce Gida, anan Ya Musa ya gabatar da Ya Haruna da dangantaka tsakanin su da kuma Abid.
Riko hannun Abdullahi Abid yayi ya riƙe, sannan ya fara mishi magana.
*Abid baya ji fa, kuma baya gani, baya magana." Kurawa Abdullahi Idanu yayi sannan ya ce.
"Ya Musa kuma baka nima mishi magani ba? Shi fa sarki ne guda haka Abbana ya gaya min!"
Ya fada da harshen Noye.
"Ina kan nima mishi magani, har yau ba a dace ba ne!"
Kwalla ta cika mishi Idanu.
Haka suka cigaba da abotan su tsawon shekaru goma sha takwas, barci yake raba su.
Haka suka taso, anyi anyi Abid yayi aure ya ce shi bai san da zancen aure ba, sai Abdullahi yayi.
Duk da yan matan da suke masifar kaunar su, amma ya fahimci Abdullahi yana son Raudah, kuma ya kasa fada dan da farko suna tare da Raudah kamar me, su uku duk da ita bata fahimci waye Abdullahi ba, a tunaninta ai Mahaifinta tausayin Abdullahi yaƙe yasa shi rike shi dan nakasar da yake da ita.
Sai ta fahimci, yadda Mahaifinta da Ya Haruna suke bin Abdullahi yayi yawa, ita a duniya bata tab'a jin kaunar shi ba, sai dai abin da ta sani tana kallon shi a matsayin Yayanta, shi yasa da Abid ya gaya mata bukatar Abdullahi, ta rufe idanu ta zage su tass.
Tun daga lokacin Abid ya gaya mishi babu ruwan shi a zancen su, shi kuwa Abdullahi yana ganin ai Ya Musa ya mishi kome, dan haka ya tafi wurin Ya Haruna ya shiga maganar, ai kuwa ya Musa yana dawowa daga lambu ya gaya masa sakon Abdullahi.
Kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan murna, ai kuwa ys gayawa Uwar Raudah wacce suke kira Gwaggo.
"Yanzun kai Malam makaho, bebe, kurma, zamu bawa Yar mu? Gaskiya ba zan iya wannan haukar ba, yarinya tana da manema amma a dauke ta a bawa mara gani!"
Murmusa mata yayi sannan ya ce mata.
"Idan kuma Allah ya nufa ta sanadinta zai samu lafiya fa? Kawai ki musu addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi"
Ai kuwa ta yi shiru, dan haka tayi ta zuga yarta.
.....
A dawo labari.
Har yau Raudah tana nan akan bakarta, wannan ya haifar musu da rashin jituwa da Abid, domin yana ganin rashin sanin waye Abdullahi yasa take musu mishi haka da zata san cewa ko a bayin da zasu gyara turakar shi bata kama kafar su ba, zata shafawa kanta ruwan sanyi.
★†★
*DAHEER*
Tun da tayi wannan mafarkin sai ya zama,ko gyangyadi take mutanen Nahara suke yawo a idanunta.
Haka take aikinta wanda jin dadin haka yasa Fure cewa ta zauna a bangaren duk ranar Juma'a ta koma bangaren su.
Ranar wata talata, tana tsaye har Fulani Aliyah ta gama shiri, kanta a sunkuye.
"Yau zaki taka min har babban dakin taro,Fulani Babba ta shirya mana liyafan da take duk bayan wata uku!"
"Tow ranki shi dad'e" Kyautah ta fada tana me satar kallon Fulani Aliyah.
"Nayi kyau kuwa?"
"Ba laifi ai kamar daren goma sha huɗu."
"Kai kyautah, gasu can ki dauka shi zaki saka muje an jima."
"Godiya nake, haske maganin duhu."
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
*.....DASHEN ALLAH 🌳*
Mai_Dambu...
BABI NA SHA TAKWAS (18)
Karshen shafin kyauta
Ganin babu wasa a kalaman Uwar Bayi Kande yasa Mama uwa ta sunkuyar da kanta, tana ji tana gani aka janye Abigail. Aka fitar da su har da Easter,
"Aikin ku sarrafa abincin da za ana kaiwa cikin masarauta, sai kuma idan kun kware za a kai ku cikin gidan domin aikace-aikace, dan haka ku kula da kanku ban da gulma, ban da sata, ban da ha'inci idan aka same ka da ko daya ne hukuncin zai yi tsammari" gyada kai suka yi sannan ta juya ta kalli me kula da sashin ta ce mata. "Batula a kula da harkokin su, na yarda dake dan haka kulawar da zaki basu ba ni da haufi"
Sannan ta kalli waya mata mata, wacce take wani cika tana batsewa ta ce mata.
"Haule ki kula da kayan masarufi idan babu sai ki min magana, nasan aikin ki ne."
Washe baki tayi tana gyada kai, kallon wata mata tayi a gefen can ta ce mata.
"Karime, a kula da wanke-wanke da sauran su."
"Godiya nake"
Haka ta nufi dakin da a ka zuba Yaran, sannan ta shiga hannunta a goye.
"Ga banɗaki can, ku shiga kuyi wanka"
"Tow!" Aka basu sabulu da soson danga, suna fitowa ta shiga nuna musu yadda zasu shirya, idanunta ne ya tsaya akan Easther da sumar kanta, kallonta take sosai tana kara hango kyan halittarta.
"Zo nan" ta yafato ta, karasawa tayi tana me sunkuyar da kanta.
Tufke gashin tai, sannan ta saka wata karamar aska ta yanke jelar gashin, dariya yan matan suka saka, ta kalle su rai a b'ace, suka rufe bakin su.
"Kina inda baki isa ki nuna kyan halittar ki ba, dan haka idan gashin ki ya kuma taruwa, ki san yadda zaki yi da shi."
Hawaye ne ya zubo mata, tana me gyad'a kanta. Sannan tayi gaba bayan sun shirya aka wuce da su sassan gidan, bayan tace Easter ta jirata. Tunda ta saka jelar gashin kanta a gaba take kuka, wani irin kaunar gashinta yana kara kamata, dan sai yau ta fahimci ita din me suma ce, ga kewar Babanta. Sai can bayan sa'a guda Kande ta dawo, kaita tayi gaban madubin dakin.
"Inda zaki zauna bai zama dole ki fahimci haka ba, amma wuri ne da kowa yake son dan shi ya zama zakarar gwajin dafi!"
Sannan ta kame gashin ta kitse shi tsaf, kafin ta sakata a gaba suka tafi har zuwa sashin Yarima Shehu. Tunda take bata tab'a ganin wuri me kyau har haka ba, sai yau dan haka ta zama bakauyiyya. Zungure ta Uwar Bayi tai, sannan ta kalli Fulani Rabi'ah, cikin girmamawa ta ce mata.
"Ranki shi dade ga wacce zata na kula da harkokin Gimbiya Aliyah."
"Sunanta!"
"Kyautah"
Sai lokacin ta d'ago kai tana kallon Easter, kafin ta mai da tana cigaba da nazarin yarinyar, Fulani Rabi'ah. Irin mutanen ne da basu cika shiga abin da bai shafe su ba, amma kuma tana da wata dabi'a daya bata son taga abin da zai wuce Yarta Aliyah domin kyauwun yarta har yau bata yarda da kowa akan Yarta ba, amma yanzu ga wata zata ganta. "Shi kenan! Ki hada ta da furerah." Itama Baiwar sashin ce, ita take kula da Khamilah.
Nufar cikin gidan Uwar Bayi tayi da Easter, sai da suka yi tafiya har suka ficce daga wannan zauren, suka sake Mikewa wata yar kofa da ta sadasu da wani karamin zaure. Mata biyu ne a tsaye a wannan ɓangaren, suka gaida Uwar Bayi, sannan suka bude mata kofar da zata shiga, a hankali suka shiga zauren me girman gaske.
"Barka dai Uwar Bayi."
"Yawwan Fure ga yar uwa nan, na kawo miki wai zata fara aiki a bangaren Gimbiya Aliyah"
Kallon Easter tayi da kanta yaƙe sunkuye.
"Hmm! Amma dai kin san cewa"
"Gata nan, ita ɗaya ce bata kai yadda ake bukata ba, idan har na kawo wata bayan ita ba zata yi yadda ake so ba. Zaku ji dadin zama da ita"
"Kyautah ga Fure tana sama da ke, dan haka babu reni. Ki kula da abin da aka saka ki"
"Tow" ta faɗa hannun ta a harde.
Juyawa Uwar Bayi tayi, ta bar wurin su.
"Nan ne kawai zata iya saka Easter, ba tare da wani damuwa ba. Domin kuwa tana hango kiyayyar da take idanun Matar Ubanta, bai zama dole yarinyar ta samu sassauci ba. Domin asalin Deehar din ma ba rangwantawa na kasa ake ba. Balle kuma ita da take da yakinin cewa zasu iya cutar da ita.
"Sai mu shiga" Fure ta ce mata,
"Tow" ta ce tana bin bayan ta.
Wani haraba suka nufa, me yar gasken kyau da shuke-shuke, ga tsuntsaye a keji suna ta wakar su da kuka.
"Nan shi ne harabar Yarima Shehu, yana hutawa shi da Yaran shi da matan shi, ki kula sosai dan ba a zuwa wurin."
"Tow Yaya!"
Juyawa tayi ta kalle ta, sannan ta maimaita Kalmar.
"Yaya!!"
Kallon juna suka yi, tayi maza ta sunkuyar da kanta.
Murmusa mata Fure tai, sannan ta ce mata.
"Kina da kyau da ya dace da fatarki, amma muje"
"Tow" ta fada suka nufi wata yar ƙaramar hanya, daki ce dauke da tarkace a cikin shi. Dauko wani abu tayi ta yab'a mata a kuncinta, me sanyin gaske. Sannan ta tsaya ta gyara mata fuskar ta ce mata.
"Dubi madubin bayanki"
Juyawa tayi, tana tab'a fuskar tana me juyawa ta kalli Furerah.
"Idan na kaiki zaki ga abin mamaki"
Sannan suka fita.
"Hassada da kyashi yana da matukar tasiri a cikin Deehar, dole a boye halittar ki. Ba a son ki fi Matan masarautan nan kyau koda kuwa ta jiki ne!"
Gyada kai tai, sannan suka nufi wata kofa. Wata yar matashiyar budurwa ce a zaune bayi sun lullube ta, ana mata tausa.
"Ina mika gaisuwa uwar ɗakina"
"Hmm!" Ta fada kanta a ƙasa.
D'ago kai tayi ta kalli Easter.
"Ita zata yi aiki da Yaya Aliyah?"
"I,"
"Tow yayi kyau."
Wucewa suka yi izuwa wata siririn lungu, kafin suka isa wata yar karamar korama, gyaran murya suka yi, kan su a sunkuye.
"Wanka take kullum da safe anan, ka'idar shine kafin ta fito za a ajiye mata kayanta sannan a ajiye duk wani abin buƙatar ta. Ba zaki bar nan ba sai ta kammala sannan ki shiga ɗakinta."
Gyada kai tayi tana cewa.
"Tow Yaya!" Suna tsaye har Gimbiya Aliyah ta gama wanka, Fure ta mika mata wani mayafi dan karami ta daure kirjinta zuwa kyawawan dogayen cinyoyinta.
Sannan ta kuma mika mata wani mayafin ta daure sumar kanta. Ajiye mata wani farin takalmi me shegen kyau tayi, sannan ta koma gefe tana faɗin.
"Barka da safiya!"
Kamar bata ji ba, ta cigaba da tafiya suna bin bayan ta har cikin zauren da zai kaita katon ɗakinta.
Tsayawa tayi cak, sannan ta juya tana kallon su.
"Barka dai!" Sai lokacin ta samu damar amsa musu. Kafin ta juya ta shiga cikin dakin.
Suna biye da ita, zama tayi a gaban katon madubi, takowa Fure tayi tana me cire dan zanin ta shiga goge mata, har ta gama sannan ta taje mata gashin kanta. Ta saka mata mai akan.
Wucewa wurin adakar Gimbiya Aliyah tayi, ta ciro mata kayan da zata saka tana zab'a. Kafin aka gama, juyawa tayi tana kallon Easter.
"Ita ce zata fara gobe?"
"Ih,"
"Sunanta?"
"Kyautah "
"Ina fatan su malikah da Radiah basu san da ita ba."
"Ko daya ranki shi dade "
"Ta zauna anan."
"An gama! Amma kin san dole zata na zuwa duba Uwar Bayi!"
"Hm!" Ta ce.
Kusan wunin ranar bata yi shi da sauki ba, domin dai shige da fice ya hanata zama, sai yamma likis, ta koma bangaren su na bayi da kayan abinci niki-niki.
Tana zuwa ta zuba a gaban Uwar Bayi Kande.
"Zoki dauka, ki ci da yar uwarki "
"Tow"
Ta ce mata, ta nufi wurin Uwar Bayi ta kwashe kayan, tana zuwa wurin Abigail, ta zube kayan Abincin.
"Wurin aikin ki ko?"
"Ih"
Tab'e baki, Laraba tayi tana cewa.
"Ai duk abin da la'ananiyya zata kawo min ba zai tab'a burge ni ba."
"Bata kula su ba, ta zuba a gaban Abigail ta fara ci, sannan itama ta fara ci.
"Ya gidan aikin ki?"
Abigail ta tambaye ta, duk da tasan an haramta ire-iren waɗannan tambyar.
"Idan kin koshi, ki ajiye gobe sai muci kafin mu fita"
Easther ta katse ta domin bata son magana, tasan halin Abigail da gulmar tsiya.
---
Da dare kowa yana barci, ban da Easter da take zaune, hangota Uwar Bayi tayi ta zo har inda take, ta mika mata hannu suka fita waje.
Sai da suka yi tafiya me dan nisa, sannan suka samu wuri suka zauna,
Shiru suka yi, suna kallon yadda ake ta sintiri da kulawar tsaro.
"Me ya hanaki barci?"
"Ina kewar Mahaifina!" Ta fada tana kallon gari,
"Ina Mahaifiyar ki? Ko ta rasu ne?"
"Tana raye, kawai ta bar ni ne anan."
"Me yasa ake tsangwamar ki?" Shiru tayi tana kallon hasken farin wata.
"Sabida na karya alfaharin Nahara ne"
"Kamar ya kin karya alfaharin Nahara?"
"An kafa garin mu da Jarumar mace Nahara, domin mutane su samu kwanciyar hankali da nutsuwa shine, ta bada rayuwarta. Bayan nan an yi tsinuwa ga duk macen da ta bawa namiji kanta matukar ba a yantata ba, shi ne tsautsayi yasa na bawa wani kaina, dalilin da yasa aka ci garin mu kenan"
Dariya Abin ya bawa Uwar Bayi ta ce mata.
"Kuma shine suka tsane ki?"
"Ih"
"Tow ai shi kenan, amma me yasa kika fadi lokacin da ake shirin duba Yar uwarki Wabi? Ko Ance miki bamu san cewa mun san bata da cikakken kima"
Matse hannunta tayi, tana kallon Uwar Bayi.
"Ba zan tab'a gayawa kowa ba, amma halin su shi zai kashe su."
Gyada kai tayi tana kallon ta.
Sun jima sosai sannan ta saka ta, suka koma dakin su. Suka kwanta, ita dai Allah ya daura mata kaunar Yarinyar.
Koda Easther ta kwanta, bata jima ba barci ya dauke ta.
---
Sara mutane ake, jini yana malala a ko ina.
Da ta rasa inda zata saka kanta dan tsoro, ga wuta yana ci a ko ina kuka da ihun mutane yasa ta ihu da fasa kara.
"Nahara!!!"
Kallonta yan matan da suke gefenta suka yi, zuwan Uwar bayi, ta dafa goshinta ta ji yayi zafi rau.
Sannan ta juya tana me kiran wata da hannu. Ta fada mata magana a kunne.
Da sauri ta juya can kuwa sai gata da abin da ta tura ta.
Juyar da kanta take, wani mutum take gani. Sai kokarin Mikewa take.
"Kyautah!!"
Uwar Bayi ta kirata, tana shafa mata ruwa a goshinta.
"Gashi nan"
Ta fada da ƙarfi, tana niman Mikewa. Mai da ita Uwar Bayi tayi, ta kuma fashewa da kuka tana cewa.
"Wayyo Babana!"
Ta farka tana zare idanu. Fadawa jikin Uwar Bayi tayi. Tana shafa bayanta.
KARSHEN LITTAFI NA DAYA KENAN MU HADU A LITTAFI NA BIYU DA NA UKU
★‡★
```GARIN NUMAN...!
KASH😭 TAWADA TA YA KARE, me ya faru a garin Numan! Ga Kyautah can tana mafarki! Fisabilillahi yaushe tawadana ya kare! Amma nayi muku alkawarin tafiyar Ƙaddara a labarin nan 500N ne
500₦... Insha Allah'
a tuntube wannan number 08130269641 Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
Ramlat abdulrahman manga 0142529598 Union bank
#Mai_Dambu
.......MASHA RUWA.....
GARIN NUMAN.
Dake yankin Adamawa, na lardin gwangwola.
Garin ya kasance gari me cike da ni'imar Allah, garin da ya kunshe kabilu mabanbanta, garin Masuntan, Manoma, Makiyaya.
Gari ne da ya tara al'umma da dukiyar ban sha'awa.
AKWAI RUGAR JUME da RUGAR ARƊO
waƴannan biyun sune Rugage biyu mafiya dogon tarihi a cikin garin Numan. Don sun wanzu ne tun kafin ƙabilar BACHAMAWA su samu mulki a hannunsu. Ma'ana dai waƴannan rugage sun wanzu tun kafin hawan Hamma Bachama na farko kan karagar mulkimsa.
Bayan rikicin da akaita samu yasa tarihin Rugar Jume ya nemi shafewa daga bakin mutanan garin Numan amma kuma har yau RUGAR ARƊO DA RUGAR JUME suna nan.
RUGAR JUME.
----
Kasancewar lokacin hunturu, baki daya almajirai sun kewaye wutar da yake ci ne a wurin, sai dadd'ar Muryan su ke tashi cikin sautukan daban-daban na Alqur'ani. Kowani almajiri gaban shi dauke yake da allon shi.
Gefen Malam Buba, kyakyawar matashi ne, rike da Alqur'ani, ba a kira shi da matashi ba, domin shekarun shi sun kai talatin da bakwai zuwa da takwas.
Kyakyawar gaske ne, ma'abocin yar doguwar fuska.
Sai yar hancin shi siriri wacce ta tsaya akan fuskar shi.
Idanun shi dara-dara ne, masu ɗauke da zara-zaran gashin idanu.
Yana da karamar saje da ta haɗe gashin bakin shi.
Lumshe idanun shi yayi, yana kara shafa Alqur'anin, kallon shi Malam Buba yayi, cikin murmushi mara sauti ya rike hannun shi, a hankali yayi mishi alama da hannun shi.
Wato ya isa haka.
Murmushi yayi shima sai da gefen fuskar shi ya lobb'a.
Rufe Alqur'anin yayi, yana me janyo wata jakar fatar shi, ya lallube ta a hankali ya saka Alqur'anin, sannan ya dauki sandar shi da hannu ya ce mishi.
"Malam zan tafi"
Kamo hannun shi Malam Buba yayi, sannan ya ce mishi.
"Tow ka gaida gida"
Jinjina kai yayi alamar tow, sannan ya juya yaran da suke karatu suka fara bashi hanya.
A hankali yake amfani da sandar shi, har ya fita a da'irar su, sannan ya fara tafiya.
Tun daga nesa ta hango shi, amma kasancewar zuciyarta ta dasa mata kiyayyar shi, ji take kamar ta dauki wuka ta burma mishi sai ya mutu. Bata gama tunani ba, ta ga Uban annamimai ya dirko daga bishiyar durumin da yake gab da shi.
Yana zuwa ya rike sandar shi.
Murmusa mishi yayi, har suka isa inda take.
Dafa kafadar shi yayi.
Sai da ya juya, sannan ya tsaya tare da riko hannun shi, ya saka a fuskar shi.
Tare da mishi alamar cewa.
"Ka gamsu ni ne a tare da kai?"
Kura mishi ido yayi, sannan ya sake murmushin da har kullum baka iya gane ta meye yake nufi da ita.
Shafa fuskar shi yayi sannan ya ɗan dunkule hannun shi ya