Showing 54001 words to 57000 words out of 105295 words
Chapter 19 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
ita bace ake tsammanin ita wannan bala'in da yake cikinta ya ishe ta riga da wando, domin ita ta cire musu kafiyar garin su, dan haka a Kore ta, domin ba a san me zata kuma janyowa wani ba.". Inji Hamid Garkuwa.
Shiru Fulani Babba tayi sannan ta ce mishi.
"A kira dattawa daga mutanen nahara"
Fita Jakadiya tayi can sai hadu tare da Mama Uwa. Haka suka shigo har zuwa dakin suka zauna.
"Wace ce take da alaka da Kyautah?"
"Gani nan"
"Me kika sani a kanta?"
"Hmm! Allah ya baki nasara yarinyar dai mayya ce, bayan haka kowa yasan ita ce ta janyo mana masifar da aka kashe dubanin al'umma da dukiya a garin Nahara, a takaice tsinanniya ce"
Lumshe idanun Fulani tayi, sannan ta bude a hankali ta ce musu.
"Da gaske haka ne?"
"Ih, ranki shi dade."
"Garkuwa kasa a fiddo ta, daga gidan Abdullahi a jifeta sai ta mutu"
Wani irin ajiyar zuciya Mama Uwa ta sauke burinta bai wuce taga bayan Kyautah ba, domin ko wurin wancan bamagujen ya gaya mata babu abin da zata iya dauka a rayuwar Kyautah ta tsani yarinyar tun daga farko har yau.
Ajiyar zuciya Garkuwa ya sauke, yasan Kyautah su Fulani suke nima, amma boye na shi guntun kashin ba zao tab'a yarda ya rasa damar ba, kuma an tabbatar mishi. Kyautah da Abdullahi ba zasu tab'a rabuwa ba, asalima kowannen su garkuwa ne ga dan uwansa. Don haka ya shirya Tsaf domin maye gurbin da yar shi, domin yasan ba haka kawai Abdullahi da Abid suka dawo ba, duk da basu nuna alamar daukar fansa ko abin da aka mu ba. Wannan dalilin yasa suka mike kafa, amma shi yaki yarda ya mike din sai ya toshe kofar da zata kawo mishi tarnaki. Yayi imani da Allah Abdullahi jinin Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ne, shi yasa yake da mugun kamun kai,mata basu gaban shi, shashanci baya cikin al'amarin shi.
Sai dai yana yawan hango kiyayya me mugun yawa a cikin kwayar idanun shi, duk da baya gani amma yana ganin yawan kiyayyar a idanun. Dan haka zai rufe wani hujjar.
Hmm ya manta akwai hujjar da bata rufuwa, dan haka suka tafi dauko kyautah.
---
Tunda suka shiga cikin harabar, suka samu ya Musa da Haruna suna tattaunawa.
"Ya Musa ina Yarinyar nan Kyautah?"
"Tana ciki"
"A fito da ita, domin tsinuwa ce ga al'ummar Noyewa su zauna da mayya a cikin gidan su."
"Mayya kuma?"
"Ih, ai mayya ce domin ana zargin ta saka wuta ne a bangaren Arshan gashi can a rai a hannun Allah"
Takowa Abdullahi yayi da sandar shi, yana kallon inda suke, tafiya yake a hankali har ya iso inda suke, sai da ya iso daidai fuskar Garkuwa, ya ce mishi.
"Kace mata na hana a fitar da ita " juyawa gefe da gefe Garkuwa yayi yana niman daga inda maganar ya fito, kafin ya kalli Abdullahi suka kalli cikin idanun juna, rintsa idanun Garkuwa yayi kafin yaja da baya.
"Yana magana ne?" Kallon shi suka yi, kafin suka ce.
"Waye fa?"
"Abdullahi mana"
"Aikuwa sai dai idan baka ka ji ba, amma baya magana ko ka manta ne?" Ya Musa ya tambaye shi, wani irin zufa ne ya karyo mishi, ja da baya yayi yana me barin harabar.
"Kun samo dalilin?" Ya furta yana tafiya da sandar shi.
"Ih, sakamakon baiwar da take tare da ita ne, ake son Arshan yayi tarayya da ita, da farko ita Fulani Babba tayi tunanin haka, tow ganin ana samun matsala a cikin fada domin har yau wasu basu yarda da Arshan zai zama sarki ba, shi ne aka ce su samo yarinyar da Nahara ta albarkace ta, ita kuma yarinyar ce a halin yanzu tana tare da abin ne, shi yasa gubar da suka saka maka bai kamata sosai ba, amma tabbas ita din ce sao dai akwai kalubalen rayuwa, domin nan da wani lokaci zata buakci sanin asalinta, iya abin da muka samu kenan "
Lumshe idanun shi yana sauke numfashi, juyawa yayi ya koma abin shi kamar ba shi ba.
"Wallahi sai na bar gidan nan, haka kawai a dirke ka a bar ka." Ta fada tana mita, juyawa tayi tana hararan shi fatar ta, guda ya fadi dan ta zuba ruwan karkashi, ita fa baki daya ta gama rena shi gani take tunda baya gani kamar ba wani abu bane, ganin ya tsalleke ruwan ƙarƙashin abin shi ya wuce yasa ta tawo ganin wurin ta gani, ai kuwa tana takawa ta tafi zuuuuuuu. Ta zube a gaban shi,
Tsallake ta yayi abin shi, ya wuce kamar bai damu ba.
"Kai ban yafe ba, da kai kamar uwar yaki"
"Buuf" aka guje bakinta, bata ga kowa ba. Jin zafin yana shiga jikinta yasa ta mike zata gudu, ta kuma zamewa "Fittt" ta kuma faduwa,
"Wayyo na shiga uku, nayi gamo." Dakyar ta mike aka kuma harde kafarta garin faduwa ta zube a jikin shi.
"Na shiga uku, na rantse da nahara ba zan kuma ba kayi hakuri" lumshe idanun shi yayi yana sauke ajiyar zuciya...
Maneji...
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
......... Bayan fitar Ya Musa Abid ya kasa hakuri ya ce mishi.
"Abdullahi kana ganin abin da yake shirin faruwa ba zaka dakatar da su ba"
Murmushi yayi sannan ya ce mishi,
"Tow me zan dakatar?" Daga haka ya wuce dakin shi, ran Abid ya ɓaci sosai, domin gani yake kamar da gayya ya bar kome yake tafiya haka, domin haka shima yayi fuska ya bar gidan, ya nufi Ya Haruna yana mishi korafi.
"Kasan me yasa yayi shiru?" Girgiza kai Abid yayi, murmushi Ya Haruna yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Yayi shiru ne domin kure tunanin kowa, har yanzu bai fara magana ba, idan ya fara magana kowa zai shiga hankalin shi, sannan idan ya fara babu me iya dakatar da shi. Ka koya daga gare shi"
"Ya Haruna ban ga fa'idar haka ba, domin a madadin kome yazo da sauki wasu abubuwan kamar yanzu ake bayyana. Ina jin tsoron kar su cutar da shi ne"
"Ba zasu iya ba Abid, wanda Allah ya kare shi ya sani ne? Bai sani ba, dan haka kome ma idan ya taso Allah yana tare da shi."
Haka suka yi shiru, domin Ya Haruna ta bashi dama ya fahimci gaskiya. Da dadre tare suka tafi wurin Kyautah. A tsakar gidan suka fara karo da surutun da ake.
"Ih, ai cikin na Yarima Abdullahi ne, tow gashi nan dai ta lalata goben ta, kowa ye zai aure ta sai dai ta tabbatar a haka domin babu namijin da zai lalataka ya koma ya aure ka."
"Ga kyau amma ya zama na dan maciji " a fusace Abid yaso magana, amma Abdullahi ya rike shi, girgiza mishi kai yayi yana matse hannun shi alamar yayi hakuri, wani irin tausayin yarinyar ne ya cika mishi zuciyar shi. Tunda suka hadu ya fahimci tana da kunci kawai ta iya amfani da damar da ta samu ne domin tayi farin ciki. Sallamar Abid ya katse musu gulmar su.
"Ina ne dakin da Kyautah take?"
Kasancewar daren goma sha daya ne garin ya haska da hasken farin wata. Kamar a mafarki yau ga Yarima Abdullahi. Mikewa suka yi suna nuna dakin,.haka Abid yayi mishi jagora har dakin.
"Dama Easther abin da kike kenan? Ana ta zagin Wabi karuwa ashe abin da kike aikatawa kenan? Easter me yasa kika yi watsi da Amanar da Babanku ya baku? Gaskiya kin bani mamaki."
"Assalamu alaikum!" Shiru Mama Uwa tayi ganin Abdullahi, yadda ta koma gefe tana kuka ya kara narkar mishi da zuciya, ga gaskiya amma an hanata magana, Abid yana rike da hannunsa. Kamar dai yadda suka saba renawa kowa hankali. Magana yayi mishi, wanda yasa shi bude mata hannu. Kallonta Abid yayi da sauri ta mike ta fada jikin Abdullahi.
"Ka tafi da ni, kaji don Ubangijin ku ka tafi da ni, ba zan iya zama a nan ba"
Daga Mama Uwa har Abigail mutuwar zaune suka yi, ganin Abid ya amshi sandar shi, ya dauke ta Cak ya juya Abid ya cigaba da mishi jagora, har waje a gaban sauran bayin Abid ya ce.
"Idan masu gulma suna son gulma tow ga gulma nan da gindinta, sai a daura daga inda aka tsaya. Cikin da aka ce na Abdullahi ne Ih na shi ne gaba ma zai kara himma domin samar da wasu, kuma ta haihu cikin koshin lafiya. Ina kara gargaden ku. Ku iya da harshen ku akan Gimbiya Kyautah" da wani irin yanayi ta d'ago tana kallon Abdullahi da yake nan kamar kullum, haka Abid ya rike mishi hannu suka cigaba da tafiya, har zuwa bangaren shi, dakin shi ya kaita ya kwantar da ita, sai lokacin ya lura da kayan shi ya b'aci da jini, amma sai kamar baya ganin, ita ce idanunta ya sauka akan kayan, domin ya kai hannun shi kamar zai tab'a jinin ne idanunta ya kai kan shi,.ai kuwa da sauri ta rike hannun shi.
"Wallahi sharri ne" lumshe idanun shi yayi, domin bai tab'a ganin tashin hankali a kwayar idanun ta irin na yau ba.
Mikewa tayi ta fara kokarin cire mishi alkyabar shi, jiri ya kwashe ta haka ta zube a jikin shi tana haki, hawaye na zuba a idanun ta. Yadda numfashin su ya gauraya lokaci guda, idanun su cikin na juna, kusancin su yayi yawa sama da kullum yasa ta kai hannunta fuskar shi tana tab'a sajen shi, baki daya duniyar ya mata kunci, sunkuyar da kan ta tayi, goshinta a bakin shi, a hankali ya sumbaci goshinta da sauri ta d'ago kai tana kallon shi, ya saka fuska kamar bashi ba.
Mikewa yayi itama ta mike, jiri ya kuma dibanta, rungumar ta yayi yana shafa bayanta.
Da wutsiyar ido yaga yadda ta b'ata gadon, haka yasa shi, juyawa da ita banɗaki ya juya, fita yayi ya kalli Abid.
"Uwar Bayi nake bukata da ruwan zafi"
"Tow Angon karni da alamu cikin nan dai naka ne ya b'are yaushe Dan iska ya ratsa cinyar yar budurwa?" Abid ya fada yana mishi shakiyanci.
Kamar zai yi dariya, amma sai ya share haka Abid ya fita can kuwa sai gadi tare da Uwar bayi, ita ta shiga tare da Ladi, wanka suka mata sannan suka kimtsa dakin, uwar bayi ta fita ta har madafi ta shiga aikin abinci a daren, sannan ta kawo mata dake cikinta da yunwa taci sosai, kafin ta kwanta.
"Ta kwanta ranka shi dade " gyada kai yayi. Sannan suka mishi sallama.
Bayan tafiyar Abid, kusan kwana yayi idanun shi biyu akanta.
Wurin asuba ne yaji tana kuka, ya leka dakin tana barci amma kuka take tana cewa.
"Zaku samu yanci Nahara zata samu yanci. Ku yarda da ni" hannun shi ya kai goshinta, yaji babu zafi sai zufa. A hankali ya shiga tofa mata addu'a.
A hankali kuma ta fara sauke ajiyar zuciya, kafin nan barci yayi gaba da ita, shima jin kamar barci ya fara fisgar shi yasa shi tashi ya koma waje yayi alola sannan ya zo ya gabatar da sallah nafilla, sai da ya idar sannan ya shirya ya nufi masallaci, sai kamshi yake Zubawa, a masalacin bayan sun idar da sallah Sarkin Malamai ya lalle shi kafin ya cewa Abid.
"Abdullahi yana cika kamsuna salawati, haka yana nuna mana cewa shugaban mu na gobe, me yawan Ibada ne kamar Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye." Murmushi Abid yayi ya koma wurin Yarima Shehu ya mika mishi hannu bayan ya riko hannun shi.
"Barka da asuba, Yaya Shehu."
"Barka dai, Abid ya wurin ka da dan uwana"
"Gashi can zaune."
"Madalla, ina fatan bai ce kome ba akan maganar bashi Mulikah da aka yi ko?"
"Ih, gaskiya bai ce ba kuma matsalar shine sun saka Ya Musa a gaba da zancen a dawo da Raudah"
"Bai ce kome ba ko?"
"Ih gaskiya har yanzu bai magana ba."
"Akwai wacce ya nutsu da ita ne?" Yarima Shehu ya tambayi Abid.
"Ih, akwai yarinyar nan Kyautah"
"Yayi kyau, ya kula da ita domin naji ana cewa, Arshan zasu nimawa aurenta, dan haka ka gaya mishi ya kula da ita"
"In sha Allah " haka suka fito masallacin, har suka iso gidan anan Abid yake mishi bayani, ai kuwa yayi shiru sannan ya ce.
"A cigaba da shiri."
Bayan sun gama magana Abid ya tafi ya musu ya shigo, shi kuma lokacin ta tafi dan tafkin wanka. Har su Uwar Bayi ta shigo tare da Ladi da kayan abinci.
Can Aaliyah ma ta shigo, suka kuma gasata sannan aka bata magani ta sha, sai lokacin ta samu bakin magana, ita lallai so take ta wanke kanta. Amma kowannen su Binta yake da idanun, bayan fitar Uwar bayi Aaliyah ta ce ta make cinyarta.
"Shegiya gaya min ya abin yake? Wai da gaske cikin Baffana ne ya zube?"
"Wallahi Fulani Aaliyah karya ne," ta fada kamar zata yi kuka.
"Karyar kaniya, ranar ai kin fito kina ihun baki ga kome ba, yau naji labarin kin yi bari anya Kyautah Baffana baya baki wani abu" rufe mata baki tayi tana faɗin.
"Rantse da abin bauta na ban tab'a yin wani abu, ki dube shi ki dube, ai ruwa ba asa'an kwando bane, kaskantaciyar baiwa mara jin magana ce zata samu dama haka, ai kawai karya tabi ƙwarya"
"Na yarda dake, amma ina fatan bakin mutane ya tabbata a aurar mishi ke domin kun dace ke magana shi kuma baya magana" Mikewa Aaliyah tayi, itama ta fito ta rakata bakin zaure.
Haka zaman su, ya cigaba da kasancewa tana jinya har tsawon sati biyu, kafin ta ware sau biyu Wabi tana zuwa mata, wani zuwan da ta mata Abdullahi baya nan dan haka ta jata suka tafi rafi wanka, tun la'asar har garin ya fara duhu, ganin haka Kyautah ta fito ruwan ta saka kayanta, kawai sai ga Yarima Arshan da Namir, hango ta da suka yi ta gama shiri, yasa suka nufi wurin.
"An gama boye ki? Bari mu ma mu baki abinda ya yake baki"
Ja baya tayi tana faɗin.
"Kar ku tab'a ni, na gaya muku."
Aikuwa Namir da yake cike da haushinta, domin dukar da Abdullahi yayi mishi a gidan Yari, shi kan Arshan bai gama warkewa daga wutar da ta kona shi ba.
Namir ya shiga dukanta, har ta fadi ƙasa.
Fita cikin ruwan Abigail tayi ta saka kayanta ta nufi Arshan.
"Yarima na ya jikinka?"
"Namir ka kyaleta domin wannan yarinyar sunanta ajali idan kasake wani abu ya same ta, Abdullahi ba kashe ka kawai zai yi ba, idan ana bin mutum lahira wallahi sai ya bika"
Takaici yasa ya kuma zabga mata naushi da yasa ta fasa wata irin kara.
Karar ne ya fahimtar da Abdullahi inda take, domin yazo niman ta ne, jikin shi na wani irin rawa suka nufi wurin da Abid, turus yayi ganin yadda suke kokarin cutar da ita.
Sandar shi ya juya sosai, kafin yayi jifa da ita, ai kuwa sai gashi kamar wacce aka rike sandar ya shiga zane su, duk suka watse har Abigail. Zuwa yayi ya d'ago ta tsaye, tana kallon shi yau ya bata tsoro, ja da baya ta fara yi, ya juya a hankali Abid ya tawo ya rike hannunta suka bar wurin, kamar dama jira yake ya dauki sandar shi.
"Abid don Allah kar su cutar da shi"
Jan hannunta yayi suka tafi, koda suka isa gidan, kin zama tayi hankalinta a tashe. Tana leka dakin shi ta ganshi zaune.
koda ya fito bai kula su ba, karshe ita ce ta yi kwanan zaune domin mamaki kamar zai kashe ta dan yariga su dawowa gida, washi gari koda ta farka yana waje yana shan hantsi ganin shi yasata jin nutsuwa a ranta.
Shigowar Sarki Yaki Uzairu yasa ta juyawa, tana gaishe shi.
"Ki riko hannun shi ku zo muje fada" haka kuwa suka nufi fadar, koda suka nufi fadar, Namir yana zaune ga Abid shima zaune, ga kuma Arshan ga Wabi.
Bayan sun zauna aka tambaye su abin da ya faru suka shiga basu labarin abin da ya musu, kallon Abdullahi tayi dariya ya kwace mata ta ce.
"Wannan basamuden da baya ji baya gani, wannan ai kiwo na ne, na rantse da Abin Bautar ku bai cutar da su ba. Domin baya gani!"
"Ke karya kike wallahi shi ne"
"Ranku shi dade, ku yarda da abinda zan fada muku ba shi bane, hala aljanu ne, domin mun dawo mun same shi a dakin shi kwance kamar ba shi muka bari a can ba, amma ai Basamude babu abin da zai iya ko ranar da na watsa mishi ruwan karkashi akan ya zame karshe haka ya bi ta kan shi bai zame ba, ai kuwa ina zuwa na zame kummm, tun lokacin na fahimci Basamude yana da Aljanun taimako, hala sune suka kawo musu farmaki, amma shi ai kiwo na ne babu abin da zai iya ku tambayi Yallabai Abid ma"
"Abid da gaske abin da ya fada haka ne?"
"Eh Alkali, ni daya na tafi niman ta, sannan na same a kwance a bakin rafin kamar an dake ta, bayan nan kuma Abdullahi ya biyo ni, karshe ya dawo gida ya bar mu a can, domin ya rasa sallah magariba "
Juyawa Alkali yayi ya fara musu fada.
"Marasa jin magana kawai" sannan ya sallami su, bayan fitar su, Chiroma ya ce mishi.
"Abdullahi yana aikata abin da yaso fa."
"Ih, kana da hujjar kama shi ne? Kamar yadda kowa yasan abin da ya faru aka rufe