Showing 9001 words to 12000 words out of 105295 words

Chapter 4 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6126

Mai_Dambu...
BABI NA BIYAR (5)


Ihun ta, ya tashi ilahirin bayin da suke tare da ita. A lokacin Ya Musa yana bakin kofar shashin shi da wasu dogarai hudu. Da gudu Dala ta iso tana haki.
"Ya Musa! Uwar dakin mu bata da lafiya jini yana zuba mata."
"Ya Allah!" Ya furta idanun shi waje, da gudu ya nufi cikin gidan wurin Fulani karama. Dakyar masu tsaron kofar ta, suka bude mishi ya shiga.


Koda ya shiga ya same ta zaune a zauren ta, zubewa ya yi bisa gwiwar shi.
"Fulani Sad'aka Kubrah! Tana cikin damuwa."
Zubur ta mike, suka fita har shashin. Suna isa suka same ta a cikin jini male-male.
"Maza ka nufi wurin unguwar zoma ka gaya mata, sannan ka tafi gidan Baba Waziri ka gaya mishi abin da yake faruwa."


Kallon Dala tayi sannan ta ce maza ta koma ta kira mata Barirah, da gudu ta fita daga shashin, ta nufi can ta kira Barirah , tana isowa unguwar zoma tana isowa, cikin gaggawa aka shiga taimaka mata, sai dai jinin zuba yake kamar da bakin ƙwarya, karshe sai da aka kira Babban me bada maganin Masarautar Deehar, ya zo da kan shi ya haɗa maganin a ka bude bakin ta, aka dura mata shi, ya ce musu.
"Matukar ya shiga cikin ta, in sha Allah jinin zai tsaya."
Haka kuwa a ka yi cikin ikon Allah, anan bata maganin jinin ya tsaya, aka shiga gyara dakin, sai da a ka gyara ko ina sannan Fulani Karama ta bar shashin, ta nufi nata wurin tsakiyar rana. Tana isa dakin ta wanka tayi cike da tunanin al'amarin, tabbas a kwai boyayyen al'amari a kan cikin Kubrah me yasa ba a hari na Zulai ba?


To ko ana son a shafa mata bakin jini ne ta hanyar zubda cikin? I haka ne idan ba haka ba, me a ke nufi? Idan ba so a ke a lalata mata suna ba, lumshe idanun tayi tana sake wani irin huci, domin zuwa yanzu ranta ya masifar ɓaci, dan haka ta gama wankar ta shirya cikin shigar da yake nuna alamar tana takaba. Ta nufi zaurenta, tana hutawa abinci aka shiga shirya mata, dakyar taci wani abu.
"Barirah an kai musu abincin kuwa?"
"A'a ranki shi dade, ai hankalin mu baki daya a tashe yake shi yasa bamu yi tunanin haka ba."
"A haɗa mata dage-dage, ta kaza sai abinci na masu jego da kunun tsamiya. A kula sosai wurin girkin."
"In sha Allah" ta fada tana me nufar madafi aka shiga aikin girkin ba b'ata lokaci.
Ana gamawa suka d'iba a ka kai wa, Fulani karama ta ci taji had'in. Sannan suka kai shashin Kubrah.
Dama suna kan girkin ne, ana kai wa kuwa, suka zuba mata, ta ci ƙad'an. Sannan ta kwanta ta ce musu.
"Ku dauka ku ci, a kaiwa Ya Musa."
Daga waziri sai Fulani karama, sune a kan Kubrah, har tsawon kwanakin da ta ji sauki, amma maganar gaskiya ciki kan babu shi babu labarin shi. Domin har fada aka kai ta, a gaban jama'a aka duba cikin aka tabbatar ya fita. A ranar tayi kuka kamar zata mutu. Domin cikin shi yake kara tuna mata da sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, ita ba don mulki take kuka ba, ba wai dan dukiyar take kuka ba. Sai dai tasan kafin ta sake samu wanda zai maye mata gurbin cikin sai ta jima.
Haka ta barwa Allah ikon shi, hankalin waziri yayi mugun tashi, don haka ya samu Fulani kamara suia tattauna. Fitowa Yarima Shehu yayi ya nufi inda suke zaune.
Ya kalle su, kamar yana ganin su. Sannan ya ce musu.
"Al'amarin Masarautar nan akwai fuska biyu,"
"Shi yasa nake cewa ko zamu mai da ita Rano ne?" Inji waziri.


Tashi Yarima Shehu yayi yana faɗin.
"Maso abin ka ya fi ka dabara."
"Ya zamu yi?"
"Ya kuwa za ayi a bar ta anan domin matukar ta tsallaka can ba tsira zata yi ba, can ma ba tsiran zata yi ba"
Ya fada yana barin zauren.
"Kowanni bangare bangare mutum ba a bin yarda ba ne." Fulani karama ta fada, tana kallon Waziri domin baki daya tsoron kowa ya fara d'arsuwa a ranta.


**
A can fadar kuwa, rigima ce ta barke domin kowani ɓangaren suna sukar juna a kan zubewar cikin Kubrah.
"Idan har masarautar Rano suka ji wannan labarin wallahi ba zamu kwashi ta dadi da su ba. Domin wannan al'amarin da akwai renin hankali a cikin shi." Inji Galadima yana kallon Waziri.
"Toh ya za ayi tunda kowa yasan abin da ya faru ba da gayya ba ce."


Karshe dai haka suka daura laifin faruwar al'amarin akan Fulani karama da kuma shi da Ya Musa, sosai abin ya yiwa Waziri ciwo, haka ya hakura.
....
Tunda aka tabbatar da cikin jikin Kubrah ya zube. Hankalin kowa ya kwanta, sannan aka cigaba da renon cikin Zulai.
Bayan wata goma cif.
Ilahirin mutanen masarautar Deehar, sun gama jira da tsumayen zuwan sabon magajin Deehar, domin tun safe aka sanar da Sad'akar marigayi Hayatudeen Abdullahi Noye, zata Haihu.
Tun safe nan ake babu ɗaya, Zulai bata rabu da cikin jikin ta, sai can dare da ya raba. Inda ta haifi kyakyawar danta amma dan karamin kamar bai cika wata tara ba, gashi har ya wuce wata tara ma.


Tun daren ake biki da murnan samuwar sabon Magaji da yawan mutanen masarautar Deehar, suna cikin farin ciki, sannan sun manta da batun Kubrah dan haka, bayan haihuwar Zulai aka sallame ta, ganin yarinya ce kuma tana da damar ta yi wani rayuwar, yasa ta suka mika ta ga masarautar Rano.
★‡★
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, da dadi ba dadi har,
Aka samu kimanin shekaru biyu.
Wanda yayi daidai da zuwan watan sallah, Kubrah tana kwance wasu daga cikin bayin da suke jin zafin ta.
"Ke Dije kije, Fulani tana kiranki." Sahura ta fada tana hararan ta.
Domin ta tsane ta, wanda ba kome ya janyo haka ba, sai zabarta da Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye.


Lokacin da ya fito rangadi, ya fara yada zango masarautar Rano ne, kasancewar sun yi shkgowar almurun ranar Alhamis, kuma yana son yayi sallah juma'a tare da kebewa da abokin shi tun na Yaranta. Domin Sarki Abbas na rano tare suka tashi.
Tunda suka kusan isowa sai ya turo dan aika a gayawa Sarkin Rano gashi nan a hanya shi da tawagarsa, ai kuwa cikin ikon Allah kafin su iso aka gyara musu masaukin da a ke warewa sarakunan da suke daular Uthmaniyya.


Karfin su iso mahaifiyar Kubrah, me suna Innoh ita aka bawa gyaran wurin da girkin sarki Hayatudeen. Mace ce da ta iya sarrafa abinci, dan haka kafin su iso ta gama kome ta daurawa Kubrah ta kai cikin gidan, sai da suka ci suka yaba. Sannan suka kai nashi na bako masauki.


Lokacin da suka iso magariba tai, domin gari ya fara duhu, dan haka Kubrah tana cikin fada, da ita ake ta gudanarwa da wasu ayyukan, domin an haife ta a cikin masarautar ta san masarautar, kuma Fulani Hadizah uwargidan mai Martaba ce, dan haka a bangaren ta, suke duk wani kulle-kullen masarauta ta sani. Kawai ita bata shiga abin da bai dame ta bane, kamar mahaifiyar ta.
Sai wurin Isha suka gama abin da suke suka fito da Sahura da Yahanasu, suna tafe, suna hiran su.
Shi kuma da su Mai Martaba sarki Abbas sun fito shan iska, suna hira. Hasken fitilar wuta da aka zagaye masarautar da shi ya hasko masa fuskarta, shiru ya yi yana karantar yanayinta.
Kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Abokina wannan lokacin na fito tafiya bani da guziri, a matsayi na na me mata hudu da kwarkwarah biyu. Zan bukaci wata kwarkwaran idan aka kwatanta adalci da wancan me sanye da shudiyar kayan sakin."
Tashi zaune Sarki Abbas na ya yi, sannan ya ce masa.
"Kai kace baka ra'ayin samar da mace a wajen masarautar deehar yau kai ne me hango wata mace?" Shafa farin gemun shi yayi wadda bakin gashi ya ratsa sama sama, kasancewar shekaru sun ja ainun.
"Wallahi sai dai wancan yarinyar ta sani ina jin kaina kamar dan saurayi me kananun shekaru, wallahi ina bukatar haka domin dare yayi kuma ina bukatar bargon da zan lullube kashina."


"Amma tayi karama fa Hayatudeen " kura mishi ido ya yi, sannan ya ce mishi.
"Na maka alkawarin zata dauke ni Insha Allah "
Domin a lokacin duk da shekarun shi, idan ka gan shi ba zaka dauka ya kai shekaru kusan sama da tamanin ba, yana da kiran jiki me kyau da ɗaukar hankali.
Har ila yau, babu sarkin da yake tsare da Dawakai, kamar shi sannan yana iya d'aga doki cak, domin a tsaye yake kamar irin samudawan nan, ga girma ga tsawo, da wannan ya cika idanun al'ummar shi ko a fada ne ba a kawo mishi wargi.
Ƙasa-kasa sarki Abbas ya ce mishi.
"Ka san kai irin mun ba ne, sannan yarinyar bata da kwarin kashi"
"Ka fito ka gaya min kai ma, ajiyewa kan ka kake kawai."
"Kar ka min sharri, yarinyar ce karama tausayinta nake ji, dan kai tsaye zaka iya"
"Na ji, ka yi min wannan Alfarman "
A daren aka kira mahaifin ta, sarki Abbas ya aka ajiye mishi tilin zinari da azurfa da yakutu.
"Malam Audi, Yarka Kubrah Abokina Sarkin Deehar yake son ta, a sad'akar shi, ya fanshe da wannan dukiyar. Dan na gaya mishi ita shuwa Arab, masu amsar sadaki da sisin gwal idan kana da ra'ayi toh wallahi laifi idan baka da ra'ayi ba za a maka tilas ba. Yarka ce ba baiwa bace....!
13/Nov/2022
*A Hausa historical Ancient*
#Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*






Mai_Dambu...
BABI NA TAKWAS (8)


*NAHMIFAK*
_Collections_


```Ina mata iyayen giji! NAHMIFAK collections tana muku albishir tare da tallata muku hajarta! Kayan mu sun kunshi Atamfa yar gaske! Laces Ubansu zuwan Lagos! Turaren zamani na wuta kana da Humra tare da Lafayyar yar Sudan, ba nan NAHMIFAK collections ya tsaya ba akwai Materials da kayan Gyara Aure na mata. Muna Garin Gombe za a iya tuntubar Number tarho din mu ta nan 08090744767 sai kun zo muna da sauki da rahusa! Kasuwa akai miki dole! Da abani labari Gara na bada```


Sauka tayi a gadon ta nufi ban dakin ta, ta wanke fuska sannan ta fita ta nufi gadonta, ta zauna kafin ta gyara ƙwanciyar ta, domin bata ga dalilin da zai saka ta hana kanta barci ba, zuwa gobe zata yi maganin abin.
★‡★
MASARAUTAT RANO.
Wani irin tausayinta yake ji, tare da shafa sumar kanta yana rarrashinta.
"Zan dawo fa nace!" Ya fada cikin rarrashinta.
"Toh" ta ce mishi,
Haka ya dauke ta sauka shiga wanka, bayan sun fita ta kwanta da wani irin zazzaɓi. Amma sai ta boye kamar babu kome. Haka suka kwana tana kwance a jikin shi, sosai ya fahimci bata jin dadi amma haka ya shirya, wuraren asuba ya bar masarautan baki daya dan sallah asuba ma a hanya yayi ta.
......
Bayan farkawarta ne ta fahimci baya nan, dan haka ta tattara kayan ta, ta koma bangaren su, duk da a cikin gidan an bata babban sashi, amma bata iya zama ba, sai kusa da Inno. Itama Inno tana kunyar bangaren Kubrah. Wannan abin ya janyo musu tsana da tsangwama a cikin gidan sarauta, wanda yasa baki daya basu da wani kuzari a cikin gidan.


Anan haka Inno ta gano cikin yar nata, bata yi kasa a gwiwa ba, ta shaidawa Fulani Hadizah ita kuma ta shaidawa Mai Martaba sarki Abbas, shine ya tura sakon a labarin cikin.


Bayan sakon ya isa da kwana biyu Ya Musa ya iso, yaso matuka gayya ya tafi da ita, amma taki bata son tayi nesa da iyayen ta. Har zuwa lokacin da Waziri ya mai da ita Deehar.
Har zuwa dawowan ta.
---
Dawo labari.
A hankali ta mike, ita kanta zuwa yanzu bata jin daɗin jikin ta, ga uban nauyi da kasala.
Kirjinta zuwa kugunta, ya sauya sosai. Domin daga sama ta sauya kirjin ya cika kamar ba yarinya ba, haka kugunta ya kara budewa da wani irin fad'i, asalima tayi irin cikar masu tsohon cikin nan ne, amma ta bangaren tumbin ta, a shafe yake kamar ba kome. A hankali take takawa, har cikin gidan. Da sallama ta shiga zauren Fulani Hadizah.
A hankali ta durkusa daga nesa ta ce mata.
"Umma gani"
"Taso kizo nan na gaya miki ke ma Y'ace ba dan kin yi b'ari ba, ai da kece uwar Sarkin Deehar."
Hawayen da ya cika idanun ta ne, ya sauko ta mike a hankali.
"Fulani wannan yarinyar ai akwai jifa a Jikinta. Ga ciki nan ya bayyana amma babu hanyar fitowa!"
Inji wata tsohuwar Bororoji, da take yawan kawowa Fulani kayan tsarin jiki, domin su yasu ma jifar juna suke, ita ce dai bata damu da ta rama abin da ake mata ba, ta kan tsare kanta ne da Yaran ta maza da suke cikin masarautar.


"Ya za ayi haka? Cikin ya zube shakara kusan uku kenan" inji Fulani.
"Hmm, kainuwa dashen Allah, ba dashen mutum ba. Allah ya shirya waye ya isa dakatarwa? Ku bani danyen madara yau insha Allah zai fito ya shaki iska kamar kowa." Inji Barmani, haka aka kawo madaran ta cewa Jakadiya.
"Dauke ta muje dakin can, idan da Allah bai aiko ni ba, yarinyar nan mutuwa zata yi da cikin jikinta, saboda zalinci irin na wasu, Yarinya karama ma ba zasu barta ba. " Haka suka wuce dakin da aka sauke Barmani, aka shiga hada mata magani.
Ana gama damawa Barmani ta shiga dakin, ta mika mata, bayan tace ta mike tsaye.
Tana mikewa ta shanye sannan ta ce mata.
"Sake kwaryan a kasa!" Sake kwaryan da tayi, yayi daidai da jin wani abu kamar an sare ta. Durkusawa tayi ita kuma, ta cigaba da had'a wani ruwa da magani, tana watsa mata.
"Wayyo Allah na! Wayyo Inno! Wayyo Baffana don Allah ku kira min Inno"
Ta fada cikin tsannanin azaba da tashin hankali.
Sosai ta fita hayacinta, tare da niman agajin Mahaifiyar ta, amma ina kunya ya hanata zuwa. Har zuwa dare abu daya ake, sai wurin bayan sallah isha, Allah ya sauke ikon shi akan Kubrah, inda ta haifi yaronta dan kankani. Kamar ba cikakken d'an Adam ba. Ta koma tana maida numfashi.
Daukar Yaron Barmani tayi tana kallon shi. Sai ka saka idanu zaka fahimci yana raye.
"Fulani a bawa Yarima auduga, kasancewar danne shi da aka yi ya mai da shi baya, a lullube shi ina man shanu da kadanya?" Kafin kace me an kawo ta, ta yanke cibiyar, sannan ta goge shi ta bawa Unguwar zoma damar gyara ta, shi kuma ta goge shi tass, sannan aka saka wutan dakin yadda ya dauki dumi, yasa zai sake ya warware.
Ita kuma uwar aka mata wanka aka gyarata, sannan aka saka taci abinci ta kwanta tuni barci yayi gaba da ita.
Gyara dakin bayi suka yi, sannan suka fito aka bar Barmani a dakin da Fulani.
----
Da murmushi ya iso dakin yana kallonta, itama murmushi take tana wasa da hannun ta.
"Hadizatul Kubra wannan nawa ne?" Ya tambaye ta, gyada mishi kai yayi.
Murmushi yayi ya dauki jaririn ya sumbata, sannan ya juya zai fita ya ce mata.
"Kiyi hakuri." Daga haka ya saka kai ya fita, Mikewa tayi zata bishi.
Bude idanu tai, ta ga Inno a gefenta tana mata murmushi.
Tashi tayi zaune.
"Sannu Kubrah!"
"Inno muje gida " ta fada idanunta cike da kwallar.
"Kin girma yanzu babu batun kuka, dan haka kiyi hakuri, ki zauna anan domin rayuwar shi tana buƙatar kulawar manyan mutane, shi kan shi Yarima ne, ba zai taso a cikin bayi ba sai dole. Dan haka ki kula da shi zan na zuwa duba ki in sha Allah "
Mikewa tayi ta shiga ban daki, tayi tsarki sannan ta dawo ta samu Inno ta bar dakin, abinci me zafi ta gani ta zauna taci ta koshi. Shigowar Barmani yasata d'ago kai.
"Shiga a miki wanka."
"Toh" ta nufi ban dakin Innar Sahura take ciki.
Ta zauna, bayan ta cire kayanta.
A hankali ta shiga yafa mata ruwan zafi. Zuciyar ta cike da hassada da bakin ciki. Take yafa mata ruwan.


Tana gamawa mata, ta ce mata.
"Kiyi wankar" ta fito, a wannan bangaren ita kanta Kubra tayi hakuri sosai.
★‡★
MASARAUTAR DEEHAR.
Yau an tashi da wata irin sirrintacciyar al'amari ne, wanda ya daure kan mutane, domin ga rana da wata, wato rana bata fadi ba. Amma wata ya fito da hasken shi.
Ya Musa da yake tare da Yarima Shehu d'ago kai yayi yana kallon sama.
_A duk lokacin da rana da wata suka fito a lokaci guda! Ka nisanta shi da nahiyar nan_


Sunkuyar da kai yayi idanun shi cike da kwalla.
"Kafin Mai Martaba ya rasu ya bani amanar a duk lokacin da rana da wata suka fito lokaci guda, na nisanta abin da za a haifa a wannan lokacin da nahiyar Deehar baki ɗaya, yau ga rana da wata a sarari amma babu abin da aka haifa."
"Hmm!" Yarima Shehu ya fada, yana kallon sama kamar me nazarin wani abu..
Haka suka kasance a wurin, har rana ta fad'i.
----
Sosai suke gudu a cikin kasungurmin dajin. Kafin suka isa kogon bishiyar Aljanu.
"Boka me duniya!"
"Ya shiga halwa ba zai fito ba sai bayan shekaru biyar"
Wannan yasa suka juya zuciya babu dad'i.
---
MASARAUTAR RANO.
Duk wani abin da ake wa me jego, an mata ga wani abin burgewa ruwan Mamanta yana da kyau, a lokacin haihuwan Sarkin Rano yana kano, dan haka ana gobe suna ya iso, da kan shi ya isa zauren Fulani, ya amshi Yaron yayi mishi huɗuba.
"DASHEN ALLAH! Sannunka kainuwa!" Ya mishi Huduba da Abdullahi Hayatudeen Noye.


Fulani taso kwarai a tura Deehar, shi ya hana ta hanyar mata bayani. Dan haka ta hakura.
Suka cigaba da kula da Yaron,
Har tsawon wata shida, sannan Barmani ta gama shirya Yaron ta cewa Fulani.
"Ba dai mutum da aljan ba In sha Allah, ni zan tafi"
Sun mata alkhairi sosai, bayan kwana biyu ta tafi, suka cigaba da renon shi. Wanda yana girma, kamanin shi da Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye yana kara fitowa, sai dai farin fatar Mahaifiyar shi da ya dauko kamar balarabe. Gashin kan shi a kwance yake luff-luff.


Watan shi bakwai a duniya ya fara takawa, domin karambani ne da shi kamar me,


Yana cika shekara daya kuwa, kowa yasan cewa akwai wani ajiyar Allah a wurin. Domin kuwa gari ba wayewa zai fita wajen bayin gidan ya zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login