Showing 33001 words to 36000 words out of 105295 words

Chapter 12 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6097

naushi gefen abokina shi.
Juyawa yayi yana faɗin.
"Allah ya baka lafiya, Abdullah."
"Mtsew."
Ta ja wani irin tsaki, sannan ta nufi hanyar gida, suna bin bayanta.
Shi bai ga wani abin burgewa a wurin wannan yarinyar me shegen rawan kan ba, amma baki daya Abdullah ya nace ita yake so.
Wai a haka ma dan bai ganta bane, amma shi kyan mace bai d'add'a shi da kasa ba.
Balle Raudah da sam kanta yaƙe hayaki.
Daga nesa ya hango Ya Musa da Ya Haruna.
SHEKARU ASHIRIN DA TAKWAS.
*BAK'AR LARABA*


Bak'ar laraba, ko a ce larabar zubda jinin al'umma noyewa,
"Ya Musa ka bamu Yaron nan, kayi tafiyar ka inda ya maka."
"Barde amana bata ce haka ba, ba zan iya baka Abdullahi ba."
dariya suka yi sannan suka ce mishi.
"Tow ga kan Uwar shi, zaka bamu shi ko sai mun kashe ku baki daya, shima waziri yanzu haka babu labarin shi. Matan ƙabilar Noye sun kasance a karkashin mu, sai yadda muka gadama zamu yi da su, ba iya haka ba muna shirin duk wata mace zamu mai da ita kamar dabobbin mu, mu shiga inda yayi mana."
"Lallai kun yi abin da kuke so, amma ba zama dole ku samu abin da kuke so ba. Har abada zaku cigaba da kasancewa a tsorace har bayyanar gaskiya" Ya Musa ya gaya musu, ganin yadda suke kokarin jifar Abdullahi da gatari yasa dole ya juya suka jife shi da Gatari a kafadar shi, fadawa a ruwan kwankwamai yayi.
Suna fadawa cikin ruwan suka nutse, guguwa ce ta tashi a cikin ruwan me ƙarfin gaske ta haɗa da su, tayi ta gudu a saman ruwan.
Har lokacin yana rungume da Abdullahi.
Watsar da su guguwar tayi a bakin Kogin Numan.
Kasancewar asuba ce babu wanda ya lura, sai da gari ya fara haske aka gansu kwance cikin jini musamman Ya Musa.
Ganin su da shigar Alfarman yasa aka kai su Masarautar Hamma Bachama na huɗu.
Kiran maganin Masarautar, suka fara musu aiki.
Sai dai duk abin da suka gwada akan Abdullahi bai yi aiki ba.
"Ranka ya dad'e! Wannan Yaron al'amarin shi da karfi yake, idan aka ce lallai za a duba shi. Zai bamu sansu wahala, sannan shigar jikin shi ta nuna mana daga wata Alkaryar yake me ɗauke da daraja dan ga tambarin ta. Shi kuma wannan jinyar shi me sauki ne, zan ji da kome."
"Tow a kai su, cikin gida."
Daukar su aka yi, zuwa cikin gidan bangaren bayi, duk da ba wata babba masarauta bace amma suna girmama mulkin su.
Kwanan su biyar, Ya Musa ya farka dake Abdullahi ya riga shi farkawa. Tun kwana biyu da suka wuce.
Kallon Abdullahi yayi, ya gan shi a takure gefe guda.
Shafa kanshi yayi sannan ya tashi duk da yana jin gajiya da ciwo.
Tashi yayi, ya nufi waje da tambaya ya nime wurin sallah. Sannan ya tafi masalaci yayi sallah,.yana idarwa suka dawo anan ya samu an ajiye musu abinci, zama yayi ya bawa Abdullahi, wanda kana kallon shi kaga maraya da yake cikin maraici sosai.
Shafa fuskar shi yayi yana jin hawaye ya zuba mishi, wani irin tausayi Yaron yake bashi.
Domin ko ba a gaya masa ba,.yana bukatar sanin inda Mahaifiyar shi take.
Rike hannun shi yayi, sannan ya ce mishi.
"Mahaifiyarka ta rasu!"
Lumshe manyan idanun shi yayi yana gyada kai, sun koya mishi magana da hannu.
Amma batun mutuwa sai da ya dauki hannun Abdullahi ya saka a wuyar shi ya ja, alamar ta mutu.
Riko hannun Ya Musu yayi yana me lakwasa su, ya ce mishi.
"Amma kashe ta suka yi?"
Shima ya bashi amsar da.
"Ih"
Hawayen da bai zata ba, ya gani daga idanun Abdullahi a hankali yake kuka har jikin shi yana rawa, kuka yake sosai na kewar Innar shi.
Haka Ya Musa, yayi ta aiki da bauta domin kula da Abdullahi.
A haka ya saka Abdullahi a makarantar allo. Lokacin yana da shekaru goma.
Ganin dawainiyar yana mishi yawa, yasa shi samun Hamma Bachama na huɗu.
Ya gaya mishi Abdullahi daga gidan da ya fito, sannan yana niman izini a bashi koda yar karamar fili ne, domin yana matukar jin kunyar yadda Abdullahi yaƙe rayuwa cikin bayi, don Allah idan da hali a nika mishi bautar da yaƙe.
Sannu Darajar mulki da kuma gidan da Abdullahi ya fito, yasa Hamma Bachama ya basu damar zama a rugar jume.
Sai da ya kwashe wata biyar yana musu bukka domin shi yafi yawa a zamanin. Sannan ya kewaye shi da kara, kafin ya samu sauƙin da afuwan rayuwa. A haka yake noma na rani da damina, mutane ma tausayin Abdullahi yasa ake kaunar su, musamman da suka gane cewa shi din bawa ne ga Abdullahi, yasa Jauro Ummaru ya bawa Ya Musa auren yar shi Zainabu wacce suke kiran da Jabu. Da farko taso kin ya Musa sai dai abin a ƙabilar Noye ce, mazan su jarumai ne a cikin turakar su.
Haka yasa ta damke shi da hannu bibbiyu.
Abdullahi yana da shekaru ashirin cif a duniya Allah ya basu cikin Raudah, koda aka haife ta. Sun daura soyayyar ta a saman na kowa, haka shima Abdullahi.
A lokacin Allah ya haɗa Ya Musa da Ya Haruna, a wani cin kasuwa da yazo yi cikin kasuwar Numan.
Ai kuwa ba karamin al'amari bane, bayan gaishe gaishe da suka yi, nan yake tambyar shi.
"A ina kasamo d'a?"
"Abid ne dan ga Wazirin Noye"
"Don Allah"
"Wallahi kuwa! Shine ɗan da muka baro gida amma Mahaifiyar shi ta koma, daga baya naji labarin an kashe su ita da mahaifin shi, amma naki gaya masa."
Shiru suka yi sannan Ya Musa ya ce mishi.
"Da ka gaya mishi, nima Abdullahi yana tare da ni. Amma shi yasan Mahaifiyar shi ta rasu"
"Ayya gashi dama burin Waziri ne had'a su abota kaga kenan ba zan kuma tafiye-tafiyen da nake da shi ba, zan bar shi a wurin ka nima sai na nemi wuri na zauna."
"Shi kenan" haka ajiye maganar, sannan suka cigaba da cin kasuwa ana tashi a kasuwa suka wuce Gida, anan Ya Musa ya gabatar da Ya Haruna da dangantaka tsakanin su da kuma Abid.
Riko hannun Abdullahi Abid yayi ya riƙe, sannan ya fara mishi magana.
*Abid baya ji fa, kuma baya gani, baya magana." Kurawa Abdullahi Idanu yayi sannan ya ce.
"Ya Musa kuma baka nima mishi magani ba? Shi fa sarki ne guda haka Abbana ya gaya min!"
Ya fada da harshen Noye.
"Ina kan nima mishi magani, har yau ba a dace ba ne!"
Kwalla ta cika mishi Idanu.
Haka suka cigaba da abotan su tsawon shekaru goma sha takwas, barci yake raba su.
Haka suka taso, anyi anyi Abid yayi aure ya ce shi bai san da zancen aure ba, sai Abdullahi yayi.
Duk da yan matan da suke masifar kaunar su, amma ya fahimci Abdullahi yana son Raudah, kuma ya kasa fada dan da farko suna tare da Raudah kamar me, su uku duk da ita bata fahimci waye Abdullahi ba, a tunaninta ai Mahaifinta tausayin Abdullahi yaƙe yasa shi rike shi dan nakasar da yake da ita.
Sai ta fahimci, yadda Mahaifinta da Ya Haruna suke bin Abdullahi yayi yawa, ita a duniya bata tab'a jin kaunar shi ba, sai dai abin da ta sani tana kallon shi a matsayin Yayanta, shi yasa da Abid ya gaya mata bukatar Abdullahi, ta rufe idanu ta zage su tass.
Tun daga lokacin Abid ya gaya mishi babu ruwan shi a zancen su, shi kuwa Abdullahi yana ganin ai Ya Musa ya mishi kome, dan haka ya tafi wurin Ya Haruna ya shiga maganar, ai kuwa ya Musa yana dawowa daga lambu ya gaya masa sakon Abdullahi.
Kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan murna, ai kuwa ys gayawa Uwar Raudah wacce suke kira Gwaggo.
"Yanzun kai Malam makaho, bebe, kurma, zamu bawa Yar mu? Gaskiya ba zan iya wannan haukar ba, yarinya tana da manema amma a dauke ta a bawa mara gani!"
Murmusa mata yayi sannan ya ce mata.
"Idan kuma Allah ya nufa ta sanadinta zai samu lafiya fa? Kawai ki musu addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi"
Ai kuwa ta yi shiru, dan haka tayi ta zuga yarta.
.....
A dawo labari.
Har yau Raudah tana nan akan bakarta, wannan ya haifar musu da rashin jituwa da Abid, domin yana ganin rashin sanin waye Abdullahi yasa take musu mishi haka da zata san cewa ko a bayin da zasu gyara turakar shi bata kama kafar su ba, zata shafawa kanta ruwan sanyi.
★†★
*DAHEER*
Tun da tayi wannan mafarkin sai ya zama,ko gyangyadi take mutanen Nahara suke yawo a idanunta.
Haka take aikinta wanda jin dadin haka yasa Fure cewa ta zauna a bangaren duk ranar Juma'a ta koma bangaren su.
Ranar wata talata, tana tsaye har Fulani Aliyah ta gama shiri, kanta a sunkuye.
"Yau zaki taka min har babban dakin taro,Fulani Babba ta shirya mana liyafan da take duk bayan wata uku!"
"Tow ranki shi dad'e" Kyautah ta fada tana me satar kallon Fulani Aliyah.
"Nayi kyau kuwa?"
"Ba laifi ai kamar daren goma sha huɗu."
"Kai kyautah, gasu can ki dauka shi zaki saka muje an jima."
"Godiya nake, haske maganin duhu."
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
......MAI RABON SHAN DUKA.....


Murmusa mata tayi, sannan ta kai hannu zata cire mata dan shunin da aka makala mata a gefen fuska, da sauri ta rike hannun Fulani Aliyah.
"Me yasa?"
"Haka aka haife ni." Kallonta Aliyah tayi sannan ta ce mata.
"Tow kar ki manta da shirin tafiya babu bata lokaci."
"Na ji" ta fada tana kwashe kayan da yake zube a saman gadon fulani Aliyah.
Tana gamawa ta fita daga dakin.
---
*SHIRAYI*
Shi ne shashin da aka warewa Arshan, tun jiya Namir ya sanar da shi batun liyafar da Fulani Babba ta shirya amma ya kwanta a kunnen shi.
Arshan ba mata shi bane domin ba za a kira shi matashin ba, dan akalla ya haura shekaru talatin da tara zuwa arba'in, sai dai irin siririn mazan nan ne, dan kyau yana da kyau dan yana daga cikin mazan masarautar da ke tara gashi ya sauka har kafadar shi., sai dai matsalar wani irin fitinannen mutum ne. Wanda aka gina rayuwar shi da lalata Mata da yan mata.
Izuwa yanzu yan matan masarautar Deehar sune kawai aka haramtawa Arshan amma ko a hanya yaga mace sai yasa an dauko mishi ita.
Arshan ya kai ko mace ya gani da ciki matukar tayi mishi tow sai ya bita.
Bayan haka yan mata kuwa, ana kawo mishi biyar kullum yana tarayya da ita, da yawan waɗanda ake kawo mishi, saboda karfin bukata wasu mutuwa suke yi.
Yau ma yan matan da aka kawo daga Nahara guda uku biyu kuma asalin bayin cikin masarautar ne.
Sai kuka suke, yana cikin ruwan wankar shi da take cikin turakar shi, kallon su yayi, sannan ya lumshe idanun shi, a rayuwar shi yana masifar kaunar yaji kukan mace tana ihu da kuka, dan farin ciki yake haifar mishi.
Cak daya daga cikin kartin da suke kula da haka,.suka dauki budurwa daya suka shiga cire mata kayan ta, sannan suka sakata a cikin ruwan.
Mikewa tayi zata fita.
Ya saka mata kafa, ta zube kanta ya bugu da karfen jikin kwarmin. Bai damu da halin da take ciki ba, ya mike da ita cak, ya cillata gadon dan bai damu da duk yadda zata kasance da ita ba. Shi kawai bukatar shi ta biya.
Fita aka yi da sauran yan matan, aka sake mishi labulayen turakar.
Yana haurawa gadon.
Ya durfaffi yarinyar nan, da tun cillata cikin ruwan nan kanta ya bugu, ta fita hayacinta.
Saka ta da yayi da jaraba, yasa yarinyar nan ta mutu yana can yana biyan buƙatar shi. Sai da ya gama sannan ya gane abin da ya faru, kuma sai da Fulani da Galadima suka mishi fada a can karon, watsar da hannu shi yayi yana tsaki.
Sannan ya koma cikin ruwan yayi wanka, ya fito ya shirya tsaf kamar babu abin da ya faru, a bakin kofar ya hadu da Namir.
"Yarima ban ji kukan Yarinyar ba?"
Cigaba yayi da tafiyar shi, yana kallon yadda kowa yake zubewa a gaban shi.
"Ta mutu" a firgice Namir ya kalle shi cikin tsananin tsoro da fargaba.
"Kace ta mutu?"
"Mtsew!" Ya ja tsaki, alamar bai damu ba.
Da sauri Namir ya sanar da dogaran da suke kofar dakin, suka tabbatar kafin su dawo kome ya kammala.
Yana gamawa da su, takaici ya ishe shi ya sami Arshan ɗin.
"Kai dai wannan ka zama ɗan taure, wallahi ka zama abin da ka zama sai Addu'a. Me kake son a cewa Fulani da Baba Galadima? Yanzu haka Allah kaɗai yasan abin da Sarkin gida zai faɗa."
Watsar da hannun shi yayi yana takun shi cikin izza da jin bai yi kome ba.
---
Sun gama shiri ta kalli Easter, murmushi tayi sannan ta dauki wani ƙaramin mayafi, ta daura mata a saman hancinta, ya rage mata idanunta da goshinta kawai a fili, sannan suka nufi wurin taron.
Koda suka isa Easter tana baya, ita kuma tana gaba.
Suna isa kofar Mulikah da Radiah suna isowa, kallon Aliyah suka yi cikin kishi da mugun nufi, suka sakarwa junan su dariya, don haka suka nufi cikin dakin taron.
Kasancewar Easther tana bayan Aliyah tana kallon yadda suke kokarin taka alkyabar Aliyah. Domin an shi kamar zubin jelar dawisu ne.
Asalima daga masarautar Kano aka kawo mata, lokacin da Umman su taje bakin diyoyin Sarkin Kano.
Kafin su zauna sai da Mulikah ta taka Alkyabar, ai kuwa Aliyah ta tafi zata fadi, Easter ta rikota.
"Sannu"
"Yawwa Kyautah na gode"
"Ba kome"
Isa gaban Fulani Babba suka yi, suka gaisheta.
Sannan suka juya zasu nufi mazaunan su, Arshan ya isa, kafin su ce sun yi wata wata, Easter ta sakawa Mulikah kafa, ai kuwa ta zube akan kayan marmarin da aka shirya a wurin zaman su.
Da sauri ta cire kafarta, kamar ba ita ce tayi ta'asar ba.
Wannan abin ya ba Arshan Mamaki, domin akan idanun shi tayi wannan aika-aikan.
Tasowa Dogarai da Bayi suka yi, aka shiga d'aga Mulikah.
"Sannu" juyawa tayi taga ko inda take Easter bata kalla ba, sai ma gyarawa Aliyah Alkyabarta zama take, kamar bata san me ya faru ba.
Takaici ya rufe ta, ta ture hannun Namir da ya kai zai rikota.
"Dalla sake ni, ku kama min baiwar Aliyah ita ce ta saka min kafa na fadi"
Kura mata ido dogarai suka yi, ganin Arshan ya nad'e hannu a kirji. Yana al'ajabin irin wannan yanayin, yarinya karama har ta ita irin wannan aikin.
"Kin ga tashi tuntube kika ci fa." Namir ya fada yana kallon ta.
"Wallahi kafa ta saka min,ku kama min ita. Fulani wallahi kafa yarinyar can ta saka min, kuma ga haka"
"Tuntube kika ci fa"
Radiah ta fada cikin jin haushi, dan ta gaji da tsayuwar.
Lokaci guda suka ki yarda akan kafa Easter ta saka mata, a hankali ya taka wurin su Easter ya kura mata ido.
Yana kallon yadda take Zubawa Aliyah ruwa a kofi. Tana gamawa ta d'ago kanta, suka yi Idanu biyu.
Shi dabi'ar shi ce, ko Yan uwan shi na masarautar basu mishi kallon ido cikin ido, hannu ya kai zai cire Mayafin fuskartar tayi baya.
Sake kai hannu yayi ta rike hannun da nata.
Saukar bulala a jikinta yasa ta zubewa akan gwiwar ta.
"Ku fitar da ita, na ganta nima "
Ya furta yana niman juyawa zai fita.
"Kasa a yanke min kaina, ayi" rufe mata baki Aliyah tai, tana girgiza mata kai.
"Don Allah Kyautah."
Zubewa Aliyah tayi a gaban shi cikin rawan murya ta ce.
"Tuba muke Baffa, don Allah ayi mata afuwa bakuwa ce daga garin Nahara bata san kome akan Deehar ba, nayi alƙawarin haka ba zai kuma faruwa ba."
"Wallahi ba za a yafe mata ba, taci zarafina " Mulikah ta fada tana matsar kwalla,
"Shi kenan, amma a hukunta ta."
Abin tausayi haka aka fita da Easter, ai kuwa suna fita, da Allah ya bata sa'a, ta gantsarawa wanda ya rike ta cizo, ai kuwa ta arta a guje.
Koda suka bita babu wanda ya iya kamata.


A cikin wurin Liyafar kuwa, sai da aka fara cin abincin. Sarkin Yaki tare da Galadima suka shigo, nufar wurin Fulani Babba suka yi, sannan suka gaya mata abin da ya faru. Kallon Arshan yayi idanun shi yana kan wata baiwa da take zuba mishi ruwa a kofin azurfa.
Yanayin shi ya sauya tun da yayi tozali da kirjinta, yaji kamar ya ɗauke ta a wurin.
Mikewa Fulani Babba tayi, suka bi bayan ta. Kiran Namir Sarkin Yaki yayi.
"Ka tawo da Yarima Arshan"
"Tow Uzairu" haka ya wuce, shima ya koma wurin Arshan.
"Sai da na gaya maka, amma baka ji ba sai ka tashi muje"
"Ina fa?"
"Fulani Babba tana kira"
"Gaskiya tsohuwar nan tana takura min me nayi da zafi zata hana ni sakewa?"
Ya fada yana jifa da kofin hannun shi.
Haka suka fita daga dakin taron.
Suka nufi cikin gidan, a hanyar su ta shiga cikin gidan, da mugun gudu ta zo ta bangaje shi, rikota yayi suka fadi tare.
Wani lokacin ƙaddara tana iya sabunta kanta, kusan abin da ya faru kenan.
Kallon idanun juna suka yi, yana rike da kugunta.
"Ke!" Namir ya daka mata tsawa,
Tashi tayi tana zare idanu.
Kafin ta kuma juyawa zata bar wurin ya riko hannunta.
"Me yasa?"
"Kaga Sarkin Mata saketa muje"
Nufarta Dogarai suka yi, ya d'aga musu hannu.
Dole suka kyale ta,
Shi kuma ya juya ya bar wurin, har sun yi nisa ya kuma juyawa, itama shi take kallo, gatsina mishi fuska tayi tana murguda baki.
Banbarakwai abin yazo mishi, saboda ba a tab'a mishi haka ba, kusan reni ne amma kuma sai ya ai ba wani abu bane.
"Uwa wancan yarinyar ba yar mijin ki ba ce?" Wata baiwa ta tambaye ta.
"Ita ce mana,"
"Kan uban can, shi ne tayi sa'ar faduwa a jikin Yarimar Deehar? Lallai wannan yarinyar Aljana ce, ta kafa tarihin da ba zai tab'a gogewa ba."
"Kina nufin shi ne yarima me jiran gado?"
"In Sha Allah, sarkin sarakuna na gobe." Wani irin bakin ciki ne ya kama Mama Uwa, tana ji tana gani yarta da suka zo ta zama baiwa a wani wurin, sai tayi kwana biyu bata saka ta a idanu ba. Duk burinta nason zama wata abar kyau ga kowa amma haka bai samu ba.
"Uwa kamar ranki ya sosu "
"A'a kawai dai yarinyar ce na tsane ta, domin sanadinta muka rasa muhallin mu, da zan samu hanyar da zan sabunta rayuwar ta sai nayi "
"Kina nufin hallakata"
"A'a babu kome kawai na tsane ta ne"
"Kin ga akwai Jarma yana nan wurin burga yana kula da harkokin dabobbi, idan kina son ya miki aikin da zata zama bita can zai yi amma shi gaskiya Aikin shi sai yayi tarayya da mace, shi ya min aikin da Delu take tare sa Galadima,"
Wato Yarta,
"Sabuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login