Showing 27001 words to 30000 words out of 105295 words

Chapter 10 - DASHEN ALLAH Book Complete By Mai Dambu from kanopost.ng.txt

20 Dec 2024

6124

da yad'a labarin da ba haka ba. Abin da ya kawo ka shi za a kayi idan har aka same ka da laifin haka toh hukuncin ka kisa ce. Sannan lallai dole kullum ana zuwa amsar abinci a wurin girki muje ku ga wurin"
Haka aka saka su a gaba suka tafi.
Sannan Kanden ta ce.
"Wajibi ne idan inda kika aiki suna nemi ki kwana kizo, ki sanar mana bayan gari ya waye kin gama aikin ki, toh ki dawo wurin nan, domin akwai gyare-gyaren filin masarautar Deehar da Harabar shi."


Suna isa wurin girkin shima zaure ne babba.
"Barka da zuwa, Uwar Bayi Kanden" jinjina kai tayi, sannan ta juya ga Yan matan.
"Nan ne wurin abincin ku, kowacce ta dauki kwanon ta kuma ban da hayaniya." Ta fada haka suka yi ta dauka. Kallon Easter tayi da take tsaye.
"Ke!"
"Baki ji bane?"
"Naji" ta fada dan haka tana isa wurin daukar kwanon, ta dauki nata ta koma gefe.
Kallon yadda doguwar rigar ya kwanta a jikin yarinyar, duk da yanzu ta fara girma, amma tana faɗin kafin nan da wasu shekaru kugunta yafi haka fadi da bunƙasa. Zata tsaya sai yarinyar ta isa matakin mace. Amma ba zata yarda ta barta a haka ba.
Hango Mama Uwa Abigail tayi, da sauri ta nufi inda take tana cewa.
"Mama na" itama Easther ta nufe su.
Dakatar da Easter tayi tana faɗin.
"Kar ki tako inda nake! Tsinanniya wacce ba zata yi albarka ba."
Kallon Easter matan dakin suka yi.
"Garin mu ya haramta mace ta bawa namiji kanta. Amma wannan tsinaniyar ta ja mana bala'i. Duk wanda ya rab'e ta sai ya fada masifa."
Takawa Uwar Bayi tayi iyaka wurin ta.
"Wace ce miki ita?"
"Yar mijina ce"
Mama Uwa ta fada da kwarin gwiwa.
"Toh ki adana kiyayyarki, domin ba zamu dauka ba....
🤣😭 Yau kamar wacce kuka min asiri nayi typing dayawa!
500N
Mai_Dambu
*......DASHEN ALLAH 🌳*


Mai_Dambu...


BABI NA SHA SHIDA (16)


Masarautar Deehar.


Yau kimanin shekaru ashirin da Takwas da rabuwa da duk wani me musu gani gani, don haka cikin nasara Galadima yana zaune wata hankaka ta shigo fadar. Tuni mayakan ko ta kwana suka fara kokarin farmakar shi, ya d'aga musu hannu.


Sauka ya yi a kafadar Galadima, ya juya yana kallon hankakan. Kafin ya mike a hankali ya nufi cikin gidan, babban zauren saukar baki na musamman ya shiga. Hankakan ya tashi a kafadar shi ya sauka a kasa, a take ya rikid'e zuwa wani tsoho me yalwan farin gashi da tarin shekaru masu yawan gaske. Rike yake da sandar karfe yana dogarawa.
"Duk da lokacin sa'a tana kara bunkasa nahiyar mu, shi yasa nake son na gaggauta gaya maka rundunar mayaka su nufi gaɓɓar takun Nahara. Sun karya alkadarin kauyen." Shafa kan shi yayi yana kallon Galadima.
"Kar ka manta ku kashe mazan kauyen da yaran su maza ku kamo matan zuwa Deehar ta haka zamu gane wacece me irin tasirin Nahara yadda zamu wanke ta mu bawa Arshan yayi kwana arba'in yana jima'i da ita, idan wa'adin ya cika zamu yankata sai mu mishi wanka da jininta yadda zamu mallaki karfin mulki da da farin jinin Nahara dan mace ce da ta shahara a duniya."


Zubewa ya yi a kan gwiwar shi, yana me cewa.
"Nasara tana gare ka, na amince yau zamu kai farmaki a garin Nahara"
"Kar ka manta ayi yadda nace domin bunkasa nahiyar Deehar."
Daga haka ya koma hankaka ya hau kafadar galadima suka fito.


Suna fitowa Fadar ya tashi sama yayi tafiyar shi, sannan Galadima ya gyara murya yana faɗin.
"Nan da dan wani lokaci, za a fara bikin mikawa Arshan mulkin shi. Dan haka yana da kyau kowa ya sani! Sarkin Yaki q shirya rundunoni da zasu tsallaka Nahara a farmake su farmakar da ba zasu manta ba. A kwaso mana mata da yan matan nahara kar wani badakare yayi gigin kallon wadannan matan domin mallakar masarautar deehar ce, matukar aka samu akasin haka toh kuwa ku shafe rundunar kafin ku iso deehar domin zan yi hukuncin da ban tab'a irin shi ba. A tsawon shekaru"
"Mun Amince!" Suka fada baki dayan su,
Mikewa ya yi ya nufi cikin gidan, a bakin harabar gidan ya hango Fulani Babba da Yarima Shehu.
Bai san me suke tattaunawa ba, amma yadda ya fuskanci Yarima Shehu yana fara'a cikin maganar shi yayin da Fulani Babba wacce shekaru ya mata shura.
"Yarima Shehu kenan! Kana tsammanin har akwai mulkin da ya fi namu adalci? Idan na fahimta hasashen ka yana tafiya ne da cewa akwai wani wanda zai iya tsaya mana a gaba?"
Murmushi ya yi mara sauti, duk da shima shekaru sun fara ja. Ya lumshe dara-daran idanun shi, masu matukar kyau da haske kamar ta Sarki Hayatudeen Abdullahi Noye. Ya bude su,
"Fulani ai ke uwa ce, sannan kin fahimci abin da nake nufi, abin da zai faru ke ce zaki fi kowa rashi. Kuskure anyi shi amma bana tsammanin daga haka akwai gyarar da zaku iya. Kar ku manta tunda kuka tab'a Abdullahi har yau kuna cikin firgici domin ku kanku baku san ta inda yakin zai fara ba. Shi can ya kawo miki labarin kauyen da idanunku yake kai" ya nuna inda Galadima yake tsaye, sannan ya juya yana tafiya da sandar shi.
Tun bayan kashe mutanen da aka yi, hatta Mahaifiyar shi sai da aka kashe, ta hanyar zuba mata guba.
Yan uwan shi kuwa raba kan su aka yi kowa yana jin haushin dan uwan shi.
Wai a haka shi daya ne kaf cikin masarautar yake gaya musu kuskuren shi.
Yanzu haka yayi aure yana da matar shi da Yaran shi biyu.
Aliyah da Khamil. Su kan yaran lafiyar su lau.
"Baka tunani akan Yaran ka ne?" Ta fada cikin kasaita.
"Kar ki damu da su, kiyi tunanin kanku Yarana kuwa ko farcen su ba zaku iya kusanta ba, balle har ku cutar dasu. Suna tare da da kariyar Allah."
Isowa Galadima yayi ya gaishe ta, yana kallon bayan Yarima Shehu.
"Me yasa ba zamu kashe wannan abin ba?"
"Waye ya gaya maka irin su Shehu ana kashe su sakarai! Ai idan dasu dole adawar tayi yadda ake so. Sannan idan suna raye dole suga cigaban mu!" Ta fada tana bin bayan shi da idanu,
"Fulani! dama akan kauyen da aka kai Abdullahi jinya ne, yau mun samu labarin sa'a zata fara daga yau. "
Kura mishi idanu tayi, sannan ta kalli Yarima Shehu da ya yi nisa.
"Yaron nan da yana gani toh tabbas da na ce a hallaka shi, sai dai ya gama nakasa babu abin da zai iya sai hakuri. Ya gaya min abin da yake tafe da kai "
Ta fada tana kallon shi.
"Me yasa kuke son farmakar Nahara?" Nan ya mata bayani cikin wayo da dabara.
"Na gamsu amma ka sani dole duk yan matan da za a kai su ga Yarima Arshan a duba budurcin kowacce mace domin kar a dauko mana bara gurbi cikin gidan mu"
"An gama ranki shi dade." Ya fada yana kaskantar da kan shi.
Sannan ta juya ta koma cikin gidan, ya bi bayan ta da harara.
Baki daya sun saka rayuwar shi cikin wani irin yanayi, bashi da ikon kan shi sai nasu, sai abin da suka fada ko suka ce. Ana ganin shi kamar shi ke juya kowa amma wallahi shi ma juya shi ake kamar gwado.
★‡★
Nahara.
Tun da ta fito daga cikin gidan su, take tafiya tana share kwalla. Tabbas Mama Uwa tayi gaskiya, amma kuma itama tana da nata burin. Haka zata mutu bata ga mahaifiyar ta ba? Haka zata kare bata ga nata cigaban ba. Haka ta nufi gidan Nahara tana kuka..
"Ki koma bake ake nima ba, domin babu yadda hasken Nahara ya bar ki, haka ki koma"
_Idan har aka fahimci bake bane ki sani shima cin zarafin alummar Nahara ne dan haka ki tsaya tsayin daka, ki tabbatar da Nahira kece_
Kalaman Mama Uwa ya dawo kanta.
"Nahira nice me laifi ba kowa ba, ni na aikata"
"Ki koma nace"
Ya daka mata tsawa.
"Ba zan iya ba! Nice Nahira nice nayi laifin ni ce na bashi alfaharin Nahara! Ni ce na bada kadaran nahara, Nahira ka hukunta sabida zunubina kafin masifar da ake hangowa zata auku ta auku"
"Ai masifa kan ta auku! Bamu da tsimmi bamu da dabara abun da bamu shirya ba, shi samu gani. Duk da nasan ba ke bace. Tawo muje" ya shiga da ita dakin bokancinsa, ya dauki wata irin sarka ya daura mata a wuyarta.
"Kar ki sake ki rabu da wannan sarkan. Kyauta rayuwar ki cike take da albarka. Zaki gana da Mahaifiyar ki amma lokacin da yana da tazara. Yanzu ki tashi na kai ki wurin me gari a miki tofin altsine sannan ki sani kece zaki dawo da al'ummar Nahara "


Sai da ya gama bata wata irin sirrintacciyar ruwa, sannan ya saka ta a gaba izuwa fadar tunba. A take aka kwabe ta. Hawaye ne ya zubo daga idanun Nahira."
Sai da aka zane ta tare da farfasa mata jiki, sannan aka ɗauki bakin shuni aka watsa mata. Sannan Nahira ya basu shawaran a dauke Yara maza da matasa maza a kai su tsibirin kakati.
Wannan tsibirin kakati wata irin sirrintacciyar wuri ne me ɗauke da kariya tun shekaru aru aru, ana dauke maza ne idan aka fahimci akwai tarzoman da zata hallaka su.
Ai kuwa matasa suka ce babu inda zasu tunda ta iya bayyana kanta, Toh suma zasu bada rayuwar su domin kare Nahara.
Dole aka kwashe Yara musu tasowa aka tafi da su da tsofaffin mata da maza.
Kallon Nahara tayi hawaye na zuba mata.
"Me haka yake nufi?"
"Makomar Nahara tana hannun ki kyautah ruwanki ne ki dawo da yancin Nahara ruwanki ne ki rushe ta har abada. Ban sani ba ko zan rayu amma alhakin kare Nahara na wuyarki, kiyi amfani da damar da kika samu domin dawo da kufayin mu."


Hawaye ne ya zubo musu, sannan aka shiga yawo da ita gida-gida ana fadar abin da ta aikata. Abin tausayi masu zaginta nayi masu jifarta nayi, kafin su dawo dare yayi, dan haka suna zuwa an hura wutar da zasu jefata, Babanta ya tawo da gudu aka riƙe shi.
"Kyautah ba zata tab'a aikata abin da ake zargin ta da shi ba, nasan tarbiyyar da na mata kar ku.."


Haske suka gani tare da fashewar wata irin abu, kafin kace me gidajen su ya fara ci da wuta gadan-gadan.
"Shi kenan! Ta janyo mana masifa da bala'i a cikin Nahara."


Hankulan jama'a ya tashi, kowa gudu yake ya domin ceton rayuwar shi, amma suna fara gudu, za ayi ta sake musu kibiya.
Matasan da suka shiga yakin, sune suka iya kare wasu mutanen, amma an gwabza yaki na fitar hankali, dake an ce sarkin yawa yafi sarkin karfi.
Kafin wayewar gari, sun yiwa garin Nahara barnan da bata a tab'a yi ba a tsawon tarihin kauyen, sannan suka tattaro mata da yan matan domin an hana a tab'a yan matan.
Haka aka bi gida gida, aka kwaso matan da suke gida a cikin su kuwa har da Wabi da Uwarta.
Idanun wani badakare ne ya sauka akan Easther wacce take zaune a takure tsirara, ta zubawa gawan Nahira da Baban ta, idanu hawaye na zuba daga idanunta.
Jini ya wanke mata jiki.
Gefenta gawar Saurayin nan ne da ya tab'a mata magana a dandali. An zo za a harbeta ya tare mata, sannan suka yi ta saran shi..
500₦
Mai_Dambu
.......MASHA RUWA.....
GARIN NUMAN.
Dake yankin Adamawa, na lardin gwangwola.
Garin ya kasance gari me cike da ni'imar Allah, garin da ya kunshe kabilu mabanbanta, garin Masuntan, Manoma, Makiyaya.
Gari ne da ya tara al'umma da dukiyar ban sha'awa.
AKWAI RUGAR JUME da RUGAR ARƊO
waƴannan biyun sune Rugage biyu mafiya dogon tarihi a cikin garin Numan. Don sun wanzu ne tun kafin ƙabilar BACHAMAWA su samu mulki a hannunsu. Ma'ana dai waƴannan rugage sun wanzu tun kafin hawan Hamma Bachama na farko kan karagar mulkimsa.
Bayan rikicin da akaita samu yasa tarihin Rugar Jume ya nemi shafewa daga bakin mutanan garin Numan amma kuma har yau RUGAR ARƊO DA RUGAR JUME suna nan.


RUGAR JUME.
----
Kasancewar lokacin hunturu, baki daya almajirai sun kewaye wutar da yake ci ne a wurin, sai dadd'ar Muryan su ke tashi cikin sautukan daban-daban na Alqur'ani. Kowani almajiri gaban shi dauke yake da allon shi.
Gefen Malam Buba, kyakyawar matashi ne, rike da Alqur'ani, ba a kira shi da matashi ba, domin shekarun shi sun kai talatin da bakwai zuwa da takwas.
Kyakyawar gaske ne, ma'abocin yar doguwar fuska.
Sai yar hancin shi siriri wacce ta tsaya akan fuskar shi.
Idanun shi dara-dara ne, masu ɗauke da zara-zaran gashin idanu.
Yana da karamar saje da ta haɗe gashin bakin shi.
Lumshe idanun shi yayi, yana kara shafa Alqur'anin, kallon shi Malam Buba yayi, cikin murmushi mara sauti ya rike hannun shi, a hankali yayi mishi alama da hannun shi.
Wato ya isa haka.
Murmushi yayi shima sai da gefen fuskar shi ya lobb'a.
Rufe Alqur'anin yayi, yana me janyo wata jakar fatar shi, ya lallube ta a hankali ya saka Alqur'anin, sannan ya dauki sandar shi da hannu ya ce mishi.
"Malam zan tafi"
Kamo hannun shi Malam Buba yayi, sannan ya ce mishi.
"Tow ka gaida gida"
Jinjina kai yayi alamar tow, sannan ya juya yaran da suke karatu suka fara bashi hanya.
A hankali yake amfani da sandar shi, har ya fita a da'irar su, sannan ya fara tafiya.
Tun daga nesa ta hango shi, amma kasancewar zuciyarta ta dasa mata kiyayyar shi, ji take kamar ta dauki wuka ta burma mishi sai ya mutu. Bata gama tunani ba, ta ga Uban annamimai ya dirko daga bishiyar durumin da yake gab da shi.
Yana zuwa ya rike sandar shi.
Murmusa mishi yayi, har suka isa inda take.
Dafa kafadar shi yayi.
Sai da ya juya, sannan ya tsaya tare da riko hannun shi, ya saka a fuskar shi.
Tare da mishi alamar cewa.
"Ka gamsu ni ne a tare da kai?"
Kura mishi ido yayi, sannan ya sake murmushin da har kullum baka iya gane ta meye yake nufi da ita.
Shafa fuskar shi yayi sannan ya ɗan dunkule hannun shi ya naushi gefen abokina shi.
Juyawa yayi yana faɗin.
"Allah ya baka lafiya, Abdullah."
"Mtsew."
Ta ja wani irin tsaki, sannan ta nufi hanyar gida, suna bin bayanta.
Shi bai ga wani abin burgewa a wurin wannan yarinyar me shegen rawan kan ba, amma baki daya Abdullah ya nace ita yake so.
Wai a haka ma dan bai ganta bane, amma shi kyan mace bai d'add'a shi da kasa ba.
Balle Raudah da sam kanta yaƙe hayaki.
Daga nesa ya hango Ya Musa da Ya Haruna.
SHEKARU ASHIRIN DA TAKWAS.
*BAK'AR LARABA*


Bak'ar laraba, ko a ce larabar zubda jinin al'umma noyewa,
"Ya Musa ka bamu Yaron nan, kayi tafiyar ka inda ya maka."
"Barde amana bata ce haka ba, ba zan iya baka Abdullahi ba."
dariya suka yi sannan suka ce mishi.
"Tow ga kan Uwar shi, zaka bamu shi ko sai mun kashe ku baki daya, shima waziri yanzu haka babu labarin shi. Matan ƙabilar Noye sun kasance a karkashin mu, sai yadda muka gadama zamu yi da su, ba iya haka ba muna shirin duk wata mace zamu mai da ita kamar dabobbin mu, mu shiga inda yayi mana."
"Lallai kun yi abin da kuke so, amma ba zama dole ku samu abin da kuke so ba. Har abada zaku cigaba da kasancewa a tsorace har bayyanar gaskiya" Ya Musa ya gaya musu, ganin yadda suke kokarin jifar Abdullahi da gatari yasa dole ya juya suka jife shi da Gatari a kafadar shi, fadawa a ruwan kwankwamai yayi.
Suna fadawa cikin ruwan suka nutse, guguwa ce ta tashi a cikin ruwan me ƙarfin gaske ta haɗa da su, tayi ta gudu a saman ruwan.
Har lokacin yana rungume da Abdullahi.
Watsar da su guguwar tayi a bakin Kogin Numan.
Kasancewar asuba ce babu wanda ya lura, sai da gari ya fara haske aka gansu kwance cikin jini musamman Ya Musa.
Ganin su da shigar Alfarman yasa aka kai su Masarautar Hamma Bachama na huɗu.
Kiran maganin Masarautar, suka fara musu aiki.
Sai dai duk abin da suka gwada akan Abdullahi bai yi aiki ba.
"Ranka ya dad'e! Wannan Yaron al'amarin shi da karfi yake, idan aka ce lallai za a duba shi. Zai bamu sansu wahala, sannan shigar jikin shi ta nuna mana daga wata Alkaryar yake me ɗauke da daraja dan ga tambarin ta. Shi kuma wannan jinyar shi me sauki ne, zan ji da kome."
"Tow a kai su, cikin gida."
Daukar su aka yi, zuwa cikin gidan bangaren bayi, duk da ba wata babba masarauta bace amma suna girmama mulkin su.
Kwanan su biyar, Ya Musa ya farka dake Abdullahi ya riga shi farkawa. Tun kwana biyu da suka wuce.
Kallon Abdullahi yayi, ya gan shi a takure gefe guda.
Shafa kanshi yayi sannan ya tashi duk da yana jin gajiya da ciwo.
Tashi yayi, ya nufi waje da tambaya ya nime wurin sallah. Sannan ya tafi masalaci yayi sallah,.yana idarwa suka dawo anan ya samu an ajiye musu abinci, zama yayi ya bawa Abdullahi, wanda kana kallon shi kaga maraya da yake cikin maraici sosai.
Shafa fuskar shi yayi yana jin hawaye ya zuba mishi, wani irin tausayi Yaron yake bashi.
Domin ko ba a gaya masa ba,.yana bukatar sanin inda Mahaifiyar shi take.
Rike hannun shi yayi, sannan ya ce mishi.
"Mahaifiyarka ta rasu!"
Lumshe manyan idanun shi yayi yana gyada kai, sun koya mishi magana da hannu.
Amma batun mutuwa sai da ya dauki hannun Abdullahi ya saka a wuyar shi ya ja, alamar ta mutu.
Riko hannun Ya Musu yayi yana me lakwasa su, ya ce mishi.
"Amma kashe ta suka yi?"
Shima ya bashi amsar da.
"Ih"
Hawayen da bai zata ba, ya gani daga idanun Abdullahi a hankali yake kuka har jikin shi yana rawa, kuka yake sosai na kewar Innar shi.
Haka Ya Musa, yayi ta aiki da bauta domin kula da Abdullahi.
A haka ya saka Abdullahi a makarantar allo. Lokacin yana da shekaru goma.
Ganin dawainiyar yana mishi yawa, yasa shi samun Hamma Bachama na huɗu.
Ya gaya mishi Abdullahi daga gidan da ya fito, sannan yana niman izini a bashi koda yar karamar fili ne, domin yana matukar jin kunyar yadda Abdullahi yaƙe rayuwa cikin bayi, don Allah idan da hali a nika mishi bautar da yaƙe.
Sannu Darajar mulki da kuma gidan da Abdullahi ya fito, yasa Hamma Bachama ya basu damar zama a rugar jume.
Sai da ya kwashe wata biyar yana musu bukka domin shi yafi yawa a zamanin. Sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login