Showing 75001 words to 78000 words out of 105295 words

Chapter 26 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6121

. 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
........Ai kuwa duk wanda yake cikin fada yasan an casu a tsakanin Galadima da Garkuwa, hankalin kowa ya tashi domin basu tab'a ganin abin kunya irin haka ba. Dakyar aka raba su,. Suna huci kamar wasu zakuna domin rayukan su ya b'aci.


***
Watsi take da kome tana bugawa da kasa, kuka take tana birgima kamar wacce aka ce mata Ya Musa da Uwarta sun mutu.
"Meye yan matan suka fini? Meye yasa ba zaka bashi umarnin ya mai da ni ɗakina ba?"
"Akan me zan mishi dole, ke da na miki dolen ba kai ni wurin wasu suka yi ba? Ko ance miki ba a gane banbancin tarbiyya da bambancin soyayya, tarbiyyar Yaran su ne zab'a musu wanda ya dace da su, ko Kyautah tarbiyyar da Addinin ta ya bata kenan kar ta bijirewa manyan mutane, balle ke yar da na haifa, domin haka su Waɗancan hoto ne a wurin Abdullahi yakinin da kishinki ya tsaya akan Kyautah, domin da ita zamu fara gamawa sai ki samu Abdullahi."
"Kamar ya Baban?"
"Kamar yadda ake amfani da kowani damar da ka samu, haka zaki shiga jikin Yar uwar Kyautah. Itama burinku ɗaya amma dole ki danne naki burin domin samun nasara a kansu."
Haka suka gama shirin su akan Wabi, tare da ajiye ta a matsayin makamin da zasu yaki Abdullahi da Kyautah, a bangaren Abdullahi baya ta ya Musa domin baya son ya fara ta kanshi, ai yasan a duniya babu abin da yake so sama da yarshi don haka ya ajiye a ranshi da ita zai buga mishi guduma akan shi. Yadda sai ya girgiza kamar zai yi hauka, sannan ya fadi abin da ya sani ba tare da sanin shi ba.
----
Da yamma likis, Wabi ta shiga wurin Kyautah, ta same ta tana wanke hannu.
"Kaga Gimbiya me ake yi ne?"
"Babu kome kawai ina wanke hannu na ne, da nayi aiki da shi."
"Kyautah da fatan baki manta da alkawarin nahara ba?" Gabanta ne ya fadi ta juya tana kallon Wabi, ajiyar zuciya ta sauke tana goge hannunta.
"Ban manta ba" ta fada a hankali kamar zata yi kuka.
"Tow na dai gaya Miki babu ke babu shi, domin."
"Amma ai kin san ban yi kome ba? Asalima nawa taimako ne me yasa kike son takura min ne?"
Jikin Wabi ne yayi sanyi, kafin ta ce.
"Amma ai alƙawari kika dauka, idan kina son na mutu shi kenan, naga dai baki da kowa sai ni, sai an jima " baki daya ta shiga rud'ani rike hannun Wabi tayi tana faɗin.
"Ki gane wani abu, nahira yasan ba Ni ba ce. Yasan kece domin ya gaya min muna iya tafiya ta inuwar juna da kaddran juna amma bai zama dole kome namu ya zama daya ba. Alƙawari ne na dauka domin ceton rayuwar al'ummar nahara, bayan nan bani da wani buri, nauyin Al'ummar nahara yana wuyana shi yasa Nahira ya bani makarin soyayya yadda ba zan iya manta da alummar Nahara ba."
"Yawwa abin da yasa nake son ji kenan dama kina son shi ne?" Idanunta cike da kwalla, a hankali ta dafe kirjin ta, da yake buga mata tana me kallon Wabi. Girgiza kai tayi hawayen yana zuba mata.
"Bana son shi "
"Yawwa tow kin ga sai an jima, dama Mama Uwa ta aiko ni." Tana gamawa ta juya ta fita, durkusawa Kyautah tayi a wurin ta rushe da kuka, kamar wacce aka mata mutuwa, duk abin da suke yana jin su, domin ya shigo ya same su a dakin girki, sai ya koma ya ji me suke tattaunawa. Lumshe idanun yayi yana mamakin duk rashin jin ta, tasan girman alkawari. Zai ci kaniyar yarinyar ce me kama da tinkiyar nan domin yasan tsaf hanya ake nima domin cutar da su.


Gyaran murya yayi, da sauri ta shiga share Idanunta. Tana me Mikewa. Kallon fuskarta yayi ta sunkuyar da kai, tana kokarin wuce shi ya dawo da ita a hankali ya saka hannun shi a kugunta, kallon kwayar idanunta yake son yi amma fir taki, janyota yayi ya rungume ta. Kwace jikinta tayi ta gudu daki, ta ma rufe kofar yadda ba zai iya shiga ba, ta zauna tare da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta.
Bai bi bayanta ba, dan yasan tana son kadaici don haka ya cigaba da harkan gaban shi amma idanun shi yana kan kofar ta har Abid yazo suka ci abinci.
"Baka bi ta kan Ya Musa ba?"
"Ina sane da shi, motsin shi nake son ji amma yaki motsawa. Kasa Uzairu ya saka idanu akan Yar uwar Kyautah sosai"
"An gama, amma wani abu ya faru ne?"
"Hmm! Akwai wani abin da suke son tayi amma soyayyar da takewa alummar ta yasa zata aikata shi ne suke nuna mata kar ta rab'e ni."
"Idan haka ne, tow dole itama ka motsata yadda zata fitar da abin da yake ranta."
"Akwai wani abin da yake hanata motsawar domin kuwa na same ta tana kuka, abin da na kasa fahimta kukan al'ummar ta ne, ko kukan ce mata da aka yi kar ta rab'e ni ne?"
"Hmm! Tow nayi nan ba da ni ba, wannan Yaren ma'aurata ne, haka kawai ba za a saka ni watsa ruwan sanyi da lafiya ta ba"
Ya tashi ya fita yana dariya, tsaki Abdullahi yayi, ya cigaba da zama har zuwa lokacin sallah, kamar da wasa taci kukan ta ya ishe ta.
A hanyar dawowar shi ya hadu da mutanen gindin bishiyar kukan nan.
"Idan kaje ka tsinka sarkan wuyarta, daga nan ya isa ba sai ka bukaci wani abu ba, su mata kamar wukar fawa suke da wasu matan ake motsa su."
"B'ace min da gani" ya fada yana wucewa kamar bai san da shi yake yi ba, koda ya shiga gidan ya same ta da uwar bayi ta saka mata abinci tana ci sai mita take, bai kalli inda suke ba ya wuce dakin shi.
"Kin yi mishi wani abu ne?"
"Tow uwar bayi me zan mishi, shi kaɗan shima jin haushim kowa yake yi, shekaranjiya da jiya kuka yake ta min me zan mishi?"
"Allah ya shirya ki" tura baki tayi ta cigaba da cin abincin ta,har ta gama Uwar bayi ta tattara ta bar gidan, domin idan yana kwanakin hailarta bata cika son cin abinci ba, shi yasa uwar bayi ke hada mata da hadi na musamman, kuma tana son Abdullahin ya gane tana da angurya ne.
Uwar bayi na fita ta wuce dakin ta, tayi wanka ta sauya kayan ta. Sannan tazo ta kwanta. Kamar zai shigo ya share ta. Duk da Uwar bayi ta gaya masa cewa bata wuce kwanaki uku zuwa hudu. Dan haka ya wuce ɗakinta tana kwance kamar me barci ta saka wani tasa ta rufe aci balbal din da ya cika haske.
"Hmm" ya mata gyaran murya kafin ya shiga da sallama, tashi tayi zaune tana kallon shi.
"Jibi zan yi aure har mata biyu"
Janye tasar tayi tana kallon shi, kafin ta ce mishi.
"Shi kenan" ta juya tana me kwanciyar ta.
"Akwai abin da kike bukata ne?"
A shake ta ce mishi.
"Babu"
"Tow" ya juya ya fita abin shi, yasan dole gobe ya tsayar da magana daya, dan haka ya gaya mata, kasa barci tayi tana mamaki dama aure zai kara? Mtseeeeeew, can kuma ta kara tashi zaune tayi kwafa.
Kusan raba dare tayi bata rintsa ba, sai tsaki take koda lokacin da barci ya dauke ta da mafarkin yayi aure tayi, tana ta kuka ya juya mata baya. Ai kuwa ta farka ta zaune lokacin dare yayi sosai, dan haka ta mike ta wuce dakin shi yana zauna a saman buzu. Kwanciya tayi a dakin shi tuni barci ya koma gaba da ita. Bayan ya idar da sallah ya juya yana kallonta.
"Rigima da kanta".ya furta a hankali sannan ya cigaba da ibadar shi har asuba tayi, ya nufi masallaci. Bai shigo gidan ba, sai da rana ta fito sannan ya shigo ya samu har ta tashi,.ita da uwar bayi suna aiki sai kananun magana take, ita ba zata yarda ba.
Yana shigowa ta kalle shi, ta ce.
"Basamude kar ka ga jiya ka min zancen zaka yi aure na ce shi kenan, don haka ba shi kenan ba, na rantse da Abin bauta ba zan yarda ba"
Maketa Uwar bayi tayi, ta kuwa tura baki tana faɗin.
"Ai gaskiya na gaya mishi, ba zan yarda ba."
Wuce ta yayi yana faɗin.
"Idan baki yarda ba, kizo daki ko gaya min"
"Tow kuwa gani nan a bayan ka na rantse da Nahara ba yarda zan yi ba" ta bi bayan shi uwar bayi da Ladi suka cigaba da aikin su, domin ba zasu iya shiriritan Kyautah ba.
"Haka kawai sai kace daga sama na fado, bayan auren kazar da aka mi..."
"Wayo Yesu Almasihu me ceto" ta fada da mugun karfi zata fice da dakin ya fisgota, ya haɗa ta da jikin shi.
"Na shiga uku na lalace, Uwar Bayi! Wayyo na shiga uku. Sauke ni kamar yadda ka ɗauke ni na rantse da Nahara ban ga kome ba,.kai na rantse da Allahn ku ban ga kome ba." Ta fada tana ihu, tare da turo shi. Tsabar dariya yana cin shi kamar cikin shi zai yi ciwo.
"Kin ce baki yarda nayi aure ba ko?"
"Ni din banza ni din wofi, kai har sai ka biye Ni" ta fada Jikinta na rawa.
"Abdullahi!" Ta kira sunan shi a hankali. Idanunta cike da kwalla.
"Maciji ne a wurin cinyata?" Bakin shi ya kai kunnenta ya radd'a mata abin da yake yawo, wani irin ajiyar zuciya ta ja ta fada a kirjin shi, d'ago kanta yayi yaga yadda hawaye yake zuba daga idanunta. Sarkan wuyarta ya cire ya maida mata wani irin shi sak, sannan ya gyara mata ƙwanciya a kirjin shi, sumbatar goshinta yayi tana bashi tausayi, sai dai yadda zuciyarta yake cike da farin ciki da damuwa yana damun shi.
"Kyautah ba zan yi aure dan na kuntatta miki ba, zan yi ne domin wani dalili. Ki tsaya a gefe na, ni kuma zan tsaya miki har abada."
Sannan ya kwantar da ita, ya wuce ban daki, ya sheka wanka ya fito ya shirya yana kallonta, sai da ya gama ya shafa mata ruwan sanyi, sannan ya zuba mata ido. Domin farkawa take son yi.
A hankali ta bude idanunta tana kallon shi.
_Ba maciji ba ne, jikina ne_
Fasa ihu tayi, zata sauka a gadon ya riko hannunta, yana me janyota jikin shi.
"Don soyayyar ka da Abin bautar ku, kar ka saka min shi bana son ganin shi."
Rufe mata baki yayi da hannun shi,.ya ce mata.
"Ki nutsu gobe aure zan yi!"
"Ni dai na yarda kayi auren ka, amma kar ka nuna min shi" ta fada tana kuka.
Murmushi yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Dole na nuna miki shi wata rana,.domin dai abokin hiranki ne"
"Na hada ka da Allah ku"
"Naji matsoraciya babu abin da zan miki, muje kici abinci"
"A'a zan tafi abina"
"Tow muje" kafin ya ce zai kara wani abu, tuni ta tsufa a dakinta ai wajen da abincin da bata ci ba kenan, domin ita idan ta tuna Wabi da Arshan da irin matan da yayi ta kashewa sai taji tsigar jikinta ya mike, ai kuwa ta fashe da kuka. Baki daya zuciyarta da kwalkwalarta sun kasa manta kome sai ma kara tuno mata abin da ya faru yake.....
*Kuyi hakuri don Allah in sha Allah, daga gobe zan cigaba da yadda nake baku satin nan abubuwa sun sha kaina ne*
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
lbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
............ Zuba mishi ido suka yi suna jiran ikon Allah, can Abdullahi ya ce su tafi kawai, aka bar su a kwance. Kamar yadda Abdullahi ya gayawa musu kar su yi nisa, haka suka koma can nesa da gidan suka tsaya, suna labe Ya Musa yazo ya gama labewar shi da duba duben wake ganin shi, sannan ya shiga dakin, ya jima kafin ya fita yana me sauri ya bar gidan maganin. Bayan nan basu kuma tsinkewa ba sai da suka hango wasu mutane dauke da makamai sun nufi gidan.
"Wai meke faruwa ne Ya Haruna?"
"Tarko Yarima Abdullahi ya danna musu da Ya Musa, shi kuma dake jahili ne ya faɗa. Allah ya kiyashe mu da muguwar tunani"
Haka suka zuba musu idanu, kafin me maganin Ya ce.
"Ya Haruna babu abin da zai same su? Tsoro nake ji kar su mutu"
"Ba zasu mutu ba, domin su din dashen Allah ne" suna tsaye a nan wurin fada me mugun karfi ya kwace daga cikin gidan, wanda kana daga waje zaka fahimci abin da yake faruwa, haka kuma kana jiyo ihun kartin maza, haka suka yi ta fafatawa har zuwa lokacin da dakin yayi shiru.
Janyo kujera Abid yayi ya ajiyewa Abdullahi ya zauna yana kallon Barde.
"Nayi fatar idan na ganka na kashe ka, domin ba zan daina hango abin da ka min ba. Tow idan na dauki fansa kamar ban san dalilin da yasa nake raye ba."
Abdullahi ya fada yana goge hannun shi da ya b'aci da jini.
Barde yana durkushe akan gwiwar shi, jini yana zuba a kowacce kusurwa ta jikin shi.
"Yaro yaro ne, har yau Yara kuke shi yasa baku gane tarkon da aka danna muku ba." Dariya suka fashe da shi har suna tafawa.
"Tow mun ji mu yara ne, shi yasa gaka a gaban mu, yara sun kama katon jarumi. Mu fa da suma muka saka muku tarko, ku kuma da amintaccen mu kuka saka mana, tow fada mana waye Yaro? Kaga ni zan iya saka Abdullahi ya yafe maka amma ba zan tab'a tilasta shi akan kar ya kashe ka ba. Domin kana da rayuwa kana da gobe waye a bayan ku?"
Takaici ne ya kama shi ya kalli hannun shi da suka sare ba zai tab'a amfani da shi ba, sai kafad'ar shi da har lokacin Gatari yake sakale da shi.
"Idan na gaya muku, me zaku iya? Idan na ce muku ga wanda yake shirya kome babu abin da zaku iya"
Kai hannu Abid yayi zai zare gatarin da yake kafad'ar Barde ya ce kyale shi.
"A kai shi dajin kwankwamai a wurga shi idan barde ya mutu, ba su ga gawan shi ba, a haka zasu nime wani ya daura musu aikin su, kaga iyalin shi sun yi asarar ganin gawar shi ma, dan haka maza nemi igiya ka daure mana bakin shi."
"Zan gaya muku"
Ya fad'a yana zare idanu shi, azabar da yake ji ma kawai ya ishe shi, balle kuma sun kai shi wancan dan iskan dajin.
A hankali y fara basu labarin abin da ya faru, da wanda ya sani.
"Alkali da Chiroma sune suka kitsa kome, bayan nan ita kanta Fulani Babba tana da hannu a kashe Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, wanda ta saka Ya Musa yayi ta zuba mishi guba a cikin ruwan shan shi. Garkuwa shi ya kashe Waziri Jafar Abid Noye, da iyalin shi. Ita kanta Mahaifiyar Abdullahi bamu kashe ta ba sai da muka dawo da ita cikin fada, baki daya masu rawanin nan suka yi ta kwanciya da ita na tsawon kwanaki, kafin suka kashe ta inda suka gayawa Duniya ai karuwa ce kai ma shege ne. Sai dai wasu daga cikin mutanen sun manta. Shirin kashe ku da ake da hannun Yarima Shehu domin shima ya fahimci an kashe mahaifiyar shi ce saboda Abdullahi, kiyayyar haka yasa ya kudiri aniyar taimakawa mutanen nan. Bayan nan akwai matan sarki Hayatudeen Abdullahi Noye da bayan Fulani Babba da suke marawa Garkuwa baya sune suka ce ya baka auren Yar shi daga haka abin da na sani umarni ne, Babban abin da yasa aka saka maka guba har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login