Showing 66001 words to 69000 words out of 105295 words
Chapter 23 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
a cikin dokokin ka?"
"Idan bai miki ba, nafasa yawwa dole idan na bukaci mu kwana wuri ɗaya kizo 8" baki daya sai da ya saka Kyautah uku yadda ta rasa gane meke damun ta, kome ke faruwa.
"A rude ta ce! Gaskiya ba zan iya yarda ka cinye min fuska ba, dan haka ban da shi." Ta fada tana shafa wuyarta.
Kura mata idanu yayi, so yake a zaman su Kyautah ta fada mahaukaciyar soyayyar shi yadda ba zata iya rayuwa babu shi a tare da ita ba, koda zata rayu yana cikin rayuwar ta kamar kaska. Ya fara kai matakin da ba zai iya kare kan shi daga gare ta ba, suna isa Deehar a daura musu aure kawai idan ba haka ba, wallahi zai far mata.
Haka suka isa bakin gaɓɓar Deehar ya ce mata.
"Saura ki gayawa wani nafasa"
"Tow"
Kallon Abid yayi da mamaki ya ce mishi.
"Kai yaƙi ake ne?"
"Tura su aka yi su kashe ku! Ni kuwa ja musu layi zuwa barzahu "
"Allah ya biyaka "
"Amin Ya Allah, da fatan ka samu wani abu a can?" Girgiza kai yayi yana kallon shi, kafin ya riko hannunta ta hauro sama ganin Abid da makamai yasa ta yin baya, tsantsin ya kwashe ta, ta fada cikin ruwa mugun nutsewa tayi. Domin tana fadawa wani abu ya riko kafarta,dukkan su biyu suka bi bayan ta. Kamshin jinin da ya shiga ruwan ne ya janyo mugayen kifayen ruwa suka kawo farmaki a cikin su har da kada.
Kafin kace me, ya nutsa da ita cikin ruwan yana son yayi loma daya da ita, Allah ya kawo maza, rufa mishi da sara Abdullahi yayi tsoro da fargaba suka cika idanunta,.dama haka yake bai da imani, ji yadda yake sarar kada kamar ya samu dan Adam. Ai kuwa ta shiga shan ruwa sai da cikinki yayi tirtsitsi. Ta koma zata zube Abid ya amshi saran shi kuma ya rikota, suka dawo bakin ruwan.
Kallon Al'ummar bakin wurin yayi sun yi cirko-cirko, ya fito da ita yayi wasu dattijan mata suka amshe ta, a wurin suka baza mayafi aka kareta, sannan suka duba kafar, inda hakorin kadar ya shiga suka shiga saka mata magani suna duba karya. Bayan sun gama lokacin Abid ya fito musu da kadar ya cilla waje.
"Sun gama mu"
Gyara mata rufa suka yi, ya dauke ta.
"Allah ya baka nasara, ita ce Fulani Babban mu?" Murmushi me ɗauke da alamar Ih yayi musu, ai kuwa suka shiga rangad'a gud'a sosai da sosai.
Haka suka kama hanya, suna kallon juna shi da Abid.
"Ban gane baka samu kome ba ita fa?"
"Ta amince zata aure ne amma zan nima musu yanci su koma nahara"
"Me yasa baka gaya kana sonta ba, rayuwar ka, kake son karewa da ita ba?"
"Babu wannan zancen zamu taimaki juna ne, idan taimaka min zan tsaya mata"
"Amma kayi kuskure Abdullahi ka rasa wani irin hukunci zaka yanke sai na wannan Abin bayan kana kaunarta? Tow idan suka samu yanci tafiya xata yi?"
"Shi ne ban sani ba"
"Mtseeeeeew" ya wuce abin shi yana watsa hannu shi bai tab'a ganin mara aiki da damar shi kamar Abdullahi ba, haka suka isa gida. Koda suka shiga sun same mutane a gidan Raudah da YaMusa da Mahaifiyarta, ganin yadda yake dauke da Kyautah yasa jikin Raudah yayi sanyi. Haka ya wuce da ita ɗaya ya kwantar da ita, duk da an gyara gidan.
Rike hannun shi tayi tana firgita, shafa kanta yayi yana faɗin.
"Kwanta babu abinda zai same ki" kamar idanunta biyu ta shagwab'e fuska sannan ta cigaba da barci. Murmushi yayi yana shafa kanta, gani yake kamar gobe ba zata yi ba.
Sannan ya wuce wurin kayan shi ya dauka ya fita yana kallon Abid da yake tsaye yana kallon karamar wasan kwaikwayon da Raudah take yi.
Wai kuka take kamar an zage ta,rab'e baki yayi ya wuce ya sauya kayan shi, ya fito yana cewa.
"Lafiya?"
Ya zauna yana fuskarta Ya Musa da ita Raudah da Mahaifayar ta.
"Ya Abdullahi don Allah ka dawo da ni ɗakina zan bika zan bi Allah "
Kallon juna suka yi da Abid wanda yake cike tam kamar zai make yar banza.
"Ya Musa kai ne ka turo ta?"
"Ko daya ni asalima na kawo ta ne domin tana taya Kyautah aiyukan gida nan "
"Tow, ita Kyautah ta gaya maka bata da lafiyar yin aikin ne?"
"Abid " Abdullahi ya d'aga mishi hannu,
"Zan duba al'amarin, ta je"
Ai kuwa ta kalle shi tana faɗin.
"Na gode, in sha Allah ka maida ni ɗakina ba zan tab'a bijire maka ba."
"Kodan yana gani,yana ji ga shi ana hasashen Deehar ta sa shi baki isa ki bijire ba, Haukar banza kawai." Ya juya ya fita. Dariya ya bawa Abdullahi, abin da ya fahimta ba iya haka ba, har da kishi yake taya Kyautah.
Haka Iyayen suka fita ita kuma ta zauna, tana son taya shi hira.
"Kin san me? Tashi ki tafi bana son Kyautah ya farka ta ganki"
"Wani irin matsayi take da shi ne?"
"Gobe in sha Allah zaki ji."
Tashi tayi tana jin kamar ta shiga dakin da Kyautah take ta shake ta.
***
A bakin jama'a labarin auren Kyautah da Abdullahi ya fara yawo, har cikin masarautar bayan sallah isha, suna zaune garkuwa ya zo har gidan shi.
"Barka da hutawa, yau naji labarin wai zaka auri baiwar ka?"
"Ih, tow ban san labarin ba sai yanzu."
"Haba nima nace haka, tow na baka Mulikah ka dai sani "
"Anya zan amshi Yarka kuwa? Domin kuwa gani nake da ita ma za a iya kashe domin naga kowa yunkurin son mulki yake "
"Habawa ai babu wannan zancen " yadda yake lallaba Abdullahi sai ya baka dariya shi kuwa ya gama shirinsa.
Bayan tafiyar shi Abid yazo ya labarta, sannan ya ce mishi.
"Ban yarda da kowa ba, a cikin su har da Yarima Shehu."
"Nima na jima da sanin haka,.kuma na jima ina zargin shi."
"Domin haka auren kyautah kamar farmaki muka kai musu, zasu sha jinin jikin su, sannan haka zai fito da nufin su. Daga baya ka saka ido kaga yadda abin zai karke domin Ya Musa shine Allah sarki a cikin su."
Murmushi Abid yayi yana faɗin.
"Mugun kwaro"
Shafa kan shi yayi yana kallon kofar dakin tana tsaye, yau tasha barci yanzu ma ba mamaki yunwa ce ta tashe ta.
"Malam tashi ka tafi sai gobe ka dawo"
"Dan iska,.ka dai yi a hankali gobe zata zama ta ka, idan rashin hakuri ya ja maka kai ka sani"
"Ni ba kai ba ne me gudun budurwa domin kar ya turmushe ta."
"Banza kawai domin na tsira da mutunci na ne, amma in sha Allah zan cinye bakinta naji yadda ke ji,"
"Da dai kayi hakuri "
"Ko daya banza "
Haka ya fita yana yana mita, tashi yayi ya nufe ta. Riko hannunta yayi suka zauna.
"Basamude, ka kashe kadar ne?"
"Hmm! Jinki zan bar wani abin da zai kai miki farmaki ne? Ai ko bana gani ba zan bar wani abu ya same ki ba."
"Ka bani tsoro ne"
Shafa kanta yayi ya shiga zuba mata abinci tana ci tana kallon shi. Kamar zata yi kuka haka take jin abincin sam ba dad'i.
"Abdul!"
Zuba mata ido yayi ganin yadda take kokarin mishi kuka.
"Tow meye?"
"Basamude ai Abdul".hannun shi ya kai fuskar ta,.ya ce mata.
"Kirani basamude zan amsa miki"
"Yanzu haka zan yi auren ban gayawa Mama Uwa da Wabi ba?....
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga bank
#Mai_Dambu
........ Haka suka shigo cikin masarautar, sai bin su ake da idanun, domin babu wanda ya isa ya tunkare su musamman Abid da aka ga takobin hannun shi tsirara. Shi daya ya shiga gidan Abid ya wuce nasu domin tunda suka dawo a gidan Mahaifin shi yake duk da babu kowa sai masu mishi hidima, yana shigo ba da jimawa ba, Aaliyah ta kawo mishi abinci. Baya son yadda take shige mishi duk da ba karamin kai zuciya nesa yake yi akan akan ta ba. Haka yasa tana kawo mishi abinci ya wani b'ata rai. Har zata fita ya ce mishi.
"Baffa nayi maka laifi ne?" Dauke kai yayi yana faɗin.
"Bana son kina zuwa nan ne ke daya, domin idan mace da namiji suka kebe na ukun su Shaidan ne"
Sake baki tayi tana kallon shi kafin ta ce mishi.
"Baffa Abdullahi fa da yake tare da Kyautah fa"
Takowa yayi gabanta, sannan ya ce mata.
"Abdullahi nayi imani da Allah ko mace ta kwanta a gaban shi babu kaya zai tsallketa ya wuce, Ni kuwa bani da tabbacin nan gaba ba zan iya rungumar ki ba, kin gane"
"Na fahimta" ta fada tana ja da baya, mutum ne a tsaye kamar an dasa shi da kaɗan Abdullahi ya fishi kiba da tsawo, dan ma suna ganniyar samartaka su ne.
........
Duk abin da ya biyo baya, tsaftaciyyar kulawa ce daga Abdullahi, domin ya hanata fita ko ina, ita kuwa kunyar abinda ya faru ya hanata sakewa. Domin duk abinda yaƙe mata ba a dadin rai yake mata bai fasa ba, sai dai yawan fada da hantara yasa ta bala'in kame kanta, domin ya zama wani masifaffe kamar dama can jira yake.
Kwanan su biyar da faruwar haka, aka bukaci Abdullahi ya zo fada shi da Abid. Dake labarin lafiyar shi ya bazu duk inda ya wuce nuna shi ake ana cewa ashe dama ba makaho bane. Har suka isa fadar, niman wuri yayi ya zauna Abid ya zauna a kusa da shi.
Shiru Fadar yayi, Galadima da ya gama cika yana batsewa ya ce mishi.
"Waye ya aike ku, gandun dajin firto kashe mutanen wurin?" Kallon juna suka yi kafin Abid ya saka hannu a bakin shi yana faɗin.
"Baba Galadima akwai dan uwanka ne a cikin su? Domin dai babu wani daga cikin kabilar Hausa a cikin su kuma ba Noyawa bane,.balle a ce mun ci zarafin al'umma"
"Kaiii!" Chiroma ya daka mishi tsawa.
"A fada kake"
"Kaiii Dattijo! Ya kasa da muryan Abid Jafar Abid Noye ne a gabanka, da ga waziri Jafar Abid Noye. Yi kasa da muryan ka. Domin tarihi baya shafewa sai an samu masu cikon shi maza yi kasa da hannun ka" kamar wanda aka bashi umarni yayi kasa da hannun shi.
"Kai Zaki kayi sanyi mana, yan fashi ne mun kashe su, akwai me hujjar kama mu? Lokacin da aka shiga dakin Sarki Hayatudeen ana zuba mishi guba a cikin ruwan shan sa, tare da Maganin shi akwai hujjar kama masu aikata haka? Ko saka wasu su kashe Kubrah akwai Hujjar kama wadanda suka yi haka? Ni yanzu bata ku nake ba, ina da uzuri idan na yawaita surutu kaina ciwo yake, kar a kuma kirana fada idan ba wani abu me karfi bane domin sai na tsinke makogaron dan aikan."
Mikewa suka yi a fadar zasu fita, Garkuwa ya ce.
"Samari kunyi abin da ya dace. Mun gode sosai "
Murmushi Abid yayi ya kalli Abdullahi suka, wuce abin su kamar babu abin da ya faru, tun daga ranar dayawan mutanen fada jikin su yayi sanyi domin lura da suka yi da Yaran sun cika zafin kai. Fitowa tayi tana kallon yadda yake fama da takuba, a ranta ta ce .
"Yakusashe kana fita zai kama huci kamar zaki"
Ta wuce tana tura baki, shi kan bai san yadda zai yi da kyautah ba. Da yamma can Ya Musa suka iso da iyalin shi, tunda suka shigo ya samu labarin hakan. Yana zaune Mulikah ta kuma kawo mishi ziyara, sai wani walkiya take tana ɗaukar idanu, kallo daya yayi mata ya cigaba da abin da yake.
"Ranka shi dade!"
Isowar Raudah yayi daidai kawo mishi dafaffiyar madara da Kyautah tayi, tsayawa suka yi suna kallon juna dukkan su uku, tab'e baki Kyautah tayi ta ce mish.
"Basamude ga madaran"
Amsa Raudah tayi tana cewa.
"Ya Abdullahi nayi kewar ka" ta ajiye mishi.
"Ki kawo min wani" ya fada yana kallon Kyautah!"
"Wannan fa" ta fada tana nuna mishi, wani irin kallo yayi mata, bata san lokacin da ta juya ba, kamar zata yi kuka haka ta wuce su tana jin kamar ta make shi.
"Yarima Abdullahi, Abbana ya ce yana son ganin ka?" Kamar bai ji ta ba, haka ya cigaba da abin da yake.
"Ya Abdullahi" itama shiru ya mata,
Cikin kisisina Mulikah ta ce mishi.
"Idan Yarima ya shirya gobe zamu fita rangadi"
"Zan duba" wani irin dadi ne ya lullube ta, ta shiga jan shi da hira.
"Ko zan dauki wannan madaran?"
"Hm" ya fada yana kallon kofar dakin girkin, ai kuwa can ta fito idanunta cike da kwalla, domin dakyar wutar ta kama, hawaye ne ya gangaro ya diga a cikin madaran, dauke kai yayi yana mamakin yadda bai mata kome ba take kuka, ita kuwa Kyautah aazabar wura wutar ce ta ishe ta. Tana isowa Raudah ta kai hannu zata amshi tiren ta kauce. Saka mata kafa tayi baki daya madarar da tiren suka tafi can zasu zube, ya tare ta.
"Ki kula da kanku" ya fada yana amsar tiren da madarar.
"Sannun ince baki ji ciwo ba?" Ya tambaye ta cikin kulawa,
"A'a" ta fada a shake, domin burinta ta mike shi kuma ya kara matseta a jikin shi.
Yana lura da yadda jikin Raudah yake rawa, haka ma Mulikah ita kanta jikinta ya mutu, wannan abin da Abdullahi yayi ko ba a fada maka ba, kasan baya ta su, domin mantawa yayi da suna wurin. Tashi tayi zubur sakamakon gyaran muryar Abid, ta kalli Raudah ido cikin ido ta ce mata..
"Wannan ya zama na karshe a tsakanin mu, kika sake min haka sai na tsagalgala namar ki, hmm" ta mata gatsine.
"Ke kin san ni wacece mishi?"
"Ke da shi ne kashin awaki karewar kusanci na dai gaya Miki"
"Ya Abdullahi kaji baiwar ka tana gaya min magana bata san ni matar ka bace."
"Da ba!" Abid ya bata amsa,
"Yarima Abid kai ne a gidan?" Ta tambaye shi tana mikewa.
"Ih, ya kwana biyu."
"Alhamdulillahi, har zaki tafi?"
"Ih, ina rokon alfarman a bani aron Yarima Abdullahi mu fita rangadi " kallon shi yayi kafin ya mai da idanun shi kanta.
"Abdullahi din ne sai a hankali, abubuwa sun sha kan shi, amma idan ya samu sarari zai raka ki"
"Godiya nake, na bar ku lafiya "
"Mun muma haka"
Haka ta fita ya rage Raudah, tana zaune sai raba idanu take, kamar wacce aka mata karya.
"Abdullahi!"
"Hmm!"
"Abid don Allah ka bashi hakuri kome ya wuce." Raudah ta fada kamar zata yi kuka.
"Tow Abdullahi kaji dai itama ta ce kome ya wuce."
"Ka dauki kayan Kyautah ka kai shago a mata irin su, kamar goma ko sama da haka"
"Ban gane ba"
"Zaka fahimta"
"Tow saurayin kwaila"
Murmushi yayi yana shafa kan shi, sunan ya burge shi kuma ya bashi dariya.
"Hmm!"
"Don Allah Ya Abdullahi kayi hakuri!"
"Abid zoka fita da ita " ya fada yana barin wurin. Zubewa tayi a gaban shi.
"Don Allah kayi hakuri wallahi ina sonka"
"Kina son mulki da ji da gani da magana dai ba dai Abdullahi makaho kike so ba."
"Basamude!" Tarrr yaji kiran a tsakiyar kan shi.
Zuba mata ido yayi, ta ce mishi.
"Ina son zuwa Nahara " ta fada tana cizon bakin ta.
"Yaushe zaki?" Abid ya tambaye ta,
"Shi na tambaya" ta fada idanunta cike da kwalla, shi sai yanzu ya fahimci wato Kyautah irin shagwababbun matan nan ne wanda kome zasu fada maka ko zasu tambaye ka da kuka ko rikici suke fadar shi. Hadiye yawun bakin shi yayi yana kallon bakinta da ya jike.
"Yaushe kike son zuwa can?"
Ya tambaye ta cikin kulawa.
"Ni Ko yanzu"
Dariya Abid yayi sannan ya ce mata.
"Kwaila ba dai yau ba" hawayen rikici ne ya kuma zubo mata.
"Shirya muje" ya faɗa.
"Abid yamma tayi fa, dare ya karato a hakura sai gobe mana"
"Wuce ina jiran ki"
Tunda ya fadi haka, Abid yasan ya yanke abinda ya yi niyya ne.
Can kuwa sai gata ta shirya tsaf, shiga dakin shi yayi ya ciro wani mayafi ya lullube ta da shi.
"Kar na kuma ganin ki, babu mayafi kin ji" murmushi tayi tana gyad'a mishi kai, haka suka fito tare da Abid shi ya tsaya a kasuwa Raudah ta wuce masaukin su, tana kuka ta zube a gaban Abbanta.
"Ita ce Kyautah?"
"Taci sunanta ai, tunda gashi ta tafi da ruhin shi. Abin da naso ki samu kenan, abin da naso ya zama Mallakar ki kenan, idan Abdullahi yana tare akwai gaskiyar da koda ya fito zai rufe idanun shi ya kauda kai domin zaman ku na har abada ne da zuri'a a tsakanin ku, amma kika shure kafa kika kai karar mu gaban Hamma Bachama."
"Abba ina son shi wallahi"
"Hmm! Abdullahi yayi miki nisa Yar nan, sai dai dole zai mai dake dakin ki amma ba soyayyar Abdullahi ba. Domin ba zaki samu ba."
"Mai gida ina ga da tayi hakuri domin ba awa namiji auren dole "
" Zan yi kuma zan fara akan ta, domin kare kaina da Laifina dole Abdullahi ya amshi Yar da zan bashi a karo na biyu, ai ba cewa yayi baya sonta ba, shi da kan shi ya bukaci yana sonta da haka zai dawo da ita."
-----
Gidan Hamid Garkuwa.
"Abba kana ganin zai soni kuwa? Yarinyar da take mishi hidima, ta gama da shi fa wallahi baki daya bai da nutsuwa sai nata, faduwa tazo yi ya tare ta kamar wata matar shi!"
"Dole yq aure ki, dole na kare kaina da auren ki a gare shi, duk abin da za'a yi a watan bawa zan bashi aurenki domin ta hana ne zan tsira da rayuwata, kar ki damu da baiwar ki damu da Yar Ya Musa Raudah domin faffatawar daga kanta za a fara....
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
........... Intermission
Kallon ta yayi na wani lokaci, ya ma rasa ta cewa kawai murmushi yayi sannan ya