Showing 78001 words to 81000 words out of 105295 words

Chapter 27 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6125

Kyautah taci domin a fahimci kana gani ko baka gani, ai makantarka ba haihuwar ka aka yi da shi ba. Ita kuma kyautah taci dama an gaya musu kar su cutar da ita domin ana son ta kwanta da Arshan yadda zai samu mulki sai gashi ta koma jikinka, Babban tashin hankalin shi ne gubar da taci zai yi tasiri ne idan ta fahimci kanta wanda babu wani maganin shi sai mutuwa, kai ma haka aka so ya faru da kai sai ya fada kanka. Ba mamaki daga lokacin da ta fahimci kanta kuka fahimci juna zata iya mutuwa sai dai akwai tsarin da ya hana abin tasiri a jikinta. Kowa ka gani a cikin masarautar nan kashe ka zai yi. Ko a waje ko a cikin gidan kowa jiran Umarni yake ya kashe ka. Nasha mamakin yadda har kuka yarda da Uwar bayi domin itama tsohuwar sad'akar sarki Hayatudeen Abdullahi Noye ce, kuma tsohuwar budurwan Ya Musa ce. Sai dai wannan izuwa yanzu na fahimci ta sauya daga abin da tayi niyya da zata kashe ku da tuni ta kashe ku."
Zare gatarin Abdullahi yayi, ya fara sarar Barde.
"Me muka muku?" Yake fada yana sarar Barde har ya cire kan shi daga gangan jikin shi yana kuka, rungumar juna suka yi shi da Abid suna kuka domin kukan da suke yafi gaban yadda ake tsammanin.


Haka su Ya Haruna suka iso, suka fara tattara gawarwarkin tare da su Uzairu. Ganin yadda suke kuka kamar ran su zai fita aka kuma rasa me basu hakuri yasa baki daya jikin su Uzairu yayi sanyi, a cikin daren aka raka har gidajen su, lokacin da ya shiga cikin dakin ta tana barci, zama yayi a gabanta ya fashe da kuka sosai, shashekar kukan shi ya farka da ita. A firgice ta zuba mishi ido, tashi tayi zaune ta janyo shi jikin ta, kanshi yana kirjinta tana shafa kan shi. A lokacin ya samu damar yin kukan shi na tsawon shekaru ashirin da takwas, bayan ya rungume ta. Shafa bayan shi take a hankali har ya daina kukan sai a ajiyar zuciya yake, kusan daren suna tare, yaki barin jikinta shi kan shi yana bukatar inda zai samu nutsuwa. Sai wuraren asuba ya janye jikin shi, kallon shi tayi tana faɗin.
"Ina zaka?" Dakyar ya hadiye yawun bakin shi da ya mishi daci ya ce mata.
"Zan yi sallah ne"
"Tow" ta koma ta kwanta, har ya fita bata kuma jin motsin shi ba, sai can ta fito zuwa dakin shi. Yana sallah sai kuka yake, zama tayi a gefen shi baki daya tausayi yake bata, tana zaune har lokacin sallah yayi, ya sallame ya zuba mata idanu.
"Abdul" ta kira sunan shi, murmushi yayi mata yana cewa.
"Meye hukuncin wanda ya kashe maka Mahaifiyar ka da Mahaifinka?"
"Basu bukatar yafiya koda a wurin UBANGIJI ne, sun cancanci hukunci da azaba" shafa kanta yayi yana faɗin.
"Na gode"
Sannan ya mike zai tafi masalaci, ya juya yana tambayar ta.
"Ya jikin ki ?"
"Da sauki bayan tafiya kayi ka bar ni, ni daya sai da aka saka ka kuka kazo" ta fada tana tura mishi bakin ta, kallonta yayi a sanyayye ya tako tare da d'ago ta yana kallon idanunta da suke cike da kwalla.
"Ya isa bari na tafi sallah, daga yau ke zaki na kome naki ban yarda da mutanen da suke cikin fadar nan ba har waɗanda suke wajen fadar."
"Har uwar bayi?"
"Ih, har ita."
"Tow shi kenan "
"Akwai barci a idanun ki, kwanta ki huta."
"Jiya hanci kome ba, har wannan kazar idan na gama zan gyara gidan sai na dumama "
Gyada mata kai yayi yana faɗin.
"Kin kyauta, kuma dama sunanki ne"
Haka ya barta tana kallon shi har ya bar dakin, da gidan baki daya ƙwanciya tayi tana sauke ajiyar zuciya, zubur ta mike ta shiga wanka. Ta gyara jikinta, ta saka kaya tazo zata kwanta a dakinta kenan ta samu Uwar bayi tana jiranta.
"Ya Abdullahi ya kwana? Sannan yana lafiya?"
"Lafiyar shi lau, ya tafi sallah ne" hadiye yawu tayi ganin Ladi zata fara aiki ta ce mata.
"Ya ce na gaya muku." Tayi kasa da kanta, tana matse hannunta.
"Me Abdullahi ya ce?"
Kasa magana tayi tana kallon Uwar bayi.
"Ina jin ki" baya Kyautah tayi hawaye ba zuba mata, jikinta ya dauki rawa.
"Ya ce kar na kuma zuwa ko?" Fashewa da kuka Kyautah tayi, tana gyada kanta.
Hawaye ne ya zubo mata tana kara kallon Kyautah, tana jin kamar zuciyarta zata fashe.
Ita din sad'akar sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, amma budurwar Ya Musa ce wacce suka yi alkawarin aure , dare daya Ubanta ya bada ita ga sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Wanda ya haifarwa Ya Musa tsanar Sarki Hayatudeen. Har yanzu lokacin da Fulani Babba ta gayawa Sarki Hayatudeen ai budurwar YaMusa ce, domin itama tunda aka kaita ga sarki Hayatudeen, fir taki yarda da shi. A lokacin da yaji labarin sai ran shi yq ɓaci yayiwa Ya Musa fada akan me bai gaya mishi ba. Gashi ko da yace ya Musa ya aure ta ba zai yiwu ba. Dan haka ya tura ta shashin bayi na har abada. Domin ko da taje gidan su ba zata samu me aurenta ba, har izuwa yau bata tab'a kusantar namiji ba.
Bayan kamo Kubrah, ita ce tayi ta jinyarta bayan su Galadima da su garkuwa sun wukalantatta, haka tayi ta kula da ita, a ranar da za a kashe Kubrah ta bata kome da kome nata ta ce mata.
"Uwar bayi, nasan Abdullahi basu mutu ba, koda zai dawo don Allah ki taya ni, nima mishi mace kamila da zai samu nutsuwa da ita, wacce duniya a abin cikinta ba zai dame ta ba. Ga wadannan a bawa matar shi, sakona ne ya bi min hakkina."


Ita kuwa ta ce mata .
"Abdullahi makiyin shi ne zai rene shi, ni ba zan ƙarbi rikon amanar shi ba, amma idan kina bawa Allah rikon shi zai kare shi. Domin Ya Musa makiyin Uban Abdullahi ne, kuma shi da kan shi ya kashe Ubana Abdullahi kinga kenan, Makiyi zai reni makiyi, ke Kubrah duk abin da kika ga ya faru shirin har da Ya Musa a cikin shi don haka zan jira dawowar shi, kuma zan shiga tsakanin su da Ya Musa, zan rike Abdullahi kamar nawa."


Gyada kai tayi, sannan aka sakata a gaba. Kwarin gwiwar da ta gani a idanun kubrah ya ruguza duk wani abinda ya shiryawa zuri'ar Hayatudeen, tawakallin da ta gani yasa ta ji a ranta zata yafe ta rungume Abdullahi domin amanar Mahaifiyar shi. Hawaye ne ya zubo mata sannan ta kalli Kyautah.
"Shi kenan" ta juya ta fita tana share kwalla.
Tana shiga dakin ta ta fara ciro kayan da Kubrah ta bata, sannan ta kuma dauka ta nufi gidan, tana shigowa Abdullahi yana shigowa shi da Abid.
"Me kika zo yi?"
Murmushin yake tayi sannan ta ce mishi.
"Na kawo sakon Kubrah ne" ta mika mishi kunshin hannunta.
"Ka bawa matar ka, shi ne sakonta."
Amsa yayi sannan ya kalleta, kasa hakuri Abid yayi ya bude.
Abin wuyar zinari da azurfa, sai munduwr azurfa da abin wuyar murzani.
Kallonta suka yi, kafin Abid ya ce.
"Meye ne shirinki akan mu?"
"Kwarin gwiwa da yarda da D'anta zai dawo da na gani a idanun Matar da za a kashe bayan." Hawaye ne ya zuba daga idanunta.
"Naga yarda da kai, naga yarda da Allah zai bi maka hakkin ka. Ita ce ta roke ni na ajiye wannan, sannan na tayaka zaben macen da zata zauna da kai. Sai gashi a ruwan sanyi ka zab'awa kanka macen da ta dace. Nasan zuwa yanzu ka fara daukar haske hakkinka ne kula da yarinyar da bata san kome ba, gubar da yake jikinta imma a samu makarin shi nan gaba, imma yazo da sanadinta domin shi aka yi ta bawa Mahaifin ka har ya bar duniya ta hanyar Amintaccen bawan shi...500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambulbishirinku mata masu Duniya mata masu Abin Atata dake nake hajiya idan kinaso kayan gyara yan gaske tau kina da damar ziyar (Dakin Amarya )domin dawo da martabarki kimarki a gurin megida har ma da Aboka huldarki A dakin maryan nane zaki samu 1, garin sabaya me kyau haka kuma Akwai garin lakuse wanda zai gyaraki ciki da wajenki ki koma tamkar halwa jikinki yi luwai luwai fatarki ta goge haka nonuwanki zasu ciko suyi cirko cirko suna tsokanar megida matarda zatayi yaye da yan mata ma duk suna iya Amfani dashi . 2, A Dakin amarya munada mayyukan kamshi da gyaran jiki haka kuma muntanadi mayyukan gyaran gashi akwai hadin buzaye mesa gashi taushi laushi da kuma santsi 3 hakama bangaren kayan mata suma ba'a barmu a baya muna hadin kaya masu inganci akwai hadin kinfi Amarya akwai zumar karya gado akwai hadin sabuzu kuwa akwai hadin dan bagigita akwai kalolin kaza dakuma tsimi da kuma kalolin san matse domin karin bayani sai ku tuntubi wanam Lambar 0805 086 4183 kokuma sakon karta kwana ta wanam lambar a man hajar WhatsApp 08164714675 kokuma saadatusadik@gamil.com sayen nagari maida kudi gida muna aikewa da sako gari gari kuma inganci kayanmu ke sayar dasu da ikon Allah ku garzayo dakin amarya muna nam garin sokoto
...........Haka ya fito ya ci abinci ya koshi, sannan ya wuce Fada yana Kyautah ga tsiwa ga tsoro, a duk lokacin da ya tuno kwayar idanunta, murmushi yayi me sanyi yadda taki bude idanun kamar taga wani abin tsoro, halin Kyautah sai shi.
---
Sai da ta daina jin motsin shi sannan ta fito, ta zabgawa kofar dakin shi harara tana tura baki.
"Kuma wallahi ni ba haka nake ba." Ta fada idanunta yana cika da kwalla.
Ita gani take kamar bata da kamun kai yasa shi mata wannan abin, baki daya a rayuwarta gani take duk abin da zai mata ai yarjejeniya ce kuma ance babu wannan abin.
Baki daya haka ta tsangwami kanta da duk abin da zata yi, dakyar take hadiye Abincin karshe da bata iya ci ba kenan, ta shiga daki tayi ta rusa kuka.
Shi kuwa yana can fada, Manyan sun zuba mishi ido kamar zasu cinye shi kowa jiran Abinda zai fada yake. Kuma suna fatan ya amsa bukatar su.
"Kasan dai kai ne sarki me jiran gado?"
Ya gyada kai kamar yaro karami, saboda maganar da Galadima yayi mishi.
"Yawwa tow kasan dai nan gaba bikin baka sarauta zaa yi?"
"Ih, amma ni bana son sarautar" ya fada yana bata fuska kamar dai yaro karamin, yana kallon Abid.
"Baba tunda baya so kar a mishi dole"
"Kai D'a nan, ka daina fadar haka ba girmanka bane kana matsayin wazirinsa kar ka gurbata mishi tunani"
"Tow ai gashi nan Allah ya baku sa'a!" Ya fada yana kallon su.
"Yawwa tow dan haka zamu bashi"
"Ya gayawa muku kuwa bai da lafiyar?" Inji Abid yana rufe fuskar shi da hannu alamar kunya,
"Kai Abidu! Ai ko ina magani take zan saka a nimo a fadin duniyar nan, kar ka kuma fadar haka gobe ne fa za a daura auren idan ya kasance aka ji labarin nan fa?"
Ya juya ga Abdullahi yana faɗin.
"Kar ka damu, kome zai wuce ai ba a kanka aka fara ba, dan haka ba za a kare akan ka ba. Aure kuma nasa Radiah zata zauna da kai haka."


Burin Waziri bai wuce Abdullahi ya auri yar shi ba, yadda idan ta shiga zata yi waje da Kyautah, kafin Abdullahi ya gama nazarin wani abu Arshan ya maye gurbin shi a wurin Kyautah yadda shi kenan babu wanda zai kawo tunanin wani abu, sai kawai a bawa Arshan mulki kafin su ankara.
Wannan shine shirin su da Fulani Babba.
"Ka daina abu kamar mara hankali, Abdullahi yana da ikon auren abin da yayi mishi, dan haka babu matsawa Abdullahi Noye cikakken mutum ne da yake tsaye akan ra'ayin shi kuma mutum ne da ya gaji magana daya dan haka ka daina harban iska." Inji Hamid Garkuwa.
Kallon juna suka yi shi da Abid, kafin ya ce.
"Na amince zan aure su" yana fadar haka suka mike daga wurin zaman su, daga nan basu tsaya ba, domin tun kafin su shiga fadar suka fada a basu Dawakai, fita suka yi daga wajen masarautar.
"Kana ganin haka shine mafi?"
"Bana tunanin akwai matsala." Ya fadawa Abid haka yana kad'a linzamin dokin.
"Idan kuma idan kuma su tunanin su Kyautah ce."
"Zan kashe ko waye, idan ta kama na shafe Deehar zan yi domin nayi alƙawarin tsaya mata, kuma zan bata duk wani kariya domin cimma manufar ta shi yasa ban nime, wani abu daga gare ta ba, domin bana son tayi tunanin wani abu nake nima daga gare ta shi yasa na kulla yarjejeniyar aurenta."


"Kuma sai yanzu na fahimci wani abu." Abid ya fada yana kad'a linzamin dokin shi, bin shi Abdullahi yayi da gudu, yana tambayar shi.
"Me ka fahimta?"
"Idan waziri ya baka yar shi yake buƙatar tayi yaki ba, shi kan shi zai yi wani yaki ne domin wani abu da ban sani ba, Hamid Garkuwa yana son ya baka yar shi ne, domin kusancin mu kar nazo hukunta shi kaki magana bayan shima yana da na shi laifin"
"Lallai Allah yayi hikima da ya bar min kai a gefe na, don Allah taya aka yi ban san ina zaune da ma'abocin hikima haka ba?"
Cikin jin dadi da jin yayi abin kirki ya ce.
"Ai baka da damuwa tunda ina gefenka, kawai ka cigaba da girmama Ni"
"Banza kawai, yar wannan nazarin naka ce zaka fara huta min hanci " Abdullahi ya fada yana hararan shi.
"Ai shi kenan, da akwai wani abin da nayi maka, tun haduwar mu da Kyautah na shiga bibiyar mutanen da suka san Mahaifinta, daga cikin su har da tsoho Damina wannan badukun da yake bakin kasuwa, ya bani labarin mahaifinta shi ne mutumin da yayiwa Abbana jagora har zuwa Nahara, Abba ya haɗa shi da Ya Haruna ne,.shi kuma Ya Haruna ya hada ni da shi. Abin da na samu shine tun kafin haduwar mu da ita Allah ya ƙaddara zata zama a gefen ka, sai dai kuma al'amarin akwai tashin hankali domin ta amsa zata sadaukar da rayuwarta domin Mutanen ta, shi yasa lokacin da kazo min da zancen kana son auren ta, domin Arshan ya kyale ta nace maka ka shigo da zancen zaka basu yanci,"
Gyada mishi kai yayi, yana jin faduwar gaba da abin da Abid zai gaya mishi.
"Kasan mu musulmai an san mu da karban ƙaddara, Kyautah ƙaddara ce a gare ka, bama wannan ba na saka an binciko min mahaifiyar ta tun daga nan har kasar Habasha. Kuma suma yan babban gida ne Mahaifiyar ta. "
"Abid akwai sauran maganar da baka karasa ba"
Kallon juna suka yi, Abdullahi ya sauka akan dokin ya zubawa Abid idanu.
"Babu wani abin da na boye maka."
Ya fada domin bai san yadda zai gaya mishi Kyautah mutuwa zata yi ba, bai san haukr da Abdullahi zai yi ba, dan haka ya janye gaya mishi wannan gaskiyar, a garin binciken asalinta da karban maganin da zata sha Badukun ya gaya mishi, ita din sadaukarwa ce ga al'ummar Nahara, sannan gubar jikinta yana cinta a hankali karfi sarkan wuyarta yasa ba jin ciwon sosai.
"Gaya min!" Ya daka mishi tsawa, idanun shi a warwaje.
"Mutuwa zata yi" wani irin cakumar wuyar shi Abdullahi yayi.
"Zan kashe ka!"
"Idan har zata rayu, wallahi na amince na mutu domin ta rayu, soyayyar da nake maka babu algus kai ne baka sani ba, wannan sarkan wuyarta shi ya hana gubar tasiri." Bai san lokacin da ya juya da gudu ba ya hau dokin ya koma Deehar a guje, shima bin bayan shi yayi a guje. Har cikin masarautar suka yi ta gudu, yana isa harabar shi gidan ya dirka akan dokin, ya nufi cikin gidan da gudu. Tana kwance a dakin shi rike da cikinta idanunta cike da kwalla. Ciwon ciki take tana juya kanta.
Yana shiga ya zube a gabanta, ya rungume ta.
"Kiyi hakuri " ya furta a hankali, bude baki tayi zata yi magana gudan jini ya cika bakinta, mai da kai tayi gefe ta zubar.
"Abdul cikina" wurin kayan shi ya shiga duba abin wuyarta, dakyar ya samu abin wuyar ya ɓalle na wuyar ya saka mata, sannan ya dauke ta suna fita Abid ya taso. Suka nufi gidan me magani da ita, yana rike da hannun ta.
Haka suka yi ta ratsa mutane, har suka isa gidan, yana kallon yadda take kokarin bude idanunta.
"Abdullahi!"
"Na'am Kyautah"
"Kayi min alkawarin Nahara zata samu yanci"
"Na miki, ki min alkawarin zaki bani kyawawan Yara irinki?" Kura mishi idanu tayi hawaye na zuba mata.
"Ina son Al'ummar nahara"
"Ina son Yara daga gare ki"
"Ni sadaukarwa ce a gare su."
"Ni kuma Amanar ki ne" ya shafi awarwaron Innar shi da yake hannunta.
Haɗa maganin Me magani yayi ya fara kokarin dura mata, ta sha dakyar. Sannan ta koma ta kwanta, gyatsa tayi tare da aman jini kore shar, me wari rungume ta yayi yana shafa bayanta har barci ya dauke ta. Yana rike da ita.
"Ranka shi dade, zaku iya tafiya."
Daukar ta yayi a hannun, suka koma ko kafin su isa labarin ya karad'e masarautar cewa ai Kyautah bata da lafiya, yayin da wasu suka yi tsammanin ko wani abu ne ya faru da ita, a bangaren Ya Musa da ya samu labarin dama yasan za ayi haka, gubar da ya fito hannun shi, da ita ya kashe Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye, kuma yau ita ce take cin Kyautah yayi mamakin yadda aka yi bata mutu ba, domin yasan adadin lissafin gubar wata guda ne, domin yadda ya saka Mama Uwa zuba mata.


"Sannun ku, ya jikin nata?"
"Da sauki ya Musa." Haka ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login