Showing 69001 words to 72000 words out of 105295 words
Chapter 24 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt
ce mata.
"Shi kenan zaki gan su, bayan nan akwai wani abu?"
"Kayi min alkawarin babu abin da zaka min? Kuma ba zaka raba ni da su ba." Kura mata idanu yayi yana son Yan uwanta dayawa bayan sun din kashe ta suke son yi.
"Nayi alƙawarin amma matukar suka cutar dake ba zan iya dakatar da kaina akan su ba."
"Na yafe musu tun kafin su cutar dani" ta fada tana kallon shi.
"Ni bana yafewa munafiki amma ina yafewa makiyi. Idan wani abu ya biyo baya ba zan yafe musu ba." Kallon shi tayi yadda ya tsatsarta da idanun ya sata sunkuyar da kanta.
"Na amince, amma ina niman Alfarman duk lokacin da suka yi laifin ka sanar min zan baka hakuri sannan zan baka damar ka hukunta ni, su din kamar nauyi na ne"
Shafa kanta yayi yana faɗin.
"Da kowa kamar ki yake, da babu sauran abokan gaba da munafukai"
"Bai zama dole kowa yaso ka ba, amma wajibi ne kai ka so kowa"shafa kanta yayi yana faɗin.
"Yau ne ranar ki ta kashe anan."
"Ina zan tafi?"
"Zaki koma wancan bangaren ne, bangaren da Mahaifiyta ta rayu kafin rasuwar ta"
"Ayya na zata a nan zan zauna"
"A'a ba zaki zauna a nan ba"
"Abdul" ta kira sunan shi a hankali,
"Na'am"
"Kayi min alkawarin ba zaka tab'a kyamar addinina ba" murmushi yayi ya shafi fuskarta.
"Me kike so bayan shi"
"Yan uwana"
"An gama Easter" da sauri ta kalle shi, sumbatar goshinta yayi yana faɗin.
"Ba zaki tab'a kuka domin Ni ba, amma qaddara idan tazo haka dole mu karbe ta."
Gyada mishi kai tayi tana rike hannun shi. Kusan wannan daren yafi kowani dare daraja da muhimmanci a gare su, dan sun yiwa juna alkawarin zama da juna tare da amana, tasan a da can Abdullahi yana d'ago mata kafa. Hamma tayi tana gyara ƙwanciyar ta.
"Basamude"
"Na'am!"
"Ban iya girki ba"
"Zan koya muyi tare"
"Basamude!"
"Na'am"
"Kar ka gaji da hakuri da ni"
Jan numfashi yayi sannan ya ce mata.
"Zan iya jure zama dake sama da zama da kowa, ke da Abid zan zauna da ku domin Allah zan zauna da ku domin kaunar da nake muku"
Jin tana sauke numfashi ya tabbatar mishi da cewa tayi barci, ya gyara mata kwanciya a zauren ya sakata a gaba yana kallonta.
Da asuba sai da ya biya wurin Uwar bayi, ya gaya mata abin da yake shirin yi. Wayyo Allah kamar ta goya shi. Haka ya ya tafi ya saka Ladi a gaba suka nufi sashinsa tana ta barci har da rufe ta yayi. Jan mayanin Uwar bayi tayi ya tashe ta.
"Maza tashi"
"Barci nake ji"
"Maza tashi na ce kafin a daura auren kina barci asarar.
Tashi tayi zaune tana kallon su, sa taji abun wani irin yanayi mara iyaka, a can masalaci kuwa shammatar kowa Abdullahi yayi, shi da Abid da Ya Haruna, aka daura auren shi bayan an idar sallah asuba, kuma dan batalikin nan ya saka fuska kamar bashi ba, ya hana kowa magana. Kallon shi Garkuwa da Ya Musa suke, idan da wani zai gaya musu shirin shi da sun dakatar kai,auren shi da kyautah kamar a ce dirar aradu ne domin ya girgiza zukatan su.
"Tow sati me zuwa za a daura auren ka da Rahdia"
"A'a sai dai Mulikah domin ita ce Baba Hamidu ya bani ita tun ba yau ita kyautah kuma ita ce zabina."
"Hmm! Raudah fa?" Tsaki Galadima yayi yana faɗin.
"Akwai wacce ta fi kowa asara irin Yarka ce? Ta samu dama ta sake. Abdullahi na gaya maka auren ka da Radhia babu fashi "
"Tow Galadima ka dai san ba ayi wa namiji auren dole" inji Garkuwa da karen shi ta kama kura, a zabure Galadima ya mike kamar zai rufe shi da duka, Abdullahi ganin ya gwara kansu, ya tashi shi da Abid suna dariya suka bar musu masalacin, kafin kace me an fara buga ganguna da algaitu. Tun kafin ya isa gidan Magajiya ta ce a gaya mishi ya turo amarya wurinta, bawan Allah nan yayi mirsisis ya ce baya buƙatar kowa akan Matar shi yasan halin gidan su yanzu a jefe mishi matar shi.
Kamar dirar mikiya haka Mama Uwa da Wabi tare da Sabuwa suka ji labarin daurin auren kuka Wabi ta saka.
"Duk yadda aka yi asiri irin na Kiristoci ta mishi ya aure ta, ba sonta yake ba."
"Kwarai Wabi kowa yasan ai ya gama da ita kuka ba naki bane share idanun ki,.dole ki Abdullahi ya zama naki."
Wasa wasa suka hargitsa kansu, kowa a cikin masarautar mamakin wannan auren daga dama ba labari.
***
Farfasa kayan shi yake yana ihu, tare da cewa.
"Kyautah tawa ce"
"Kome zaka yi zaka yi sai dai kayi amma Kyautah kan kasan Matar Abdullahi ce,.idan ka kuskura kayi shirme mutuwa zaka yi" Namir ya gaya mishi .
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Auren Abdullahi da Kyautah, zaburar makiya yayi domin ta ko ina kowa yana shan alwashin matukar yana raye Abdullahi da Kyautah ba zasu zauna a wuri guda ba. Yayinda Uban gayya ya shirya tsaf domin kare rayuwar Kyautah.
Can wurin la'asar Uwar bayi ta kira Mama Uwa da Wabi, su kebe domin ganawa.
"Auren cin amana ko Kyautah? Bayan kin san cewa ke din Sadaukarwa ce ga nahara, hankalin ki ya kwanta dama kun saba da kwakule juna sai ku cigaba tunda ga damar haka ya samu, wacce bata san ciwon kanta ba. Mama uwa tashi mu tafi ba zan tab'a barin ku , ku samu zaman lafiya ba matukar ina raye wato dan nayi mu'amala da Arshan shi ne bari ki auri Abdullahi tow kiji da kyau wata sati za a aura mishi Mulikah."
Duk da sun hanata, magana haka suka gama cin zarafin ta kamar yadda yayi musu, sannan Mama Uwa ta ce.
"Duk abin da ya miki ko rike hannun ki yayi, tow ki gaya min zan turo baiwar da zata na gayawa Wabi."
"A'a Mama Uwa sai dai na shigo a matsayin baiwar domin kin san kanta rawa yake idan ba ina ganin su ba, ba zata shiga hankalinta ba. "
"Kin ji dai sai ki gaya mishi Wabi tana cikin masu miki hidima"
"Tow"
Bayan tafiyar su, ta share Idanunta sai ga Raudah ta shigo har dakin.
"Arniya mara addini, bayan maguzanci bai isa ba sai da kika mishi asiri irin naku na arna ki sani Abdullahi nawa ne ko zaki mutu sai na dawo wurin shi, jaka karuwa waye bai san abin da kika yi a masarautar nan ba."
"Ban cika damuwa da haushin mahaukacin kare ba,.nafi damuwa da munmunin kare me bakin baki" Kyautah ta gaya mata haka,
"Ke ni kike gayawa magana?"
"Hala ke kanwar gyatuma ta ce da ba zan gaya miki magana ba, lokacin da kika ce baki yin shi kin zata kowa sakarai ne? Ai ke da Abdullahi nan gani nan bari dumammen mayya "
Kan Kyautah tayi ita kuwa ta fashe da dariya tana faɗin.
"Ai ko mi lalacewar masa tafi kashin shanu, haka kome kankantarta gawan giwa tafi kwando goma, Malama fita karki lalata min daren farkona " ta nuna mata, cikin takaici ya juya a bakin kofar ta hadu da Abdullahi da Abid.
"Abdullahi meye Arniyar nan ta fini?"
"Gudun duniya da kwadayin abin cikin ta, ta aure ne bawai dan na isa ba, ta aure ni ba dan na kai ta aure ni ba,.ta aure ni ne domin ta taimaka min bata aure ni dan wani abin burgewa ba, asalima samun mace irinta da zata aure ka zuciyarta babu algus ai duniya ce "
"Abid don Allah kace ya dawo dani "
"Lokacin da kika kai shi wurin Hamma bachama kin manta akwai ranar yau ne? Ko Abdullahi yace sai dawo dake sai na yake shi ya daina numfashi." Ya gaya mata, karshen kiyayyar da yake mata kenan, ya kara da cewa.
"Shi din mallakin Easter Jacob ne"
Tana ji tana gani bayi mata suka yi waje da ita, tana zaune a tsakiyar shimfidar sai kallon shi take.
"Basamude kayi kyau"
Dariya Abid ya kunshe, lallai fa Basamude.
Haka ya musu nasiha, tare da musu bankwana yana fita Uwar bayi ta shigo da katon tire da kayan abinci, godiya yayi mata, ita kuma ta musu bankwana.
Ganin kaza yasa Kyautah sauka a gadon, ta cire lullubin ta fara ci tana girgiza kai.
"Ta nan kika fi auki " sai da taci har ya ishe ta, kafin ta shiga ban daki tayi wanka, kamar yadda Uwar bayi ta ce mata, tana fitowa ta samu baya dakin. Kwanciya tayi bayan ta saka wata doguwar riga. Tuni barci yayi gaba da ita.
---
Cikin dare taji kamar an takurata a wuri guda, dakyar take jan numfashi. Bude idanu tayi tana kallon shi. Wato da ta buga wani tsalle ta dirka can gefe guda Jikinta yana rawa.
"*Ƙarki sake ya kwanta dake wuri ɗaya, domin ke sadaukarwar Nahara ne, idan kika sake haka ya faru har wani abu ya shiga tsakanin ku, baki daya mutuwa zamu yi hatta ke burin ki bai cika na ganin Mahaifiyar ki ba"*
"Zo nan ki kwanta"
Ya fada mata,
*Zai ta lallabaki domin kizo ki kwanta, tow abin da arshan yake mana shi zai miki, kin ga Arshan yan mata sun mutu babu iyaka a wurin shi dan haka kika sake ya saka miki dodon wandon shi mutuwa zaki yi ko Mama Uwa*
" A'a ni ka kyale ni!" Ta fada Jikinta yana rawa,.zuba mata ido yayi kafin ya ce mata.
"Shi kenan zoki kwanta" ya sauka a gadon ya dawo kasa ya kwanta, tsalleke shi tayi ya koma gadon ta zauna bata yi barci ba, har sai da gari ya kusan wayewa tana kallon shi ta tafi masalaci, kafin ta kwanta barci yayi gaba da ita." Koda ya dawo bai tashe ta ba,.yayi wanka ya tafi fada.
Yana zuwa ba zato ba tsammani, Tafida ya ce mishi.
"An baka Magajin garin Deehar, wata sati idan za a daura auren ka da Mulikah sai a yi bikin baka sarautar"
Murmushi abid yayi sannan ya ce musu.
"Allah ya taya shi riko! Allah yasa ba wata manufa a bashi muƙamin"
Daga haka ya yi shiru, haka Abid yayi ta niman magana da tsokanar mutanen fada, domin kawai a tanka mishi yayi tijara, har an tashi a fada zasu fita Chiroma ya ce mishi.
"Tunda har yau babu waziri me zai hana a bawa, Abid Jafar Abid. Sai a bashi Radiah tunda."
"Sarautar dama ta gidan mu ce, ba laifi amma batun Radiah a kai masukin, a bani Aaliyah ita nake so" shiru kowa yayi suna kallon shi wato Abid idanun shi a bude suke, ya mike yana faɗin.
"Nifa ita nake so, idan kuma Yarima Shehu bai bukatar zama suruki dani ba damuwa"
"Waye zai jarumin namiji irin ka, me dakawa yan maza gunba......
Karshen BOOK 2 zan tafi hutu Asabar da Lahadi ba zanyi update ba, sai Monday😍👎🏽
500₦... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0142529598 Ramlat abdulrahman manga Union bank
#Mai_Dambu
........ Abdullahi yana kallon yadda Yarima Shehu yake rawan jiki a jin Abid yana son Yar shi, wani abin da yake bashi mamaki yadda wasu lokutan Yarima Shehu yake nunawa bai da ciwo bayan akan fuskar shi yana iya nuna ainin asalin shi. Ya fadi cewa zai amshi Abid ne amma a cikin kwayar idanun shi bai ga wannan al'amarin ba, haka yana nufin yar shi itama makami ne a gare shi, ko wuta ake kurba mishi yasan dai yar shi ba zata tab'a auren shi ba, tunda abu daya ne ya samar da su. Tow kuwa Abid ya dace ya bawa Auren yar shi ba wani ba, amma bari ya ga iya gudun ruwan shi tunda dai gashi akan fuskar shi da jama'a ya amshi tayin Abid bari ya gani me zai faru gaba domin abin da mamaki.
***
Tun ranar da suka kwana yana can tana can, bata kuma ganin shi ba asalima daga ita sai Ladi da uwar bayi ta turo mata, sai take jin kadaici kamar ta rasa wani abu, yau da al'adar maranta ya fara ciwo, bata cika yin abin ba sai ta shafe wata kusan bakwai takwas kafin ya dawo, ko wancan ranar ita bata san zai zo ba. Kuma bata san shi ba ne. Amma yadda take jin har cikin ranta tana kewar shi. Fita tayi kanta babu mayafi sai tufke gashin da tayi baya, ta fito can filin gidan, ta baya tana shaƙar iskar yammacin ranar, hango shi tayi ya dauke katon kututture icce a kafad'ar shi, kugun shi daure yake da wani irin zani ya mata nadin kunzugu. Daga yalwataccen gashin kirjin shi take kallo har zuwa cinyoyin shi da suka yi murd'a murd'a, yadda gabanta ya shiga bugawa da sauri da sauri, shi ya haifa da fitar wani irin jini daga mararta wadda ya saka mata ciwon mara sosai. Zata iya kiran ganin shi da tayi haka shi ya haifar mata da wannan yanayin. Lumshe idanunta tayi tana cizon bakin ta, a hankali ta juya zaurenta, ta zube a kan shimfidar alfarma da aka zagaye ko ina na zauren da shi.
"Uwar ɗakina, wani abu ke damunki?"
Lumshe idanunta tayi tana k'amk'ame marar ta.
"Cikina yana ciwo"
Ta fada kamar zata yi kuka, bata kaunar a tab'a ta, shi yasa take kara k'amk'ame jikinta.
"Kar ki tab'a ni "
Ta fada da sauri, idan ta fara Uwar bayi bata yarda ta tab'a ta,.domin ji take kamar uwa ake dandana mata a fatar ta. A dan dame Ladi ta mike ta ficce ta nufi inda yake faman d'aga icce.
"Ranka shi dade, a gafarce ni. Uwar dakina bata da lafiya sosai"
"Hmm" ya fada yana cigaba da d'aga iccen, juyawa tayi ta koma ta tsaya a kan ta. Ganin yadda take juya kai yasa ta itama jin kamar ciwon a Jikinta yake. Ko yau da jiya ya lekata tana barci fa, shekaranjiya kuwa basu yi kwanan aminci ba, shi yasa ya nisance ta domin zuciyar shi zata iya jagorantar shi ga aikata wani abu na daban. Baya son ya je mata da bukatar shi sai sun shaku a turbar aure baya son ya mata abin da zata fara ganin kamar abin da yasa ya nime aurenta kenan. Ajiye iccen yayi ya nufi cikin gidan bayan ya saka rigar shi.
"Wash cikina, wash bayana wayyo kataryata. " Sautin muryanta ya mishi Barka da zuwa.
*Dama ya lafiyar giwa*
"Sannu" ya furta a hankali, lumshe idanunta tayi tana rike cikinta.
"Tun yaushe ta fara?"
"Yau ta fara da ciwon kai, amma zuwa yanzu ciwon ya ci karfin ta."
Kai hannun yayi zai tab'a ta, ta fashe mishi da kuka dole ya kyaleta yana kallon yadda jikinta yake rawa.
"Bata son a tab'ata."
"Kira min Uwar bayi"
"Tow"
Kuka take sosai tana juyar da kanta, rungume ta yayi ta shiga dukar kirjin shi da yakushe shi. Matseta yayi yana me tura hannun shi bayan rigarta, yadda yake shafa bayanta zuwa kugunta yasa ta komawa tayi luff a kirjin shi, hura mata iska yake a kunnenta yana shafa bayanta, a hankali kukan da rigimar ya ragu, sai shashekar kuka da take yi,a hankali hannun shi ya dawo gaban rigarta ya kamo na fulaninta, ture hannun shi tayi tana kokarin barin jikin shi, ya kuma rungumar ta.
"Assalamu alaikum!" Sallamar su Uwar bayi yasa ta kwace daga jikin shi.
"Amin wa'alaikumunsalam," ya amsa yana kallon yadda Kyautah take kuka sharshar.
"Ranka ya dade, meke damun ta?"
Iskar bakin shi ya fesar yana kallon Kyautah ya ce mata.
"Hm, ban sani ba"
Matsowa uwar bayi tayi zata tab'ata ta ce.
"Ni dai kar ki tab'a ni"
"Abin ne yazo kenan?" Kuka ta kuka saka mata, dan dole ta fita can sai ga magani ta hado mata,dama tana da ajiyar shi ta wanke. Ta kawo aka shiga dafa mata, tana kwance a wurin shi kuma yana tsaye yana kallon yadda take juyar da kai, can uwar bayi ta kawo maganin a kofi ta bata, Dakyar dakyar take hadiye maganin. Can aka kuma kai mata ruwan zafin ban daki, tana tashi ashe ta bata jikinta, yana ganin haka ya saka hannu ya dauke ta, ya kaita ban daki ya ajiye ta. Sannan ya fita ya zo ya samu Ladi zata tab'a shimfidar ya ce mata.
"Bari"
"Tow" a hankali ya ya kwashe kome na wurin ya kai dakin shi, da kan shi ya gyara kome, sannan ya shiga daki ta wanke kayan da tab'a, ita kuma tana wurin Uwar bayi tana wanke ta. Sai rufe kirji take,.bata damu da haka ba. Ita dai ta gyarata, sannan suka fito har ya shanya kayan. Dakin girki ya nufa ya shiga kallon abubuwan da yake cikin dakin. Fita yayi yasa aka kira mishi Abid.
"Ka yanko min kaji hudu"
"Tow, amma me zaka yi da su?"
"Ina ruwanka?"
"Tow" ya juya ya fita can kuwa sai gashi da manyan zakaru uku a yanke, ya shiga dasu gidan, dan wulakanci irin na Abdullahi cewa yayi.
"Gyara min ina jiran ka"
"Kasan dai ni ba bawanka bane?"
"A'a cewa nayi taimaka ka gyara min" dake ya fadi maganar da girmamawa take Abid ya fara aikin shi, sai ya kalli Abid ya kunshe dariya, wannan abin tun suna samari idan suka shiga daji kama fakara da zabi suke su gashe su adaji. Yana gamawa ya amshi kajin ya fara aiki kafin kace kwabo sun hade aikin su, domin Ya Haruna ya koya musu girki, sai magariba suka gama. Abid ya wuce gida yayi wanka. Yana cikin wankar yaji kamar mutum a bakin kofar shi. Karamar wukar shi ya dauka ya rike tare da jan mayani ya daure kugun shi, hasken wurin a ka kashe. Cikin zafin nama ya bude labulen ban dakin. Daga hasken da yake shigowa wurin ya fahimci mace ce.
"Wacece?"
"Aaliyah!" Mai da wukar yayi ya zuba mata ido.
"Me kika zo yi?"
"Naji ance an baka aure na ne, kuma baka tab'a zuwa ba."
"Shi