Showing 57001 words to 60000 words out of 105295 words

Chapter 20 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6098

shima haka yake kome kuma babu yadda aka iya da shi dan haka ku rike hujjar da zamu iya kama shi....
(Allah ka shirya mana Kyautah 😂🤣🙄🤔 kiwon ta ne shi 😹😂🤣 duk ranar da kika shiga hannun basamude zamu banbance haka)
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
....... Sake ta yayi ta fadi "kummm" ta fashe da kuka, kamar ana zare ranta haka ya wuce ya bar ta a wurin, ai kuwa tayi ta kuka, can da ta mike ta nufi hanyar waje, anan ta hadu da Fulani Babba, dawowa da baya tayi ta zata koma cikin gidan.
"Zoki wuce " idanunta ya cika da kwalla,
"Tow" ta furta sannan ta bi bayan Fulani.
"Idan aka tafi da ita, waye zai cigaba da kula da Abdullahi?"
"Akwai bayi kaca-kaca a cikin Deehar"
"Abdullahi ya ce ita yake bukata"
"Ka gaya mishi na tafi da ita"
"Fulani Babba, baki da iko a kan duk wani abu na cikin Deehar!"
"Da gaske? Ya Musa! Ka manta ni na saka a ka rufe zancen mutuwar Hayatudeen akan kai ne ka kashe shi? Tow idan baka sani ba, bari na gaya maka dan na lura" buga sandar hannun shi yai da mugun karfi, sai da ta d'ago ta kalle shi, Abdullahi ne amma bata fasa abin da tayi niyya ba.
"Ku tafi da ita, gidan kaso"


Juyawa tayi tana kallon kofar bangaren Abdullahi, hawaye ya zuba mata ai tasan duk lalacewa ba zai tab'a bari a tafi da ita ba, shi kuma yana sane da an saka a kamata kuma yasan Fulani Babba tana niman ta, yasa shi kin tankawa, sakamakon shawarar da Ya Musa ya bashi, idan ya cigaba da hanawa zasu iya cutar da ita, kuma haka zai zama kamar ita ce raunin shi. Dan haka yayi kokarin ganin ya ɗauke kai, sai ya bullo musu ta wani hanya, dan zuwa yanzu sun haɗa hujjojin kalubalantar Fulani Babba.

---
A fada kuwa, zama garkuwa yayi yana kallon mutanen Fadar, kafin ya ce.
"Ya Musa na hawa Abdullahi auren Yata Mulikah." A razane Galadima ya d'ago kai domin ai yarjejeniyar su, Mulikah za a bawa Arshan da zarar ya zama sarki, garkuwa da Tafida suna cikin waɗanda suke nad'a sarki (a turance ana kiran su King maker) tow idan haka ta faru fa? Kallon Chiroma Galadima yayi ya ga shima ya dauke kai.
"Tow Masha Allah" ya furta da kwarin gwiwa, domin ya fahimci akwai wata gaskiyar da suke boyewa don haka, wani irin b'acin rai yake ji daga kasar zuciyar shi domin kuwa yasan wannan wata shiri ne na daban.
"Zan tuntubi Abdullahi ko yana da bukatar iyali a wannan lokacin, domin nayi kokarin nima mishi auren Yar wurina zaman bai yi ba, amma zan tuntube shi."


"Yarka????" Suka tambaye shi, domin abin da mamaki ace mace taga Abdullahi taki aurar shi, ai ko ba don ba nakasa ba, namiji a duk inda yake namiji ne, ko mata hudu aka bashi kari da kwarkwarah zai dauke su tsam, ai sun san ƙabilar noye ba ragwayen maza ba ne, amma sai gashi wata ta ce bata bukatar shi.
Kallon Ya Musa Galadima yayi sannan ya ce mishi.
"Ai kuwa ba za ayi haka ba, wannan al'amarin cikin gida ne, dan haka Yarka zata koma ɗakinta, nayi alƙawarin haka, domin ba zai zama butulci ga hannun da ya rene shi ba."


Shiru Ya Musa yayi domin bai da ta cewa, koda ya koma bangaren su ya sanar da Abdullahi abin da yake faruwa, dauke kai Abdullahi yayi sannan ya mike abin shi, domin ta kasa cewa kome ne. Bayan tashin sa sai ga Galadima da Fulani Babba.
Zama suka yi a zauren, sannan Fulani yayi gyaran murya, kafin ta fara kokarin ganin ta kawo shawarar da ta da ce.
"Ba zai yiwu ace ka ɗauki lokaci kana kumaeda Yaro dare daya ya maka butulci ba, sannan ita Yarinyar ai akwai kuruciya a tare da ita, dan haka a dawo da ita dakin, jibi jumma'a sai a daura auren domin ba zai yiwu Yarka ta cigaba da zawarci ba."
"Ih, shi na gani Fulani taya ga matar shi, a dauki wata mace a bashi ina ga su daidaita da matar shi kawai."
"A'a Fulani ita Raudah da kanta ta ce bata bukatar Abdullahi, kun ga idan aka yi haka za a koma gidan jiya."
"Ni kuwa sai nake ganin ka dai yi tunani, idan aka yi wannan gyaran aka hada karfi da karfe zumunci zai kuma danko, sannan duniya zata yi alfahari da mun rike bayan Hayatudeen Abdullahi Noye "


Shi dai bai ce uffan ba, dan haka suka gama zantuttukar su, suka bar gidan. Ajiyar zuciya ya sauke Abid ya ce mishi.
"Ban ga wani amfanin jin wannan ta tatsuniyoyin ba, domin kuwa babu al'amarin alkhairi a cikin shi, ita Raudah ta bukaci a raba ta da Abdullahi sabida nakasa, sannan yau a dawo ace ta koma jikin Abdullahi bayan taki shi, duk wanda yaki ka lokacin da kake bukatar taimakon shi, ba masoyi ba ne, wanda zai kaunace ka a lokacin da kake bukatar taimakon shi, shi ne masoyinka kuma ga shi nan Yarinyar nan sai nawa ana cutar da ita dan kawai zata zauna a jikin shi? Kayi hakuri Raudah Yarka ce amma ba zan iya ganin Abdullahi ya kuma zama da ita ba, bana goyan bayan haka wallahi "


Suna cikin haka, Ya Haruna shima yazo yaji abin da ake fada, shiru yayi yana kallon Ya Musa, tsakani da Allah sun cusa mishi ra'ayin haka, amma kuma kar ya fito ya goyi bayan yar shi yasa shi ƙasa d'ago kai a zancen dan haka ya ce musu.
"Shi kenan "
Domin baya son Ya Haruna yayi magana, yasan idan yayi magana wani abu sai kuma faruwa.


---
Kyautah a gidan Yari, burin Mama Uwa ne a dauke ta baki daya, yadda yarta kawai zata iya shanawana cikin gidan sarautar.


Dakin da aka kaita, babu kowa sai beraye bata iya barci domin tana rufe idanunta suka daina jin motsin ta, zasu fara gwaguran ta,.yasa ta daina barci. Duk abin da suke tana jin su. Kwana biyu kenan a dakin ko bakin kofar bata fita kuma ma ba a barinta ta fita, ko tafin hannunta bata gani, ta gama galabaita tana durkushe aka bude kofar dakin, masu kula da harkokin gidan yarin ne,.suka shigo da wani irin sarka aka daure ta, sannan suka fita. Ba zata iya cewa tasan me yasa ba, amma qaddara ta kawo ta inda bata da wani gata sai ta Allah.


Tana zaune aka shigo dakin bata san waye ba, yana zuwa kanta ya nufa tare da rabata da kayan jikinta.
"Waye kai? Yarima Arshan me nayi maka" dauke ta da mari yayi sannan ya shiga rabata da duk abin da ya ci karo da shi, burin shi ya biya bukatar shi, hannun shi ya kai kirjinta. Ihu da Niman taimako take amma babu wanda ya fahimci haka, burin shi ya shiga inda ba a san da zuwan shi, sai dai kuma a daidai wannan lokacin, aka tokari kofar sai da ta balle, shake wuyar ta, yayi tun tana tari har ta kasa motsi, rufe shi aka yi da wani irin kazamin duka da wata bulalar karfe, ihun da birgima yasa shi bai iya sanin waye ba. Sai da aka mishi ligi-ligi, sannan aka ɗauki sarkan karshen aka daure shi da su. Cire babbar rigar shi yayi ya goyata, jikinta mara kaya ya hadu hadaddiyar surar shi, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke yana me gyara mata zama, sannan ya fita kamar yadda ya shigo. Har dakin Uwar Bayi ya kaita, ya kwantar da ita.
A hankali babbar rigar shi ya zame daga kirjinta, wannan shine karon farko a rayuwar shi yaga jikin mace,. musamman kirjin da kullum take boye shi kar a gani, yasan duk ranar da tasan ya ganta babu kaya, Deehar sai ta musu ƙad'an domin ba yarda zata yi ba, hannun shi ya kai yana son ji yadda suka tokare mishi baya, haka suke a hannun. Can kuma ya ja rigar ya rufe ta, sannan ya fita yana murmushi idan ya tuna yadda ya ganta, rigar har zuwa cikinta ya sauka ga dan ramin cibiyarta. Murmushi ya sake. Kamar wanda aka kuna mishi wuta yaji kamar abu ya motsa a kasan wandon shi, tare da zubar abu.
Akan lokaci ya koma bangaren shi domin babu wanda ya san ya fita, koda ya shiga ya samu Abid har lokacin yana tattara wasu abubuwan. Wucewa ban daki yayi wanka, sannan ya fito amma ina Abdullahi karama ta ce bata ji zancen nan ba, haka ta fito yana matseta, amma sai da Abid ya hango yadda tayi gefe can. Tattara tarkadun yayi yana kallon wandon shi.
"Kai wani irin Iskanci ne haka?" Nishi ya sauke me dan ƙarfi, yana me jan wani mayafi a zauren ya lullube kafar shi zuwa cinyar shi.
"Meye nufin ka? Idan kana son Mulikah Hamid Garkuwa sai a baka ita." Ya fada yana zare idanu, gani yake kamar Abdullahi zai turmushe shi. Wannan shine karo na uku da yaa Gandhi cikin wannan yanayin, tabbas shima yana yawan jin haka, musamman idan yayi arba da Aaliyah, kwana yake yana jika jar kanwa. Yana daga cikin dalilan da yasa baya son su hadu, idan kuwa suka hadu zai ta bata rai da bakin hali dan ta bar shi.
"Abdullahi!" Bude idanun shi yayi yana kallon Abid.
"Kayi aure kasan a cikin ƙabilar noye mune har yau bamu yi aure ba, amma kananan yara akewa Aure gudun kar su karya mana darajar mu. Don Allah kayi aure."
A yanzu shi kan baya bukatar wata mace idan ba dai wancan motsatsiyar za'a bashi ba, shi baya jin kome a kanta sai bukatar kusanci, ga Ya Musa da Garkuwa.
Lumshe idanun shi yayi, a cikin kwana biyu nan yayi mugun kewarta, da haukar kawai yasan yayi kewar Mahaukaciya lamba daya.
----
"Galadima an samu wani ya bi bayan Yarima Arshan ya kuma dukan shi."
Sake kofin yayi yana faɗin.
"Kar ku sake Fulani ta sani a dauko min shi"
"Tow, amma ya Musa yana son ganin ka." Duk da yana cikin tashin hankali, amma bai hana shi cewa.
"Ya shigo"
Haka suka yiwa Ya Musa iso, ya shiga bayan sun zauna ya saka aka kawo mishi kayan ciye-ciyen.
"Na san zaka yi mamaki me yasa nace maka, kazo tow ba kome bane sai akan Raudah da Abdullahi, babu uban da zai gama wahala sannan ya tashi akan tutan babu. Ai ko baka gaya mana yadda ka rike shi ba, mun san ka sha wahala dan haka kayi tunani me kyau babu yar da ta dace da Abdullahi kamar Yarka Raudah, ina son na kara dankon zumunci ne, yadda ba zaka yi nadama ba."
"Tow Galadima zan duba, idan da yiwuwar haka zan mishi magana, idan babu damar haka zan baku hakuri domin auren da babu soyayya ba shi ne aure."
"Ka dai duba dai, ai haka shi ne mafi alkhairi."
Sosai yake daura Ya Musa akan son zuciyar shi, burin shi ya shiga cikin yadda Garkuwa ba zai iya kome ba.


Da haka suka yi sallama, hankalin Ya Musa ya rabu gida biyu.
;;;;;;;;;;;;;;;;;
Lokacin da ta farka kunun tsamiya Uwar bayi ta bata, sai da ta sha ta koshi sannan ta kalli Uwar Bayi ta ce mata.
"Uwar Bayi!" Kallon ta tayi, cikin so da kauna domin tana masifar kaunar Kyautah.
"Na'am kyautah"
"Yaushe zan bar Deehar?"
Kura mata idanu tayi, domin bata zaci haka daga bakinta ba, murmushi tayi mata sannan ta ce mata.
"Kin gaji da tashin hankali ko?"
"Ih, gara na mutu na huta na gaji, ba zamu tab'a samun yanci ba, tow meye amfanin zamana anan"


Shafa kanta tayi yana murmushi sannan ya ce mata.
"Lokaci ne ya zai nuna mana amfanin ki a nan din"
Suna cikin wannan yanayin,labarin abin da ya faru da Yarima Arshan a gidan Yari ya karade ko ina, a cikin wannan yanayin Mama Uwa ta fahimci Wabi tana da ciki, dan kota tambaye ta, na waye bata boye mata ba, ta gaya mata na Aminin Arshan ne wato Namir.


Ai kuwa tasha mari, dan haka ta rasa ya zata bullowa al'amarin, kyautah ce ta fado mata a rai, zata yi yadda za ayi. Tunda taji labarin kyautah tana wurin Uwar bayi, dan haka ta shirya zuwa ganin Kyautah.
🤌🏽😹🤣 (Ku min addu'a Allah yasa a samu na dare)
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
....... "Abdullahi ban fahimci shirun nan da kake ba, gara ka fito ka fadi abinda yake ranka ko samu nutsuwa" lumshe idanun shi yayi sannan ya bude a hankali yana murmushin kafin ya juya ga Abid.
"Hmm!"
Yadda ya tsare Abid da idanun ya sashi dole yayi kasa da murya.
"Wai cewa nayi idan da hali kayi wani abu mana"
"Kar ka damu" gyada kai yayi yana kallon tsuntsayen da suke kejin harabar gidan.
"Dama naga sun sako ya Musa a gaba ne"
"Ai shi ba yaro bane, kuma idan ya dauki abinci a hannun ba hanci zai kai ba." Sannan ya mike, wannan dabi'ar na Abdullahi yana mugun burge shi, bai cika takura kan shi da ɗaukar fansa ba, amma ya san yadda zai haɗawa kowa zafin kai. Shi yasa yake kome sai sa sai sa.


Kuma abin burgewa yaki magana, sai ma harkan gaban shi da yake wanda haka ya zame mishi al'ada. Shiru a lokacin da ya dace yayi magana, haka yana sakawa mutane tsoron ka, ai tunda aka fara zancen Raudah har yanzu Ya Musa bai mishi magana ba, kuma bai ce mishi ga abin da ake ciki ba, haka ya kara mishi fahimtar Ya Musa shakkar shi yake,. Don haka yana kallon iya gudun su ne, yaga me Ya Musa zai ce.


Wani lokaci shiru ma magana ce, inji me tsinkayen hankali ai ba kodayaushe maganar ya da ce yayi amo da sauti ba, shi yasa Abdullahi yaƙe raka su da idanu, abin da aka yi shekaru ashirin da takwas ba za a kuma maimaita shi a cikin awa ashirin da takwas ba, shi yasa yake danne zuciyar shi, baya jin zai iya faɗa domin kowa ko kan shi, amma zai iya bawa Kyautah kariya a boye ko a sarari.
---
Sai da ta samu abin tabawa, sannan ta nufi dakin Uwar bayi. Kallon juna suka yi uwar bayi da Mama Uwa, bata hanya tayi domin itama zata fita ne.
"Da fatan ba wani sharrin ya koma kawo ki ba?"
"Haba ina kawai naji kyautah bata da lafiya ne nazo" ta fada cikin wani makirin murya irin wadda kowa yaji zai dauka ta Allah ce.
"Tana cikin dakin!"
Shiga dakin tayi, ta same ta zaune tana kallon abincin gabanta. Da alamu tunani take.
"Yar nan" d'ago kai tayi tana sake ajiyar zuciya.
"Mama" ta kira sunanta a hankali, domin har yanzu bata gama cike gurbin yunwa kwana biyu ba, zama tayi tana kallon Kyautah cikin tausayawa, sannan ta ce mata.
"Ashe baki ji dadi ba?"
"Ih, da sauki sosai"
"Sannun kin ji"
"Yawwa" suka yi shiru. Kafin Kyautah ta tambayi Wabi.
"Ina Abigail?"
"Tana nan lafiyarta lau"
Tura mata abin da tazo da shi tayi, sannan ta ce mata.
"Gashi nan na kawo miki"
Shiru tayi tana kallon nama soyayye.
"Kici mana"
Hàdiye yawu tayi, sannan ya fara ci a ranta tana jin kamar Mama Uwa ta dawo tana sonta kenan, sai da ta cinye tass sannan ta yi gyatsay.
"Na gode"
"Yawwa, Kyautah"
Shiru suka yi, can ta lura da Mama Uwa tana share kwalla.
"Lafiya Mama Uwa?"
"Yar nan, Wabi ce bata da lafiya tana wuri na, kuma aiki ya min yawa nake son niman arzikin ki,.ko zoki kina taya ta zama"
"Tow Mama Uwa, ai wannan me sauki ne zan zo an jima"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login